Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
zai dauki mataki kan irin zancen nan kice ina
ruwansa ?
Saida mama ta nisa tace aini yau yariyar nan ta nuna min iyakata a gidan nan don ,,,,,,,, dakata don
Allah gaskiya danki ya fada tun farko na fada maki ba aiwa yaran yanzu haka.
Duk kama girmanki da kikeyi kina kau da kai ga rayuwansu sun dauka baki da amfani a gidan nan yadda
yar nan ta nuna ?
Yau gashi salima da abin ya isheta itace ai tayi fadan akan ki don bata da kunya zatazo da wanan
shirmen haka a gaban mu.
Wanan hali naki dubu shiyasa mutanen gidan ku duk wanda ya dauko sharansa akanki yake juye
tsiyarsa .
Wanan sanyin zuciyar taki tayi yawa Dubu kima godewa Allah daya baki yayan da suka san zafin ki
amma anyi mutum haka bai iyawa kansa katabus ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sallah nayi na kwanta saboda gajiya a dakin da anty Salma ta kaini don bamu ko zauna munyi wani hira
da ita ba a lokacin saboda gajiya.
Sallah la,asar ya tayar dani na falka kinsan hakan baiwane ga musulmai da zaran lokacin ibada yayi in
barci kikeyi sai kin falka saidai shedan yayi kokarin rinjayanki ki koma barcin.
Hakama idan idon ki biyu da zaran lokacin nan yayi sallah ce zata fado maki a rai musulmi na kwarai duk
abinda yakeyi a rayuwa sallah tana a zuciyarshi hakan aka san musulmin kwarai dashi.
Nima irin hakan yake kasancewa dani komai nauyi barci zan falka a daidai lokacin ko lokaci ya dan
gwauta kadan in tashi in gaida ubangiji subbahanahu wata,alah.
Bayan na idar da sallah ina zaune na jawo wanan karamin ledan da yaya ya miko min a hannuna
lokacin da zan fita motan shi daya kawoni.
Na fara budewa kudi yan dubu daya sabbi,fill dinsu duk daba nauyi kudi na sani ba a lokacin balle na
kiyastasu nasan wanan yafi karfina a lokacin.
Sai wasu sarkoki da bangus da yan kunne guda biyu bangus biyu masu kyau ga kudinsu nan a manne
jikinsu ga yar takardan da akaiwa rubutu ja.
Mamakine fal a fuskana na dalilin sayan kayan nan duk da nasan shi mutum mai alherine dama mutane
na fadi ina ji uwarsu kuma ko yaushe tanawa abinta kirari wajen alheri kullum ina ji.
Ban kara girgiza ba saidana mike da sauri na fara budan suran ledan gabana nafaduwa nake zaro
dogayen riguna masu kyau da daukan hankali guda ukku ko wani da gyalensa a ledansa.
Tsorone fal ya dira min a zuciyata mu fulani mukance alherin namiji gareka nuna alaman sone ko kauna
sai wanda ka damu dashi kajin lamarinsaa zuciya kakewa alherin bajinta irin haka ?
A take wani gefe ya gargadeni da ke wawiya wani so yaya Jafar nefa ina so zai shigo tsakanin ku kuma
yadai nuna ke kanwarsace yasa ya saya minsu.
Ko kuma don zancen da sukayi na cewa abinda matansa sukai min yake kokarin wanke min zuciya sai
gashj nafi amincewa da wanan na karshen wanda kuma haka dinne ko a wajensa.
Don yaya Jafar nauyi da kunyana ya dinga ji na abin daya faru yana sane kuma nima abin yayi matukar
tabamin zuciya hakan yasa na tsame kaina ga lamarin kowa a gidan.
Karshema sai gashi na yanke shawaran in dawo Abuja inzo inyi sallah wanda yaga sakacin dan uwansa
Habu daya yarda nazo abuja din idan shine haka ya faru ba zai bari naje ko ina ba zai tsaya ya tura masu
haushin abinda suka aikata wanda sai sunyi dasun sanin hakan da sukai min a lokacin.
Koda muke tafe hanya yana da takaicin Saiba amma kuma yana sake saken ta yaya zai dan farauta min
ba tare dana rikesu ba a zuciyana don cin fuska bai da dadi ga mutum irin haka balle ga yaro karami.
Shine yana jin banda waya yaga rashin dacewan hakan gara ina da waya a hannuna aji halinda nake ciki
a nan yayi shawaran saya min waya din sai ya ga wa yanan kayan kuma ya hado min dasu.
Yarinyar ba laifi gaskiya tana da dadin zama ga tsabta ga ladabi ga hsanin ya kamata bata da hayaniya
ko daukan magana duk abinda matansa keyi bai taba jin yaran sun tsaya sun mayar masu da martani ba
koda agabansu akai abin.
Hakan yasa yake ganin girma da kimar sarakuwar tashi da kanwata duban irin simple rayuwan yaran
yakan burgeshi wallahi tundai tsabtansu da wanan yakewa matasa gori wanda sukuma suke kara jin
kiyayyan yaran a zuciyarsu.
Haka ya kama hanya bayan ya saukeni tare damamakin wani irin halakace tsakanina da mutanen nan
haka ?
Don da ganin gidan ba gidan karamin mutum bane dole akwai wata halaka mai girma a cikinsa koma
meye ya godewa Allah da bai ajeni a wullakace ba.
Gara da Allah ya bashi dubara danyi min sayayyan nan da yayi don a ganni a cikin mutuncina da kima
ba zaiji dadi su ganni cikin irin suturan da habu ya barni ina sakawa duk dai da baisan daliliba amma dai
babu wadatuwa gareni gaskiya.
Yasan haka halin dan uwanshi yake tun suna kananunsu habu bai damu da wani rigimar duniya ba kan
shima bai fitar da kanshi kunya balle wani.
Wayanshi dake karane ya katseshi ya dauko yana duba dan uwan nasa da yake tunanene ya kirashi
yana mashi ya hanya ?
Alhamdullahi Habu na sauketa tun dazu na saya mata waya don ta rike don nace ta kira idan da matsala
tace bata da waya a hannunta.
Why habu zaka kasa saiwa yarinyar nan dan waya koda karamace da zata rika meyasa kake hakane
wai ?
Yaran nan kaika daukosu a karkashinka suke a gidan nan da anga kana darajasu da ba macen da zata
nemi tozarta makasu a cikinsu.
Bai kamata irin hakan na faruwa ba marayune fa Habu kasan yawan ladan da zaka samu a wanan
taimakon da kayi gaskiya banji dadin hakan ba wallahi na dai saya mata da wasu kaya tunda banyi
tsamanin ta samu dinkin wa yancan ba da zata saka.
Shiru Habu yayi yana saurarenshi na dan lokaci saida ya kare magana yake fadin Nusaiba ta kira wayan
kane ?
Nusaiba wani abubya farune kuma dazun dai da zan fito tazo tana min rubbish akaina ban tsaya kulata
ba don bata da hankali nake gani.
Bata dashi kan akan ka dauki Rahama yau tashigo wajen su mama tayi tijara iya son ranta katse dan
uwan yayi da fadin What ?
For what reason zata samu mama to Salima dai bata kyaleta ba itama bata kyale salima din ba sunyi ba
dadi a gaban mama wanan yasa na kasa hakkuri na kiraka .
Irin wanan abin yana taba mutuncin mahaifiyar mu sosai don bata magana su kuma sunga ko sunyi ba
mataki kake dauka ba yasa suke cigaba da hakan tundai ita Nusaiba din.
Saiba saiba takai karshena wallahi amma bari laifin mama din ne dake hanani daukan mataki akansu
kome sukayi mama tace inyi hakkuri haka mata suke basu da tunane komai girman su zankiraka habu ina
zuwa don Allah ya fada a gagauce ya kashe wayan.
Me wanan yarinyar take nufi danine wai yana neman layinta data kirashi danzun yana zancen zuci a fili
ta dauka ni dan iskane irinta kome yaji ta dauki wayan cikin basarwa tana fadin hello J.
Ke Nusaiba yanzun nan ki tafi gidan ku kada ki bari in dawo zaria yau in sameki idan ba haka ba wallahi
saina katse duk igiyan dake tsakanina dake a yau din nan ya kashe wayansa yana huci bai jira cewanta
ba.
ABUJA
Ina saka wayan a caji aka shigo na juyo yar aikin antyce wata yar budurwa mai guntun buje da ganin
shigarta nagane ita din yar aikice agidan .
Abinda basuyi muna ba ke nan a lokacin sam ba a gane cewa mu yan aikinsune kuma ta gargadi mama
dake katobaran fadawa mutane hakan.
Ranan da hjy taji tayi fada da mama sosai take fadin mu bamu daukeku a yan aiki ba a yan uwa muka
daukeku kowa kuma yasan abinda nake fada ke nan don kun zama yan uwa a wajen mu yanzu.
Tun wanab lokacin ummah bata sake wanan katobaran ba tana kafa kafa da abinda ke batawa hjy rai
akai zama lafiya sosai a tsakanin mu.
Wanan yasa na nasa a raina cewa yarinyar nan ta huta indai har anty Salma ta biyu halin hjy mama da
yan aikinta zataji dadi sosai a wajensu.
A falo na samu anty salma din tana waya alama tayi min da hannu inzo na karasa ta nuno min fuskan
wayanta dake hannunta.
Fuskan hjy mama a cikin massalaci zaune ga larabawa suna gittaiya mama kinga Ramaah kin yadda ta
girma ta zama big girl yanzu.
Mama ina wuni Ramaah ta lafiya lau ya kuke yaya yanda da jikinta yaya yan uwanku na amsa da
Alhamdullahi.
Ya ibada mama tace Alhamdullahi gamu a cikinta aini mamakin ganin yadda Ramaah ta girma nakeyi
mama din ta katseta da fadin anyi sallah ki bari zan kira ku anjima.
Ta kashe wayan tana fadin yau mama zataji dama ace tana garin nan ta ganki murmushi nayi ina
dukar da kaina kasa.
Take tambayana ya jikin Yanda da sauki ko babu dai wani matsala dai ko na amsa da taji sauki sosai
lafiya na barta jiya muna asibiti tare a can na wuni dasu.
Ta koma tambayana karatu nake fada mata nagama secondry school yanzu gaba zaki ko sai nayi
murmushi ban bata amsa ba don banda abinda zan fada mata lokacin.
Duk da nasan ana zancen zuwana gaba din amma ita ban fada mata komai ba tunda banda tabbaci
akan hakan yanzu saidai abinda shawara ya yanke a kai.
Tunda su Salima na karatu ni kuma yanzu rikona ya dawo hannun yaya Habu nasan yana da wuya ban
je higher institution da nake son zuwa ba.
Zamana gidan anty sallama a ranan ya tuna min abubuwa da dama a rayuwana wanda yasa jikina yayi
sanyi don tuno da mahaifinmu da zaman Abuja da nayi.
Zaria duk yadda Saiba taso ta kira mijin nata yaki daukan waya don yayi blocking dinta a lokacin
karshema kashe wayan nasa yayi don mama ta fara kiranshi tana son taka mashi burki.
Wanan karon yasha alwashin sai ya koyawa Saiba hankali sai ta gane ita ba kowa bace in ma
rabuwace ai a rabu din ya gaji da wanan irin halin nata na rashin kwabo.
Bata kara sanin da gaske bane saida ya Habu ya dawo yana fadin yace ta fita gidan kafin ya dawo har in
ya dawo ya sameta gidan wallahi kowa yayi mata tsaye yau sai ya raba igiyar auresu ga baki daya.
Iya najin hakan tace maza ki tatara ki nufi gidan ku kada kaddara ya zaunar dake yazo ya aikata abinda
ya fada zaman ki gidan nan ya kare maki.
Babu yadda ta iya don mama tayi shiru batace komai ba a wanan zancen hakan ya kara tunzurata ta
shirya kayanta a cikin yar karamar jakka ta nufi kaduna.
Ana magariba tana sauka gidansu cikin tashin hankali ba wanda yace mata komai don ta samu ana
hada hadan shan ruwa a lokacin.
Baya bata da kadan don ko tana fita ba,a jima ba ya iso gidan bai tsaya ba ya sauke abinda ya sayo a
hanya ya nufi cikin gari don samun sallah a unguwarsu inda suke shan ruwa.
Maigadi ya jido kayan zuwa part dinsa dana iyayyenshi iya take tambayan maigadi ina Jafaru ?
Yace ya fita yanzun nan kayan kawai ya sauke ya juya ya fice daga gidan ba zai shigo ba ai tunda yasan
abinda ya aikata uwar ta fada.
Keko meya aikata kuma ba zancen ki bane asalima nasan saboda ke yaron nan yake son daukan mataki
tunda kinji wayan da sukayi da dan uwasa don haka ki sa masu ido kawai yayi iko da iyalinshi.
Yarinyar nan tana bukatan gyara a gaban mu tazo tana zagin yarinyar nan koke maisa ya dauki
matakine kan abin nan data aikata ai.
Shawaran Iyan mama tabi don koda Jafar din ya dawo batayi mashi zancen ba shiru tayi har ya gama
hiranshi da iya ya nufi part dinshi.
Takaicine ya kamashi yadda ya samu fslon nasu a ya mutse ga kujerun falon da basu dauki wani lokaci
ba a gidan har sun fara ya mutsewa da auren Yanda ya sayo masu shi da akai gyaran gidan.
Abin takaici ranan daya shiga falon Habu yaga nasu zakice ranan aka kawo masushi part din don komai
ba suyi ba sai walkiya da sukeyi.
Takaici ya kara kamashi haka ya taka zuwa dakinsa ga wani bashi dake tashi ba alaman ma tayi wani
soye soye don shan ruwa a ranan.
Yana gab da shiga dakinsane yaji muryanta a bayanshi tana fadin ai kadowone ashe na dauka ba yau
zaka dawo ba ai naga Saiba ta tafi kaduna da yamman nan ?
Bai tsaya bata amsa ba ya murda kofan dakin ya shiga ya rufo sai lokacin ya shaki kamshin dakin don ko
yaushe shike tsayawa ya gyara abinsa yadda yake son ganinsa.
Kayan jikinsa ya rage yashiga wanka yaso ya kwana a Abuja saidai saboda ya kure saiba ya dawo zaria a
ranan tayi arziki daya dawo ya samu tabar gidan don daya shayar da ita mamakinsa a ranan.
Why zata zargesa da irin wanan mumunan abin ta rasa wanda zataiwa sheri irin wanan saishi kuma ?
Dashi dan iskane yadda take zato akanta zai fara nuna halinsa ai amma sai ya juya abin zuwa aure a
tsakaninsu tabbas itace da farko ta fara nuna mashi so da kauna .
Don tun bai gane ba har yazo ya fahinci me take nufi da farki yaso ya guje mata amma ta hillanceshi da
dadadan kalmanta har yaji ya kamu da kaunanta itama saboda yadda take matukar bashi kulawa zakice
ko itace matar nasa duk a lokacin ta fake ga besty dib Asmau take masa wanan.
Tsoki yaja lokacin daya murda famfon ruwa ya kare hakan ya tabbatar mashi da ta kasa fita ta kunna
ruwa ke nan a ranan .
Dole yayi amfani da ruwan roban da suke tarawa acikin kyankyami saboda ruwan ya dade a rufi bayan
ya fitone ya shirya kansa bai fito daga dakin ba nan ya zauna bakin gadonsa yana waya da wani mutumi
da zasu hadu dashi a Onicha.
Tashi yayi ya sakawa kofan key yana mai jin haushin matan nasa aransa a haka barci ya daukeshi don
koda Asmau tazo tana murda kofan duk yayi barci a lokacin.
Sai tsakar dare da yunwa ya tayar dashi irinta wanda ya wuni da azumi a cikinsa hakan yasa dole ya fito
ya duba falo ko zai samu abincinsa aje sai dafa duka da ganye.
Kitchen dinsu daya dade bai shiga ba ya nufa a can ma ya kwammace da bai shigo kitchen din ba a
lokacin don kayan takaicin daya sama a kitchen din.
Drinks ya dauko a fridge sai bread dashi yai sahur ya kwanta cike da takaicin duniya akan matan nasa.
Idan kaga Asmau a zahiri zaka dauka mace ce mai tsabtan bala,i don iron yadda jikinta yake ashe abin
ba hakana bane halittace kawai a hakan .
Ita kuma saiba datayi mai dadin baki tana da dan dama saidai ba sosai ba ga kuma cin mutunci har na
tsiya a bakinta.
Abin yana daure mashi kai yadda mace tayi boko zata tsaya tana wanan kazantar haka sai wace batayi
karatu an koya mata tsabta ba tafita.
Da safe kuma asubanci yayi yabar garin zuwa Abuja inda ya shiga jirgin zuwa Rives don haka koda
mahaifin Nusaiba ya nemeshi baya gari bai sameshi ba.
Saarece wajen binciken ta ta dauko kayan nan da matan ya J suka dawo min dashi a cikin kayana tana
nunawa mahaifiyarsu.
Tana fadin wai mama kinsan yarinyar nan ashe bata dauki ko tsinke daga cikin kayan nan ta tafi dashi
ba.
Yanzun nan ina neman gyalena na gansu a kayan ta yadda aka bata haka ta ajesu a nan din bata dauki
ko tsinke daga cikin kayan ba.
Haba dai Saare yanzu bincike kikai mata a kayanta kema kinsan babu gyalen ki a kayan Ramaah wace
take hada muna kayan mu itace zata daukar maki gyale kuma ?
Mama yarinyar nan tana min katsalamdan a ciki zancena kwanan nan wallahi idan tana min hakan za a
jimu da ita.
A cikon takaici mama ta juyo tana fadi rufa min baki mara hankali ai gaskiya ta fada inba rashin wayau
da tsegumi ba meya kaiki cikin kayan yarinyar nan yanzu don Allah.
Wanan wani irin dabi,ace Saratu ina kula dake a gidan nan idan nabi ta naki yarinyar nan so kike ki
hadani da yaran nan sam bansan meyasa kike haka a kansu ba.
Haka yarinyar nan dake asibiti tun tana tambayana ke har tagaji ta kyale ta daina tambayanki kwata
kwata a yanzu kinki zuwa ki gaida ita.
In habu ya gane wana halin da kika tsiru nasan ba zaku kwashe dashi da dadi ba tsorona Allah a yanzu
kada sunan ki ya fito cikin zancen yarinyar nan Nusaiba.
Don ban tantama idan ba kece kika fada mata cewa yarinyar nan zatabi yayan ku ya sauketa a Abuja
kika haddasa wanan fitinan a tsakanin su.
Kallon uwar tayi tana fadin haba mama ni ina naga Nusaiba a ranan balle in fada mata ga Ramaah
zatabi yaya idan ma kece ai ji zamuyi don Nusaiba fada zatayi kin sani.
Wanan ai shashancine jafaru din ta zarga ko wanan yar komu ta dauka bamu san abinda mukeyi ba
lamarin wanan yar yana ban mamaki ke kinyi kwancen mijin nan hannun kawarki kuma ki koma kina
nuna kowa bakya son yai mu,amula dashi saboda me hakane wai ?
Har kizo kina neman batawa mutane suna akan abinda bashi ba isan wani yaji wanan shirmen ai zancen
zai juya wani abu daban kuma ?
Iya na sauke zancen mama ta dauka da ai yanzu