Chapter 78 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   78 / 101

231K to 234K   out of 302.2K words

a bakin yara ya fito bako manya ba ban taba gani ko jin yadda dan uwa zai batawa dan
uwansa jininsa haka tun baizo duniya ba ?

Yarinyar banzace daddy ayi hakkuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba da yardan Allah kwanan nan
duk aure za ai masu su kama gabansu.

Kaiya ko kun masu aure ai suna tare daku kun taba ganin inda wuya yabar kai sai gangan jiki kawai ?

Yanzu ga yarinyar nan ai a kusa muji ta bakinta na fada maku tun farko ba zan mata dole bani don bani
shiga hakkin mutum a rayuwata.

Kafin ya rufe baki na amsa da daddy ni gaskiya ba zan koma ba su aiko min da takardana kawai in huta
ina fada a cikin kuka sai salati mama da iya sukeyi .

Mama na fadin yar nan da bakinki kike fadan haka a gaban mu me mijinki yai maki da zaki yanke
danyen hukunci haka tsakanin ku ?

Iya take fadan hakan kuka sosai nasa ina fadin iya niba zan koma ba inda ba a kaunata ba kuma ba mai
daukan min mataki ga hakan saidai aga laifina idan na dauka ni gaskiya ban komawa gidan nan kuka
sosai nakeyi a lokacin.

Haba yar nan kiyi hakkuri zancen nan ya mutu a nan ki shirya mu koma gida amma zancen ba zaki
koma ba ai bai taso ba mama ta fada.

Mama nagajine nagaji nina san abinda ake min kan ya jafar ina hadewa gara kawai in bar gidan zaifi ni
dai bani bace na dafewa yaya saina aureshi shi yaje yasa iyayyena suka aura min shi bada sanina ba
kuma nayi hakkuri na zauna dashi duk da irin barazanan da nake gani a gidan wallahi ba zan koma ba.

Cikin bacin rai don ya nuna min shi wanine a gareni lokacin ya mike tsaye yana fadin Iya ku tashi muje
tunda hakane don taji ance ba zata koma ba udan bata so zata tsaya tana muna wanan shakiyancin
haka ?

Habu ke fadan hakan cikin bacin rai ya mike yana fadin su tashi suje nan dan uwan yace a,a bros ba za
ai hakaba dole mu lalashe ta tunda laifi akai mata.
Me kake son muyi yanzu tunda an fada mata matakin da za a dauka kan abin tace ba haka ba ba saita
zauna gidan ba ban taba mashi rashin kunya ba sai a ranan .

Nima a hasale nace dashi a barini mana sai me idan na zauna gidan ai yafi min sauki da zama inda ba
asan darajata ba sai wajen amfani .

Ko an barni aiba mutuwa zanyi ba hakan ma tafi min dadi da zama inda a kullum laifina ake nema a
gorantawa iyayyena don ana daukan mu marasa gata.

Rahama ni kike fadaqa wanan maganan yau haka ya fada yana kallona da sauri mama tace kai habu
gyara mukazo yi ba barnawa ba don haka kabi abin nan sannu don Allah.

Nima shina gani tunda har yarinyar nan tayi haka an dade ana cusguna mata tana hakkuri yanzune
take ganin tagaji koma waye gaskiya haka zaiyi.

Baiyi magana ba har matanshi shiru tayi shiko ya juya ya fice falon yana fadin ummah nina tafi ke nan
sai anjiman ku ya fita.

Daddy yayi murmushi yana fadin ga alama nan ya nuna kanshi ko a yanzu yarinyar nan an tabata a
rarasheta amma yana son ai mata dole ta koma ?

Ba dole yayi min hakana ba tunda kansu hade yake da dan uwanshi amma aishi da aka tasa matarshi
gaba ya dauketa yabar gidan a lokacin duk da ban gidan ban huta ba tunda har inda nake ake biyoni aci
min mutunci akan gaskiyana.

Dashi da jafar din waya taba daukan mataki udan ba iya ke kusa ta tare min ba bagaji wallahi ni ba zan
iya ba gaskiya na fada na mike zuwa ciki ina kuka .

Ajiyan zuciya ya daddy ya sauke yana fadin wanan abin dole a tsaya a natsu abawa yarinyar nan lokaci
don Allah harta sauko don na fahinci ranta abace yake yanzu.

Idan munce zamu mayar da ita da karfi da yaji abin ba zaiyi dadi ba gara dai a bari ta dan huce zaifi
sauki saita koma din.

Abinda nakewa gudu ke nan nasha fadawa dubu hakan tana ganin bai zama komai ko kuma ta dauka
ai basu da gatan irin haka yau gashi dai din ya faru ai.

Amma na dauka akan Saaratune da abokan zamanta matsalan ai yazid ya fada yana kallon iya iya din
tace ai kaji metace ko yanzu kokai matanka ai don suna ciki kullene ko yaushe basu kwasa da ita.

Bar dubu inda ka ganta akan yaran nan da kawun ku hardai ace maka sun hade da shedanin nan guda
dauda to ka barsu kawai na gayama .

Ni yanzu aiba mu koma babu yarinyar nan bace yaron nan Jafar ya rikece muna yadda yayi jiya ni shine
tashin hankalina a yanzu.
A to mama tunda ance a barta ai dole mu barta din har ta huce yaya zaiyi kuwa banda hakkuri tunda
ba tare aka haifesu ba dama ?

Yasan yana sonta haka yarinya tana kokari dakai baka iya kareta ga kowa anatayi mata cin fuska yana
kallo bai dauki mataki ba da nine gobe wata ba zata kara ba ai idan anga irin matakin dana dauka.

Yaren fulancin da mariya tayi tana mikewa tsaye shine yasa suka bita da kallo itama ummah yaren tayi
mata tana bata amsa don fadi take wai akan me zanyi haka tunda an biyoni bari ta ganni.

Shine ummah din tace gaskiya itama bata son a barni in koma kawai kowa ai hakkuri yakeyi a gidansa
shine ta nufi dakin wajena.

A kwance ta sameni na kifa cikina ina hawaye tashigo ta tsaya a kaina tana fadin yanzu ke kinga haka
yafi maki kizo ki zauna nan ?

A fusace na dago na tareta da fadin ai dole kice haka tunda bake bace akewa abinda akemin a gidan
koda yake ke naga hakan bai dameki ba ai dama toni ban daukan hakan .

Kiri,kiri mama ta nuna bata son zaman mu da diyanta abinda take muna idan ayiwa diyanta zata dauki
hakan ta kyalene ?

Ko gaida matar nan nayi duk zuwan da nakeyi gidan nan bata amsa min sai taga dama duk abinda
sararu tayi min da sanin mama .

Tunda sunce ni ba alheri bane ga yaya Jafar sanadina abubuwa da dama suka sameshi na barshi don
abubuwan su wuce din garesu tuda nice matsalansu.

Ashe in kina bin zancensu ba zaki zauna da mijinki lafiya ba kuwa don su ko ajikinsu kuma kina gani tun
baki aureshi ba ai yadda sukeyi damu a gidan .

Ku kikace Yanda ni baku nane ai don ban iya daukan hakan nagaji wallahi amma baki mashi adalci ba
Rahama udan kinyiwa yaya haka ?

Naji ke kije kiyi mashi adalcin bashike nan ba ta tare da fadin akankifa ya saki Nusaiba jin hakan data
fada yasa na dago na tsareta da idanu ina fadin.

Aikanafa kikace Maria kaina ya rabu da matarshi tace akankine mana nace akanshi dai idan baki san
abinda yasa yakai ga sakinta ba nina sani kuma ban fadawa kowa ba duk da fadin da akeyi kainane ya
saketa din dama yana da niyar hakan.

Ki dai tashi muje kawai kinga har habu yayi fushi dake yau na sake jefa mata kallo a cikin mamaki tare
da mikewa zaune nace habu ubanane ko yayana maria ?

Shigowan ummah dakin ya hanani cigaba da maganan tashigo tana fadin habu ba ubanki bane amma
kamar uba yake gareki ai don shine gatanku acan din.
Kememe na kafe duk abinda suka fada ban yarda na bisu ba mama tashigo muyi sallama da ita a cikin
dabara nan take fada min kin mun daidai Rahama dabaki yarda kin koma ba a yanzu sai dubu ta kawo
kanta gidan nan da kafanta.

Lokacin zata gane kina da ma,ana a wajensu idan ba haka ba bata da niyar barin wanan halin banzan da
dan uwata ke dorata a kai na fahinci gaskiyan tsohuwar nan dauda ke zuga dubu ga duk abinda tayi mara
kyau don ya zama dattijon banza.

Wanan maganan na mama yasa na kara kafewa kyam ban yarda na bisu ba ina jin suna sallama da su
ummah suka tafe .

Ummah harda fushi dani don bayan tafiyansu yinin ranan daure min fuska tayi ko nayi mata magana a
dake take amsa min yasa nima nayi shiru na kyaleta.

Saida safe taga ina shiri take tambaya nace gidan mu zanje can garin mu nan kuma ta hauni da fada
wai na rainata in tafi gidan indai kawune ai nasan abinda zanje in sama a gidansa .

Ina kuka nake fadin koma meye ummah yafi min tunda gidan mune ko yayi min kansa yayiwa da in
zauna mama tanaci min fuska don kawai danta ya aureni shike nan ta dauku kiyayyan duniya tasa min.

Ni abinda saratu ke min bai damuna kamar na mama dake fadin zamu mallake mata diya su koma sai
abinda mukace kamar yadda kika maida daddy nan haka mun asirce su daddy Abuja sai abinda mukace
sukeyi akanmu shine itama za a kawo mata ga iyalinta.

Nan ummah din ke fadin matan nan fa na dade da fahintar ta tun zaman mu asibiti da mukayi da yar
uwarki ?

Agabana in kun kawo abinci zata kama fada tana fadin ana barnan abinci ana saki abin miya haka da
yawa don ba asan wahalan nema ba.

Bayan wanan kashin kudin da aka dauko masu a yanzu kuma a koma ana barnan abinci haka ita ba zata
yarda da hakan ba a diga kirga nama kafin a saka a miyan.

Wanan ma kadan ke nan ai na fada na dinga bata labari ta hau tana fadin ita wallahi ba zata yarda da
wanan cin fuskan ba ai muma yayane kamar diyanta bawai bata son mu bane ai koda sukaga tana nuna
hakan kawaicine kawai nasu na fulani take muna.

Wanan yasa ta dauki zafi akan zancena din take fadin ki zauna sai tazo gidan nan da kafanta ta sameni
na fada mata abindake raina nima kafin ki koma din.

Tun bayan barunsu gidan habu ya fisgi mota yana gudu Iya ta lekoshi daga bayan mota inda take zaune
tana fadin kai hanu kajamu a sannu don Allah ?

Kana zuciya kamar an maka wani abu yarinyar nan tana da gaskiyanta inma laifine ita dai akaiwa shi ba
karya ta fada ba ai.
Tunda yarinyar nan ta kafe haka abin ne ya isheta don Allah nasha fadawa uwarku ta guji irin wanan
ranan kada haka ya faru amma bataji ba.

To wai ni iya ban gane ba me akewa yarinyar nan haka wai naga gidanta daban mana yazid yake
tambayan hakan ?

Kadai fadi duk yadda akeyi Yazid J yayiwa yarinyar nan amma wai shine don jin dadi zatawa mutane
rainin wayau haka din taga yana yinta haka sosai a cikin matanshi.

Allah sarki dama hakane ai idan namiji ya nuna kai yakeyi sai ace komai yi maka akeyi ita fa baku
fahinceta bane har yanzu nake gani habu ?

Yarinyar nan takafe akan ba zata dawo gidan nan bane kan irin cin fuskan da uwarku take mata a
gaban kowa Dubu take nunawa yarannan hattara da kyamansu tana sakin maganganu akansu.

Kasani kowa kuma yasani idan matsafane ko mayu aida yanzu sun baiyana daba hakaba da sauri iya ta
dafata tace madallah Amina kin gane matsalan kenan ke ashe ?

Shi wanan bai san komai ba sai zuciya a gaban yaran nan take nuna bata kaunarsu batayin lamarinsu su
din ba kowa bane sun shigo rayuwanku zasu juya mata kanku .

Wani tsuki yayi yana fadin nasan wanan mama aiga maria nan wani irin cin fuskan mamane bata gani
ba a gidan nan kan matan J da bako kyautata mata sukeyi ba kamar ita kuma tayi hakkuri ta zauna .

Ba zaka hada ba habu don idan anyiwa matarka kana tsayawa tsatin daka ka nuna bacin ranka kan
abin shiko jafar fa bai iya komai saidai ya juya ya wuce kawai har can gidansu fa take binta itada dauda
suyi mata kaca kaca su dawo zakace kadata nuna itama mutunce don Allah ?

Inda laifi daga Jafaru har dubu da yan banzan yaran nan duk suna da laifi saidai kawai ace ayi hakkuri
kawai shine yanzu amma abinda yaran nan sukeyi banga sarakuwar gidanmu dakeyin hakan ba gaskiya.

Yarane da suka san mutunci da kimar babba da darajan dan adam mutum indai daga bangareku ya fito
yaran nan zasu darajashi yaya ake son mace tagari ta kasance wai ?

To mama ai na dauka don kawai wanan abin daya hadata da Saaratu ne take wanan zuciyar ashe bashi
kadai bane tarawa tayi ta amaye muna komai lokaci guda haka ?

Inda zata amaye din ne aida ta amaye muna idan watace ba tas zata fada a gaban kowa ba cewa ga
abinda ke nan amma ita kaga tayi hikima takafe akan bata komawa kawai ?

Dole aiwa abin tufka gaskiya bansan yaushe mama ta juya ta koma hakaba bayan tafiyana koda yake
ance kawune matsalan komai a yanzu shike hura mata kunne yake zugata.

Tundana dawo nake son a zauna naji zancen kudin mu dake wajenshi matsalan nan na j yasa na kyale
amma yanzu ai dole mu hadu tunda ina son kudina na fara dan bussiness dasu .
Habu na fada maka kabar zancen kudin nan don babu su rayukane kawai zasu baci a karshe don ko
mama ta sani babu kudin nan a yanzu.

Babu fa kace bros haba dai wanan wasane kawai kubar zancen agama wanan don Allah kada ku tayar
da wani zance a yanzu muna fama da wanan ?

Shiru sukayi don habu ya fahinci iya saboda mamace dake cikin motan abin daya shafi iya sune zancen
kudin nan bai kamata ace wani na wajen dakinsu yaji zancen nan ba.

Shiko yazid bai gano hakan ba sai fada yakeyi yana fadin kawu zaisan koshi waye bai sanshi bane
wallahi jin kowa a motan yayi shiru yasa shi fara fahintar akwai matsala.

Sai mama din ke fadin kai yazid ai kaji iya tace ka bari agama zancen nan toka bari mana hakan ya isa ba
sai ka bata ranka a yanzu ba ai.

Koda suka isa zaria la,asar tayi don haka su basu shiga part din ba saukesu Habu yayi yace zaikai
matarshi gida ya dawo.

Shi kuma Yazid part dinsa ya nufa saisu Iya da mamane suka shiga ake masu sannu da zuwa don nan
suka samu kawu da mama dubu a zaune tare dashi.

Tayi masu sannu da zuwa tana fadin ina yarinyar ko an sauketa gidan can ne don bata ganni ba iya tace
wani gida yarinya kan na hannun iyayyenta sun rike abinsu kamar kowa .

A,a duk da kunje basu baku itaba ke nan kuma yau ga mutanen banza marasa mutunci har anbi bayan
yar ku kuma ku hanata dawowa akan wani dalili wai kuma ?

Shi nake son ji kawu ya fada a cikin bacin rai iya ta juyo tana fadin akan dalilinku na cin fuskan da kuke
mata ta hakkura tabar maki gidan da danki a zauna lafiya.

Sallah ya sallame daga inda ya zauna ya juyo yana fadin wai bata dawo bane iya da gaske ko tana can
gidan kun sauketane ?

Bata dawo ba Jafaru ta nuna bata dawowa gidan nan a yanzu ban sanarwa gaba ba inda rabin
dawowanta ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/7, 6:50 AM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣9️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Wani shewa ta sake wanda yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gareta inda take zaune tana waya
bayan kiran da Saare tayi mata din.

Don tana ganin itace tasan da magana hakan yasa ta mike tabar wajen ta koma gefe daya don taji meta
samu ta kirata kuma yau ?

Nan ta fara sheda mata albishirinki Anty Saiba tace goro cikin zakuwa tace yar iskan nan Rahama tabar
gidan nan tun jiya .

Ke ki bari don Allah saiba ta fada tace wallahi yau su ya habu sunje kaduna wai su dawo da ita tace dasu
bata dawowa gidan nan wai ?

Haka suka juyo suka dawo su kaidai taki ta biyosu shine dslilin shewan nata da har ta dawo da hankalin
mutane gareta.
Saida sukaji tana fadin aina fada maki saaratu bashi taci wallahi indai nice yadda tasa nabar gidanku
itama saita barshi wai abin haushima yayanki ai yafi ban mamaki saaratu.

Wai ace yaki zuwa yaki ya turo tunda nabar gidan nan kamar dama yana jiran haka ya faru tsakanin mu
to shegeb cikin jikintafa yana nan kota zubar ?

A kema kinsan yana nan ai tunda tana son ace ta haihu da yaya ba dole tabar cikin ba saiban ta amsa
da fasin shegiya ai bataga komai ba.

Gara dani ba goyo ba ciki nabar gidan itako yar banzan ko zaman ciki ai ya isheta yar iska tana wasa
dani saina mayar da yar iska ko abin sayen goro.

Waima meya farune tabar gidan take tambaya ?

Wani irin dariyan shakiyanci Saare din ta kwashe dashi tana fadin kin manta dani ke nan ai dana saka
yar iska gaba saida naga bayan shegiya .

Wallahi yarinyar nan baki san irin haushinta da nakeji bane ai hana shegiya shakar iska nayi ko
walwalan kwarai ban bari tayi ba.

Nusaiba tace dakyau nawa ina sonki irin wajen nan wallahi a aina fada maki ki barni da ita ita a dole
tazo cin arziki to taci din mugani yar iska kawai.

Saura wanan shashan matar habu din itama haka zan ta zuga mama akanta sai naga bayan shegiya su
tattara subar muna gidan yan iska muggan iri kawai.

Aini ba barin gidan wanan yarinyar ba Saratu naso har munafukin cikin nata ya zube banson ma tabar
wani alaka a tare dashi wallahi ai in ta haihu dashi taji dadi kota abinda

78 / 101