Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
kirakine a matsayina na yayanki tako wani bangare.
Munzo munga waje masha Allah abu yayi kyau sosai Allah yasa afi haka a rayuwa muna fatan hakan
akoda yaushe don Jafar mutumne da kowani mahuluki dake tare dashi zai mashi wanan fatan.
To amma ke kuma ina rokonki da ki natsu ki gyara halin nan naki da kowa ya ahedeki dashi na kazanta
da son jikin banza.
Duk da Jafar yayi hakkuri yana kuma kanyi kuma bai taba kawo karanki kan ya gaza dake ba kema haka
to ina son ki sani ba zamu saka ido kina cutar da dan uwan mu ba don son jikinki.
Jafar namune kema tamuce a yanzu don koba aure akwai hakkin makwabtaka daya zama zumunci
tsakanin gidan mu da gidanku a yanzu donshi nake gargadin ki wallahi in har baki canza halinki ba
Asmau zan shayar dake mamaki sosai wallahi.
Ganin kallon da yan uwan ke mashi yace wallahi kwarai da gaske don sai tabar gidan nan wallahi kuma
in saka Jafar auro mata biyu a lokaci daya su maye ko ina yadda ba zata dawo gidan nan ba.
Meye ranan kazanta don Allah kun tauye yaro ba dama ya dawo gidansa ya huta wari da ganin takaici
ya hanashi zama don tsaban sakarcin tsiya kawai yayi mata tas a gaban kowa tana hawayen munafunci.
Bashi ba duk wanda yazo gidan korafin da yake mata ke nan ko a gabanshine kuwa za aja mata kunne
akan kazantansu.
Ni dau bance zanje ba tunda batazo nawa gidan ba idan ita watace mai lissafi ya kamata ace da muka
dawo asibiti ko daga gidansu tazo ta duba jikina ai ?
Amma sai ta share wanan yasa nima na sharesu ban kula da inje in gano ba ga kuma kummalon mata
da yake cina a zuciya duk da gidana baida wurin da ya kasa amma wanan halin matane ko yayane sai naji
wanan abin koda kadan ne kuwa.
Ita kuma saiba da tambaya da yake mutane da munafunci saida ta samu wanda ya nuna mata gidan ta
tafi ya riga dayayiwa maigadinshi magana don yasan zata aikata hakan yace koda wata tazo ya nuna
mashi photonta yace kada a bari tashiga.
Donshi washegari ta juya ya koma son zai fitane lokacin sunan Amir kawai ya tsayar dashi sai zancen
tarewansu wanan gidan kuma yazo.
Tana zuwa maigadi ya shedata yako hanata shiga gidan ashe harda shirginta ta kwaso nan ko maigadin
nan ya rufe get ba ita ba duk wanda yazo a ranan sanadinta ya hanashi shiga gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/12, 8:14 AM] +234 803 298 6552: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Karfe biyar na yamma ta shigo garin zaria a by pass ta sauka ta nemi shatan mashin zuwa gida kai tsaye
tana bin ko ina da kallo.
Kofan gida ta sauka bayan ta gyara mayafin kanta da kyau don kada a shedata don ita kanta tasan ba
daidai take ba balle wani ya ganta a hakan .
Dakatar da mai mashin din tace tana zuwa bayan ta dan shiga da kayanta ciki kadan tafiya take tana
bin gidan ko ina da kallo indai ba idonta ke mata karya ba a yanzu sai tace gidan nasu a yakuce yake
kamar babu kowa dake zama a cikinsa yanzu.
Daba don sautin karan tv dake aiki shiyan Yazid da shine fara isa ba da taja da baya ta koma waje don
sai tace gidan kaf babu mai zama cikinsa yanzu.
Cikin sanyi jiki ta karasa kofansu ta dan buga tanayi tana waigen kayanta data baro a kofa don kada
mai mashin din ya gudu dashi a tunanen ta uwar zargi.
Bugun kofan da mama dubu taje ga kuma muryan saratu dake kiran sunanta da mama yasata mikewa
da sauri zuwa kofan ta bude.
Itace dai saratu din ce a tsaye tana ganin uwar take fadin mama akwai dubu biyu in biya dan mashin
kudinsa bata samu magana ba illa juyawa da tayi ciki don dauko kudin ta mika mata.
Jun maganan su yasa salima bude kofan part dinsu ta leko tana fadin umm,ummm saratu dama zaki
zone bamu sani ba tana magana ta karaso wajen ta kama mata kayan data jawo niki niki zuwa ciki.
Ban karya ba tun safe wallahi ta fada ta nufi kitchen din mama da salima suka dubi juna suna mamaki
akwai abinci shi ta debo tare da ruwa ta nufo falon.
Ta zauna ta fara ci duk sun kafeta da ido yadda take aika cibi a bakinta kamar mayunwaciya sai lokacin
mama ta nisa ta soma fadin wai sararu lafiya kuwa ta dauki kofin ruwan data zuba tana fadin ba dai kun
gani ba mama ku godewa Allah dana samu kaina gida a yau.
Ta duka taci gaba da cin abincinta can kuma saiji duka ta fashe da kuka mai karfi irin na tashin hankali
din nan da sauri salima ke fadi ke kuma daga magana sai kuka ai saiki dagawa mutane hankalisu kuma ?
Ni take son ta dagawa hankali bayan wanan da nike ciki yanzu ace mutum baida kwanciyan hankali
akan yayansa duk kokarin da nakeyi kanku karshe irin abinda zan gani ke nan kuma ?
Da wani zanji da zancen yan uwanki da suka juya min baya suka bi matayesu koda naki dana yar uwarki
barakha ko salima dake gabana ba aure ?
Mama ai gara salima da bata da auren hankalinta da nake a kwance yake nida suna nayi aurene fa
tunda naje ba kwanciyan hankali kullum cikin tashin hankali da fargaba nike wallahi .
Tana kuka ta shiga labarta masu irin abindake faruwa ta basu labari kaf na irin zaman da takeyi gidan
aurenta da abubuwan daya faru da ita a can din.
Salima ta nisa tana fadin wai wanan lamari dame yayi kama don Allah sai kace wa yanda akaiwa baki
kamar mu kadaine a duniya yau a tashi da wanan gobe wancan za a tashi dashi kuma ?
Ga wanan sakaran taki barin gida sai fitina takeyiwa mutane kuma yaya yace bai mayar da itakuma ta
zauna tana hauka akan sai ta koma sabon gida itama.
Ta saci kallon uwar tana fadin kici abinci kije kinyi wanka ki kwanta ki huta in kinyi sallah har su yaya su
dawo dan basu garin nan gaba dayansu ba kowa garin nan suna wajen tafiya.
Salima kona kwanta ban iya barci yanzu sai inga kamar za a zo min da sabon fitina kuma wallahi na gaji
niba zan koma gidan nan ba kuma .
Ki daiyi hakkuri yanzu ki huta kafin su dawo asan abinyi akai amma don Allah ki daina wanan kuka haka
kina daga muna hankali in kina wanan kukan ?.
Kallon salima din mama tayi don tafita karfin hali a lokacin don ita jikinta ya gama mutuwa da zancen
tana zaune tana ganin kamar a mafalki take gani saratu di a hakan.
Hankalin salima duk ya tashi auren har yaushe akayishi da yar uwarta zata koma haka ba dadin gani da
badon tasan waye saratu ba da sai tace gaskiya hakan ba zai faru da ita ba.
Sun zauna shiru falon kafin saratu ta kawar da shirun da tambayan naga part din su yaya kamar ba
kowa mana ?
Sun kwashe sun bar gidan nan ai suna sabon gidansu daya gina sabon gida yaushe ya gina gida kuma
bayan tafiyana ?
Waya sanar mashi ance gidan ya jima ashe yana aikinsa bai fadawa kowa ba sai yanzu da zasu tare
shida iyalinsa shidasu suka tare ke nan ita Rahama har yanzu tana gidanta daban koya hadasune ?
Haba dai tana nata gida Asmau kuma tana sabon gida saiba fa shiru salima din tayi bata bata amsa ba
ta kawar da kai hakan yasa ta juya ta dubi mahaifiyarsu.
Saiba fa mama bada ita aka tare bane a gidan mama din ta nisa kafin tace jiya ta tafi ta koma gidansu
kaduna jiyan .
Gidansu kuma a to tunda tace bata da mutunci bata iya bin abu sannu ba sai tayi tujara ai taga karshen
tujara a wajenshi kuwa.
Nifa ban gane ba don ta kwana biyu bamuyi waya da ita ba ranan ma na kirata waya na ringing bata
dauka ba nace ko bata kusa da wayan ne ?
Ta dauka tunda kowa laifin ya shafa a wajenta yanzu rashin mutuncinta ya karanto mata karya kuwa a
wanan lokacin don cikinta yayi.
Kema banga dalilin kiranta ba kina fada mata sirin ki tana baradaki a gari tana yawo da sunanki kan
cewa bakiyi dacen gidan aure ba ?
Mama ta juyo a hasale tana fadin ita data dace ai halinta yasa ta zauna a gidan daula ko banda dai
sherin kishiyoyi ai ita Saratu ba a ji tayi cin mutunci ba.
Wai mama meyasa ta koma kaduna kuma ana zancen tarewa sabon gida ko sunyi fada da yayane kuma
yace ta tafi ?
Salima ta mike tsaye tana fadin kin damu da ita ke nan matar da tabi kowa tana fada masu duk abinda
kike kiranta kina labarta mata a waya zaki tsaya jin meya faru ?
Ko ba,a fada ba aikin sani rabuwa sukayi mana dashi zata kawo mai iskanci ya nuna daidai yake da ita ya
sallameta ta kuma koma ganin laifin mamanki a karshe ta hadasu ta zage tsula har tana fadin mama ta
tanka in bata shigo ta murjeta ba a falon nan.
Yau ga yar iska mama din zata duka ai ga mama din kiji a bakinta in,ni baki yarda da zancena ji da kanki
don Allah fita batun wata mara mutunci can .
Mama wai don Allah da gaske salima takeyi haka akayi ta dago tana fadin Saratu don Allah kiji da
abinda ke gabab ki bar min zancen wanan yarinyar mara kan gado.
Eeh lalai kuwa Saiba takai yar iska mamace zata zaga har da fasin ta yi magana ta murjeta duk halarcin
da mama tayi mata a gidan nan.
Aita manta hakan yanzu tunda dan mama yafi karfin mama tace don yabar yarda da ana labawa ga
mama ana tauye mashi hakkinsa .
Nikun isheni da rashin hankalin ku don Allah mama ta fada a tsawace garesu shigowan iya yasa duk
sukai shiru a dakin.
Wa nake gani nan iyan ta fada ta amsa da nine iya ko baki shedani bane kema zamani ke amarya har
yaushe aka kaiki da zaki zo gida ?
Jiya ta amsa ma iyan tana daure fuska don ba shiri sam tsakaninsu wai yaushe tazone iyan ta juya
wajen salima tana tambatanta kafin ta mayar da idonta kan kayanta dake gefe daya aje.
Iya dazun nan ta shigo mama taba iyab amsa takai zaune tana fadin lafiya dai ko sai saratun ta mike
taja bag dinta zuwa daki tabar mama na mayarwa iyan da zuwanta din.
Kwance yake yana barci a dakin matarshi ta biyu yaji sallaman uwargidanshi a kofan dakin ya mike
zaune yana fadin shigo mana fati ta karasa shigowa daga ciki tana gaisheshi cikin hade rai wanan
dabi,antane matukar ba dakinta yake ba yana wani dakin har in ta fahinci ya kwana da mace zata wuni
tana hade mashi fuska a gidan .
Bashi ba har yara a wunin ba zasu gane kanta ba lokacin gata haihuwansu takwas amma yana bala,in
shakkunta ta riga data shige mai gaba sai abinda tace za ayi a gidanshi.
Hakan yasa sauran matan da suka san irin rayuwan kishinsu sukaci maganin zama da ita suke binta
sauda kafa don a zauna lafiya.
Amma ita saratu taki hakan ta dubeshi tana fadin ina ganin fa amaryanka kamar bata kwana gidan nan
ba jiya ?
Da sauri ya dubeta yace bata kwana ba sai wanan matar da yake dakinta tace ta kwana mana don ko
dazun da zan shiga bandaki na ganta har mun gaisa.
To zan mata karya kika nufi ko mai dakinta dai a rufe take inko ta kwana ina take yanzu shiru matar tayi
kada a dora mata laifin daba nata ba a kai.
Ya mike tsaye yana fasin ina zata amma koni naga haske a dakinta da zanje sallah maganan jamilata sai
dai inda sahena tabbar gidan ya mike zai fita ta hararoshi tana fadin in kuma zaka ?
Ya koma ya zauna da sauri yana fadin wai da in dubuta ko tana gidan su ladi don can naga ta lakanci
shiga kwanan ga ?
Na tura ance batazo ba yasa nacema bata nan ta juya ta fita sai lokacin ya samu ya mike tsaye yana
zura riganshi dake rataye.
Dama naji tana waya tana fadin ita gida zata bata iyawa sai ya hauta da fada da kinkaji shina baki
fadamin ba ai dauri ki hwada min in sani.
Ya fita yaga dakin kargame da kwado ya nufi wajen gidab nasu ya tsaya idon matan dake zaune waje
suna aiyukansu duk a kanshi bai damu da hakan ba wuce wajen gidan yana dube dube.
Allah ya gani yana son saratu amma ba yadda ya iya da fati matarshi ta farko don macece ita mai
tsananin kishi da dokoki matukar bata amince da mace ba, bata taba zama gidan.
Don ta shiga gallaza maki ke nan sai kinbar gidan don kanki kuma iyayyen miji suna matukar son ta don
ta iya kissan sace zuciya.
Ajiyan zuciya ya sauke ya dawo cikin gidan hankalinsa tashe yana bada baya yaji matan sun kwashe da
dariyan shakiyanci gareshi baidai juyo ba ya shige dakin daya fito.
Wayanshi ya dauka ya kira layinta ana cewa layin a kashe yake haka ya wuni kira ko wani lokaci amsa
dayane shine kashe layin nata yake.
Ya kira layin yaya J shima ance mai baya samu nan hankalinshi ya kara tashi kada yar mutane ta bata a
hannushi ya daiji idan ta isa gida hankalinshi ya kwanta.
Bashi ya samu wayan nata yashiga ba sai wajajen goma na dare kuma taki dagawa ya tura mata text
tana ina ta bashi amsa da gidansu zaria sai lokaci hankalishi ya dan kwanta.
Ina kwance a falo muna hira da mama Aminu ya shigo cin abincin dare don duk fitanshi bai wuce karfe
takwas a waje ya dawo gida.
Shikewa mama hira da cewa ashe mummy saratu tazo ne dazun na ganta da naje gidan su kauwa anty
salima sako wai yau din nan tazo .
Na dago kai nace Saratu fa kace tazo yace wallahi na ganta har mun gaisa ita kuma matan uncle ance
jiya tabar gidan bayan taciwa mama da uncle mutunci ba irin zsgin da batayi masu ba.
Kai Aminu mamafa taciwa mutunci kace to ba zata iya bane don ance taciwa dubu mutunci aiba abin
mamaki bane tunda bata samu yadda tayi tsamani ba yanzu.
Dama shirin aiba na Allah da Annabi bane akeyi na munafuncine dama yanzu kuma Allah ya nuna masu
abinsu sai haka zai biyo baya rabu da abinda ba a farashi da gaskiya ba dama a haka ake karewa.
Mama dubuce ke dogon sharfin da yasa duk muka tsaya muna saurarenta shi Aminu ya dora da fadin
wai har cewa tayi mama ta tanka a dakin nan tashigo ta murjeta.
Kai fa yace iya ke ban labari kinsan iya ta tsani wanan matar donshi tace azo a sakawa kofansu makulli
kada ta dawo tace zata zauna nan yake bamu labarin taje gidan da suka koma maigadi ya hanata shiga
don an fada mashi ya kulle gida yace ba zata shiga ba tayi cin mutunci ta dawo gida kuma ta dora wani
don mama tace tayi hakkuri ta hau zagin nama din har kowa bata ragawa jiyan ba.
Shine yau tunda safe ta tafi tana fadin ga gidan nan tabar masu abinda mama da danta sukai mata sai
sungani a rabon su kuma wallahi sai ta hanasu zaman lafiya a rayuwansu.
Bata isa ba maman tudu ta fada tace yarinyar nan bata da mutunci ko kadan aniyartane ya koma masu
daga ita har dubu din data marawa karya baya.
Dama ta dawo gidan nan da niyar fitar da Rahama dakinta sai Allah ya nuna masu yana bayanta duk
abinda sukeyi bai taba samunta ba kuma baisa ta saduda ba ga hakan rabu da wanda Allah ya tsarkake
zuciyarsa kaji.
Wai koda ake cewa na fadawa yarinyar nan ta tashi tsaye tayi hankali da ita sam ban taba fada mata
ba balle hankalinta ya tashi hakan yasa nayi murmushi ina fadin.
Mama nifa bafilatan asalice bani sheri ga kowa in kaimin ya bika haka nima idan nayi ba zai barni ba
donshine mu fulani bamu damu da yiwa mutum mugunta ba muke kuma cikin daji zaune da dabbobi
lafiya.
Kai Anty kikace fulani basu mugunta karshe ke nan Aminu ya fada yana dariya Aminu bamu mugunta
saidai ramuwan gaiya a cikin fushi.
Bafulatani duk ka cuceshi da safe shi kuma zuwa yamma sai ya dauki fansa ko shekara nawa akayi sai
mun rama abu ga mutum don bamu mantuwa.
Saida ya tashi mama ke fadin akwai dai ba banza yarinyar nan saratu tazo gida ba dole akwai dai don
in zatazo ai tare da mijinta ko wani nasa ya kamata ace tazo zuwan farko.
Amma haka kimkam ace Saratu tazo dole akwai dai ba bamza ba gaskiya koma meye ai zamuji bari dai
mijinku ya dawo zamuji ko meye don duba ba zata fada ba yanzu.
Allah ya sauwaka nace na dora da fadin ni nazata tazo ganin gidane tace wani ganin gida har yaushe
tabar garin nan da za ace tazo boyewa sukeyi amma auren ba dadi tunda aka kaita.
Can dana je gida nake ji wai ashe yazid yasa an kulle kawunsu gidan yari ko kudinsa ko fursuna yanzu
jafaru ake jira ya dawo aji.
Kuma ance shi yazid din ya koma abuja abinshi ya zauna bayan yasa an kulleshi amma ai kinga dubu
bata fada muna ba sam bata son asan komai kan diyanta.
Shi kuma mijin ku bayayi saida yan uwansa yanzu shi yayanku shike kokarin a sako kawunku din amma
suki sunce sai wanda ya kawoshi