Chapter 99 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   99 / 101

294K to 297K   out of 302.2K words

kara yazo nasan kudi ya basu don suyi mai haka din.

Yayan ku yace Yazid ya fada mai kudinsa yaci yaki fitowa dashi idan yaji matsi zai fito mashi da abinsa
so yake a bada hakkuri a manta zancen ya cinye kudin daga baya shiko bai yarda da hakan sai ya bashi
kudinsa koda zai sayar da gidansune.

Kaj amma yazid bai kyauta ba kawu zaisa a kulle ai yaci ragowa a wajensu ko don mahaifiyarsu dan
uwan haihuwantane fa ?

Baki san yazid ba ko yazid baida kunya haka ya tashi da rashin mutunci tun yana karami zuwa karatun
nan da Alh ya turashi waje shinema saukinsa yanzu .

Nashiga daki ina mamakin wanan rayuwam na mutanen gidan mu na yau daban na gobe daban kullum
a cikin rikici suke zancen kudin nasan dashi na dau boyewa mamane kamar ban sani ba ashe abin har
yakaisu ga haka.

Ni yanzu a kwanakin nan ba abinda nakeyi sai tuno da yan uwana da muka bari a rugga cikin wahala
musane ya taba zuwa maria ta haushi da fada lokacin don me yazo ace mun taru mun cika masu gida .

Haka tashi gaba muna kuka ta sallameshi washegari ya koma gida tun lokacin bai kara dawowa zaria ba
banjin koda mama tayi aure kaduna sunzo kin san mu fulani da rikon tsiya a zuciyar mu.

Saida naba matan hardo sako da sukazo sunan Amir akai masu tare da wasika a ciki nace su kirani har
zuwa lokacin banji kiransu ba ni duk yadda yaya jafar yake da yan uwansa ina son yadda suke rayuwansu
a waje daya din nan amma mu tamu kaddarance mu taso ba tare da yan uwan mu ba.

Dan uwa fa rufin asirine yau da dayansu zaizo ba zan taba korashi ba zan rike abinane duk abinda
mama zatace saidai tayi matukar ba mai gidanne ya koreshi ba.

Amma ita tsoro da zurfin ciki yasa tayi masu abinda ba zasu taba mantawa da ita ba a lokacin saida
mukai karamin gaba da ita na gaji na sake zancen yanzu ko ina son ganin su sosai a raina.

Ina dadin muna cikin daula su suna cikin wahala ba tare da mun taimakawa rayuwansu ba sun fito fili
tunda tare mahaifin mu ya barmu dasu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/12, 10:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



9️⃣9️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Dare daya Allah ke nashi ikon idan ya tashi ba wani mahalukin daya isa ya hana wanan faruwa a duniya
saishi daya bayar ya isa ya karbe abinsa duk lokacin dayaga daman hakan ga bawa kamar yadda ya bayar
din.

Wanan tafiyan da yaya yayi sati biyu kacal ta daukeshi ya dawo a cikin tarin dukiya mai dinbin yawa tare
da abin arziki ga yan uwa da masoya don tafiyace data zamo wace ba za a manta a cikin tarihi ba.

Wani lokaci Allah kan jerabi bawansa ya dora mai jerabawa a rayuwansa wace zata zamo mai alheri a
gaba matukar bawan nan ya iya juriya ga hakan ya samu ikon cun jerabawansa da hannu biyu a karshe
sai Allah ya juya hakan ya zama mai alheri a rayuwansa.

Don kuwa zance da ciwon yaya da shiga fatarsa da ganin wasu halaiyan da bai zata ba ga yan uwa duk
hakan jerabawane daga ubangijinsa Allah.

Don sanadiyan wanan ciwon da yaya J ya kwanta abubuwa da dama Allah ya jerabeshi dashi yaga
duniya sanadin hakan dukiya ya salwanta lafiya ta kubce masa yan uwa sun gujeshi don baida iyali sun
nuna nasu halin a gareshi abokai ba kowa ke saurarenshi ba duk da halarcinsa garesu a baya.
Sai gashi Allah ya dawo mai da dukiyansa inda ubangiji yayi ikonsa kayan sun ninka kudinsu sama da
lissafin mai lissafi abin baiko faduwa.

Wani saurayin Maibe dake can ya adana kayan a wajensa kamar yadda ta bukata yayi daga baya da
suka samu labarin jin saukinsa aka baiyana mashi inda kayan suke yabi kuma suka shiga a cikin lokaci aka
samu alherin daba,a taba tsamanin hakan ba gareshi.

Ruwa aketa shega muna a garin hakan yasa bamu tsaya wani dogon hira ba duk da ba matsalan mu da
ruwan muna cikin rufin asirin Allah mu bamu ganinsa balle ya tabemu.

Amma yanayi yasa mun kwanta da wuri a ranan nagama shirya Amir nima na kimtsa kaina zan kwanta
naga wayana yana haske na dauka.

Yaya nagani yana kirana lokacin na dauka yaron kuma yana min kukan nono na fara daukan wayan
nakara a kunnena kafin nakai hannu na dauki yaron ina mashi sallama naji yana fadin kun rufe gidane
nace ehh yaya ki bude min gani nan zuwa ya fada.

Na amsa da to cikin mamakin yadda ya iya tafiya a cikin wanan ruwa ga dare haka duk da shadaya ake
nema a lokacin amma gari yayi tsit a lokacin.

Na saba yaron a kafada na fita zuwa falo na bude kofan a daidai lokacin maigadin mu ya bude get din
gidan motoci ukku suka shigo a jere lokaci guda haraban gidan.

Dawowa nayi na zauna don Amir daketa tsala min ihu hakan kuma ba halisa bane shi yarone mai
hakkuri yana da wuya kiji kukansa sai can ba a rasa ba amma akwai zuciya gareshi mama kance ya gado
na fulanin a gareni watau zuciya.

Haka ya shigo ya sameni zaune na fara ba yaron nono yana tambaya ina key din dakunan boys quaters
suke na mike na dauko mashi ya fita na zauna nacigaba dabawa Amir nono a falon.

Ya dan jima ina falon zaune ina tunane a cikin raina Aminu ya dinga shigo da wasu manyan jakkuna
shida mai gadin gidan kusan biyar kafin shiya shigo daga baya don ruwan ya dan tsagaita a lokacin.

Tun kafin yakai zaune yake tambayana mama fa tayi barcine nace ta kwanta tun dazun nima wanan ya
hani barci yau da sauri yake tambayan meya sameshi kuma ?

Nace dashi yau dai kuka yakeyi tun yamma mama tace kila cikinsa ke ciwo anbashi balma kuma bai bari
ba.

Ya mika hannu ya karbi yaron nace abinci fa yace bar zancen abincin nan yanzu bamu da yunwa
hankalinshi na kan yaron yana dan dube dube a jikinsa yake ban amsa.

Yakai zaune yana fadin ko zamu kaishi asibitine a dubashi da sauri nace da daren nan a dai bari da safe
mugani yanzu ko mun fita a cikin ruwan nan wa zamu samu a can ?
Baki da tausayi don ciwon ba a jikinki yake ba zakice har saida safe idan bai bar kukan nan ba dole
mukaishi asibiti nayi sa,a yarin yabar kukan shima ya mike zuwa dakinshi yana gyara kayan da suka shigo
dashi din ciki.

Yaron na goye a bayana na shiga na sameshi ina fadin yaya bafa gidan nan zaka zo ba naga kazo muna
a cikin daren nan baiyi magana ba saida ya gama dora kayan ya juyo yace Allah ko ?

Ina ya kamata in tafi nayi shiru tunda nasan tambaya dai kawai yakeyi saida yakai zaune nace saura
kwana ashirin da biyu muyi arba,infa yanzu.

Sai akace kada inzo sai kinyi arba,in ko banda wanan koda kikaga ban zama saboda mamace kuma aiki
akai maki kina son hutu yasa nabarki ki huta don nasan innazo zaki wahal da kanki da aiyuka yasa na
daure har wanan lokacin.

Kamar ince yanzu ko kagaji da hakkuri da zamanta ka dawo ko karanta zakayi daga gidan iya dai tunda
mukaje suna bata dawo ba tayi zamanta gida tace na samu sauki ai saidai.

Banyi magana ba na shiga bandaki na hada mashi ruwan wanka amma saida na koma daki na dauko
ruwa a cikin flask don ba ruwan zafi gashi ana sanyi a ranan balle ya watsa ruwan sanyi.

Ya shiga wanka na koma dakina muka kwanta da Amir ban falka ba sai Asuba na tashi nayi sallah
kitchen naje na hada muna ruwan zafi don yin wanka har lokacin ba wuta a garin gashi engine din gidan
ya baci ba a gyara ba har lokacin duk da ban jona mashi kayan nauyi dama.

Na juye ruwan na fara hada breakfast don bakin dayazo dasu mama najin motsina ta fito daga daki
tana fada nace aina sa biba ta kwashe min ruwan takai min.

Lafiyayyen breakfast na hada nayi wanka na gyara kaina lokacin mama ta fito tayiwa Amir wanka ta
kimtsashi ta miko min shi in bashi nono Biba ta shigo tana fadin Anty naga wasu motoci a wajen gidan
nan fa ?

Da maisu a gidan ai motocin me kuma kinkan fara maganan ki ke nan mara ma,ana nace ta ganine
mama yaya ya dawo jiya da dare kuna barci.

Cikin mamaki mamake fadin lalai munyi barci jiya ban kayi dogon zance mai tsawo da ita saidai ita ta
dinga min hira ina murmushi ba ita kadai ba kusan hakan dabi,atace rashin dogon magana mai tsayi da
kowa hakan nake.

Shine ya fito yana muna sallama mama ke fadin yanzun nan take fada muna ka dawo jiya da dare ina
tunda iska ya taso aka fara hada hadari muka shige daki ai suka gaisa dashi tayi mai yaya hanya ?

Bayan sun gama gaisawa ya juyo yana fadin mutanen nan zasu kama hanya yanzu gashi na makara ba
ayi masu abin karyawa ba kuma ?

Nayi na fada a sanyayye kinyi fa eeh na soya dankali da kwai sai dan ferfesun dana hada da sauran
kayan cikin daya rage muna a fredge amma kin kyauta wai da nafitone in kaisu su karya su kama hanya.
Biba ta fito da kayan zuwa wajensu ya jima a can din kafin ya dawo bayan ya saukesu inda zasu shiga
mota na na hada mai ruwa yayi wanka sanan ya fito karyawa .

Bayan ya zauna yake tambayan mama nake fada mai tana daki yace nayi mashi magana da ita nashiga
na kira mama din tazo.

Mama din tafito tana fadin ka dawo ashe bakin sun tafi ko yace sun tafi mama daga can nazo dasu sun
jawo min motocine zuwa nan yan kamfanine aikinsu ke nan idan ka sayi mota a wajensu zasu jama sukai
maka duk inda kake so.

Tana mamaki tace su kuma ta haka sukeci da iyalinsu Allah ka rufawa bayin ka asiri ya amsa da amin
tafiya ai tayi kyau sosai mama addu,anku yana aiki sosai a garemu kullum sai kara ganin haske a rayuwa
mukeyi mama .

Addu,an mu da alherin ka ga mutane malam da zamu samu irinka biyu zuwa ukku a cikin mu da yanzu
an gama saninku a ko ina fadin kasan nan hannu daya akace baya daukan jinka.

Anyi ma yawa akai malam dole jiki yayi tsami ko a hakan mama Alhamdullahi don tafiya anyita a sa,a
sosai wana karo ban taba tafiya mai sa,a kamar wanan ba a rayuwana ba.

Mama ta gyara zama tana fadin Alhamdullahi haka muke son ji ko yaushe gareku muji kuna samu
karuwa tako ina shine addu,an mu gareku ai.

In sha Allahu mama bana ina son ku taka arfa gaba dayan ku da yardan Allah cikin mamaki tace gaba
dayan mufa kace yace insha Allahu hakan nake fata mama.

Allah yace malam Allah yace daga gefe na amsa da amin a cikin murna tace dadina dake yar nan
hankali yau da watace ya fadi hakan saita nuna bakin ciki a fili wasu matan basu da lissafi a rayuwa ko
kadan wallahi ni dai nayi murmushi ina fadin mama aikoni keda hali haka zan iya kaiku insha Allahu.

Haka shike yata nasam zaki iya hakan idan Allah ya hore aka kwashe da dariya suna ta hiransu yana
karyawa har ta dauko mai zancen yadda saiba taje tayi hauka da kuma zancen zuwan saratu gida.

Nan ya tsayar da cin abincin yake fadin me kuma saratu tazoyi gida yanzu ko haka akeyi kazo gida daga
kaika gidan miji wai ?

Towa zai sani malam uwarta ta boye zancen ga yan uwanku nasan kai ake jira ka dawo yanzu daka
dawo ai dole a nemesu ai yaja tsuki da alama abincin ya fita mai rai yace Allah mama naje gida banji
wani abu mai karfi ba yau din nan tana konawa dakin mijinta.

Basu san ka dawo ba ke nan tace shigowa na gari na yo nan gidan don bakin nan dana zo dasu nasan
idan na kaisu can karsheta inji kunya don haka nayo dasu nan gidan ai.

Bai wani jima ba dai yabar gidan muka zauna hira da mama tana kara ban tarihin rayuwansu lokacin
mijinsu yana raye kafin ya rasu.
Gidan Asmau ya fara biyawa a lokacin ya samu suna karyawa ta dan fara kame kame tana fasin ta zubo
mashine tace wani ai tun jiya na dawo garin ina gidan Rahama can na sauka.

Tayiwa bakina abin kari sun karya har sun kama hanya sunce sun wuce kaduna tun dazun nasan kona
kasu nan takaici kawai zaki barni dashi ace yara kananu sai wajajen sha dayan rana suke karyawa kina
kwance kina barci don baki damu dasu ba ?

Yaya ban damu dasu bafa kace ko nayi abin karyawa tun dazun karshenta baci zasuyi ba cikin tsawa ya
hauta da fada yana fadin nasan maganin ki yaya Auwal zan fadawa shi zai dauki mataki a kanki.

Da sauri tace yanzu dai ai na dinga tashi da safe ina hada masu bashike nan ba ka kaini kara wajen yaya
Auwal kasa yazo har gida taci min mutunci ga banza.

Fita yayi ya kama hanyar gidansu mama da ita ya fara cin karo zata unguwa ganinshi yasa ta dakata
tana tambayan yaushe ya dawo yace jiya da dare.

Tare suka shiga wajen iya suka gaisa da ita Salima ta fito suka gaisa har tabada baya zata koma daki
tayi brush ya dakatar da ita yana fadin yaron nan kabir yana gari ko yayi tafiya ?

Yana nan yaya kice yazo karfe hudu ina nemanshi yakira layina yaji inda nake lokacin ta amsa da to
yaya tashige don kimtsawa ya dubi iya yace zaman salima da Nafisa a gida yana damuna iya ?

Ina son ayi aurensu a huta aji da wa yanda ke tasowa yanzu kuma ita Nafisan tana da mijine yarinyar
da uwarta ta koya mata kitihi iri iri wa zai aureta ?

Haba dubu kikan fara maganan ki ke nan nafisa dince da kitihi har kala kala haka ita wace ba a koyawa
ba tayi auren ne ina mamaki gaka da abin zagi a gindinka kaje zagin nawani ?

Irin abubuwan nan tambayan bawa sukeyi a rayuwa ke da girmanki meye na fadan hakan akan dan
wani don Allah kinsan nufin yaron nan akan auren nan akan yaran nan daya fada ?

To iya nidai bada wata manufa ba fada ba din Allah dukkansu aure zasuyi kwanan nan ita saratu bagata
can gidan mijinta ba yanzu an huta da ita.

Wace saratu saratu saratu kan na dakin uwarta yanzu ka ganta tashigo gidan nan tace zata gidan
kawarta a kwashe mata kai.

Saratu fa iya garin yaya ta dawo gida kuma iyan tace ka tambayi uwarta ita tasab dalili nayi magana
tunda mijinta ya bugo ta koma ance ina nafito.

Ya kuma turo abokinshi uwarta tace bata komawa sai yazo ya juya wajen mama din yana fadin mama
yaya akai haka kuma ban sani ba ?

Ta yaya zaka sani tunda baka nan yau kwananta goma sha daya da zuwa miji ya dauketa ya kaita kauye
ya aje cikin matanshi ina saratu zata iya aikin yawa da sukeyi ?
Mama ba aure taje yi ba su wa yanda ta sama ba haka suke zaune dashi ba tunda suna son mijinsu ta
tareshi da fadin sai ta zauna wahala ya kasheta ke nan ko ?

Mama dakata don Allah kin taba jin inda wuya ya kashe mutum don Allah ita mace fa da hakkuri
akasanta ita dabance a cikinsu daba zata iya hakkuri da mijinta ba ta zauna yadda kowa ya zauna yana
hakkuri ko tafi sauran matan nashune da suka zauna su ?

Ina an fada mata tace tana iyawa karya ake mashi saida na zauna daku kafin duk su yaya su saka baki
cikin maganan tana iyawa tace min tana son shi san nan yanzu zata dawowa mutane gida don tana yar
iska uba me tadawo yanzu ayi mata to nan ?

Kana magana kamar baka fahinci mutane ba ina saratu zata iya girkin mutum kusan dari don Allah ?

Amma mama ita tace tana sonshi ai yau din nan zata koma ai tasan yana da iyayye yana da mata da
yara tace ta amince ta aureshi mu zata dawo ta rainawa wayau yanzu ?

Irin rainin wayau da na guda ke nan gun Asmau don nasan sakarauce ta mayar da kanta sha,shasha
saboda son jiki nazo da baki dole gidan Rahama naje na sauka jiyan.

Ina zakazo da boka a barshi da yunwa yanzu dana biya gidan sai yanzu na samu wai tayiwa yara abin
kari zasu karya yaro za a bari da yunw har wanan lokacin saboda sha,shancin banza da suka dorawa
kansu.

Dama nasan za a rina wanan daban tsiyan da suke taruwa sunayi a wuni ba mai iya yiwa kansa abin
kwarai yanzu gashi duk ta dauka in anyi magana mama kice an matsa mata ba a kaunarta ina tsiya ina
girki ga mace girkifa za ace ya koro mace gidan miji idan ba tsiya da samun waje ba.

Naki bai hadaki da mijinki ba sai zancen girki din Allah mama ta amsa da fadin ai shima ya shafi mijin
tunda yasan inda ya dauketa da zai kaita kauye yace sai tayi kalan aiyukansu.

A ina ya dauketa gidan attajirai ko gidan sarakuna naga dai har gobe gidanku suna aiyukan hannu na
hausawa iya ta fada yanzu inane yar nan Nafisan da kike zagi ba zata iya shiga ba ?.

To taje kauyen ita amma saratu bata komawa kauyen nan sai dai asan abin yi gaskiya kauye kan ta fito
ke nan cikinsa in sha Allahu.

To shike nan mama tunda haka kikace saidai ku sani duk

99 / 101