Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don bai bari na shiga
gidan ba balle in dauki wani abu .
Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan kaya ka saya na juya na
bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode.
Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin tsakiya zai zauna a cikinsa
shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a cikin tsarguwa da hakan da yayi min din.
Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan ba naga kina
kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo muna fitina ko tsegumi ki barshi
can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna mana don me zai nufo nan gidan haka kai tsaye.
Shiru nayi ina nazarin zancensa a kaina tabbas gaskiya ya fada don ba mutanen arziki bane alheri sai ya
zama tsiya a wajensu.
Zama na gyara ina fadin ni naga ba zaizo nan mu koreshi ba ai yaya tunda yazo din sai ayi hakkuri don
kai ba za aga laifinka ba sai nawa tunda yariga da yazo kayi hakkurin hakan don Allah.
Bai kira yace dasu yaron na gidansa ba hakan yasa hankalinsu ya tashi lokacin da uwar ta bugo waya
tana tambayan ko yaron yazo nan ?
Duk hankalinsu ya tashi haka ba wanda yai dabaran kiransa ni dai ganin har magariba banga yana
shirin komawa gidan can ba sai mamakin hakan da zaiyi nakeyi a zuciyana.
A bangaren yaya barakha an nemi Aminu a nan gusau ba a sameshi ba har washegari hakan ya daga
mata hankali ta bugo waya nan zaria tana tambaya ?
Mama Dubu hankalinta ya tashi har dare suna buga waya gusau din suna tambaya ko an ganshi sai ace
har yanzu dai ana nemansa ba,a sameshi ba.
Ga jafar da suke sa ran shigowan gidan har goma na dare ba labarin shi hakan yasa mama sa a duba
mata ko yazid ya dawo aka dubo yana gida.
Da kanta taje part din yazid din ta sameshi tana tambayan malam fa don sunan malam Jafar marigayi
da sukai jahadin da,awa a cikin kasa yasa duk wani Jafar yawanci ake saya sunan nasa a cikin girmamawa
ga malam Jafar din dake tashe alokacin.
Yagane dan uwansa take tambaya donshi ake kira da wanan sunan na malam din take fadin malam fa
yace yana lafiya ta amsa da aina sani tunda naji shiru ?
Tambayanka nayi har yanzu bai shigo ba kai gaka ka dawo gida ko da kansa zai dawo yau ya kamata
ace yana nan ga zancen yaron nan da har yanzu ba a gansa ba ko za ayi wani abu a nan ?
Mama J aiba zai dawo gidan nan ba yau ban ma tsamanin nan kusa gaskiya kin ga a yan kwanakin nan
yadda ya koma kuwa ?
Dakata don Allah nasan duk bakin ku daya shi zai fara yace bai dawowa gidan nan a yau da kuwa na
sameshi a can naci masa mutunci.
Acan kikace mama kwarai ko kana tsamani ba zan iya bane kagani ya dan dubeta ya kawar da kai ya
soma tafiya yace zaki iya masa hakan nasani to kira min shi yanzun nan .
Ko kaje kazo min dashi yanzu gidan nan yanzu fa mama gomafa ta shude da nan da can ai dayane
nagani meye ruwanki da zamanshi can din ke ?
Yazid kai abin da nace kada ranka ya baci dani a wajen nan Ok yayi bari na kirashi naji in zai dawo sai
naje na daukoshi din.
Ya kira wayansa bai shiga ba haka yasa ya fada mata gaskiya itama kuma taji matar computer tana
sanar da hakan a wayan .
To kinji wayansa a kashe yake yanzu yaya ke nan kaini gidan idan ku ta shanye ku aini bata shanyeni ba
har ita karamar yarinyar ta isa ita da masu taimaka mata din kar nake kallonsu.
Bai haifawa jikokin fulani diya ba balle suzo su mallake min yaya da raina da lafiyana ina kallo shi kuma J
far din zaizo ya sameni ai zai jini.
To bari in shirya in fito ya fada ya koma ciki itama ta juya zuwa dauko hijabinta don tafiya ya shige ciki
yana dariya.
Har ta fito yazid din bai fito ba nan kofa ya tsaya yana kallonta yana gyara rigansa hakan yasata daga
murya tana kirasa a hasale tana fadin zata saba mashi fa idan bai fito sun tafi ba.
Iya dake cikin tana jin sautin muryan mama ta fito tana fadin lafiya anga yaron ko don tana cikin
damuwan rashin ganin yaron a lokacin.
Karan budan kofan da iyan tayi yasa salima dake kwance tana charting ta biyota tana fadin iya lafiya ?
Iya sai fadi take anganshi ko cikin rawan jiki a lokacin Yazid ya karaso yana fadin mama shiryawa fa
nakeyi don nayi shirin kwanciyane kika zo .
Nace kunga yaron ne iya ta sake fada karo na uku ba a ganshi ba iya gidan Jafar zamu mama ta dauko
shi ya dawo nan.
Jafar kuma ta daukoshi kamar yaya iyan ta tambaya to ni dai tace in kaita ta daukoshi can din wai nan
ya kamata ya kwana a yau ?
Dubu iya ta fada cikin mamaki tana kallon yar nata da wani irin kallon dake baiyana mamakinta karara
ga yar nata dake wanan magana.
A,a iya rashin hankali yake son ya tafkawa mutane waishi ga salamame zaije gun yarinyar nan Rahama
ya tare don rashin hankali ya daukarwa kansa zunubi.
Zunubi a wajenwa Dubu wajen ki ko wajen wa zai dauki zunubin da kike fadi dubu ?
Dubu dubu kanki daya kuwa da yaron nan yayi wata da watanni a gidan nan meyasa bakice a kwashshi
a kaishi can ba lolacin kada ya kwashi zunubi sai yanzu ?
Iya wanan ai lalurane itama din ai tana tare dashi a nan kuma, zaman nan din aida ita akayishi da yanzu
zatace a maimaita mata hakan da akayi ?
Ta fada maki cewa sai an mata maimaicin hakan a gidanta wai dubu meke damunkine haka wai ?
Kai Yazidu koma dakinka ka kwanta don ba inda zaku a cikim daren nan da wanan rashin hankali na
uwarku don kina mara hankali zaki gidan surukarki da wanan zance na hauka idan kinje kice masu me
yanzu ?
A,a iya ki bari nayi maganinsa tunda yana ganin ya isa ne yanzu har zai kwashi kafa ya koma can ya tare
bai fadawa kowa ba ?
Kamar yaya Dubu don ni ban fahinci wanan rashin hankalin naki ba har yanzu waiko dubu akwai
hankali akanki kuwa ?
A fahintana Dubu kamar kishi kike da yaran nan fa don abin nan da kikeyi bana kai sake bane dubu ban
taba gani ko jin irin wanan rashin hankali naki ba gaskiya.
Iya yanzu sai a kyaleshi yaeinya karama tana juyashi ana kallo ba a dauki mataki ba jinyar da tazo nan
tayi nasa ai yan uwanta dashi ta cuta ga hakan ?
A,a ba juyashi tayi Dubu mulkeshi tayi iyakar juyawa dai ko aiki ya sameki babba idan kikace kishi zakiyi
da matan yayan ki ?
Duniya da mutanen cikinta suna shirin maki dariya jeki dan mutuncin dake gareki a idanun yarinyar nan
ya zube aikin banza aikin wofo kawai da rashi kamun kai ?
Kai yazidu koma wajenka ka kwanta ba inda zaku ni naga rashin hankali yau a filin Allah ashe ke ba
zancen yaron nan daya batane ya dameki ba shirmenki kike a zuciyarki ?
Yau ni naga hauka na rubutawa a jarida Dubu baki tsoron bakin duniya ko wanan halin da kikewa
yayan mutane ya tambayeki nan gaba ?
A,a iya don Allah abar zancen nan baikai har kiyiwa yaran nan baki ba a gareni yaje ya zauna tunda ya
zama sallamame a wajenta.
Karamar yarinya kamar wanan yau zata juyawa Jafaru hankali yana wanan abin a gaban kowa iya dole
inyi magana abin yayi yawa dama an fadi matan fulani haka suke idan sun shigo waje.
Kai Yazidu dawo ka kaita ta dauki matakin da zata dauka iya ta katse mama din dake magana ta juya
tabar wajen yazid kuma bai ko juyo ba ya shige part dinshi.
Washegari da safe kodana tashi kamar kullum na hada mai abinda zai rike mai ciki kafin mu gama
breakfast ya dan kwanta.
Hakan da nake mashi ba karamin kara mai lafiya yake masa ba ga sunan Allah da zaibi jikinsa da ruwan
zamzam ga kuma kuzarin da jikinsa zai dauka yana daga cikin abinda Yazid ya hango na annuri a garesa
yake fadin yaga ya canza mashi lokaci guda.
A gurguje nake aikina ba don wani abu don kawai nasawa raina cewa suna iya zo min gida a ranan don
Aminu dake nan wajen mu.
Mun gama na jera mai a kasa don na fahinci a yanzu yafi son ci a kasan don kamar baijin dadin zama
saman kujera yaci abu a yanzu da baida lafiya din nan.
Na gama na shirya kaina na umurci biba data jetayi wanka har tace ta dauki abincin Aminu takai mai
ne da sauri na juyo nace a,a ki barshi nan kitchen har ya shigo.
Ba son komai nace haka ba saboda ban manta wani case din daya faru akan wata uwa dake tura yarta
kaiwa saurayin gidan abinci ba.
Amma haka mutumin yayi amfani da wanan daman ya batawa wanan matar yarta akaita case din
karshe dai an cuci yar da uwar don har yakai ga dirkawa yarinyar ciki dole aka haifi dan hakana kuma
yarinyar karamace sosai a lokacin.
Wanan ya tsaya min a rai yasa nake kafa kafa da yar mutane ban yarda ko maigadi tayi wani dogon
mu,amula dashi iyaka gaisuwa a tsakaninsu.
Gareku mata wanan abin ya faru da gaske wallahi mutum koke kika haifeshi yanzu ya zama dole a
gareki ki saka ido ga mu,amulansa na yau da kullum Allah ya tsare ya kare amin.
Wasu dogon riga na saka a jikina _onion_ colour da adon zaiba har kasa anyi rigan mai dagware a
sama kamar alkyaba yana daga cikin dinkin da anty salma tayi min na aure a Abuja.
Zaune na samu yaya a dakin na shigo ina fadin ka tashi ashe yake fadin yazid ya tayar dani da waya wai
yaron nan sun dauka ya batane ashe basu san yana nan ba ?
Aminu na fada cikin mamaki yace shifa kiji ba yace muna ya tafi can ba ashe karya yakeyi ke nan nan
yayo direct wajen mu.
Ikon Allah amma cewa yayi ai yaje ya samu baka nan ace kana nan yace karya yakeyi yanzun ka fada
masu yana nan dai ko ?/
Na fada masu ya fada a sanyayye nasan zasu shigo yanzu ai tunda sunji yana nan amma Aminu bai
kyauta ba daya dagawa mutane hankali haka ?
Bar dan iska kilama abinda ya fada karyane barshi kawai bari suzo din muji ai nasan za a fada masu
abinda yayi ya gudu nan yau din nan zai bar min gidana.
A,a yaya na fada da sauri ya katseni cikin tsawa da fadin ke karki tsoma min baki cikin maganan su ki
barni kawai dasu.
Nayi shiru kafin nace wanka zakayi ke nan yace haka naso na mike zuwa bandaki na hada mai ruwan
wanka ya mike ya shiga saida ya gama na cude mai jiki da ruwan addua ya saka kaya muka fito falo.
Mun zauna ke nan na zuba mashi ya fara ci biba tana gefe daya tana cin nata don sosai muke sakewa
da yarinyar harshi sukan dan taba hira wani lokaci da ita.
Muka ji sallaman Salima shigowa gidan ashema dukkansune tafe sai Asmau ce sai matar Yazid suka
bari a gida lokacin.
Ban daina mika mashi fruit din dana gyara ya zama juice ba da nakeyi na amsa sallaman nata ba tare
dana juyo ba suka karasa shigowa gidan gaba dayansu.
Nagama na dago ina fadin sannuku da zuwa ina kwanan ku a cikin jam,i bansan waya amsa ba ko
wanda bai amsa ba a lokacin don na basu bayane ina zaune amma naji muryan yazid.
A,a a a mutumina inafa zaka koma gida wanan riritakan da yar nan keyi shine ka gudu ka barni ba azo
cin dadin amarcin dani ba ?
Iya ba gaki kinzo ba yanzu saiki zauna muci dadin yanzu kada in kwareki kaidai tunda ina da rabo a cikin
na yanzu sai in zauna inci amma zan barwa amaryaka aronka kwana biyu ai don tasan ina da kara amma
fa a tuna damu muma kada a shagala suka kwashe da dariya.
Ai fakaice baiyi iya gara ki fito mashi fili tasan yabar wasu a gida ba nan bane kawai gida a gareshi don
shi naga hanyar konewa ya zaba yanzu.
Bani ganin hakan cikin zuria,ata insha Allahu daidai lokacin namike a kusa dashi zuwa gaban mama na
durkusa har kasa ina gaida ita.
Kamar dole ta amsa min ba kin dawo lafiya na juya wajen kawu na gaidashi sai iya dake fada na rike
hannunta sai lokacin ta dakatar da zancenta take fadin.
Ke dai yar nan kin dawo lafiya yaya kika bar yan gidanku duk suna lafiya dai ko naso nazo banda wanda
zai kawoni in maki sannu da zuwa.
Iya ba komai na fada ina mikewa tsaye na nufi hanyar dakina muryan ya J naji yana fadin ina kuma
zaki ?
Daki zan tafi har ku gama na bashi amsa sai yace abincin fa wazai ban kizo ki zauna muci kema baki
karya ba ai bari dai ku gama na fada.
Kizo ki zauna nace me zamu fada wanda ba za aso kiji ba iya na fadin zo ki zauna abinki ai ba komai
zamuyi ba ballema ina zata iya ?
Yadda yake magana hakan yasa na dawo na zauna a inda na tashi duk suka zuba muna ido gashi sai
magana yake min a cikin rashin damuwa da suna wajen a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/24, 10:20 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Aminun yana inane mama ta kawar da shirun dake falon kaina a kasa ya J yace da ita ga uwarshi nan
itace ta bashi mafaka a nan .
Don ni tun jiya da yazo gidan nan ban yarda dashi ba koransa nayi don yadda yazo min nan a gigice sai
hakan bai kwanta min ba.
Itace ma ta saukeshi ta bashi wajen kwana a nan gidan dan idan tannei zai koma tun a jiyan ai da bai
kwana a gidan nan ba .
Wai dama ita Rahama tasan yana nan shine bata kira ta sanar da mutane ba don isa kuma ta ajeshi
tabar mutane suna wahala hankali tashe ?
Ke zanci abu kazan ubanki wajen nan ke meyasa kike yar iskane wai kamar kinfi kowa baki ban hanaki
idan manya suna magana ki tsoma baki a ciki ba ?
Me kika dauki kanki ko kin fi wanan biyun ya nuna salima dani baki da suka kama kansu agaban manya
basuce komai ba ?
Na dago kai nace ya Yazid don yaya ya kori Aminu ni sai na yarda ya bar nan din a yadda na ganshi
nasan inda zai nufa kuma idan ya bar gidan nan ?
Kwarai kuwa kedai yar nan kinyi daidai haka ake son macen arziki ta kasance dama ta kula da mijinta
da kowa nasa wanan shike nuna halin alherinta .
Bar sakaran nan da bata san komai ba sai rawan kai da iya makircin banza meye na ganin laifin yar
mutane a nan daga ta taimaka muna da bata rikeshi ba yanzu har muzo a sameshi nan.
Bakin saratu shi zaija maki matsala bansan irin bakin wanan yar ba a rayuwana yaron nan a nemansa
an kuma ganshi a inda ya dace .
Barta kawai dai idan itace mai mugun halin nan irinsune masu iza dangin miji nisa da dan uwansu
wanan zata iya haka tsab yazid ya fada.
Yanzu ina Aminun yake mama ta sake tambayan nasan don Yazid ya katse zancensane kan yarta ta fadi
hakan a lokacin.
Biba je baya ki kira yayanki Aminu kiyi maza ki dawo don Allah kada ki tsaya da sauri Biban ta fice don
kofan a bude suka barshi saida ta dawo ta rufe tana fadin gashi nan zuwa anty.
Bai jima ba shima ya shigo da sallamanshi yayi kyau a cikin kanyan dake jikinshi duk suka juya suna
kallonshi sai yayane tun bai zauna ba yake tambayanshi.
Dama da kaya kazo shine ka shigo min gida jiya da shigan iskanci kamar dan ginan zinari mutsu mutsu
dakai ba dadin gani.
Da sauri yaron yace a,a uncle mummy ta ban kudi jiya naje nan kasa na sayo kayan nan ya fada yana
kallona daga inda nake zaune nace kudi na bashi nace ya sayo yan suturan sauyawa don yadda yazo.
Ba dole ku gamshi hakana ba uwarshi tace ya dawo daga wajen ball ne ai ya samu a na rikicin ya
kwaceta sun tarar mata kamar jaka zasu kasheta ya bambara uban daga shakar da yaiwa uwar shine
haushinsa da dan don me bai bari ya kasheta ba ya bambarashi .
Allah ya saka maki da alheri yar nan aiko hakan kin wadatar wallahi angode kinji kinyi komai wallahi
iya ke fada min hakana.
A Rahama ai dabance gaskiya ni halinta yana mun sosai wallahi wai har wanan sakaran zatawa mutane
maganan iskanci don samun wuri.
Tayi mana tunda ta sabayi tana cin banza naso ai ace bakai magana bane takai karshe a dazun din naci
muruncin ta idan ba Rahama din datayi masa haka ba ni yaushe zan tsaya kallon dan Barakha yanzu ?
Kallom J din kowa yayi da yake wanam kalaman nasa yace kwarai ko a zaron ku