Chapter 74 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   74 / 101

219K to 222K   out of 302.2K words

barni da nauyi da kunyar iyayyena.

Wanda ko kafin su daddy su wuce a ranan saida su kai ta zolayata a bakin mota ina hawaye badai
kamar anty Salma dole ganin yadda nake kuka yasa takai ga rikeni a lokacin.

Haka suka tafi suka barmu a cikin tausayin mu don sun fahinci muna zaman hakkuri a wanan gidan
gidane da baida alkibla baida tsayayyen babba da zai tsawata akai yaran maza sune tsaye da gidan kuma
su din dai tunda akwai uwa da kaka dole komai zasuyi akwai taka burki da tauyewa ga irin zaman nan.

Zamane da wasu iyayye ke zabawa iyalinsu don gashin kan zuciyarsu su wanda akasari ya sabawa
al,ada da shari,an mallam bahaushe.

Zakiga iyayye masu irin halin nan suna nisanta iyalen su da yan uwa suna kamesu daga shiga dangi ko
wani harka na zununci wanda uwace zata zauna ta dinga shimfida doka iya son ranta ga zurianta.

Irin wanan rayuwa muka tsunci kan mu a cikin gidan nan matukar ba naku yazo daya ba da irin matan
nan mata da yawa suna fuskanta bacin rai a zaman aurensu koda ya kasance kuwa miji na aon matarshi
uwa ba zata bari a zauna lafiya ba irin haka aji dadi.

Abin mamaki na zata maria zata dan zauna dani ta kara min shawara ina tsaye wajen bayan wucewan
su daddy saiga Habu ya fito yana cewa da ita muje ko tsayuwan nan kada yai maki yawa.

Haka suka shiga mota suka tafi suka barni ina kallonsu a cikin mamaki har suka bacewa ganina naja
kafata zuwa ciki inda na samu mama da iya zaune a falo suke fadin Allah sarki mutanen kirki sun tafi
Allah ya saukesu lafiya.

Amin kawai na iya fada na shiga dakin yana kwance shi kadai a dakin yayi shiru yana kallon saman
dakin yanayin kwanciyarsa zai nuna maka cewa ya shiga zurfin tunane a lokacin .

Kwanciya nayi ba tare dana kallo inda yake kwance din ba nima na fada nawa tunanen muna wajen a
haka har aka kira sallah magariba.
Na mike zuwa bandaki na hado komai da nake mashi alwala na fito saida nayi mai ya tayar da sallah
nashiga na dauro alwalata nima na fito.

Falo na koma ranan nayi sallah haka kawai nake jin tsanarshi na karuwa a zuciyna ina zaune ina addua
wayata ta dauki kara bayan na duba naga ummah ce a layin lokacin na dauka take fadi bayan mun gaisa.

Ramaah yaya na batku dazun kiyi hakkuri kinji kowa da tasa kaddaran kar kiyi mamaki duk sanadin
wanan cikin Allah ya kwantar da mijinku jinya irin haka saboda hakan kawai ya faru a tsakani ku.

Wani dan, taurine dashi kafin yazo duniya sai uwa da uba duk sun girgiza wani lokacin ubane kan fara
laulayi da jinyar ciki kafin a sakawa uwa ta karasa saukin haka manya suka fada.

Ance sai uba yayi jinyan fitar da kwansa kafin ya samu ya fito daga jikinsa kamar yadda mace kanyi
wahalan haihuwa suma maza din suna da tasu jinyar kalan fitar da kwai a jikinsu.

Don haka nake ganin duk wanan jinyar kamar ta wanan halittan dan da a yanzu kuka samune dashi sai
kiga in har hakan gaskiyane a cikin yan kwanakin nan insha Allahu mijin ku ya samu lafiya ya mike kamar
bashi ba.

Ta jima tana rarashina kafin mukai sallama ina aje wayan kiran mummy yana shigo min a wayan na
daga itama din dai hakkuri ta bani kamar yadda duk wani masoyina iya hakkuri zai iya ban a yanzu kawai
don dama shi muka gada tun kakanin a arewa.

Na dai idar da sallah ina zaune naga shigowan mahaifiyarshi hakan yasa ban damu dana koma ciki ba
na zauna a falon abina ta jima a ciki zaune kafin ta fito da bacin rai ta fice daga part din.

Ikon Allah naji maman tudu ta fada daga bayana don iya bata falon namu lokacin zuwan Yazid da family
shi yanzu bata faye zama damu ba ko yaushe.

Amma akwai aiki a wanan rayuwan kice komai yaro keyi da iyalinsa idon ki yana kai a wanan zamanin
ka kawar da idonka ma yaya aka kare dakai balle kace saka ido zakayi.

Dubu tana da wahala a rayuwanta zancen nan da mutumin nan ya fada shine yanzu take faman hasala
akai duk da yaron nan yana kwance bata duban hakan ita.

Saida ta sameshi da wanan zancen bata duban zancen nan bana yau bane balle ta duba halin da dan
nan yake ciki ta tausaya mashi ga hakan.

Amma wai haka dubu ta rutsa yaron nan yanzu akan zancen nan dubu sam bata kaunar diyanta suna
alheri wayema me alherin ciki banda shi jafar din ?

Jafar din dai mijinku shine ya buwayeta yake alherinsa ba tare daya fada mata ba kada ki dada ki kara a
wanan tsanar da tayi maki a yanzu kan rilon yar nan diyan baby da kikeyi yana daga cikon abinda yasa ta
tsaneki haka ?

Ta dauka ban sani bane har mutunci taci masa daya dauko maki yarinyar nan ta manta Nafisa na gidan
take fadin ta rabasu hurda da duk wani dan uba nasu amma baya jin hakan .
Tunda mutumin nan yayi zancen gida a gabanta nasan ya bambarowa yarshi magana har su kuwa indai
dubune ki zuba ido kiga yadda zasu kwashe da ita a gidan nan yanzu.

Ai tunda ta gane inda take hasashen yana narka kudinsa ba a nan abin yake ba yar nan a yanzu nata ya
sameta kuma da dubu a gidan nan zakice na fada maki wanan zance kuwa indai itace .

Sai lokacin na dan murmusa ina gyara kwanciya tace aiki barsu zakice na fada maki don sai ta
zazzagewa yarinyar nan fushinta tas zataji saukin hakan a ranta yamzu.

Sukan ba zakice tsohuwar nan iya ta haifesu ba son sam basu dauko halin iya ba ta ko ina sai jikokin ne
suka dauko iyan a wajen sanyin hali sam iya baka rashin gaskiya ita a gabanta.

Ni dai har barci ya daukeni ban sani ba a wajen sai dare sosai naji mama din tana tayar dani inshiga
daki na koma daki na kwanta sai safe.

Kamar yadda na saba a kullum hakane ya faru a wanan karon nayi sallah ban zauna ba na shiga aiyukan
cikin daki saida na kawo wirin gada kamar a mafarki naji ya rikeni da hannusa da bai iya dagawa lokacin
sai gashi ya rikeni dasu gam.

Na dago ido ina kallonshi shima ni yake kallo idonsa a cikin damuwa yake magana fushi kike danine
Rahama da nayi maki laifin me kike wanan fushi haka dani ?

Ni ka sakeni ba fushi nakeyi ba na fada ina kokarin kwace hannu na daga rikon dayayi min din sai naji
ya sasauta rikon yana murmushi yace.

Da kina da wayau Rahama da baki fushi dani ba a wanan abin ko kinyi fushi dani ni bana fushi dake
saidai ina son ki sasauta fushin nan naki don bake daya ke rayuwa a yanzu ba.

Hakan daya fada yasa na kalleshi a lokacin ya daina kallona hakan yasa na kyaleshi na share dakin ruwa
na hado nazo nayi mashi wanka dasu yadda na saba nagama na goge dakin na saka kamshi kafin na hado
magani na zauna nayi mai addua na bashi ya sha na kuma hada mashi tea mai kauri kamar yadda na
saba yi mashi kafin duk su kawo abinci sai na tabbatar da yaci wani abin a cikinsa kafin na bude kofa a
kullum.

Bugun kofan da akeyine yasa na nufi kofan don in bude saidai kafin na bude din naji muryan maman
tudu tana fadin haba wanan dukan ai sunji dole a bude indai Rahamace yanzu haka ita ta tashi tunima
tana aiyukanta ai.

Ina budewa Saiba ta kutso kai a cikin dakin kamar zata bankeni naja gefe daya ta kutsa kai ciki tana
fadin munafuncin banza da wofi kawai.

A labe da sunan yaudara ana ha,intan mutane ga hakan Allah dai ya tona maki asiri ai kowa ya gama
ganin ki da abin kunyar da kikayi .

Abin kunya ai yana a gindin kowa don gara da nawa bada katon waje nayi ba da mijina nayi wasu
kuma zarginsu akeyi da mazan waje ai ?
Allah yafiki yafi sherinki nusaiba don ya kwatoni daga sherin da kikaso ki kulla min shigowan mama ya
hanata ban amsa don mama ta shigo cikin daga murya tana fadin .

Yarinyar nan kina da hankali kuwa ina zancen nan an kasheshi tun jiya yanzu kuma kizo da farar safiyan
nan ki tayar da mutane da fitina haka ?

Aina fada maku yar nan bata da mutunci dama nasan ba zata bar zancen nan ba ai kishin mahaukata
kawai ta iya ita.

Niba fitina nazo yi ba nazone a raba kwana abawa kowa hakkinsa tunda ba ita kadai bane kuma bata fi
kowa da za a barta tana abinda taga dama haka ba ?

Kanki daya kuwa to anki a raba kwanan yadda aka saba din haka za ayi ai dama ba wanda ya hanaku
halinku shine ya koreku ba wani ba ko kun tsaya din me zakuyi mashi?

Ki duba ki gani yadda yarinyar nan ta tsaya ta gyarashi ta gyara mashi muhalinsa a cikin ku wa zai iya
wanan din ?

Keko Amina tace hakan mana sai an raba kwana a yanzu mana tabi dare tayi mai fyade tace sai yayi
mata cikin dole yadda yayiwa yar uwarta tunda ba Allah ta sani ba ita ?

Saida na daga kai na dubi iya dake wanan maganan lokacin kafin na mayar da kallona gareshi yana
kurum ya zuba ido yana saurarensu a cikin takaici.

Ashe hayajiyar su yasa mutanen cikin gida sunji sai gasu gaba dayansu sun shigo part din yazid ne a
gaba yake tambaya da iya lafiya da safen nan kuma ?

Inafa lafiya yazidu wanan mara kunyar ta buga muna kofa da tijaranta tunda safen nan wai tazo a raba
kwana a tsakanin su a hakan .

Halama jiya nasan batayi barci ba da zancen hakan ta kwana a ranta shiyasa ta bugo muna wanan uban
sammakon da tijara yarinya haka ba kunya ?

Kawai muji kin turmujeshi cikin dare kina kwantan hakinki wurinshi koda karfin tsiya kuwa hakan data
fada yasa su salima yin dariya a fusace yazid ya juya a kansu yana fadin .

Ku kuma yan abu kazan uba dama shiya hanaku aure ai don iskanci karya iyan ta fada ba abinda zai faru
ba kenan aga kawai ya zubewa mutane.

Wai me take fadane meya kawo fitinan nan kuma haka yanzu da safen nan mama data shigo karshe ita
da Asmau take tambaya cikin son sanin abindake gudana.

Tazone itama a bata hakkinta yazid ya fada yana nunata da hannunsa yace tazone danki ya bata ciki
itama ya fada cikin halin ko in kula a gaban manya.
Wani irin zancen banzane kai kuma abata ciki kamar yaya haka ake bada cikin gatsau kamar tumakai ta
juya wajen saiba din dake tsaye cikin tijura tace nusaiba lafiya kika shigo masu haka da fitina da safen
nan ?

Mama niba fitina nazo dashi ba daga kawai nazo akan zancen raba kwana tunda abin hakane amanan
mu takeci shine iya take min sababi haka .

Ai dole Nusaiba dole iya tayi maki hakan tunda aikin hankali bai hakan ke wace irin fitsarariyace wai
Nusaiba ?

Mama niba wajensu fa nazo ba wajenshi shida ita nazo don kowa zai karbi girkinshi tunda cutarmu
akeyi ashe ace mu bamu iya kula dashi ba sai ita.

To ba za a raba kwanan ba nace ai gara ita Rahama din Allah ma ya gyara yaya ta gane tun farko data
yanke wanan hukunci don da kun halakashi tun,tuni ban sani ba.

Ta dai halakashi mama tunda ita take ha,intarmu kowa kuma yagani ai yanzu ke
r,,zz,z,,z,z,z,,z,d,zd,z,z,z,, muna mu sheda juna dake a gidan
nan .dzzzzzzzzzzzzzzzdzzzz,zzzzz,z,z,z,z,d,zzzzzzzzd,z dzzdddz,zdzzzzzzz

Malam bafa dakai nake ba magana nazo yi dasu za a hade min kai kuma a hanani magana hannu yazid
din ya daga da nufi marinta da sauri maman tudu ta hana hakan tunda mu,,,,,,,,,,

Daga saman gadon da Jafar yake kwancen yana saurare sai ji mukayi yana fadin Nusaiba enough kije
gida nasake don Allah.

Cak ta tsayar da maganarta tana saurarenshi itama hakanma yafi wallahi taje kowa ya huta haba me
ake da wanan hali naki don Allah abu haka ba marmari saboda Allah ?

Yau mamace ke fadin hakan akan nusaiba wanda ba nusaiban ba duk wanda ke dakin saida ya kalleta
tacigaba da fadin me ake da halin yarinyar nan mama ?

Yarinya ba abinda ta rike sai cin mutunci a kullum kuma tafi kowa cin riba a gidan nan amma babu
godiyan Allah kasheshi zakiyi a kwancen ko me ?

Ai dole kiyi hakan tunda kina bakin ciki da wani ya rabeshi ya samu na fahinci yarinyar nan bashi ta
damu dashi ba abinsa ya dameta yanzu ?

Dama shita biyo ai hakan yasa ta shiga ta fita tayiwa rayuwansu kutse ta hanasu zaman lafiya gashi dai
ubanki ya fadi har gida ya saya maku amma duk hakan bai isheku ba.

Saikin kashe min shi da ransa kin karasashi don bakin cikin yana tare da wata a ranan dai Nusaiba taci
zari agun mama ido rufe ba ita ba har mu dake wajen saida ta hada damu din .

Ta kuma kafe sai Nusaiba tabar gidan kota bata mamaki a ranan haka kawai wajen bakar jaraba irin
namu ita ba zata yarda ba in abin ya koma haka duk mu watse mu koma gidan iyayyen mu.
A,a dai su meye nasu a cikin zancen nan ita dai da tayi din ai ta samu abinda take nema ga yaron nan
yau hakkurinsa ya kare ai.

Sun jima suna surutunsu nidai na koma falo tun saiba na dakin nida salima tana fita Saare tabi bayanta
suka fita ta jima bata dawo ba sai daya kai wajen awa biyu sai gata tashigo rai bace tana cewa.

Abu haka ba adalci don Allah aimaka laifi kayi magana kuma ace za a sakeka wanan aida gani kasan
aikin asirine wallahi.

To wa kike nufin yayi mata asirin yanzu waya damu da ita balle ya tsaya yiwa Nusaiba asiri salima dake
zaune kusa da iya ta fada.

Sai iya ta amsa da kinsan dan fara daya suke da ita dole su dauka abinda sukeyi shi kowa keyi a gidan
wakeda lokacin hakan a yanzu kowa abin gabanshi ya dameshi.

Kedai saratun nan baki da halin kirki wallahi yanzu cin mutuncin dan uwanki da tayi bai sa kinji
haushinta ba sai namu ?

Nifa iya kada ki daureni don ban ambaci sunan kowa ba a nan maganata dai nakeyi yaya za a taru a
bata rashin gaskiya bayan kuma ga gaskiya a fili su ake cuta kowa yasan haka ?

Tas tas taji saukan mari a kumatunta saida takai gurfane a wajen yazid dake tsaye kanta yana huci
daga kofa muryan mama ke fadin kara ma yar iska mara kunyan banza kawai .

Ko hakan ma aiya isa iya ta fada yayin da take tsugune tana wani irin kuka a dafe da fuska duk mun
zuba mata idanu cikin mamaki.

Ta jima a wajen su mama na zaginta kafin ta mike ta fice a cikin kuka a hankali na lumshe udanuna ina
nazarin abubuwa da yawa dake faruwa a gidan .

Ranan ko gyaran part din ban samu yi ba don wanan fitinan da muka wayi gari dashi sabo ga yan
uwansa maza sun zo dubashi sun jima a wajenshi basu tafi ba sai kusan azahar muna tare da salima a
dakin mama muna hira.

Wanda hakan yasa na dan sake jikina a nan Asmau ta same mu taso a dauko zancen saiba amma sai
duk muka share zancen .

Nasan halinta tun ban auri mijin su ba tana da son kananan magana ayi da wani a bayansa wanan yasa
ban yarda inyi dogon hira da ita.

Saida darene muna zaune mama ke fadin ai mahaifin Nusaiba ya bugo waya yana bada hakkuri amma
sunce a barta gida har tayi hankali tunda bata da mutunci kowa bata ragawa a gidan.

Wanan yasa na kara sanin cin mutunci baida alheri ga mutum don idan ya tashi tambayanka saika raina
kanka.
Ko yayane ka koyi girmama na gabanka don wanan halin rashin ragowan shiya kaita ga hakan don wata
kila databi abin cikin mutunci dole tsofin namu su tsaya su duba masu a raba kwanan a yanzu yadda
suke so.

Itako Asmau don munafunci sai cewa takeyi wallahi ni sam ban damu da hakan ba kici gaba da
kokarinki Raamah don Allah ya gani ba zan iya yadda kikeyi ba ni.

Da wuri na kwanta ranan don gajiyan dake tare dani har barci ya soma dibana Yanda ta kirani sai
lokacin take tambayana yaya jikina tare da fadin ashe kuma wanu fitina akayi a gidan ?

Ehh kawai nace mata tare da fadin ni bai shafeni ba shiyasa ban daukeshi komai ba na kashe wayana ga
baki daya na kwanta.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/27, 10:34 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣5️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Baifi sati daya ba da wanan rikicin Maria ta haihu ta haifi danta namiji na shiga cikin sahun yan murna
amma banje barka ba.

Don halin,mu na fulani daya motsa ance rikon magana sai bafullace gaskiyane wanan maganan don
kuwa muna da hakan a cikin jinin mu idan kai muna abu zamu ajeshi a ran mu na tsawon lokaci komai
dadewa sai mun dauki fansa akan abin gareka wanan haka yake.

Nima ta haihuwanta na haketa don naki ko nuna zanje barka har akai kwana ukku da haihuwa ta bugu
tana tambayana wai lafiya nake kuwa ?

Amsan dana bata shine ban jin dadin jikina kawao don itama haka takan fada a lokacin Allah ya baki
lafiya Ramaah ta fada ta kashe wayan don ta fahinceni.

Aka kai kwana biyar yaya jafar da kansa yake fadin kinko je gidan Habu

74 / 101