Chapter 43 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   43 / 101

126K to 129K   out of 302.2K words

rayuwanshi ya gane yayi auren zamani shima irin na sauran
maza.

Na mike tsaye na sake fadin da kijira yaya din ya dawo sai ya kaiki mana tace ai banson ya dawo ya
sameni dinne yasa zan wuce yanzu.

Don Allah Rahama kiba marada kunya ga wanan aure ido aka saka aga matsala koda kadanne kema
daga wajen ki ace mashi gwai don haka ki daure ki koyi son shi a zuciyarki.

Har duk wani abinda kika iya ta bajinta ki gwadawa yayashi Rahama ki kawar da kunya dajin nauyi a
yanzu shi mijinkine ba wa ba don haka saikin zage kin dai san bakin ramin kura kike.

Haka kuma ki kara hankali da mu yan uwansa kindai san komai za azo a dinga bukin cikinki kamar da
gaske sonki akeyi sai idan anji sirinki a koma bayan ki ana zunden ki.

Duk abinda ya shige maki kai ki kirani in sha Allahu har idan na sani da yardan Allah zan haska maki shi a
yanzu zan nisanceki kada a zargemu amma akwai waya na nan komai ke nan zamu dinga waya dake in
sha Allah

Na dago kai cikin yanayin damuwa ina fadin nagode anty Nafisa a gaida ummu amma ina zuwa don
Allah na fada zuwa dayan dakin dake rufe turmin zani na dauko mata da wani dogon riga sai su sabulai
da turare na dibo kayan buki mai yawa na kawo mata ina mata godiya.

Har bakin kofan falon na rakata tace na tsaya nan ta tafi na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa ciki ko ina
na gidan nabi da kallo wai yau ni Rahama nice ubangiji yaiwa wanan baiwan a lokaci guda haka.
Alkawari na dauka zan zauna da yaya tsakani da Allah in masa biyayya kamar yadda shari,a ya
kidanyawa mace tayiwa aure biyayya kamshi na fesa a falon har zuwa dakinshi dana shiga ns gyara mai
hakan yana daga cikin abinda ke hadashi fada da matansa nasani yasha korafi kuma a gabana cewa ko
muhalinsa babu mai iya gyarawa a cikinsu sai inya gyara da kanshi.

Na koma daki ke nan na tayar da sallah naji dawowanshi bai shigo ba sai daidai na idar ya shigo har
dakin nawa da sallamanshi na na shafa addu,an na juyo ina amsawa tare da furta sannu da dawowa a
gareshi.

Yauwa amarya ta yaya kike ya amarci kuma ya fada yana karasowa inda nake zaune saman sallayata
ya rage tsawonshi zuwa tsugunni yana fadin ya gidan Rahama hope ba matsalan komai dai ?

A,a bakomai na fada ina kokarin dagawa ya mike yana miko min nasa hannun alaman in kama in mike
ai zan iya na fada .

Baki son na taimaka maki ke nan ya fada a,a kada dai in wahalal dakaine kawai banso amma da karfina
ai zanyi iya mikewa.

Wayau ko ya fada to ban yarda ba ya fada banyi aune ba sai naji ya sukuceni baki daya zuwa bakin
gado dani ya aje zakice ba yaya Jafar bane a lokacin.

Hijjab din wuyana daya kula ya tauyeni kamar ya shake min wuya don yaga inata kokarin sasautawa da
hannuna hakan yasa ya dan kara rankwafowa saitin fuskana yana kokarin cire min daga jikina.

Ina jin yadda ya sauke ajiyan zuciya lokacin da yayi arba da suran jikina daya dan baiya afili daga
yanayin dinkin rigan jikina.

Dagawa yayi daga rankwafin da yake naga yana shafo suman kanshi da hannunsu wani irin soyayyata
yana fisganshi lokaci guda duk ya dan daburce yana fadin kinci abinci dai ko ?

Bana jin yunwa na bashi amsa a takaice ina mikewa daga yadda ya barni a kwance don irin kallon da
naga yana kare min sai lumshe ido yakeyi a cikin wani yanayi na gajiya.

Da alama baki son cin abinci Rahama kosai na zauna kwana biyu ina baki da kaina zakicine ina kula ko
dazun bakici komai ba koso kike antyn Abuja tace ina maki sakacin kiyon ki ?

Ni ba sai ka zauna ba dama haka nake ba ko yaushe nake cin abinci ba sosai nafi son abu mai ruwa
ruwa dashi na saba rayuwata da nake zuwa kiyo a rugga.

Hannu yakai ya ja min hanci yana fadin bazan taba yarda da hakan bani donki na aje komai a gidan nan
Rahama.

Kici sai kince min kin gaji da nau,insu na cabza maki wasu don kanki saina turo baki cikon shagwaba ina
dan kauda kaina gefe daya.

Yayi murmushi yana fadin watarana basai nace kici ba Rahama kece dai zaki dameni da inci din ranan
da kika haifa min kyawawan yaya masu kama dake ba zakiso ko kudi ya sauka a kaina ba lokacin.
Saidai zanso ki haifa min ya mace mai kama dake sak mai irin tsayinki da hancin nan naki da gashin nan
yakai hannu yana kokarin taba gashin kan nawa nayi saurin gwaucewa ina murmushi.

Falo muka fito tare zuwa dining ya zauna na fara bude abincin ina kallon sanda ya lumshe idanunsa
naci gaba da hada mai na aje komai na zagayo na duka a gabanshi yabini da kallo.

Takalman dake kafanshi mai belt don na kula yana son saka irinsu shi din dan gayune na karshe idan yai
shiga saikin tsaya kina satar kallonsa wani lokaci.

Komai nasa a nutse yakeshi nasan kuma shida kansa ke tsayawa yiwa kansa lalura wani lokacin koda
wanda ya kamata ace mace tayi masane ya rigada ya saba da hakan.

Kafafuwan nasa ya kara miko min na karsa zare dayan ina kokarin mikewa naji ya dafa kaina yana fadin
sharp kinga na manta da takalma a kafana na zauna.

Allah ubangiji yayi maki albarka Rahama sunan ki yayi daidai da halinki na kirki da sanin ya kamata
daidai da addini yadda ake son mace ta kasance harta bawa yara tarbiya ke nan.

Nidai dai murmushin iya baki na sauke na juya da takalman zuwa dakinshi naji yana fadin wai ina
Nafisane ?

Ta tafi gida dazun nan ta wuce wai zataje ta duba su inna sai yayi dan murmushi ya kada hannu a
ruwan dake gefenshi yana dauraye hannunsa .

Na juya nakai takakman dakin na dauko mai wasu sifas masu kamar gashi a jikinsu wanan duk hikiman
anty Salmace saida ta jaddada min kan wanan akidar na kula da bashi takalman tafiya a cikin gida ta
kuma nuna minsu din hakan yasa na fara amfani da nasihar nata a lokacin.

Na zo na aje masa a gefe inda inya daga zai saka na zauna a kujeran dake gefenshi abincin naga ya
debo ya nufo bakina dashi na noke kaina ina fadin zanci ai idan ka gama.

Bai tsaya saurarena ba ya mika min dole na bude baki na karba a haka mukaci abincin waya ya mikar
dashi daga wajen wanda na fahinci daga matansace dake mashi cin mutunci a cikin wayan a kaina.

Kayan na shiga tattarawa na nufi kitchen dasu ban fito ba saidana dauraye na kife na dawo nagoge
dining din na nufi dakina don ya shiga dakinshi tun lokacin.

Kayan jikina na sauya na kara muke jikina da dan kamshi mai saukin shaka na dauko riga cotton bubu
mai gyale na daura a kaina lokacin wayata tadauki kara ina dubawa anty Salmace a layin.

Na dauka da sauri muka fara gaisawa ina tambayanta yara da gajiyan hanya take fadin suna lafiya suna
wajen lesson .

Kafin naji ta dora da fadin to yaya ashe ango ya dawo sai ta kwashe da dariya nima a bangarena
murmushi nayi kawai a lokacin.
Take fadin komai daidai ko murmushi mai sauti na sake kawai tace ato na dai fada maki yanzune zaki
koyi narkar mashi da zuciyanshi akanki kada ki tsaya wanan sanya da kauyanci.

Kiyi kokari ki kafa taki gwaunatin a zuciyarsa ta yarda zai mata da irin ukuban daya saba dashi wajen wa
yan can garorin matan nasa.

Duk abinda kika sai zai farauta masa Rahama ki daure kiyishi don Allah kicire duk wani kunya da nauyi
ki nuna masa kulawa fiye da zatonsa tunda abinda yajashi gareki kenan dama samun natsuwa a wajenki
din.

Muryanshine ya katse muna hiran da yashigo yana fadin kin kwantane Rahama ina son na leka
gidancan in dubusu ban samu tsayawa dazun ba dana shiga abubuwa sunyi min yawa a lokacin.

Saika dawo yaya agaidasu dasu dasu hajjaju da iya ya amsa da zasuji har yakai kofa ya juyo yana fadin
kada kice zaki sake wani girki ki huta hakana sai gobe don Allah zan riko muna abinda zamuci da daren.

Saida yakai kofa nake fadin da anty Nafisa zaka dawo ko ?

Sai naji yace kina son ta dawone shiru nayi na kasa cewa ehh don irin kallon da yake jifana dashi
lokacin ya juya yana fadin banjin hakan su dan huta a gida kwana biyu.

Yana fita muka cigaba da hiran mu da anty salma din dake min sherin a,a komai zam kan ga alama nan
naji da kunnuwana .

Kin gane yanzu fa abin kamar compertion ne a tsakanin ku kowa ya biya allonsa ya wanke suma zasuyi
kokarin ganin kin zama banzace a wurinsa don haka shiga gidan mata biyu akwai hatsari babba ga mace
sai ka iya takonka sosai dasu.

Mun dai dauki lokaci zancen ke nan guda akan zamantakewan aure ta yadda zan zauna da kowa kafin
mu dauko hiran su hjy yabi muna dariya wanan ya shagal dani na manta da komai saida aka kira sallah
na mike zuwa alwala.

A gidan su kuma yana isa yaran ya sama a kofan ya Habu suna wasa da Abba ya fito mota ya nufi
wajensu.

Zaune yayi ya dorasu saman jikinshi yana dan jansu da hira irinta yara jin shiru yasa maria bude falon
don taga ko Abba yana kusa.

Sai tayi arba da ya J din ta dan daburce don tunda abin ya faru basu hadu ba sai wanan karon suka hadu
dashi din.

Shine ya fara gaida ita wanan karon taji abin wani banbarakwai tana fadin sannu da dawowa yaya ya
hanya lafiya yaya gida dasu Abba koda yake gashi nan yana fada min wai yana son karatu .

Tayi murmushi ta juya zuwa ciki ta barsu a wajen yake fadin gashi ai zamu shiga ciki take fadin dama
wanka zan mashi nake nemanshi.
Ya iza yaron zuwa gareta ya rike hannun yaransa zuwa part dinsa inda ya samu matan basa a zaune
falo duk da suna a waje daya kowa da abinda takeyi a lokacin.

Sallamanshi ma da yayi sai Asmauce ta amsa mashi da kyar itama dai a cikin basarwa tayishi bai kula da
hakan ba ya zauna a tsakiyansu

Yana fadin ya Asmau ya karfin jiki kuma sai saiba taja tsuki ta mike kafin ma asmaun tayi magana tabar
falon a cikin hasala binta yayi da kallo ya dawo da dubasa ga Asmau sake fadin lafiya gamu dai muna ja
ai.

Ai watan haihuwan ki ke nan zai kama ko tace haka akace saidai idan Allah ya raba kawai yanzu Allah
ya rabamu lafiya ta amsa da amin.

Badai wani matsala ko tace da sauki gaskiya kinje asibitin da kikace tace naje naga likitan shima yake
fada min edd dina ok ya fada.

Yarshi data hau saman cinyarsa tashishi ya biye mata suna hira kafin ya mike ya shiga wajen saiban
dake kwance ta kafawa siling din dakin ido tana tunane.

Nusaiba ya wai meye matsalankine haka ta dago daga yadda take ta watso mashi harara tana fadin
matsala matsalan me kagani a wajena ?

Naga kin gani kina basarwa mana kamar baki ganni ba tace oh so kake in daukeka in goyaka tunda ka
tuna damu kazo garemu yanzu ?

Yayi murmushi yana zama a bakin gadon daidai kafafunta ta wani jaye kafanta da sauri gefe daya ya
sake fadin wai meye hakane wai ?

Cikin kyarmar murya ta soma magana tana fadin me kuwa ko kagawani abune a wajena kaje wajen
wace kake tunanen ta fimu wani abin daka zabi tozarta mu a idon mutane .

Tozarci kuma ya fada tace koma meye dai kaika sani da abin kunyanka tunda baka daukeshi komai ba
ya mike yana fadin Allah sarki auren da nayine abin kunya kuma yau Nusaiba ?

Ashe aure yana zama abin kunya a wajen ki don na auri wace kika sani na hadaku a waje daya a
matsayin matana ?

Wanan kuma kaiya shafa don ni wanan figagan yarinyar karamar yar iskan da kake kallo a mata bata
isheni ko kallo ba balle .

Allah ko niko kinga ko gajiya baniyi da kallonta da tayi min dari bisa dari ko kifta ido idan tana kusa ban
iya yi yanzu .

A hakan kai har kaga mata ke nan ita dai Ramaah din dana sani ko ancanza mata kamane kuma ?

Ya gyada kai yana fadin itafa yanzu ai in ba itaba banganin kowa a mace yarinyat data san zafinka tasan
ciwon ka ako wani hali ka shiga ina zanga daidai da ita.
Don haka inma kushe min mata kike kokarin yi gara ki daina don ita din tauraruwanace a yanzu tunda
ba zata taba guduna ba duk halin da nake ciki kuwa yasa kai ya fita ya barta tana ta zunduma ashar.

Ya jima a falon kafin ya shiga wajen iya daga can ya wuce masallaci bayan an fito sallah ya dan sayo
kayan sanyi da nama ya shigo masu dashi ya aje a falon yayi masu saida safe baijin akwai wace ta iya
amsawa a lokacin.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/16, 8:05 AM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



4️⃣5️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Mummy zulaihat Allah ubangiji ya baki lafiya yasa hakan ya zamo kaffarane a gareki ubangiji Allah yasa
anyi aiki cikin nasaran ubangiji Allahuma Amin ya Allah.

Mama Amina kema Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kafarane yasa hannu ya warke a cikin kuduran
ubangiji Allahuma amin sauran uwayena da bab kira ba da yayyun mu ya Allah ka basu lafiya masu
damuwa Allah ka yaye masu kamai dashi alheti a garesu Allahuma amin jumma,at mubarak gareku yan
uwa musulman duniya.

Fada yake sosai gaban matarshi hafsatu tana kara zugashi akan Habu wanan karon fushinsa ya sauka
don Habu din yake zagi saboda yana ganin shine ya kawo mashi cikas a ranan.

Idan badon shawaran da habu ya kawo ba da duk yadda akayi a ranan saiya mallaki wani abu daga
cikin kudin nan ranan.

Amma ga kudi yana gani ido da ido amma dan banzan yaron nan Habu yai masa bakin cikin su shigo
hannunsa saboda wata akidarsa ta banza dayace wai sai ankira wasu malamai can .

To kai malam waisu yaran nan dake gagawan fadin yadda za ayi da tasu kason a sakebawa yayan nasu
me suke nufi da hakan yanzu matarsa hafsatu ke tambayashi cikin katse mashi tunanen da yakeyi.

Sai daya nisa ya kallota ta sake fadin yanzu kyalesu zakuyi da shawaran ya asake karban kudin kuma a
hannunsa ?

Kafa san idan suna hannunsa ba zai yarda agani ba balle a taba yakamata kayi wani abu akai hakana
malam koda baka da gadon mai fata ai kaima dai ka wahala dashi gashi

Yaron nan Jafaru fa malam kana sane ko kashi ya rika ya shiga kasuwa dashi sai sun zama kudi a
wajensa na rasa wani irin albarka Allah yaiwa yaron nan haka ?

Dan banza gashi da iya boyon kurwa wai ace akwai wa yan nan kudin haka amma yake daukan dan
kudi ya mika maka kaine baka iya kashin kudi ba ke nan ?

Abin ne da daure kai kema kin sani hafsstu ba irin karba da bayin da sunan yaran nan amma kamar ina
aika dutsene ba abinda suka canza saima gaba gaba suke karawa.

Wai, kinji yaron nan ashe harda gidaje yake kokarin ginawa yan uwansa bai fadawa kowa ba sai yau din
nan yake fada a wajen haduwar nan.

Sai nake ganin yanzu kamar ya fara fahintar manufarmu akansu don ya fara yin abubuwa ba tare da
sani ba da farko ba haka bane na samu kansu fiye da tsamanina.

Amma sai gashi yanzu da nake hango kudi sun zauna mashi haka yana kokarin ya juya min baya a
tafiyan yanzu.
Harshi ya isa malam wallahi bai isa ba komawa zakayi a kara nemo makashi a hannunka sai yadda kayi
dashi a rayuwansa .

Shi wanan Habu dai tauraronshi bai haskawa kamar nasa nake gani don har yanzu bai kaiga samun irin
na Jafar din ba amma duk da hakan tunda bakinsu gudane shima ba barinsa zakuyi ba ai malam.

Dole ai insan abin yi a yanzu ya zama dole na sake sabon shiri akansu kafin komai ya jagule muna don
ina ganin wancan na farkon ya dushe .

Kwance ya sameni da waya a hannuna har barci ya soma daukata lokacin ya shigo cikin dakin da
sallama tsaye yayi a waje daya yana kare min kallo kafin ya tako zuwa bakin ya karbi yawan yana dubawa
gamen din engela yana ta playin da kansa.

Dan murmushi yayi yana kashewa kafin yakai zaune a gefe daya yana aje ledan daya shigo dashi a
hannunsa sai lokacin naji motsin zaman mutum a kusa dani na dan zabura kadan naganshi .

Komawa nayi ina sauke numfashi tare da dago fararen idona na kalleshi ina furta sannu da dawowa a
bakina .

Sai naga ya lumshe ido yana amsawa yace har kinyi barci by this time sorry na tsaya da iyane ban
fargaba ashe lokaci yaja haka ban sani ba.

Allah sarki Iya suna lafiya a cikin hamma dake nuna kasala ya amsa da lafiya lau suna gaida ke nayi dan
murmushin da nasan zan tsokaleshi na yunkura da niyar tashi zaune .

A lokacin naga ya dadirce da kyat ya iya sassauta muryansa yake fadin ina jin yunwa fa Rahama ?

Na juyo da sauri ina fadin kace kada nayi girkin dare kuma yace ehh muje falo ki ban abu yana can na
aje hakan yasa na yunkura na mike zaune daga kwancen har jikin mu yana gugan juna dashi na samu na
mike tsaye.

Zanin dana daura saman rigar barcina na gyara

43 / 101