Chapter 94 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   94 / 101

279K to 282K   out of 302.2K words

mu har da
asibiti take adawa akai wai da gangan Rahama tazo ta kwanta akai mata aiki.

Don kawai a kashe mata kudi da ganganfa mama ta katseshi da fadi yace wallahi mama ita kuma
shashashan nan mai bakin kishi ta dora nata sai Asmau ce tayi min Allah sauwaka kuma sukaga laifinta.

Ita dubu har abin yakai haka gareta to Allah ya sauwaka don abin nata sai addua iya fa ta fara ban
labari dazun ashe ta fada maka hakan kaima Allah ya sauwaka toh.

Mama ni habu zai hanawa kudi sai wani banza can na waje bare aboki dana taimakawa taimakon da
baikai nasa danayi mashi ba shine zai dauko kudi ya ban masu yawa inyi lalurata dashi.

Amma ko habu bai kyauta ba barshi insha Allahu ko talauci zai kasheni bani kara tambayanshi komai a
duniyan nan in Allah ya yarda.

Habu ko bai kyauta ba ko ana mashi kirarin rowa har dakai zai hada yayiwa rowa a duniyan nan meye
bakai masu ba a rayuwansu kaf dinsu gidan nan.

Barshi babu komai mama ya fada cikin wani irin murya ina kwance ina jinsu ya ban tausayi a yadda yake
fadi yana bata labarin yadda yabar mashi aikinsa na farko na mai da habun keyi yanzu .

Haka kuma suka kama dukiyansa suka durmuye dashi dasu kawu har kayansa suka salwanta baiyiwa
kowa korafin hakan ba kuma.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/6, 9:43 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



9️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Kwana biyu muka samu sallama dama da iya da mamane sai salima muke zama asibitin da inna dake
zuwa itama ta wuni damu wace a yanzu na fahinci taga kamar mama ta karbe matani don da farko itace
muke tare da ita.

Amma zamanmu jiyar yaya dasu maman tudu din sai muka saba sosai da ita fiye da inna duk da
dukkansu suna da halin sukan mama dubu da iyalinta a gabana saidai ina nuna masu hakan bai damuna
don ba halina bane zama yi da mutum.

Wanan kuma nasan cewa halin kishin mu na matane yasa suke hakan tundai mama gaskiya tana yawan
magana da korafi kan halin mama amma wanan matsalansuce ta manya ai bai shafeni ba amma kuma
tana da fadin gaskiya dasa mutum a hanyar da zai fusheshi.

Din haka koda muka dawo gida mama tudu itace ta biyo mu zata zauna dani ke nan yan kaduna sunzo
tun washe garin haihuwan sun dubani hakama Yanda a ranan da dare tazo ta dawo kuma washe gari har
dare tana wajena kafin ta tafi.

Duk da bai fadi ba kana kallonsa kasan akwai damuwa a tare dashi a yanzu ba lokacin da zai iya fada
min ko maye don ko yaushe muna tare dasu mama idan zai shigo wurina.

Yayi kokari sosai zamana asibiti haka abokainai da yan uwa suma sunyi nasu rawan ganin a lokacin
gaskiya gashi wanda duk yazo da alherinsa mama ke karba idan yazo ta mika mai da farko ya nuna
abarmin aimu aka ba.

Amma mama ta nuna mai ai damu dashi dayane don haka ya karba ya rage lalura dashi ga asibitin na
kudune sai demand suke saka mashi na kawo kudin kaza kawo kawo dai a asibitin har aka sallamo mu
muka dawo gida.
Ina barci da dare ranan yaya habu yazo dubamu ya jima suna hira dasu mama don lokacin yana gida
nabar labari a baya don kuwa mama dubu itama sun shigo a ranan da aikai min aiki ita dasu Asmau da
Nusaiba .

Ta dauki dan ta kare mai kallo mama ke fadin dubu kinga farin miji kin kasa ba uwayensa su dauka su
gani budan bakin mama sai cewa tayi ga faein miji kam amma yazo a yanayi.

Baizo lokacin daya dace ace fari yazo ba walwala ba maman tudu tace jam meye na rashin walwala
kuma dubu ga yaro da uwar kafiya kalau dasu.

Ummm,hummm yaya ke nan nabar zancen don ba zaku fahinta ba Allah dai ya raya muna shi ta amsa
da amin tace mikoshi kada ki shaye zakin angonane dai ni kadai ko Ladi tayi ta barni da abina da cewa
inna.

Da haka aka wasance zancen nata lokacin iya tana waje tana sallah akai hakan suma suka karba sai
Asmaucema ke fadin kai lalai mama kinyi ango wanan aiya kosa a ciki sosai tubbarkallah masha Allah ta
juyo tana min sannu nayi murmushi ta mikawa Nusaiba ta dan karbi dan a dakile ko minti daya baiyi a
hannuta ba ta mayarwa matar yazid dashi ta fice daga dakin wai tana waya.

Basu jima ba suka tafi wai yaya na gida yana jiran a kawo mashi mota ya fita don dayan motan tashi da
suke fita ta lalace lokacin.

Haka zancen mama ya tsaya min a rai don na kasa fassara abinda hakan ke nufi lokacin saina bar
zancen a raina.

Tare da mama muka kwanta a gado iya kuma falo ta tsaya don lazumin da takeyi da dare washegari
tunda safe mama ta tayar dani nayi wanka don anty Nafisa na gidan har lokacin.

Ya shigo suka zauna da iya a falo suna gaisawa mama ta fito suka gaisa yake tambayansu dare tace
Alhamdullahi maigidan nawa ai bawan Allah neshi baida fitina ko kadan.

Kamar dai sak nacewa dubu kai ya biyo amma take fadin wai baku da kama yaron nan kaine ai sak
babu inda yaron nan ya rageka gaba daya diyanka ba wanda ya daukoka irinsa duk da uwayensu sukai
kama sauran ba dai kamar wanan mai yawan ciwon ita bata rage uwarta ba ko ina ?

Ya mike da zuman zuwa daki wajena wayanshi yai kara ya tsaya daukan wayan yana karawa a
kunnensa a cijin harshen turanci ya soma magana da maishi har ya shigo dakin ina zaune nayi zufa na
gama shan tea ke nan a lokacin.

Hannusa yakai yana share min zufan tare da fadin eh nine kwarai kuwa nike magana ya tsaya ya saurra
da kyau ga bayanin da mutumin yake mashi na daiji yace Allahu akbar kabiran .

Jin hakan yasa na dago na dan dubeshi daga inda nake zaune din ya hannusa yana rike da nawa har
lokacin godiya ya somayi kafon ya kashe wayan yana rungumeni ya furta Iam back Rahama in sha Allah
kayana da suka salwanta anganosu yanzun aka kirani daga can.
Farin cikine ya kasheni ina murmushi na furta Alhamdullahi Allah abin godiya wai Allah mun godema.

Ya sakeni ya juya falo zuwa falo wurinsu mama yana shiga ya daga hannu yabawa Allah kirari da godiya
ya duka yayi sujadan godiya ya dago yana fadin me zance mama wanan mijin naki lalai arzikine an gano
kayana da suka salwanta a can kasan aka kirani ana sanar min.

Masha Allah suka dinga furtawa a cikin murna budan bakin mama sai cewa tayi Allah ka rufa wanan
asirin dama na fadawa dubu hanya Allah yawa gareshi yanzu me zatace don Allah kuma ?

Tace wanan dan bai zo a sa,a ba don yazo ba a cikin walwala don haka ita batayi dashi nace mata
hanyan Allah da yawa yake yanzu gashi ?

Ita dubun ta fadi hakan yaushe tayi wanan zancen banzan haka banji ba a ranan da sukazo asibiti
mama taba iyan amsa tana labarta masu yadda akayi.

Yoo kuji zancen bamza don Allah jininka zaka tsaya fadawa wanan zance haka abin kunya abin takaici
wai meke damun dubune kamar wace kwaro ya hau kanta don Allah jinin ja zakaiwa wanan furcin ?

Wanan kam saidai a kirashi da arziki yaci babban suna mohammad za,a saka mashi insha Allah dama
dashi nayi mashi hudu babane ya dawo .

Gaskiya kam yaci wanan sunan wanan da arzkine yasha sara da suka da sassaka da kushe tun yana cikin
ciki har fitowanshi duniya ba a bari ba kai jama,a Allah na gwadawa mutane isharanshi tun a duniya.

Dubu dubu meya samu jan yarinyar nan ne nikan sai ince ko mutanen boye sun shafetane wai ba a sani
ba dariya taba kowa datake zancen nan .

Kubar dariya don Allah iyan ta kara fada tana fadin nifa abinta ya fara daure min kai jama,a kutayani
duban zancen nan na dubu jininka yazo duniya ka nuna bakin ciki a fili kana wanan furcin haka abin
dubawane zancen nan ?

Ta fada don nima abinda tace min ke nan a lokacin wai Rahama bata da sa,a gashi ta haifo da a cikin
rashin sa,a yazo babu komai sai wahala.

Duba fa wanan zance haka ina ya fito ki kyaleta iya komeya faru kaddaratace a hakan ai Rahama tayi
hakkuri sosai da abubuwan nan don haka ki kyaleta muyi mata addua inma wani abin ne ya hau kanta
Allah ya yayye matashi iya.

Ina ganim gobe insha Allahu zan tafi lagas zan bar nan zuwa Abuja inshiga jirgi don suna nemana ai ina
ganin suna ba satin nan ba ko yake tambayan mama.

Ina sai maijego ta kara samun lafiya dole a dage sunan nan don aikin da akai mata saita mayar da karfin
jikinta .

Haka nayi tunane ban fada bane kada ace wani abu ya fada mama ta bashi amsa da fadin haka abin
yake ai sai an mayar da sati daya ko biyu maijego ta murmure ake suna idan aiki akaiwa mace.
Sun zauna nan suna hiran yadda abin ya kasance haka lokacin daya kwanta ciwo yana processes din
fitan kayan nasa ciwo ya kadashi sai wani abokin hurdanshi kirista ya dauki kayan ya boyr a can da suka
isa.

Nan kuma ankira a tura kudi habu yabi don kada kayan ya salwance yace ba kudi a hannusa a turo mai
daga wajensu sun turu din kuma aka kama amfani dashi wajen magani.

Har kudin sukai rauni koda habu ya samu zuwa kuma ba issasun kudin da zasubi kayan shi kuma baiyi
dabaran karawa da nasa ba a samu kudin su fito don maganan su saiba a lokacin kan yana tausan
dukiyan su kadai shida yazid ba a basu komai.

Ke mai karatu kinsan harkan wani zumunta da zama a babban gida gidan yawa yana tara mabanbantan
mutane masu banbancin ra,ayi sai a cakude ayi ta zaman tsama a tsakaninsu.

Irin wanan halin shiya shafi habu donshi dan no case ne suna wanan maganan ya shafi dan uwashi har
kowa nasa ya hau fushi tun a lokacin ya fita batun komai daya shafi J din saboda zuciya.

Tunda ya bar gidan yake zirga zirgan neman kudin tafiya don dan kudin wajensa daya tsira dasu
lokacin ya saka a wani aikin kuma don dai a samu a karu din kada akai kasa warwas.

Saiga Allah yayi ikonsa kayan sun fito ba abinda ya samesu yayi sadaka ya godewa Allah yayi hamdallah
har yamma basu da labari don ko mama bai fadawa abinda ke nan ba.

Saida Aminu yaje gidan take samun labari da yake fadin wanan haihuwan maman zaria ya jawowa
uncle alheri ta juyo tana kallon yaron shekeke don jin furucinsa.

Amma kai yarone wani yaro yazo a sa,a yaron da zuwanshi duk ba alheri a cikinsa sai tsiya Jafaru dake
cikin walwala auren yarinyar nan da samun cikinta ya zamowa mutane tsiya yanzu a gida.

Don baka san yadda muke bane a baya kama sani ai kana zuwa kana gani ko bakazo ba uwarka daku
kuna gani a tallen ku yanzu fa wakeci banda ita, ? itama din yanzu ina ma ya gansa balle waninta yaci
din ?

Amma dai tsohuwar nan uncle da dukiyansa ya fito zaki tsaya kina fadan hakan ya fito gidan ubanka
mama ta jefawa yaron zagi.

Haba mama wanan abinda kike fadi kan jaririn nan wallahi bai dace ba shi yaro ai Allah kadai yasan
arzikinsa sai masu hassashe ke fara fahintar arzikin yaro tun yana karami.

Amma kina fadan hakan iyayyensa sukaji ba zasuji dadi ba wallahi haba dai don Allah mama salima ke
fadan hakan ga uwar tasu.

Mummy wa zai tsaya saurarenta ma yaron da uncle ya bude baki ya kirashi da arziki sanadin
haihuwanshi dukiyan uncle ya fito jiya kowa na murna da farin ciki ke kina kirawa yaro mugun abu ?

Wai tsaya Aminu me kake fadine mama fa bata gane ba naji kamar kana son fada mata wani magana
ita kuma bata gane hakan ba sai fada takeyi.
Ai shine mummy jaki brain kega tsohuwar nan no school kayan uncle da suka bace a can kasan waje
sune aka kirashin angani kowa na murna da farin ciki ita tana kirawa yaro tsiya.

Gashi har anata zuwa mashi murna ana kiran yaro da arziki ke kuma kina nan kina zuba shirmen tsufa a
gida baki gane ba kanin mu arzikine babba sanadinsa yazo muna da alheri.

Aminun ta kurawa ido tana sauraren bayanin shi don a yanzu ta fahinci me yaron yake fada mata ga
katobaran datayi game da yaron kala kala laifin uwarshi ya shafi dan jinjirin da baiji bai gani ba a duniya.

Allahu Akbar kai Aminu kace min alherin Allah ya sauka muna a gida lalai wanan yaron arzikine tunda
alheri ya baibayemu a yau.

Salima ke fada cikin jin dadi tana nuna farinciki nisawa mai karfi mama tayi tana fadin lalai da ya zamo
arziki kwana uku da haihuwanshi alheri yazowa mahaifinshi.

Kai kuma duk kai min karya kam abuda bashi ba saina saba maka a gidan nan ta yaya abu irin haka zai
samu amma mu bamu sani ba saikai zaka jiyo kazo fada muna shi.

Shi yana fadin a,a ni banzo fada maki ba cewa nayi kanina arzkine don zuwamshi duniya alherine a
garemu tunda ga irin hasken da muka gani a sanadinshi kai, arrrh mamata ta katseshi da fadan hakan.

Salima kuma tace mama ai dole yace haka tunda yaga baki san alherin da ya samu ba amma ai
tunda,zun yake zaune gidan nan bai fada ba.

Tayi shiru na dan lokaci ta nisa take fadin abinda ban gane ba shine kudine masu yawa ya samu ko
kuma wani aikine ya samu a kasan wajen ?

Ban fada ba don ban sani ba nidai naga mutane suna zuwa kuma naji ana murna a gidanmu din nasan
kuma alherine insha Allah.

Ni baein tafi karki matsa min da tambaya ace kuma nice ba ruwana ban fadi komai ba tayi mai dakuwa
ya fita yana dariya salima tasa mai kira ya dawo take fadin gida zaije ko wani waje a lokacin.

Yake fada mata ba gida zaije ba tudun wada ya nufa yanzu mama ta aikeshi ya bada kudin abincin
dabbobinta can ya nufa.

Har yakai kofa yaji mama na fadin can kuma ka koma kaima ana kullawa dakai yanzu na fara tsoronka a
rayuwata.

Ya fita yana dariya baice da ita komai ba bai jima da fita ba yaya ya shigo ya samesu a waje suna
magana mama na tambayan su abin arzikin meya samu Nusaiba tace bata da labari bayan wanan
haihuwan wahalan da akai mashi.

Haba dai haihuwar kuma itace wahala Asmau ta fada cikin nuna mamakin jin hakan a fili Nusaiban tace
ban daiyi dake ba don Allah don ai nima bance kinyi dani ba kalman takice dai ke bukatan gyara gaskiya.
Naga kowa na haihuwansa ai ba wanda aka aibantawa sai ita da babu ko ruwanta da kowa batama saka
kanta a cikin duk abinda akeyi gidan nan ba.

Kai ku rufa min baki don Allah ku wasu irin marasa hankaline wai baku da kishin juna saina abin banza
ana maku kokari mijinku ya dawo hannun ku.

Amma kuda baku raina abin fada nazo ina tambayan akan abinda da naji game da mijinku kun tsaya
kuna min shirme yanzu .

Yanzufa yaron nan Aminu yake fada min ta kwashe abinda sukayi da Aminu din ta fada masu abinda
Aminun ya fada saida ta kai karshe Asmau tace gaskiyane dazun naji yana waya da yake cin abinci saidai
ban kula dameya faru ba.

To kunji abinda ke nan Saiba ta tareta da fadin yanzu shine bai iya fada muna ba koke mama saidai
Aminu yaji a wajen wacan yarinyar yazo nan ya fada.

Ke nan mu dai duk bamu da amfani yanzu idonsa gaba daya ya rufe akan wanan yarinyar ita kadai yake
dauka a matsayin mace ke nan ?

Har yana kiran danshi da arziki ko mu ke nan namu yayan ba arziki suke ba shiyasa bai damu dasu ba
ko sai yanzune aka haifa mai dan gwal.

To ni dai banga wani abu cikin zancen nan ba tunda abin nan in an samu kowa zai amfana dashi ai
Asmau take fada ta juya zuwa kitchen duba girkinta lokacin ya shigo ya samu mama da saiba din a tsaye.

Kallo daya yai masu ya fahinci wani abu na faruwa ya dai bude baki yana fadin sannu da gida mama
lafiya dai na ganku haka tsaye.

Ai dole ka ganmu nan Malam tunda har alheri na iya samunka ka boye muna saidai muji a wajen wace
ka maryar mata yanzu ?

Menene kuma akayi mama yake tambayanta cikin mamaki tace yanzun har wani abu zai iya samunka
sai dai inji ga ahanun talla Malam ?

Yaron nan Aminu yazo yake fada min wani zance dazun shine abin yake ban mamaki nake zance da
matanka ko sun sani ?

Meya fada maki kuma zancen wai wani aiki ko kaya yake fadi ni bam dai gane zamcen ba gaskiya don
kasan haka yake kamar shu,umi wani lokaci.

A,a mama yake dai gyara maki zance amma ai Aminu bai zo don ya fada maki maganan ba da kike irin
maganganunkine fa yace shi kam kanninsa arziki aka haifan masu yake kora maki maganan salima ce
data fito a cikin shiri ta samu suna zancen take fadin haka.

Wai zancen kayana eeh anga kayana da akace sun bace wani abokina ya rike a wajensa dama kada su
salwanta shine yanzu da yaji naji sauki ya fito min dasu ya kirani.
Yanzu na gama shiri gobe nake son zuwa cika wasu bayanai don ina son inbi kayan idan angama
sha,anin sunan nan da za ayi.

Haba malam zancen nan baiyi ba badon yaron nan ba kilama ba

94 / 101