Chapter 70 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   70 / 101

207K to 210K   out of 302.2K words

daga sosai ina take tazo ta gyara dakin a mayar dashi cikibinyaso mu
muyi amfani da dayan dakin shike nan aga abinda Allah zaiyi kuma.

Tun wanan ranan aka dauke yaya a falon zuwa dakin wanda hakan yayi min dadi sosai don Allah ya
gani zamanshi a falo sam bai min ba dama don ba dama nayi masa wani abin idon tsofin yana kanmu
saidai yayi ta faman bin na da kallo duk inda na gilma da idanu.

Haka kuma duk wanda yazo iyakansa falo yanzu ba kowane suke yarda ya shiga wajensa ba sai su
shakikyansa kadai sukan shiga su jima a ciki wani lokacin tare dashi ni kuma in samu barci koyin wani
abin.

Na samu daman zama dashi a yanzu nayi maganan da zan mai duk daba amsa min yake iya yiba haka
dai zai kafeni da idanuwansa .

Bani kadai ba dukkan mu matanshi muna shiga gunshi mu kebe dashi na dan wani lokaci za,a zauna
nan tare dashi koda barci yakeyi saina fahinci wanan tsarin na mama bani kadai yaiwa dadi ba ashe
yanzu.

Abin dana fara kula wata rana ina zaune da dare bayan nagama shafa mashi magani zamu kwanta sai
kawai tunane ya dibeni sai kuka na fada jikinsa in kuka a hankali kamar a mafalki naji hannunsa na
kadawa a hankali yana dagasu zuwa kaina.

Innalillahi na samu ambata tare da katse kukan da nakeyi ina binsa da kallo amma ya kasa abinda yake
son yi din don hannun nasa ya kasa daguwa yadda yaso din.

Naja bakina nayi shiru daidai a yanzu nakan kama yatsunsa din ina masa massage dinsa har dana
kafafu da duk inda jijiyansa suke kafin mu kwanta .

Cikin irin haka ranan banyi aune ba su mama tare dasu yaya Habu da sukai tafiya suka shigo suka
sameni ina masa hakan.

Muryan Yazid ne ke fadin gaskiya wanan kina da fasaha sosai nayi wanan tunanen ince ko za a dinga
dan masa hakan sai gashi ashe kina masa hakan zai taimaka sosai wajen karfin jikin insha Allah.
Ni dai ganin sun shigo yasa na daina na sakeshi na koma gefe na rakube can dai na mike na dawo falo
na samu iya zaune ta idar da sallah muka dan fara hira jefi jefi.

Hiran dai bai wuce akan jikan nata ba take tambayana ko biba ta kara shigowa nan nace ninace ta daina
zuwa don ranan da sukazo kuka tayi sosai har saida ta kwanta ciwo hakama yar uwarta da sukazo tare
wai iskanta ya tashi itama da suka koma gidana a ranan .

Ba kaji ba iya ta fada ai duk wanda keda iska yaga jafaru yasan da iska aka hadashi bashi kadai bane don
irin yanayin da yake ciki duk mai hankali zai gane hakan.

So sukayi suyi mai farat daya Allah bai yarda ba shine suke wahalal dashi haka insha Allahu Allah yafisu
yafi sherinsu ai kinga har yau kawun ku ya kasa zuwa gidan nan .

Da yasan ba komai aida tuni yazo gidan nan da fada tun ranan yace anwa yar gwal dinsa kazafi yaciwa
mutane mutunci haka itama kinga ba wani mataki aida ta dauka ga abinda yaron nan Yazidu yai mata.

Nan suka fito suka samemu muna maganan mun dan jima suna zancen kafin su fita muka rufe part din
namu yaya ibrahim shike kwana a falo yanzu.

Mu kuma muna daga ciki sai daga baya bayan yan gidan su Saiba sun kara zuwa dubanshi sai ga zance
ya tashi saiba din taje wajen mama wai suna son a basu hakkinsu suma su dinga kwana dashi kamar
yadda nakeyi.

Mama dubu din tazowa su mama da iya da zancen iya ranan tayi fada sosai take fadin na kula dubu
kema ba lafiyan yaron nan kike soba ?

To anki a raba kwanan su mayar muna da jinya baya muna ganin sauki suja muna hasara ba za a yi
hakan ba data zauna dashi a baya wata uwar take tsinana masa a lokacin banda sharan barcin ta da
takeyi a nan saman dogon kujera.

Dole dai akaci gaba da hakan don dai kada tsegumin yayi yawa na fara komawa gida ko gidan yar
uwata in zauna sai dare zan dawo gidan.

Ma,ana dai su, su wuni dashi da rana ni kuma in kwana dashi da dare saiya kasance wahala da
dawainiya ya fara komawa kan tsofin don su zasuyi ta fama dashi hakana har zuwa lokacin dana dawo.

Suko matansa excuse din girki ko kula da yara suke bayarwa abindai ba dadi wallahi don gaskiya bai
cancanci haka a garesu ba za ace dai ina fadane kawai don in yaba kaina in bata su gaskiyan zancen ke
nan nake fada a yanzu.

Burin su a fili yake shine yaya zai mutu su kuma suci gadonshi don takan ce kura da shan bugu gardi da
kwatan,kudi.

Gara dasu dai kome za ace ace su dai keda riba tunda su suka haifa sune kuma keda Jafar aje ayi ta
aikin wahala din don neman yabo .
Alkawari nayi insha Allahu ba zan kara biyewa shirmensu ba idan sunayi ko da dangwarana mace
zatayi matukar muna cikin wanan halin na rashin lafiyan mijin mu.

Gata da wani hali kamar tashin kauye da yawan habaici da sake magana kowa tana iya yiwa hakan
abindana fahinta ke nan yasa naba banza ajiyanta yanzu.

Ni kadai zan iya cewa ga cigaban da aka samu yanzu kan matsalan nashi saidai ban fadawa kowa hakan
ba har maman tudu dake kula dashi din.

Don ita mama dubu iyakarta ta shigo ta dubashi inda wani shawaran da zasuyi kuma zasu zauna suyi a
kan matsalan iyakartavke nan tunda mama ta nuna ita din uwace gareshi.

Ankai yanzu yana dan iya daga hannu tun iya iya motsawa har yakai ya fara dagasu yana dan juyawa
saidai ba bakin magana gareshi har lokacin.

Anty Salima ko nafisa sai idan sunzo gidan zakiji bakina ko in muna tare da iya wani lokacin tare da
salima din mukan fita muje can gidan mu wuni.

Ranan ma mun shirya din zamu fita don na kwana biyu ban leka gidan ba yasa nacewa mama din zanje
in gyara gidan tace ya kamata shine muka shirya zamu tafi din.

Suna falo zaune a lokacin dana fito duk daba wani shigar azo a ganine a jikina ba amma ta dago kai ta
kalleni ta kawar da kan nata gefe daya.

Tsanar da tayi min take jin yana karuwa a zuciyarta duk zata kalleni takan ji kamar ta daina ganina har
abada a duniyan nan don bata kaunan ta bude ido dai ta ganni saboda haushin da takeji nawa din kishi
ke nan.

Nima dai din ina jin haushin ta saidai baikai nata ba don ma taki zaman lafiya danine ya kawo hakan da
zan iya rufe ido in kawar da duk wani kishinta da nake ji a raina.

Kishi mukayi da itakata kwashe ranan ta zauna ta kwashe min kaina da tsiya da komai haka na zauna
tayi min kitson a kaina sai kusan goma muka dawo gida.

Tunda muka shigo da sallama naga irin kallon da mama tayi min nasha jinin jikina tana zaune tana cin
abinci muka gaidasu nake tambayan iya tace tana ciki.

Na mike zan shiga naji ta kirani tana fadin Rahama ina kuka shiga haka dan Allah keda kike da mara
lafiya ki bar gida don gudun bacin ran wasu ba zaki dawo gida da wuri kiga halin da mijinki yake ciki ba ?

Yau jikin nasa da zazzabi ya wuni saida likitanshi yazo yai mashi allura ya samu dan barci yayi amai
yakai sau uku gashi kin barmu da tabararrun nan a gida sai shirme suke muna sin kasa anyana komai
akansa.

Da sauri na fada dakin ban tsaya jin karasan zancen ta ba yana kwance yana barci nagaida iya ina
karasawa wajensa na dan dafa wuyanshi da hannuna.
Zubur ya bude idonsa ya sauke min yana kallona sai kuma ya mayar da idanun nasa ya lumshe a hankali
sannu nayi mai na zauna a kusa dashi hakan baisa ya bude idon ba.

Sai lokacin muka gaisa da iya dake zaune a kasa tana lazumi take fadin yau jikin nasa ya tabu bayan
fitan ki masassara ya kamashi.

A hankali nace haka mama ta fada min yanzu amma da sauki ki daina wanan fitan don kawai kina
gudun zargi ko wani abu yau ai uwarsa taga amfanin ki don kwasan amaima jidali ya zamawa wavyancan
balle kula dashi din kinga ai tun kafin magariba da suka gudu basu leko ba .

Duk yadda kikayifa sai an zageki wasu kuma su yabaki ki daure kici jerabawan duk nan mun san dalilin
dake saka kina wanan fita din hakan kuma ba wankeki zaiyi daga zargin kishiya ba tunda anki mata yadda
take so.

Na dan waigeshi yaban tausayi matuka na mike na kwabe kayan jikina dakin da akace yayi ta aman
nashiga gyara na tsabtace shi na saka kamshi.

Har ban dakin saidana gyaro na koma dayan dakin da suke amfani shima na gyaro masushi likitan ya
dawo tare da Yazid sun kara dubashi sai lokacin nasan ya daao garin .

Sun dan jima suka fito na samu nashiga wanka na fito na zauna na dan gyara jikina na saka rigan
barcina falo na fito na hada mai shayi mai kauri koma dakin.

Cikin dabara na samu na tayar dashi na bashi yasha saidai na kula kamar yana fushi ko kuma yanayin
ciwone hakana yake damunsa oho ?

Saida kafa ya dauke na rufe part din don mama ta fada min ya Ibrahim bai nan yaje Abuja da safe cab
zai kwana kuma.

Na jima zaune bayan na fafa mashi magani ina mashi addua nakan koma saman kujera in kwanta
amma haka kawai nace na kwanta a kusa dashi ranan don yanayin da yake ciki din.

Nakai kamar minti goma da kwanciya a gefesa kamar a mafalki naji saukan hannunsa saman jikina
saida na dan zabura nayi mamakin jin ya rikeni a ranan.

Cikin fargaba nake fadin yaya kaine kuwa ba bakin magana kai kawai ya daga min bai iya ban amsa ba
hamdala nayi a zuciyana jin yadda hannunsa ke motsi a jikina din.

Sannu a hankali naji abin yana rikida zuwa wani yanayi don ya wuce tsamanina a hankali na runtse
idanuwana acikin fargaban abinda zai iya faruwa a lokacin.

Ba lakka bane a jikinsa ko wani kuzari don haka na kyashi yana abinda yake tsamani zai iya a lokacin
amma ya kasa sai ajiyan zuciya zuwa can kuma bayan mun rugume junane naji saukan hawayenshi a
saman jikina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[4/18, 10:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣1️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Kusan hakan yake faruwa a tsakanin mu tsawon wata daya saidai na kasa fadawa kowa wanan maganan.

Wa zan tunkara da wanan zancen nace ga abindake wakana a tsakanina da mijina alhalin yana kwance
haka sharkaf dashi bai ko wani dogon motsi balle magana.

Har abin yakai ya fara damuna da zaran dare yayi banda katabus dashi ya dinga bina da ido kenan
harsai yaji mun hada jiki dashi a sannan zai dinga jero ajiyan zuciya yana saukewa a fili.

Dole zan biye mashi da abinda yake so na fannin wasannin aurataiya a tsakanin mu har zuwa lokacin da
naga ya samu gamsuwa na jaye jikina daga nasa in koma gefe ina hawaye a cikin kunci.
Ganin dai a kwai sauki sosai dake shigansa na gane hakan kuma nadaga cikin karuwan samun
kuzarinsa a lokacin don yakanyi barci a daren da duk hakan ya kasance a tsakanin mu sosai.

Washe gari nakan kula da fara,a a fuskanshi da walwala idan anyi magana zakiga yana dan murmushi a
gefen fuskanshi sai gashi kwatsam naji suna zancen cewa zasu fita dashi kasan wajen.

Nafi kowa sani a yanzu ciwon yaya bana asibiti bane ciwone dake da alaka da jinnu ko sihiri da akewa
mutum wani lokaci.

Ranan babu kowa nake fadin mama niko sai naga da an dakata da wanan fitan da za ayi da yaya a
yanzu don yana samun sauki sosai kawai dai kamar baison a gane hakan ne a yanzu.

Nayi tunanen hakan Rahama ina kula da kusan hakan a tsakaninku saboda a yanzu kin rage yawan
tashin hankalin da kika shiga a baya game da rashin lafiyan nan a yanzu duk babu shi sosai wanan yasa
na mayar da hankalina a kanku dole nasan akwai dai ?

Dan murmushi na sake a gefen fuska ina kawar da kaina gefe take fadin ai bari almuri zan samu lokaci
nayi magana dashi shima sai kuma ta koma tambayan .

Yanzu wani cigaba kike gani ga lamarin nasa wanda ke nuna akwai sauki sosai ga laluran nasa don
hakan ke nuna alaman lafiya idan ya fara wani abu ?

A zuciyana na amsa da abu ko mama tunda ya iya raye dare daga kwance yake iya biyan bukatanshi
nada namiji a hakan amma a fili cewa nayi da ita.

Yanzu mama yana iya daga hannunsa wani lokaci har yana kokarin yunkurawa ya tashi zaune ko yayi
kokarin kiran sunana idan yana son wani abu.

Masha Allah koda ya boye hakan ba laifi bane don zamanin nan da muke ciki wanda baka zata ba
bakayi tsamani ba shine zai ha,ince ka banga laifinsa ba idan har ya boye hakan gare mu yanzu.

Yanzu matsalan shine ni kinga kamar sun ma fara gajiya da nine nan a yanzu yadda dubu da
sarakuwarta ke nunawa zamana daku a yanzu yakai masu ko ina don na tare gaba na tare ba a garesu.

Matsalan dai tasan tun Alh yana raye irin dokan daya kafa muna a gidan nan da kuma irin hadin kan
daya sanya na dole tsakanin mu.

Aida dubu nada hankali da bata karbe zancen da duk wani laluran jafar da iyalinsa a hannuna ba din ko
shi dan dakinane kamar yadda kikaga Nafisa yar dakinta a yanzu tun Alh yana raye irin dokan daya kafa
muna ke nan .

Idan ke mace zaki yaye danki zai kira wace zaki ba yayyen dan haka kuma rikonsa zai koma hannunki ke
nan har girmansa.

Sai bayan rasuwan Alh ne kan mu ya dan rabu tun wajen robon gado da kowa ya nuna nasa halin akan
abinda Alh ya barmu dashi.
Yanzu da kokarun mijinki yayi dabaran dawo da hadin kai a tsakanin mu donshi haka halinsa yake
kamar na mahaifinsa .

Shigowan matan su yaya Auwal ya katse muna hiran mu don haka mukan zauna wani lokacin muna
hira tsakanin mu saboda shakuwa da ita da yanzu nayi sosai takan ban labari irin na kunne ya girmi kaka
a yadda na kula zamane akayi a baya irin zaman mumuke a tsakaninsu.

Irin a fili ana son juna ana nuna babu matsala amma ana kishin mumuke irin zaman kakanin mu da
iyayyen mu da ba a gane kan gida din nan .

Anan falon aka zube da matan su yaya din ana hira lokacin Iya da matar Yazid suka shigo falon sam
bata da marmari don bata sakin jiki da kowa sai iya da mama kadai take dan zama dasu bayan hakan ko
yaushe tana part dinsu bata shiga mutane.

Zakice tana gudu mutane fuskanta kuma sam ba fara,a acikinsa matan gidan suyi gulma sun gaji sun
saka ido don sun fahinci itama ba kanwar lasa bace ashe.

Bayan sun gaisane da iya suke tambayanta ko itace matar Yazid din iya ta amsa da fadin itace to bai
zauna ba balle ya kaita wajen yan uwa a cewan iyan.

A nan muka wuni dasu abinda yasasu tafiya yunwa don an jima ba a gama abinciba kamar kullum haka
kuma da za a kawo aka zubo dan kadan waina mu dukan mu part din ke nan.

Ina jin lokacin da mama takece masu suje gida su nemi abinda zasuci don wanan ma komu ba zai isa ba
balle su din kullum haka ake abincin kamar na rowa a kawoshi bai isn mutane saukin abin ma yanzu wani
lokaci ita nan takan yo muna dabara daga can gidan ta idan ta tafi shi muke samu muci.

Da zasu tafi na yafa mayafi na rakasu har bakin get amma saida suka shiga suka sallami mama dake can
part din ance wai tayi bakine bandai san ko suwaye ba.

Sun tafi na koma don in gyara part din na samu Asmau da yara sun shigo muka gaisa na gaida ita da
aiki take fadin tun safe tana tsaye bata huta ba yasa wai bata leko ba.

Dakin na fito na barta da mijin don in suna ciki nakan dawo falo ko dayan dakin in dan kwanta wani
lokacin kuma inyi barcin gajiya .

Hakan ne ya faru don ban tashi ba sai wajajen karfe biyar saura na tashi nayi sallah na fito na fara
gyaran falon har lokacin suna ciki da mijinsu da yaransu na dai shiga mun gaisa dasu din na fito naci gaba
da aikina.

Nayi mamakin rashin shigowan mama a wunin ranan don tun safe data shigo bata samu dawowa ba
wai tana can tare da baki ake fadi ashe ba wasu baki bane ita da yarantane a lokacin.

Saida dare iya bata shigo ba naji mama na fadi cikin kashe murya yau akwai abinda dubu da yaran nan
suka samu don tun safe suke hayanita tsakaninsu.
Jin hakan yasa na dago na dubeta take fadin kinsan mu ba a son mu sani don kamar makiya ake daukan
mu duk da iya ta dan kyankyasa min .

Wai yaran nan matan Jafar to har dake dai ke nan ake nufi ko sunce Habu da yazid din sun dulmuye
dukiyan dan uwan nasu suna ci su barku a haka a kula daku dashi.

Ko ita mahaifiyar taku ta kama masune shine habu kin sanshi ya dawo da komai na jafar da yake
juyawa yanzu yace ya daina kula da dukiyan a baya ba an taba wanan maganan ba yanzu kuma sun tayar
da zancen ke ban kuna nake tambayan ta ?

70 / 101