Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
gida Nusaiba ke ta kuka tana waya
da yan uwanta tana fadin cewa an kita ana son hada mata kai yan uwan jafar sun tsaneta suna kinta.
Da korafin yayi yawa uwar tace taba Asmau waya zasuyi magana shine Asmaun ke fada masu abinda ya
faru uwar tayi masu fada dukkansu kamar yadda ta saba tace ai dole zasuce hakan tunda kuna nuna
kamar baku damu da halinda yake ciki ba a yanzu.
Ta yaya zaku tsaya karamar yarinyar har tazo ta fiku iya fallako ta karbe maku miji kuna gani ai ba sunce
bane inda suke ganin kauna suke jin taushi tunda rayuwansa ake nema a yanzu koma meye ku bari gobe
zamu shigo ai.
Da haka suka samu ta hakkura don cewa tayi da zata dawo gida tunda an nuna mata kiyayya a nuna
bata da amfani ga jafar din.
Ranan sunyi shirin da suka jima basuyi ba a tsakanin su don sunyi zama na shawaran kan abinda zai
fitar dasu daga kallon tuhuman da yan uwa suke masu din.
Su mama basu dawo Zaria ba sai karfe biyu saura na dare ina zaune a dakin da hasken wayata ina
karatu mama tana kwance a gefena suka shigo don basu nufi gida ba asibitin suka nufo kai tsaye .
Jin an turo kofa yasa na dago kai ina duban kofan dakin sune dasu yaya suke shigowa hakan yasa na
dan taba mama da barcin ba nisa yayi ba a lokacin ta tashi muna masu sannu da zuwa.
Suka amsa da tambayan ya mai jikin aka basu amsa da saukin tun dai dazun din barci yakeyi a hakan
yadda yake bai kara wani abuba kuma har wanan lokacin.
Iya ta karaso tana fadin Allah ya baka lafiya jafaru ubangiji ya tada kafadan ka a cikin mu suna amsawa
da amin kafin ta juya gun mu tana fadin Salamatu ashe kina nan mama ta amsa da ehh iya zuwa gidan ai
baida amfani gara na tsaya a nan din tare dasu.
Rahamatu kina zaune baki barci ba ke nan ta juyo kaina tana fadan hakan cikin nuna kulawa nan
mama ta karba da fadin .
Ina ai yar nan akwai kokari ko dazun din daya rikece itace tayi namijin kokari akansa kafin likitocin su iso
tayi dubaran datse hakoran nasa da cokali daya taune harshen nasa ai duka don ba mai dabaran hakan
acikin mu kowa ya rude.
Nan tashiga rabtabo masu labarin yadda abin ya faru zaune habu yakai a gefen dan uwan nasa ya zuba
mashi idanu yana kare masa kallo a cikin tausayi.
Can ya juyo yace ko dan kokon daya dan karba yanzu ya daina sha ke nan ko mama tace ina ai tunda
sukai mai alluran nan ya samu barci hakan nan daka ganshi yake tun dazun din.
Saida kyat suka samu suka bar asibitin don mama data matsa masu suje gida su huta tunda muna nan
asibitin mu hakan yasa suka tafi.
Har iya dake son hutu a lokaci tabisu zuwa gidan yaya habu duk a nan suka kwana ranan sai kawu da
suka sauke gidanshi har lokacin ya kasa furta komai a garesu.
Tun da asuba na jona ruwa na gyarawa yaya jikinsa da taimakon mama na samu na tsabtace masa
jikinsa muka saka mashi wasu kananan kaya sai ya fito dan few dashi don rama da yanayin jikinsa yayi.
Nabi dakin na gyara na fesa kamshi da yaya Auwal ya sayo ayi amfani dashi na gyaro har ban dakin
koda suka dawo daga sallah sun samu har nagama komai a lokacin.
Lokacin kuma yaya habu yayi sammakon zuwa asibitin shima don duba dan uwan nasa daya kwana
dashi a rai.
Ásmau ce data kira layina tana tambayan ya mai jikin nake fada mata idan zasuzo suzo da koko don
Allah ban jira me zatace ba na kashe wayan.
Sai wajajen takwas suka shigo asibitin da yaransu mun gaisa lafiya suna muna ya mai jiki mama ta amsa
da sauki nan rake fadin .
Tunda kunzo sai ku kamawa yar uwarku taje ta huta ke Asmau saiki zauna dashi zuwa karfe biyu sai ita
nusaiba ta karbe ki zuwa yamma don ita yar nan ta huta don batayi barci ba a jiyan.
In yaso zuwa dare saita karbe ki atakaice dai mama ta raba muna wanan taggadaman a tsakanin mu ke
nan kuma hakan ya zaunu saidai ina jin hakan na fara haraman zuwa gida don ina son dama gyara jikina
robona da wanka tun da zan fito gida zuwa wajensu a jiyan .
Ina saka hijjab nake jin suna zancen bashi kokon dasu da mama dubu na gama kimtsawa na dauko
jakata ina fadin zan tafi sai anjima bisa ga umurnin mama duk suka juyo suna kallona zaki gidane naji
mama dubu ta fada .
Ehb zanje na dan watsa ruwane mama na bata amsa take fadin ibrahim yana kusane ya kaiki zan fita ko
zan samu wanda zai saukeni na bata amsa sai naji tace min to indai babu kowa saiki dawo habu ya
saukeki ko ?
Nayi masu sai anjima na fita daga dakin cikin sanyin jiki cike da mamakin sanyi mama a kaina lokacin
ina fita na hadu dasu anty Barakha da yan uwanta nan muka tsaya muka gaisa suna tambayan jikin dan
uwan nasu.
Muryan Asmau naji tana kirana hakan yasa muka isa tare dasu take fadin mama ke magana dani
nashiga take fadin kada ki tafi ai ki tsaya abashi kunun nan don kece kikafi sanin yadda yake kamawa
idan anbashi.
Hakan yasa dole na kwabe hijjab dina na muka soma kamashi don mu dagoshi dole saida na dan hau
gadon na rungumeshi duk sun zuba min ido na soma da kiran sunanshi a hankali ina mashi sannu.
A lokacin su yaya habu suka karaso dakin suma sai yayi kamar ya bude idonsa ya kalleni nace ka daure
ka dansha koko koda kadan ne don Allah yaya ?
Wani irin ajiyan zuciya ya sauke lokaci guda duk hankalin kowa ya dawo kanshi da sauri ya habu ya
karaso yana tambaya hankali tashe da yaya dai ?
Murya a kare nake fadin ajiyan zuciya ya sauke na kallo Asmau da jikinta ke rawa nake fadin ta bani
kunun ta miko min na kara fadin ka karba yaya don Allah kashe kada ka zauna da yunwa haka tunda bai
shiga ta roban da ake baka din.
Bskin nasa naga yana bukatan a kara wankewa hakan yasa na nuna mata ruwa ta miko min na diba a
hannu ina dan wanke bakin nasa .
Ya kara sauke ajiyan zuciya a hankali nake fadin ya taune halshesa ashe jiya har yaji ciwo a bakin muka
gama na bashi kunun ya karba sosai kamar cibi biyar aka samu yasha ya habu yace in barshi hakana zan
saukeshi a jikina yayi alaman a,a .
Ita Asmau ke fadin kamar ya girgiza kai fa nace hakane ya habune yace ki zauna dashi haka yake nufi.
Nan anty barakha ke fadin Allah sarki yasan itace ta rikeshi ke nan ya habu yace ya sani sosai idan tayi
mai magana ai yana nuna ya ganeta.
Ikon Allah ai dole inda zuciyarsa take ke nan dole ya shedata ai mama dubu ke fada hakan ta matso
tana fadin sannu jafar ya jikin kai ya kara dagawa a cijin karfin hali.
Suka shiga gaidashi daya baya duk daba amsawa yakeyi ba sun dai gaidashi din ne kawai irin na al,ada
da akeyiwa mara lafiya.
Yaron Asmaune aka shigo dashi yana rikici suyi lalshi yaki shiru mama ke fadin ta fita waje dashi.
Hakan yasa na karbeshi daga inda nake zaune daidai fuskan uban na nuna mashi shi ina fadin ga baba
yana gaida kai yaya sai kawai ya bude idanunsan tarr akan yaron .
Da karfi saare ke fadin wallahi yaya ya bude idonsa hakan yasa duk suka matso garesa a cikin farin ciki
sai kuma ya mayar da idonsa ya lumshe a hankali.
A hankali ya habu ya leko yana fadin J ya jikin sai ya kara bude idon ya sauke ga dan uwan nasa ya sake
sake lumshesu ya bude ya kafawa Habu din ido na wani dan lokaci.
Likitocine suka shigo dakin suka sameshi a hakan sunji dadi sosai a yadda suka sameshi hakan yasa aka
rage a dakin harni a lokacin na samu na fice na nufi gida.
Ban dawo asibitin ba har yamma don saida nayi barci bayan nayi wanka na kwanta na samu barci sosai
sam na manta da zancena da dan uwana Dage saida kira ya shigo min a wayata yana fada min gashi ya
shigo zaria hakan yasa na tashi da sauri ina salati.
Kwatace yayi min inda yake maigadi na tura yazo dashi tsamo tsamo don da ganinsa a tsorace yake
saida ya hangoni tsaye kofan gidan mu ina dakon dawowansu hankalinsa ya kwanta.
Nan falona muka zube na bashi abinci yaci yayi wanka saida akai sallah muka samu kebewa dashi ya
soma yi min bayanin abinda yazo dashi din .
Haka kuma ya sanar dani cewa sammako zaiyi ya koma washe gari don gida ba a san nan ya nufo ba
yazo min da abubuwa masu amfani sosai.
Nayi godiya nayi mai alheri iya abinda zan iya wanda yake ganin kamar na tsomashi a aljanna ne tare
mukaje asibitin dashi da yaya habu dana kira nayi mai bayanin komai .
A saibitin ma ya habu bai boye ba don yace hardon mune ya toroshi ya kawo muna maganin da za ayi
amfani dashi ya fadawa yan uwansa haka tare suka koma zai kwana a wajensu dasafe ya sakashi motar
farko ya koma gida suma sun mashi alheri ya tafi.
Kuyi hakkuri din Allah ba yawa anty Samira gashi da fatan kinyi hakkuri da kanwarki hakana yanayin
jikine ya kawo hakan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[4/10, 11:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to
join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA bWANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Duk saurina ban manta da zancen maganin dana hada na ruwan dokin da Dange yayi min bayani ba a
kwanaki bamu samu amfani dashi ba yayi wanan tafiyan daya dawo a cikin rashin lafiya.
Rashin lafiyan daya zamowa kowa a cikin family na tashin hankali don ga mutum kwance sharkaf baida
wani moriya ba umm,uuumm asalima baisan a hanlin da yake ciki ba na tsawon kwanaki.
Za a iyacewa dai kamar ya shiga common ne ko kuma jinnu sun shafeshi kamar yadda hausawa kefada
in mutum yashiga irin wanan halin da ba asan kansa ba.
A iya binciken asibiti sunce su basuga wani abinda ke damunsa ba saidai suna hasashen ko
kwakwalwansane ya tabu ko kuma ya bugu a kai hakan ya sameshi.
Bayan hakan su basuga komai a tare dashi ba bayanin da sukaiwasu yaya Habu ke nan a karshe irin
hakan wai amma zasu ajeshi acigaba da bincke ko za a gano inda matsalan yake.
Jin hakan yasa hankula ya kara tashi sosai ga yan uwa kowa ya saduda a yanzu don irin hakan yana da
wuya ace mutum ya mike sai yawancin rai da rabon mikewa din.
Kowa kika gani fuska ba annuri don labari ya karade kowa ga abinda likitoci sukace game dashi din sai
koke koke ke tashi tsakaninsu.
A cikin irin hakan ne na karaso asibitin tunda na tunkaro naga yanayin fuskokinsu sai jikina yayi sanyi
na rasa wanda zan tambaya meya faru dakin na nufa da sauri a zatona ko ya cikane na gansu a hakan .
A yadda na barshi haka nayi arba dashi kwance shambal saman gadon ba motsi na gaidasu a tsatsaye
na karasa bakin gadon ina kallon numfashinsa dake sauka wani iri.
Muryan mama tudun wadace naji a gefena tana fadin yana nan ai a raye saidai lamarin nasame keta
kata muni kamar dai wanan ciwon bana asibiti bane.
Bana asibiti bane mama na fada ina juyawa wajenta rabin da take na sake gaida ita da wuni nakai
tsugune cikin girmamawa muka gaisa na aje jakata a gefe daya inda nata yake .
Ta cigaba da fadin ni lamarin nan yana ban tsoro dazun don yadda gaba daya yanayin jinyar tasa ya
canza a yanzu yana sauyi da kamar iska ko hannu a lamarin.
Binshi nayi da kallo a yanayin da yaken tacigaba da fadin ni a ganina kawai abar asibitin nan a koma
gida dashi zaifi idan an koma sai a surka ayina gatgajiya dana asibitin.
Abu daine da baka da iko a kansa da ina da ikon da zan fada aji dana bayar da shawara a kwasheshi
zuwa gida ayi na gargaji yafi zaman asibitin nan da akeyi a cikin duhun kai.
Ni tunda naga sun kwashi jiki sunyi tafiyan nan shekaran jiya nasan akwai inda suka tafi game da
lamarin jikin nan nasa amma kin san ba fada muna kome ke akwai cokon lamarin zasuyi ba nidai abinda
nagani kawai su kwasheshi a koma gida aje ayi na gargajiya zaifi wanan zaman da akeyi nan.
Mikewa nayi daga inda nake tsugunne a kusa da mama din zuwa bakin gadon ina kare mashi kallo
zakice ba Jafar din nan bane da kikeson karawa kallo duk ya fita hayacinshi.
Ga kamsuba da suka fito mai a fuska yayi wani baki sai dogon hancinsa kawai zaki hango zaram
bandashi ba wani abu daya rage a cikin jikinshi.
Abin dai dana saba nayi mai addua donshi duk wani mosoyinsa zai mai a lokacin donshi yafi bukata
garemu.
Yayin da zuciyana yake wani irin halbawa a cikin fargaba da tashin hankali don gaba daya nikan na
sallama a raina mun rasa yaya a wanan lokacin don gara wancan ciwon na baya yana a cikin hankalinsa
wanan kam baisan wanda yazo ba baisan wanda ya tafi ba.
Sai bayan tafiyansu mama dan yanzu dagani sai maman tudun wanda da iya muke kwana su yaya
kwana biyu suna gidajensu amma basu barin asibitin sai wajajen karfe daya da wani abu na dare koshi
sai iya ta matsa masu akan su tafi zasu wuce din.
Iya na daga waje tana sallah bata shigo dakin ba tukun na na dubi mama a cikin karfin hali nace mama
naso nayiwa yaya wankan magani a gwada a gani amma ina shakkun hakan da zanyi din.
Kwana uku zanyi mai hakan amma sai abinda kikace shiyasa ban fada ba a gaban mutane ta yunkura ta
mike zaune tana fadin idan zaki iya ki gwada a gani mana yar nan ai sauki ake nema ba wani abu ba
dama kuma zaman hakan muke a nan din.
Tana zaune tana kallona na hada komai sai naji ta mike tana fadin bari naje daga waje in tare
tsohuwar nan kada ta shigo.
Ta fice ta barni dashi a cikin karfin hali hakan kuwa na cude mai jiki da ruwan hadin maganin na kuma
bashi ya sha sosai na mayar dashi ya kwanta a nan na kife a jikinsa ina kuka.
Sai da mama taji shirun yai yawa ta leko tana fadin yayane har yanzu cikin karfin hali na dago ina fada
mata angama.
Sun shigo sun tsaya akanshi suna kare mashi kallo tare da fatan alheri a gareshi kafin suka juya suka
samu wajen kwanciya don ni ban faye kwanciya ba ina zama a kujeran dake gefen gadon nasa koda
yaushe.
Tsawon kwana ukku muke a hakan dashi kullum da safe kafin su shigo zan shafa mai na bashi yasha
bayan na gama mulke masa jiki ko ina da wann ruwan da doki yasha ya raga don ba karamin magani da
alfanu yakewa mutum a jikinsa ba.
Kamar yadda dage ya tabbatar min ni kuma na fadawasu mama da iya ance ka,idan maganin har in
akwai alaman sauki kwana ukune kacal za ayi amfani dashi ga mutum aga alfanun maganin.
Don mutum zai fara nuna wasu alamomi na jin sauki ko wani sauyi nadaga ciwon halin da kake ciki din
Allah da ikonsa kuwa ranan na gama mashi amfani dashi na bashi yasha na zauna ina rufe goran nakai
idona akanshi sai na ganshi ya kura min ido kuri yana kallona.
Da sauri na cusa magani a cikin jakata na karasa wajensa ina kiran sunansa saidai bai amsa ba illa idon
daya kafa min din baya kyaftawa hakan yaban tsoro na nufi su mama ina kiransu hankali tashe.
Suka shigo dakin gurinsa suka nufo cikin kidimewa suna mai sallati da kabbaran iya ta karasa tana fadin
Jafaru idon kane nan ?
Sai ya dan lumshe idanuwan nasa kamar ya sauke ajiyan zuciya ya mayar ya rufe can kuma ya kara
budewa yana kallon mama dake mashi sannu a lokacin.
Ya Allah yadda ka nuna muna hakan ka tayar muna da kafadan yaron nan a cikin mu cikin salama da
kudirinka ya dawo muna a hayacinsa ya koma walwala kamar kowa.
Hawaye kawai ke fita min daga idanuwana na kurasa masa ido a cikin tausayi ni kaina a lokacin abin
tausayi nake na sani amma duk bacin ran da bawa zai shiga matukar yana lafiya ya godewa Allah don na
kwance ya fishi shiga tashin hankali.
Ganin yadda ya kura min idanuwanshi din yasa iya min magana tana fadin ki daina wanan kukan ki
karasa kusa dashi kiji ko wani abin yake so don ke yake kallo a yanzu din.
Hakan na dan karasa gabanshi na dan rankwafa ina fadin yaya kana son wani abune da idon daya kifta
min na gane yana nufin a,a sai ya maida idonsa ya rufe a hankali.
Ya Allah kasa hakan saukine a gareka jafar Allah ya kaddara tashin ka a cikin yanayin nan ya baka ikon
cin jarabawan nan da Allah ya aiko maka muka amsawa mama dake fadan hakan da amin.
Munyi tsaye cirko cirko a kansa sai iyace take fadin ko abinci yake bukatane ni dai banyi magana ba
don nasan yana da wuya idan hakanne.
Saidai na karasa gaf da fuskanshi ina fadin a hado maka ruwan shayine zaka sha yaya sai naji iya tace
keko dai ai basai kin tambayesa