Chapter 49 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   49 / 101

144K to 147K   out of 302.2K words

ba look Habu kabar min matana
da surutu taji da rashina da zatayi a yanzu kusa da ita zo Rahama ya fada saidai na kasa zuwan dole saida
ya mike ya biyoni har dakin mun dade a rugume yana lalashina kafin ya Habu yasa mashi kira yana fadin
zakabi ta Rahama wallahi ka rasa jirginka ka fito mu wuce kawai malam.

Dole ya sakeni yana fasin zamuyi waya na amsa saida yaya habu ya fita na iya fitowa falon na dan labe
ina mashi Allah ya tsare suka fice daga gidan.

Sai kuma lokacin naga gidan yayi min girma duk da ga yarinyar nan biba daya kawo min ga kuma
maigadi a wajen gidan.



GIDAN KAWU

Kawu dauda dake zaune yana lissafin kudi jin motsin matarsa hausatu yasa ya maida filo saman kudin
ya taushe saidai yayi shuka a idon makwarwa don hausatu taga abinda yake nufi lokacin.

Jug din furan data dauko wanda yaji nono da sukari tana ajewa ta mike tana fadin malam meye duniya
naga tun shigowan kudin nan ka tsiro wani sabon dabi,a a zuciyar ka.

Kana nuna baka son ma inmatso balle insan komai dangane da kudin nan karka manta komai daya faru
har kudin nan suka shigo hannunka nice na shiryashi gidan nan ?

Kai ya dago yana fadin yanzu me kuma nace ko nayi hafsatu me nace akan kudin nan dole in kula da
dukiyan mutane ai don yaran nan kinsan ba kirkine dasu ba.

Zasu iya hada kai nan gaba su binciko kudinsu a wajena donshine bani son wasa da wanan kudin kike
ganin kamar wani abune hakan ?

To yanzu dai ba wanan ba malam ta kai zaune tana fadin kasan dai Allah ne yayi damu zamuci kudin
nan muma a gidan nan tunda ya kwatosu ya dawo muna dasu hannun mu.

Katseta yayi da fadin to sai akai yaya ta kara gyara zama tana fadin to shine nakema tuni da yaran nan
mardiya da dija kasan dakunan su yana son gyara ko kwashi muje din nan na bakin titi da ake kafawa aka
kwasan masu zasuji dadi kasan mazan yanzu basu son ganin daki ba komai sai wullakaci da raini ya shiga
tsakanin miji da mata.
Ko wani miji dai a yanzu so yake yaga wurin kwanci gyarare da kuma mace mai dan maiko ba yar bani
bani ba kadai san komai basai na fadama ba .

Shi kuma yaron nan sale a samu abinda aka bashi ya huta da yawon tasha din nan da yakeyi idan kayi
hakan ni kayi min komai wallahi nasan naci a gida ni in koshi tunda kai naga ba irin mazan zamanin nan
bane da suke son ganin daki yana walkiya.

Hakane fa to zan duba saidai zancen Sale gaskiya ban maki alkawari ba tunda ko an bashi a wajen shan
wiwinsa zai kare don me zan dauki dukiyan mutane in danka mashi da sukarye a banza.

Malam yau dai kome sale ya zamo dankane ba a canzawa tuwo suna su wa yan nan daka rike suka
zamo abin kwarai ai yanzu sun gujeka sun nuna maka halin yan duniya.

A,a hafsatu muka dai nunawa juna mu dasu tunda yakai har yaran nan yanzu kamar sungane me muke
kullawa a kansu don gaba daya yanzu Jafaru ya daina fada min komai nasa kinga kuwa kamar ya ganeni
ke nan yanzu.

A bakin yan gari nake jin wai,wani harka ya samu na ma,adaine shine yaje gun sarki ya gabatar da
kansa kinsan ko tunda kikaga hakan harkace babba amma yai bugun gaban kanshi yake gabatar da
komai ba tare da sanina ba a yanzu.

A,a,a,a aiba ido zamu saka mai ba son mun kwaci wanan dan kudin a hannunsa yanzu dole mu sake
shiri a kansa a nemo makashi kamar baya ?

Nagaji da wanan abin hafsatu tunda yaran nan ba mantawa sukayi dani ba gara dai in sun tuna dani
inci din yanzu abin nan dana rufewa Halima yana damuna a raina tunda duk yadda nabi a karshe dai
kwaliya bata biya kudin sabulu ba kan yaran .

Kai ke ganin haka malam da badon hakan ba aida baka samu kansu hakan daka gama fadi ba a baya
saidai kaima ka koma cikin yan kallo a yanzu.

Haka dai ta gama dadin bakinta ta matsa mashi yasha furan yace zai sha don a yanzu ya fara zargin
tana mashi asiri don bai iya kyatare zancen hafsatu din har wani shakkunta da tsoro yakeji nata idan ta
fadi magana dole a bita koba dadi.

Yanzu ko ya daura dammataran kwato kanshi kan abinda ya dade yana buri a zuciyarsa duk da yasan
hakan ba karamin abu bane wajensu hakan zai jawo masu.

Itama dai a bangarenta mikewa tayi cike da tunanen mijin nata da a yanzu yake kokarin juya mata
baya don ganin ya damki kudin da suka dade suna shiryawa akansu sun shigo hannusa yake kokarin juya
mata baya a yanzu.

Yazama dole ta kara shiri akan malam din don bata tsamaci kudin ba a hannunta zasu zauna ba sai gashi
duk da suna wajensa yana kokarin karta ganima da idonta hakan me yake nufi ke nan ?
Takai wani lokaci a wajen tana tunanen hanyar da zata fitowa malam din dashi kafin ta mike ta shiga
aikin gabanta tanayi tana saka da warwala a zuciyarta.



Musalin karfe dayan rana Salimace data gama shirin ta tsab ta fito daga dakin kwanan su da yar
karamar jakkar hannunta saidai ganin saiba tare da mama yasa ta kasa magana lokacin ta zauna.

Kamar hadin baki saiga mariya ta shigo da abincin ranan data girkawa su mama din ta fara gaidasu iya
ke fadin yar albarka yar tofon lada kamar kinsan tun dazun yunwa nake ji wajen nan zaune.

Ruwan shayi da biredi mai zaiyiwa mutum a cikinsa ba wani abu mai nauyi da mutum yaci tun safe
malalatan yaran nan sunki su girka abin kwarai da mutum zaici har yayi sauransa yaci da safe ya dora a
cikinsa don kiuyan banza irin nasu.

Amma iya ai kinji ina masu fadan dafa dukan da sukayi jiyan nima ba sonsa nake ba amma tace min wai
ta zuba ko dole na kyaleta.

Iya bata tankawa mama din ba dake magana tace bude min nan kinji ban iya bude abin nan takecewa
maria din data aje abincin gabanta.

Maria ta duka ta bude da sauri iya ta kyalla ido kan abincin tuwon alkaba da miyar danyan kubewa sai
manyan nama guda biyar da miyan ja da ya cika kulan miyan bata san lokacin da hannunta ya dafa kan
maria din ba tana fadin Allah yai maki albarka yar nan ya kareki daga idon mahassadanki alherin Allah ya
bi rayuwan ku har karshen duniya.

Kaji iya da wani zance shi kuma mijinta daya kawo abincin fa mama ke fadan hakan ?

Iyan ta dago tacewa mama din ai kinji jam,i nayi mata ai bance rayuwanta ita kadai ba har kowa nata
nake nufi a zancena dubu.

Idan nayi mata kamar habu din nayiwa ai don duk daya suke wajen mu daya kuwa iya mama ta kara
fada iya dai tace miko min plas in diba kinji takecewa yanda din.

Ta mike zuwa kitchen da dauko mata plate koshi saidata tsaya ta wanke tas ta fito ta kawowa iya din
ta zuba mata duk saiban tana zaune tana kallon abindake faruwa.

Maria din ta mike tana fadin ke kuma gaki da jakka a gabanki mana kamar me tafiya tana cewa
salima ?

Kamar kinsan tafiya zanyi zan tafi Abuja yau din nan inje in huta da surutun iya da sauri suka kalleta
suna fadin Abuja kuma ?

Tace ehh gidan Rahama zan tafi dazin mukai waya da yaya yace ya wuce can zani na dan zauna da ita
kwana biyu kafin ya dawo nan ai lagos ne gidan kwamacala gidan kowa da kowa can ko ai kinga gidan
hutawane nayi.
Maria kan tunda ta daga batace komai ba tasa kai ta fita tabarsu nan suna karawa da Salima din da
Saiba dake fadin ohh dama nufin ku ke nan ashe gidan hutawane can din.

To bari yayan naki ya dawo muji in hakane kowama ai yana son hutu a rayuwansa wa zaku mayar dan
kauye bakauyama kun kaita abuja balle mu yan birni.

Ke Nusaiba fita batun Salima don Allah shirmenta take fadi shi abujan dame yafi lagos din ?

Yafi mana mama Saare ta fada daga gefeb da take kwance ai tunda kikaji Salima ta fada nufin yaya ke
nan can ne gidan hutun nasa nan kuma na kwamacala.

Wanan karon kingansa gidan nan sosai kamar yadda ake ganinsa idan yana gari komai dai mutum zaiyi
ya tuna da Allah .

Halan Rahama din tafi wanine ko wata kai da za a tsabareta a gefe daya a rabata da yan uwa akaita can
mama don bakiga gidan bane fa shiyasa ba zaki gane gaskiya Salima na tafadi ba irin ginan zamani din
ban komai tsone a gidan gwanin ban sha,awa.

Kai haba don Allah akan dan uwanki kike fadin wanan maganan haka yar nan iya data cika baki da
abinci take fadin hakan ga Saare din.

Ta samu ta hade tana fadin shike nan Allah ya bashi ba zai nuna ba akansa aka fara hakan ina nan
kukaso ku tozarta shi kuga inda zai saka yarinyar nan yayi maku bazata akan hakan.

Yanzu kuma kuna son kakaro wani zance salima tace nima iya bada wani manufa na fadi hakan ba
wallahi sheri dai nakewa mariya din ita kuma saare tana son maida zancen babba ta mike zata fita da
jakkarta mama tace da ita dawo.

Da sauri iya tace ta dawo kamar ya ke jeki Allah ya tsare ki gaida ita sai munzo duk sukai shiru sai
Saarece ke fadin toke iya ina ruwan ki ai gara a hanata zuwa din don bata san ciwon kanta ba gidan
kanwar bayanta zataje ta tayata zama gototo da ita Rahama sa,artace don Allah ?

Ke ya isa haka don Allah mama ta fada a hasale sai saare din tayi shiru amma mama kin daiji abinda
ake fada ko a bayan mu yau shi salima ta fada a gabana ko ?

Don salima ta fada mijinki ya fada maki hakan wai akankune aka fara hakane miji ya raba gida in kubi a
sannu indai Jafarune Allah yai masa budi tunda kukaga hakan koku yana da niyar raba maku din mutum
ya kasance mai hakkuri koda yaushe ba gagawa ba zancen yaran nan zaki dauka ya wahal dake a karshe
to ki zuba mashi ido inkinji ta tawa.

Ta dade zaune kafin ta mike ta fice zuwa part dinsu a hasale take har lokacin tana shiga saiba na zaune
tana cin abinci take fadin kinji ni da yar iskan nan Salima ?

Me tayi Asmau ta dago tana tambayanta taja tsuki ta zauna tana fadin wai nan gidan shine gidan
kwamacala don haka lagos ne nan can kuma gidan daya kai yar iskan nan shine Abuja gidan hutu.
Dariya Asmau ta kwashe dashi tana fadin kai lalai salima dai yar takalo zancene yayin da nusaiba din
kewa Asmau kallon shasha,sha tace wai ke ranki bai baci bane ?

Tace akan me shi kanin miji kana fushi da zancenshine Nusaiba ai lokacin daya gane kana fushi da
abinda yake ma lokacin zai kara abinda zai bata ma rai .

Ina ruwan mu da Abuja ko lagos tunda nan ma bamu rasa komai ba nifa kinga raina bai baci da wanan
abin bacin raina dayane shine ace shi mijin ya juya muna baya ya fita zancen mu bai kulamu bai damu
damu ba amma ni duk wanan abin nasan wata rana kamar mu zata koma itama a dai fara aje yaya ki
gani itama tabi layin mu din.

Kafin tabi kina nufin mu zama yan kallo Saiba ta fada tace dama ai haka abin yake kin sani dole in
ankawo wata kayi hakkuri don baka zamanin ka kaina wani ni wanan yasa kikaga ban wani damu kaina
ba tunda nasan haka abin yake dama .

Ohh Allah hakane ai bansan da cewa ni kadai ke yakina ba gara da kika fadi naji yanzu kai nusaiba ke
nan da wani zance kike to ke wanan abinda kikeyi riban me kikaci wajen sa don Allah ?

Ta mike zuwa daki tabar Asmau din data bita da kallo zuwa kurewanta tayi murmushi tasan abin ya
taba mata zuciya amma ta godewa Allah data taushi zuciyar nata kan abinda take ji din.

Da badon yan uwanta da iyayyenta da suka tsawata mata ba da haka zata biyewa Saiba din suyi ta
hauka ana masu dariya tare miji dai na kowane ba na mutum daya ba don haka kowa tashi dabaran ta
fitar dashi a gidan.

Suna isa Abuja direct airport ya nufa dashi don saura kiris jirgi ya tashi yana fitowa daga mota kirana na
shigo mashi ya dauka yana fadin.

Amaryata ya kike ?

Saida na sauke ajiyan zuciya na amsa a cikin sanyin murya da lafiya lau yayana yaya hanya yaya ya habu
ya amsa da yaya habun ki lafiya lau yake Rahama to ya akayi.

Na dan kashe murya ina fadin ba komai yaya sai dai kewa gidan yayi min shiru ya ba dadi sai naji yace
ohh god ko in dawone to ?

Ke Rahama ba zai dawo ba ki koyi zama ke kadai mana ita maria da nake tafiya na barta kin fitane da
zaki wani marairaice murya da sauri na kashe wayan na kifa kaina a filo.




ZAINANB IDRIS MAKAWA[2/23, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



5️⃣1️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Saiba kuma ya habu ya fada don ganin Saiba again tana kiran dan uwan nasa a lokacin ya fadi hakan yana
mikawa yayan nasa wayan.

Ya karba yana mannawa akunnesa yace hello Nusaiba wallahi J sai Allah ya isar muna mucuci kawai
azzalumi don yarinyar nan kake kokarin nuna mu ba komai bane a yanzu wajenka ?

Yau har yakai a na fada muna cewa wai mu din kayi doping din mu ka koma wajen wace ake ganin tafi
mu wallahi kai azzalumine J sai ,,,,,

Dakata Nusaiba wanan wani irin zancen banzane kika kirani kina min mara amfani ina kan hanyar tafiya
neman kudina ko wani yace daku da Rahama nazo tafiyan nan ?

Aiko da itace ba a mussun hakan don zaka iya yin hakan a yanzu tunda ka iya ware ta daga cikin mu ka
nunawa duniya tafimu wallahi ka dawo ansan wace za ayi don ni ba zan yarda da hakan ba kaji na fada
maka.
Ok ai ba sai na dawo ba Nusaiba ko yanzu kije gidan ku ba matsala na sake ki wuf Habu ya karbe wayan
daga hannunsa yana haba dai J zaka biyewa haukanta ku zama daya ?

Duniya ta zageka a kuma zagi Rahama a banza da bataji ba bata gani ba irin wanan abubuwan naji
maka tunda ka kawo zancen auren Rahama a wajena .

Nasan dama sai kun kwasa da Saiban sosai akan haka don haka don Allah ka kara hakkuri ka daure ka
fita zancen ta kawai kaba banza ajiyan ta don Allah .

A zaria ihun da Nusaiba tayine ya tayar da Asmau dake barci a falo ga yara sunyi kaca kaca da falon
nasu da shinkafan da sukaci sub watsar ko ina sun zubar da ruwa samab center carpet din duk kiriniyarsu
a lokacin baisa ta tashi daga barcin da takeyi ba sai ihun da saiba tayine ya tayar da ita agigice.

Lafiya take fada tun kan takai dakin Saiban tayi dirsha kasa tana salati tana shiga take fadin lafiya
maman ikiram ?

Ita inda ranta yakai shine mijinsu wani abu ya sameshi tunda shine ke hanya a lokacin don haka tasa
shi wani abin ya sama dai.

Yaya J ne ko me ta kara fada tana matsawa kusa da ita a hasale ta dago ta kalleta tana fadin don Allah
ni kin cikani da tambaya shine din.

Burin ku ya cika yau tunda ya furta min saki amma ku sani wallahi yadda na rabu da J kowanku sai ta
rabu dashi rabuwa na har abada gidan nan.

Ba daini akaiwa haka ba to wallahi ki rubuta ki aje na fada maki har bafilatan nan da yar uwarta saina
fitar da ita gidan nan dukkan ku .

Wai me kike fada hakane don Allah meke faruwane sai wani magana kikeyi kamar wace ta samu
laluran kwakwalwa ?

Ehh hauka nayi ki fita kawai ki ban waje don Allah Asmau banson gulma tunda kinji meya faru dani ko ?

Fita tayi daga dakin kamar yadda tace saidai bata zauna ba part din iya ta nufa ta samu Saare take
fadin kijefa ina ganin mutumiyarki ba lafiya tsakaninsu da yayanki

Ita da yaya kuma shida bai gari koya dawone tace ina ganin kiransa tayi da cin mutunci dai amma ki
daije kiji ko meye ta mike da sauri ta fita daga falon iya din.

Asmau takai zaune wajen iya tana fadin Nusaiba bata ji saida na bata magana nace tabar zancen nan
taki nasan ta kirashi a wayane sukai cin mutunci ya saketa.

Shine wai gaba dayan mu har mariya sai mu bar gidan nan yadda aka saketa daga kawai naje ina bata
magana ta dinga fadan hakan akaina.

Nasan za akai ga hakan don yarinyar nan bata da kirki ko kadan badai kan dan zancen nan da Salima
tayi bane ta hakeshi ta kirashi da cin mutunci.
Shine kuwa nasan ma shine iya saiga mata ta fito daga daki take tambayan meke faruwa kuma nan
suke mayar da abinda ya faru ta mike tana fadin saki kuma ?

Sakifa shi jafar ina ya koyo sakin mace daga dan magana ko da gaske kansa ya burgene ban sani ba kan
yarinyar nan ?

Wani irin zancene haka ga dan cikin ki dubu hau kika gansa dashi ko me da zaki fadi hakan kan danki
dubu akan wanan yarinyar da batayi maki ragowa har kike kokarin aibanta danki ?

To iya

49 / 101