Chapter 32 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   32 / 101

93K to 96K   out of 302.2K words

dan cakula abinci badon baki naso ba saidan ciki ya dauki nauyi na dan zauna da anty muka
taba hira ranan hiran mama mukayi don suna germany sunje ganin likita a can.

Tana ban labarin ga kafa na ciwo kuma mama taki daina cin nama da akace ta rage munyi dariya da
take fada min tace ko taci ko bataci ba ciwo dole tayi.

Ita kan namanta zataci gashi duk ranan da taci naman washegari kafan nata zai tashi da fitinan ciwo da
sai tayi data sanin hakan.

Lokacin sallah ya tayar damu muka shiga daki bayan na idar zama nayi ina lazumi a wurin har aka kira
isha,i na mike nayi sallah don haka ko a gida da bi,an mu yake saboda kwadayin ladab dake cikin hakan.

Zancen zuci na zauna yi wayana ya dauki kara na mika hannu na dauko a zatona yar uwata maria ce
don a ranan bamu gaisa ba tun safe da ita.

Number ce ba suna hakan yasa nake kwankwanton ko waye ya kirani lokacin na dai dauka ina fadin hlo
muryan yaya J naji yana ajiyan zuciya yana fadin.

Da fatan zakiyi hakkuri don nasan na barki a cikin zullumi da tunanen bukatan danazo dashi a kanki yau.

Tsananin sonkine Rahama ya hana min sukuni don na tsunci kaina a cikinsa don haka na kasa sukini da
natsuwa a tare dani ke kuma kika zabi guduwa ki barni a cikin damuwa.

Rahama kiyi hakkuri ba zan iya boye abin da zuciyana ke ji akanki ba yanzu ko a gaban waye idan
hakan dana aikata kuskurene kike gani ki ki daure ki fahince ni don hakan ba kuskure bane a wajen Allah.
Ina son ki sani duk wani dan adam da yake rayuwa a doron kasan nan to kuwa yana tare da kalubalin
rayuwarsa ni na dauka aure shine matsalana a rayuwata.

Katseshi nayi da fadi a cikin kyarmar murya dana samu ba hada haruffan a bakina ina fadin don Allah
yaya kayi hakkuri ba zan iya hakan ba kai yayana a matsayin yaya nake kallonka wajena.

Amma sai naji yace nima haka ai Rahama har gobe har gata ke din kanwatace hakan ba yana nufin
zamu daina zumunci mu bane saima mu kara donkonsa a tsakanin mu Allah kadai yasan mutanen da suyi
alfahari da wanan hadin namu nan gaba.

Kit na kashe wayan don na fahinci idan na biye masa da sauraren kalaminsa zan iya mashi rashin kunya
girma ya fadi to kada akai wajen yasa na kashe layin ga baki daya.

Na wurga wayan saman gado ina jan tsuki don na faginci tabas da ake fadan namiji baida kunya hakan
gaskiyane saidai subar ke mace da jin nauyin idon mutane .

Koda anty ke wani zancen wai na garasa inci abin hannunsa ni ba zan iya yaudaransa ba free,falo zan
fito mashi fili in,nuna bani kaunan manufarshi kawai ya rabu dani



A ZARIA

Tunda ya habu ya dawo a cikin dare yana part dinshi bai fito ba har karfe goma na safe ya samu ya daga
don tun bayan sallah asuba ya koma ya kwanta barci.

Wanka yayi ya shirya ya fito falo matarshi na zaune tana ba Abbati abinci ya fito ya samesu a nan din
dinning ya nufa don yayi breakfast kafin ya fita.

Wai ina Rahama tun jiya banji motsin ta ba ya fada yana kallon matar nasa shiru tayi bata bashi amsa
don har lokacin a kufule take da zancen.

Bakiji bane nace ina Rahama ?

Bata nan ta bashi amsa a takaice.

Tana ina ?

Tana Abuja tun lastweek .

Abuja kuma meta tafi yi abuja ba a fada min ba bayan a karkashina take zaune ehh don a karkashinka
take ai shiyasa ake muna yadda akaga dama a gidan nan.

Kamar ya ban fahince ki bafa ?

tace zancen ke nan ai tana Abuja tunda an hada kai ayi matasheri da kazafi don a tozarta mu tsawa ya
daka mata ta fada mai meya faru ta tsaya tana wani zancen banza.
Nan dai ta kwashe komai kamar yadda Nafisa ta bata labari bayan tafiyana don bataji ainihin yadda
zancen yake ba da farko.

Mikewa yayi ya bar abincin dake gababshi dagashi sai jallabiya a jikinshi da gajeren wando part din iya
ya nufa yana tambaya ina Saratu ?

Tana part din ya j salima ta fada yace good ya juya zuwa can din inda ya sameta rashe rashe saman
doguwar kujera kwance.

Basu ankara da shigowansa ba sai ganinsa sukayi gabansu fuska daure yace ke uban me kike a part din
nan ?

Saida ta dan jefo mai kallon rashin kunya take fadan ba komai tare da sauke kafafuwanta kasa ta tashi
zaune hakan ya bashi daman wanka mata mari biyu masu kyau a fuskanta.

La,illah kaiko Habu me tayi maka harda mari haba dai kai kuwa an hanata shigowa nan part din ne
dama ?

Shoute,up ya fada saida ta dan kadu tana ja da baya ya kallo Saare din yace get lost kafin na tatakaki a
nan sakarai mara hankali kawai da haka zaki samu mijin aure.

Bayan kina haddasana a tsakanin iyalinmu ko yaushe duk wani makirci da za a hada gidan nan kina
cikinsa why kika bata kanki haka ?

Ki rasa wanda zakiwa sheri sai J dan uwanki riban me zaki samu idan kin batawa dan uwanki suna ?

Ni yaya yaushe na hada fada a gidan nan wani mari ya kai mata saida hancinta ya soma zubo da jini
ganin hakan baisa ya kyaleta ba .

Wai kasheta zakayi habu don ta fadi gaskiya ai ba itace ta fada ba nice nan don kowan mu ya gani da
idanusa idan ba wani abu take nema gareshi ba zata tsaya tana magana dashi a gaban mu ?

Au ke uwarsace ke nan bansan abun naki har yakai haka ba ai Nusaiba ashe doka kika bashi sai wanda
kikaso yayi magana dashi a gidan nan zaiyi.

Shiru tayi tana mazurai ya juya kan kanwar tasa yana fadin ki shiga hankalinki ni ba J bane na sake
ganin ki a nan ba tare da yan uwank ba zaki gane baki da wayau.

Wai kai ka zata wai zaman tsegumi muke yi a nan dama ai ,,,,

Marin daya sauka mata a tsakiyan fuska da yasa ta ga wasu wuta sun gilma a gabanta yasa ta dafe
fuskan ta soma hawaye tana fadin habu nika mara ?

An mareki ko zaki ramane ya fada yana kara nufo inda take da niyar kara kai mata wani dukan su
mama suka shigo falin.
Tun daga kofa mama take fadin habu kai habu fa bada kai nake magana ba ko kayi haukane wai kul ka
sake tabata ranka zai baci .

Wai, Lafiya meye haka meya faru hakane ina daki iya kece min gaka can kana neman Saare zuciyata ya
ban babu lafiya ?

Wai meya kawo hakane don Allah takai kallo ga yarta dake kuka wiwi ta tare hancinta da hijab din
jikinta.

Bata san lokacin data nufeta ba hankali tashe tace munaga rasulu haba Habu dukane haka ko abu ka
kwada mata ?

Wallahi dukane mama a kan matarshi ta fada mai karya da gaskiya yayi muna hakan wallahi ba zan
yarda ba karansa zanyi dan isk,,,

Keko yar nan baki da albarka a gaban mu zaki bude baki ki zagesa ke wace irin mara tarbiyace wai ?

Barta iya barta ta karasa yau sai an kwasheta a wajen nan duk kika bude baki kika zageni, zan gwada
mata lalai dan iskan nake da gaske kuwa.

Ai bata cika ba tunda ba ita tafito tayi muna haka ba idan ta isa ta fito mana ai gamu tazo an fada duk
abinda ta fada maka an fada din .

Ya kara zabura yayi wajenta mama dake tsaye tace habu kana kara dukan Nusaiba zan saba maka rai
sosai wallahi.

Ji abinda kaiwa yar uwanka ka kyauta ke nan habu ita din mace ce fa, habu, duka haka kamar ka samu
jaka ?

Ke Dubu ki rufe min baki a wajen nan kafin ranki yafi na yarki baci idan har ba zaki tayashi tsawatawa
yar uwasa ba to ki fice daga nan.

Haba Dubu ke wata irin uwace wai abinda yaran nan suka aikata alherine haka da sukayi dan uwanta
fa aka hada baki da ita a bata mashi suna kan zina ?

Na tambayeki nace kazafi da cin amana alherine fadansa koda hakan ya kasance gaskiya ?

To balle kowan mu nan ya san babu kamshin gaskiya a cikin zancen su dole ran habu ya baci ya dauki
wanan matakin ai.

A hankali mama ta sake hannun saratu data kama tace ai yanzu kin gani idan kince ba zaki natsu ba sai
ya illanta ki a banza ta juya ta fice daga falon.

Kallonsu iya tatyi tace ku saurari sakamakon ku idan kuna jin dadin kunci gari balufacen mutum baya
mata zance har mutuwa.
Gaba kuma kun kulla dashi ke nan daga nan har yumal,imadi indai bafulatanin asaline zakuce na fada
wata rana don sai sun rama shanmatan da kukai masu irin wanan.

Ai saidai su rame na fada din suyi duk abinda zasu iya shi a dole gashi mai mata yazo daukan mata
fansa zai gane ya mareni wallahi.

Ki dai iya bakinki Habune dai kinsa zai iya fiya da hakan kidai san halinsa yanzune zai iya dawowa ya
jibgeki Asmau data taso take fadan hakan ga Nusaiba.

Malama rufe min bakinki ai tare dake muka hada plan din amma da kikaji yana jibgan mu lafewa kikayi
daki ai gobema kusane zan rama .

Ranan dai mama bata ji dadin iya ba don sai da tayiwa mama din tasa akan irin yadda take saka ido
gida na kokarin lalacewa gasu kuma suna ganin hakan.

Kowa ya shige daki daga mama har saare suka bar iya a falo tana fada saida Nafisa ta fito ita da salima
suka samu ta dakatar da fadan nata.

Ranan dana fara zuwa wajen training nasha dariyan zuci saboda wai wanke wanke ake tambaya yaya
ake wanke kwanoni kafin a saka abincin da za aci ko anyi amfani dashi.

Wanan yasa na dauki lecture a shirme ashe abin ba haka yake ba akwai yayan hutu da basu san yadda
zasuyi abubuwa da dama daya kamata ace mace ta sani tun tasowanta ba.

Irin wa yan nan yayan hutun da gata su sam basu san me auren yake nufi ba, sun dai dauka cewa kawai
za,ayi aure aita soyewane da miji shine ma,anan auren.

Cikin dan kwana biyu danake fitan sai gashi nima da nake ganin ai nasan wasu abin ashe bansan komai
dagane da rayuwan mace a gidan miji ba.

Shi aure ba yana nufi ki ba miji abinci bane ko kiyi ta aiki kamar jaka dole akwai matakan da mace zata
bi don rayuwan aurenta yayi lasting a zamanance.

Sosai na mayar da hankalina ina koyon abubuwa da bansan dasu ba ilimi ance gishirin rayuwa tabbas
haka abin yake kuwa.

Don ba karamin kuskure rayuwa matan gidan mu ke aikatawa ba har yar uwana kuwa dama ance zama
da madauki kanwa shike kawo farin kai.

Kar kice yaya ya hakkura ya daina kirana har wa yan nan kwanaki sakonsa kadai sun cika min wayata
irin kin tashi lafiya kinyi sallah kinci abinci ?

Kome kikeyi yanzu har yanzu baki barci ba wasu irin kaya yau kike sha,awan nasa Rahama ire iren wa
yan nan maganan da sannu sabo hakan ya fara shigana ba tare dana sani ba.

Inda har yakai kwana biyu banji wanan irin tambayan nasa ba da nake dauka daya mai dani karamar
yarinya ashe ko hakan ne don da nuna damuwa da kulawa ake sace zuciya.
Sai gashi rashin jinsa a yan kwanakin ya fara sakani dan danuwa kadan kadan zan tuna dashi a inda
zuciyana ta fara raya min Allah yasa dai ba matsalan jikinsa bane kuma dai ?.

To yanzu wa zan tambaya inji duk wanda na tambaya koda yar uwatace zata soma zargina a kanshi
haka na dake dole da dan damuwa yayin da wani sashe na zuciyana yake ban shawara da in tambayi
anty Nafisa ita kadaice ba zata taba fadawa wani komai game dani ba.




ZAINAB IDRIS MAKAWAMURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,



3️⃣4️⃣




GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wasa wasa zancen sati biyu yake batun sharewa bai gida run bayan tafiyan wuni dako kila ya kwana
yabar zaria dashi sai gashi kwanansa goma sha biyu da tafiya .

Wanda yai daidai da tafiyana don tafiyana kwana goma sha,ukku ke nan yanzu hakan yasa matan yaya
din a cikin damuwa .

Ga iya dake sake masu zancen cewa saboda bakin ciki sun kora mata jika ya tafi shida ba lafiya ya
isheshi a jiki ba amma masifansu yasa yabar gida dole.

Irin wanan maganan da iya keyi yasa Nusaiba ta fito fili ta nuna damuwanta ga tafiyan nasa inda itama
ta fara nuna damuwanta ko waya basu samun shi gaba daya ya daina amfani da sim din da aka sanshi
dashi da farko .

Daga Abuja ya wuce matatar mai don yin wasu cikin takardu daya dade yana neman daman cika hannu
a cikinsa.

Sai gashi kwatsam an kirashi yazo ya cika takardan an bashi daman yin hakan a lokacin don shi ya
kwasa zuwa fatakwal din.

Kwanasa hudu ya gama abinda ya kaishi daga can ya nufi lagos a lagos din ya samu aiyuka da yawa da
suka shagal dashi wanan yasa su a zatonsu suke ganin ya bar gidane saboda matsalan daya faru din.

Saidai Habu yana da labarin komai da yake gudanarwa don ya sanar dashi abinda ya taso masa don
haka duk surutan da akeyi ido kawai Habu din ya zuba masu baicewa kowa kala ba.

Nikan na zata ya hakkura da zancenane don jinshi shiru da nayi har anty salma namin sheri wai na kore
yayana da hali ya kama kansa dani.

Har take cewa Ni dama nasan za,a rina wai ansaci zanin mahaukaciya don matansa sun riga da sun
girgizaki dashi Ramaah.

Dama kuma ance kuskure daya mutum keyi a rayuwansa mai ban haushi don haka shi tun farko yayi
kuskuren rashin daukan mataki a lokacin.

Saidai ni a waje ke Ramaah irin matakin da yake son dauka din shine ake kira da gyaiyya don yafi
wanda kika so ya dauka zafi don shi naso ki nuna masa aiba komai har su fahinci akwai kauna a
tsakaninku ta gaskiya.

Amma yanzu ai ba zasuji haushin komai ba tunda basu san kunyi hakan dashi ba kuma bame fada masu
balle hakan ya damesu.

Ajiyan zuciya na sauke ina lumshe idona a lokacin banjin komai a raina saina daukan fansa matukar ban
dauki wanan fansan a garesu ba ina iya hade zuciyata duk sanda nayi arba dasu kuwa.
Idona da suke a lumshe na,dan bude ina kallonta nace wanan saiba din ko don ita da saare zan iya
hakan a yanzu anty .

Nafisa ke fada min sunce wai kunya yasa na bar gari wai da bakinsu suke fadin sherinsu yayi aiki saura
anty maria komai dadewa sai sunsa tabar gidan nan.

Kutumuu,lesi ai uban kuturu yai kadan wallahi gida kuma zaki koma cikin sa tsunbul ba maria ba har ke
sai sun gani a gidan tsakiyansu kuwa.

Munyi hakan da kwana biyu na gaji sosai ranan don practical din da mukayi a training center din mu
donshi ma na kwanta da wuri ranan.

Misalin sha biyun dare a daidai wanan lokacin wayata dakr ajiye a karkashin filo ta dinga kara da alama
kirane ke shigowa a lokacin.

A cikin barci naji sautin karan yana shiga kunnena tare da verbiration din da yake fita daga wayan.

Dan guntu tsuki naja tare da mika hannu cikin magiyan barci saboda dadin barcin da nake ji a lokacin.

Jikina gaba daya tsami yayi nakai hannu na dinga lalubo wayar kasan filo ba tare dana tsaya duban mai
kiran nawa ba na kara a kunnena bayan na dauka.

Muryan yaya na tsinkayo yana fadin Ramatu Rahama tabbas kinci sunan ki don na fara sheda hakan a
gareki.

Ai na zata ba zaki daga wayan ba saboda dare yayi duk da dai dare baiyi ba a wajen matafiya ni gani
nan yanzu haka airport ina jiran Jirgin mu ya tashi.

Kalman da yake fada din yasa na gane yana shirin tafiyane wani waje lokacin shirun da yaji nayine
yasa ya kara fadan hello kina jina kuwa ?

Da kyat na iya bude bakina da yai min nauyi na amsa da ina ji yaya Allah ya tsare hanya aje lafiya a
dawo lafiya Allah kuma ya bada sa,an tafiya.

Masha Allah nagode kwarai Rahama kece kadai na kira a duk yan uwa ina sheda maki zancen tafiyan
nan don ina kyautata zaton jin hakan dama a gareki.

Rahama ke din Alherice a gareni sosai na fahinci hakan a yan kwanakin nan tabbas akwai alheri a
taraiyana dake Rahama domin naga hasken dake tunkaro rayuwata tun zancen nan bai kankama ba sosai
a tsakanin mu.

Kiyi hakkuri da yayanki Rahama ki karbi bukatata dani dake din taraiyan mu akwai alheri sosai a cikinsa
in sha Allahu zakice na fada wata rana.

Kinsan meyasa nace hakan a gareki dole kinsan ina da dalilin hakan dana fada don kuwa nina san irin
farin cikin da Allah ubangiji ya jefani a cikinsa cikin yan kwana kin nan.
Rahama abinda na dade ina mafalkin samunsane Allah ya banshi a wanan lokacin .

Don haka zuciyana taban ke din alherice a garemu baki daya don bani kadai ba kowa dake kusa damu
wanan alherin zai shafa insha Allahu.

Kalaman dayake fada min sunyi matukar daure min kai a lokacin saboda ban fahinceshi ba sam don
haka sai nake fadi a yar siririyar murya da Allah ya kara tabbatar muna da alherin ya amsa cike da jin
dadi da amin Rahamata.

Sai naji abin wani bambarakwai a kunnuwata wai nice yaya yake kira da Rahamarsa haba dai maza
ashe haka suke saboda soyayya sai

32 / 101