Chapter 55 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   55 / 101

162K to 165K   out of 302.2K words

Ta juya zuwa kitchen din ta fito da basket din dana shirya din da zamu jewasu iya da mama dashi na
tsaraba ba komai bane yasa hakan don basu taba zuwa gidana sunci girkina ba yasa nayi wanan dabaran
hada masu abincin muje masu dashi.

A kofan gidan ma saida ya tsaya yana tambaya meye wanan kuka dauko hakane wai yana nuna basket
din da nake gyarawa biba zananshi a bayan mota da take zaune.

Na juyo ina fadin iya da mama zan kaiwa girkina suci sai yayi murmushi ya bude mota muka shiga
maigadi yana tsaye har muka fita yana muna a dawo lafiya .

A hankali yake jan motan har muka kai wani shago ya tsaya yace mu jirashi ya fita sai gashi da drinks
na kwalaye masu sanyi saida ya zauna yake fadin ki hada masu da wanan din idan kuje nayi mai godiya a
fili.

A raina kuma nace Allah na godema da dabaran hakan yazo min nayi wanan abincin don iyayyensa din.

Tunda muka doshi gidan na fara jan addu,a a bakina na neman tsari gako wani irin fitina daka iya
tasowa ga zuwan namu har ya dosa kan motan zuwa cikin gidan muka shiga.

Da Saiba muka fara ar,ba tsaye da wasu matan abokanshi da sukazo barkan haihuwan da farko
inaganin bata san tare muke ba saida dayan take fada mata haka yasa ta dago tana bin mu da kallo.
Da alama tayi matukar razana da ganina don ba karamin tsoro shigana ya bata ba tagama fada masu
akan yar kauye yake son ya wofintar da ita itako zata nuna mashi ko wa take.

Sai ga matar Nura na fadin kai Nusaiba kardai ince wanan kike kira da yar kauye ina itace amaryan taku
ai ko ?

Jin hakan data fada yasa ta dago da sauri ta kallomu tabbas din kuwa nice nake fitowa daga motar ina
dariya don cewa da yayi bai ban bakin shiga wurin yanda ba sai wani lokacin nake fadin haba yaya kaima
kasan aiko don Abba da akace baida lafiya zan shiga ai yace don kinsan ban iya hanaki zuwa duba
babana ko kikace haka ?

Part din su iya muka nufa da kayan dana dauko din muka bar saurab a cikin mota don ba anan zanyi
amfani dasu ba na abokan zaman mamace da yace zamu je gaidasu daga nan.

Shine agaba muna biye dashi mukai sallama muka shiga iya na zaune da tasbaha a hannunta mama na
kasa zaune tana waya saidai shigowan mu yasa ta katse wayan da takeyi din cikin bacin rai ta amsa
gaisuwan da muke mata din.

Don tun kan na zauna na rusuna ina gaida ita kana na juya wajen iya dake fadin kai kakai amaryace yau
a gidan namu haka ?

Lalai marhabin da amarsu ta ango bakya laifi ko kin kashe yar masu gida kuwa laifinki kadanne a wajen
ango nayi murmushi ina fadin iya mun sameku lafiya ya bayan rabo ?

Yaki nan ki zauna ta fada tana nuna min kusa da ita a gefen kafan mama dake zaune a kasa din nace a,a
iya nan ma yayi min barkan mu da arzikin saukan anty Asmau Allah ya raya muna.

Tace amin yar nan haka akeson Allah ya sauke sauran al,umman Annabi baki daya na amsa da amin iya
na sake juyawa wajen mama din nace mama barka da arziki ?

Ta amsa da barka dai Rahama tare kuke tafe ashe ban amsa mata wanan ba din take fadin barakace ta
bugo waya tun dazun suna rikici da mijinta akan kudin ta wai dake wajenshi.

Ta fada tana kallon dan nata dake kokarin zama a gefen iya inda tace in zauna da farko din naki.

Naji yace jam rikici kuma akan me ba ita tabashi kudin ba son me kuma zatace suna rikicii kan hakan ai
dole suyi rikici ya karbe mata dan kudin ya cinye yanzu kuma ya dauko mata kishiya.

To meye laifinshi a nan Dubu yayan kima ai kusan haka dinne shima ba aure ya kara yanzu ba da kudin
ku ya shiga hannunsa abinda duk nakewa gudu ke nan ai tun farko gashi ko ya faru.

Shima kawu aure yayi kome yana tambayan iya din cikin mamaki tace au bai fada maka ba ke nan to
ina zai fada tunda yasan bai da gaskiya koshi ?

Na juya wajen anty Saratu da fuskanta ke hade kila don zancen anty baraka dinne ko wani abu ke
damunta nace anty saratu mun sameku lafiya ?
Ta sauke ajiyan zuciya tana fadin ke dai Rahama lafiya kalau yaya gida ya amarci kuma ta fada tana
kokarin gyara yanayinta din na farko.

Ta dora da fasin wai wanan yar kamar yar wajen yaya Ai ko da cewa biba data aje basket din nace tazo
gefena ta zauna itama a kasan da nake zaune din.

Itace habiba na fada don ban tsaya wani sanyin da zataga hanyar sakar min wani zance ba don nasan
zata iya indai anty saratuce shiyasa na sake ina magana ta bajin nauyin su kamar yadda suke zato da
farko idan mun hadu.

Wanan yasa na zake na shanye duk wani kawaici a idona ina bata amsa a lokacin saidai bana wuce
gona da iri ba irin hakan .

Iya zancen yaya daban da wanan fa don yaya ko yayi aure bai farawa ya taba muna kudin mu dake
hannunsa ai wanan kuma fa duka kidin ta dauka ta mika mai don sakarci.

Akwao kudinku ke nan a hannun kawu ya tambaya sai tasha kunu a fuska tana fadin akwai mana zai
fara ya taba min sune tunda yasan yadda kudin suke?

Mama meye rashin zama dayansu ai gaskiya iya ta fada gashi ya ban kudi daga cikin kudina ya hana
kusan wata daya ke nan fa ana binsa ya bani sai yace wai suna hannun wanda ya dankawa.

Saratu nikan wai meyasa baki da hankaline wai don Allah haba kinyi maganan kudin nan yace ga
uzirinsa ba sai a jira kayan su zama kudi a kawo maki ba ?

Hakafa kike abinki wani lokaci baki tunane idan abinki ya motsa saiki koma kamar da yaso fitowa ciki
ranan ni banson irin haka wallahi yanzu da zancen yar uwarki zamuji data dameni da koke koke ko naki
da kike son dagawa mutane hankali dashi.

A,a mama ni bance zan dagawa ko hankali ba ai adai bani abin dana tambaya ko aban kudina duka
tunda abin ya fara zama haka ?

Ke tashi muje ki gyadasu ya fada ya mike tsaye ba tare daya tofa komai a cikin zancen ba sai na mike da
sauri kamar yadda ya umurceni din na juya ina fadin iya ga abinci nan na girko maki tunda baki zo kin ci a
can ba ?

Kai kai kai kice girki amarya yau zanci gidan nan ke nan bari na kurkure baki nazo na dandana ko kin iya
girkin muka fita muna dariya.

Bayan fitan mu takecewa yar kin gani ai abinda kike nema ke nan dama har dan uwanki yasan
abindake gudana yai muna dariya ana zancen yadda za a kwantarwa yar uwarki da hankalinta a samu
kudinta ya fito kin dauko wani zance kina son tayarwa mutane da hankali.

Mama nifa bance komai ba kudin nan tunda kikace kawu za aba nace maki a,a kika hakeni na yarda
yanzu kuma kinsan abinda nake sonyi da kudin nan kuma za a ga laifina ?
Don ganin iya ta mike zuwa baya yasa mama din tausa murya tanawa Saratu fadan abinda take kokarin
yi din akan kawu gaban yayan nasu duk daya nuna bai damu ba amma sai bataso hakan ba a lokacin.

Tare dashi muka shiga part din akwai mata sosai a wajen nasu yan barka wanda na sheda wasu don
harda salima da Nafisa suna part din tare da yan gidansu Asmau don a unguwa daya suke don haka
ansan juna.

Ihu suka saka min ita da Nafisa kafin su shiga gaida yayan nasu na dan dara muka rugume juna aka
gaisa su suka kaini dakin mai haihuwa dake zaune kanta babu ko dan kwali balle hulla kan ya dankare da
kitson da akai mata din zanen yawo.

Muka gaisa yar uwarta na fasin ga waje in zauna a gefen gado da aka shiga tattara kayan wajen
saidana zauna nida habiba aka miko muna yaron muka dauka.

Nayi mashi addu,an Allah raya mun dan kai kamar minti ashirin a zaune shiru na mike na karbi ledan
dake hannun biba na mika ina fadin ga zanin daukan yarona.

Yan uwan nata suka shiga godiya muka fito daga dakin dake wani irin bashi duk da kanshin turarena ya
bi dakin lokaci guda amma haka bai hanani jin wanan bashin ba kona meye oho ?

Falon muka fito muka kara zama banjin ya fita lokacin nafi zaton yana dakinsa don can ya nufa tunda
ya gama gaisawa da mutanen falon.

Ina anty Saiba tana ciki kije ku gaisa kizo muje wajen yandan ki Anty Salima ta fada na dan kalleta ta
mike tsaye tana fadin muje ai yanzu tabar wajan nan itama duk muna nan zaune.

Bata dakin da alama tashiga bandakine dataji shigowan mu muka fito bamu tsaya jiranta part din
muka fice zuwana yar uwata dana matsu muyi arba da ita a lokacin don a yanzu nasan tasan munshigo
gidan tunda munyi waya kafin na fito gida.

Wanda a yanzu zaune take kawai gidan bata wani dogon hurda da kowa sai salima da iya dama dai
kusan hakan ake zaune saidai na yanzu din yafi worse ne kawai saidai haihuwan nan na Asmau tace dani
ta danga canji ga Asmau don data shiga barka Asmau ta mata bazata don ta mika mata yaron wai ta
shafa mai man zaitun donta samu an mashi wanka lokacin.

Iyace dai mai wankan yaran idan sun haihu dama ba wata ake daukowa ba tunda da dan karfin ta har
yanxzu shine tana shiga iyan ta gamawa yaro wanka tace a ba Yanda din tayiwa yaron shiri ita kuma
tashiga nata wankan.

Wanda bata zaci hakan ba tunda da farko duk sun dauki zafi a kanta kan zancen aure masu miji dani yar
uwarta nayi a cewansu asirine mukai mashi muka sameshi haka a bagas din.

Koda muka shiga ashe Saiban na tsaye ta windon dakinta don shike facing din part din yanda din tana
kallon mu zaune takai saman gado ta jawo waya ta dannawa yar uwarta ikilima kira.
Tana dagawa tace Saiba ya akayi yazo din anyi magana tace anty ikilima inafa ya dai zo da wanan yar
iskan yarinyar tayi barka.

Anty Iklima kinga yadda yarinyar nan ta koma kuwa cikin dan kwana biyun nan wallahi koke kika ganta
sai kince ba ita bace Ramaah da kika sani a baya.

Takoma sak irin manyan matan nan da yake korafin son yaga mun koma da kullum yake fada yana son
ganin hakan a kan mu.

Mena fada maki Saiba ai dama nace kibar biyewa Asmau kuna wanan rayuwan kidadancin kamar wasu
jakuna kinki ji ?

Yanzu gashi dan hakin da kuka raina na nema ta tsone maku ido keda bakinki kin fada ko wanan baisa
ya fita batunku ya baku baya tunda abinda yake so ke nan dama ?

Tundai ke kice baki da aiki sai cusa mai bakin ciki ance ga yadda zakiyi ki tsaya kina takama da kin gama
dashi bai iya komai sai abinda kikace dashi ?

To yanzu kin gani masu iya magana sunce ko kana da kyau ka kara da wanka kin dai san Jafar yayi
kokarin zama daku haka Nusaiba ku zauna yayi takashe maku kudi amma a banza baki amfani dashi
saidai ki sayar ko ki kimshesu cikin akwati tun farko abinda inna take maki gudu ke nan amma baki ji
Nusaiba ai yanzu kin gani.

Anty Ikilima nagaji da zuwa gidan malam nan wallahi bani ganin biyan bukata gaba daya yanzu
abubuwan sun juye min yadda ban tsamani ba sam inayi kamar banayi wallahi don banko gabanshi balle
na samu aiwatar da abubuwan dana karbo din.

Ki bari ai zan shigo ana gobe suna kuma naji inna tace zasu zo barka kinga nasan zata zauna dashi ai
donshine ma bazan biyosu ba don ina son inzo in kwana din idan nazo sai musan yadda zamu bullowa
zancen nasa.

Sun dauki lokaci suna waya kafin dai ta taushi yar uwar nata ta bata shawaran da ita saiban take ganin
yana da wuya ta iya hakan ga jafar din da take gani idan ta sameshi yanzu saita hukuntashi fiye da
tsamaninta.

Zai gane shayi ruwane idan ya shiga hannunta saita bashi mamaki sosai ta rama duk wani takaicinshi
dake zuciyarta abugeka a hanaka kuka shine abinda jafar yai mata a yanzu kan Rahama.

Muna shiga maria na zaune tana ba Abba abinci tun daga kofa nace da yaron baby na ya juyo da sauri
yana kallona sai yai kamar zai dago zuwa gareni sai kuma ya noke zuwa jikin mamanshi yaki zuwa wajena
din.

Wai Ramaah kece haka abinda Maria din ta fada ke nan tana min kallon mamaki na dan bata rai ina
fadin kinga duk na lalace ko ?
Ta watsa min harara tana fadin wani lalacewa kuma gaba daya kin sauya kamar bake ba ummah nacan
tana damuwa akanki kullum sai tayi min magana a kanki wai naki zuwa in duba matake .

Ni kuma ya Habu ya hanani zuwa gidan duk sun sakani a gaba kan maganan ki na karasa ina fadin to ai
gani nazo yau muka fara gaisawa da ita lokacin Nafisa ta shigo part din tana dariya tace.

Wai ashe bakuga saiba ba da kuka shiga yanzu ta fito tana fada dake Salima wai zakuyi tsiya idan kina
shiga huruminta dolene saita gaisa da yarinyar nan da zaki kwasheta zuwa dakinta ?

Allah sarki shi gaisuwan ma wani fitinane ashe banzata haka bane da bance muje a gaisa ba ai ?

Mun bar zancenta aka dauko hiran anty baraka data dagawa mutane hankali tunda safe wai tun cikin
dare ta kira waya ashe zata dawo gida ita mama dubu ta hanata dawowa dagani har yar uwata bamu ce
kala ba don ba abinda ya shafemu bane .

Muna zaune kanwar Asmau matar yaya J tashigo tana fadin amarya angonki yana neman kifa ?

Wai ashe suna zaune falon gaba dayansu ya fito yake fadin ina Rahama ?

Sukai shiru ya bisu da kallo kafin yace ke Rashida kira min ita part din habu don Allah ya juya ya koma
dakin nasa shine ta taso tazo kirana din .

Jiki a sabule na mike cike da mamakin don me zai aiko nemana a wanan lokacin gidan matanshi irin
hakan zai iya kawo wani matsala kuma tunda dai gidansune na shigo ai ba nan din nake ba.

Namiji oho donshi ko a jikinshi a dole zai saka mata kunci a zuciya ya nuna hakan ba komai bane ai
tunda nima hakinsace na karasa falon na shiga gabana sai faduwa yakeyi suna zaune ana surutu sai sukai
tsit lokaci guda.

Yana ciki Rashida din ta kara fada na nufi hanyan dakin nashi da sallamata yana kwance yana waya na
sameshi ya dago yana fadin.

Kije wajen Iya ki dubo min abincin da kikazo masu dashi din nan yunwa nake ji zuwan kawu dazun ya
hana in tsaya in karya da kyau a gida.

Na juya zan fito muka hade da saiba da zata shiga fuskanta kawai na kalla nasan akwai magana a tare
da ita lokacin.

Ni dai kala bance da ita ba na dan rabe ta shiga ni kuma na fito daga dakin yan falon ko na samesu
sunyi tsit sun kashe kunnuwa suna sauraren abinda zai faru a lokacin.

Part din iyan naje na samu har lokacin dai ba dadi a yanayin dana samu mama din don itama waya
takeyi lokacin don haka da iya na samu yin magana ina fada mata sakonshi din.

Iya ke fadin shi kuma jafaru baici a gidan bane da zai kwashe muna wanda aka kawo muna nace kadan
zan dibar mai ai iya.
Na bude na kyafata mai komai na rufe ina jin Saratu na fadin bari dai in diba kafin ya kare naga an fara
kwashewa haka kowa baici ba.

Kai wanan matar bata san harara ba ban taba kawowa a raina zata ko kalli abinda na daho din ba balle
tayi fadan taci har nakai kofa naji mama na fadin idan kinje ki kira min shi daga nan ana magana ya mike
ya fita ni zasu bari da tashin hankalin da baraka ke son ta dauko muna akan mijinta ?

Tunda na doshi kofan nake jin muryansu daga dakin hakan yasa naja na tsaya naji yana fadin har ke kin
isa ki kafa min doka a gida Nusaiba ?

Na fada na kara Rahama matatace kamar yadda na auri kowa a cikinku tana da ikon shiga duk inda
taga dama a cikin gidan nan ko da kudinki na hada na gina gidan nan ne ?

Nace ki koma gidan ku kince ba zaki koma ba to ki zauna tunda zaman mama kikeyi bazan koreki ba
don kin zauna zamanta amma kada kice zaki takurawa kowa a gidan nan cikin iyalina kinji na fada maki .

Kikace zaki tayar min da fita a yanzun nan ba sai anjima zan shayar dake mamaki cikin gidan nan oho
ashe ba dadi lokacin da kika zarga min ciwon fitana a kaina ita kuma sakaran nan ta mara maki baya kuke
gudana.

Don yanzu na samu wace bata gudana tana iya zama dani ko wani hali nake ciki zaki kuma ce baki yarda
da hakan ba kije nace ki samu mai lafiya irin ki don Allah ki barni in huta hakana a rayuwata.

Dakin na fada dauke da abincin ta zaburo kamar zatayo kaina na gwauce Allah ya gyara abincin bai
zube ba har na falon duk suka mike tsaye saboda muryan yaya dake fadin kika taba ta wajen nan yau sai
kin kwana asibiti Nusaiba na fada maki inkon zata karyane ki gwada taba Rahama ki gani a gidan nan.

Ni basai ka rama min na ina da hannuna nice zan ramawa kaina ai amma wanan abin baikawo kallo ba
a tsakanin ku a cikin jama,a don Allah .

Kaje mama tana magana da kai idan ka gama na fada na aje abincin na fito daga dakin na barsu a ciki
yan falon tsuru tsuru ban tsaya ba na fita daga part din.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/5,

55 / 101