Chapter 26 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   26 / 101

75K to 78K   out of 302.2K words

dan uwasa din hankalisa duk a
tashe yake haka kuma shike gudanar da komai na kasuwancin dan uwan a yanzu.

Zuwan ummah biyu daga kaduna suna wuni a nab su duba jikin nasa ita da maigidanta sai ya ajeta ya
shiga gari wurin yan uwansa.

Ba wani rashin jin dadi ko takura a jikinta tayi fes da ita dama gwanar tsabtace ita don haka gyara a
yanzu ya samu waje.

A kullum ummah tazo takan min korafin yaushe zanzo naga mazaininta saidai inyi dariya kawai banyin
magana.

Ni damuwana yan uwan mu da muka baro a gida duk yadda birni ya lalace yafi kyau mu muna nan
muna jin dadi su kuma suna can bamu san halin da suke ciki ba .

Don ni a nawa ganin banga abinda zaisa ummah ta barsu a can hannun hardo ba tunda ita dai ba
haihuwa take nema a yanzu ba.
Har yakai na kasa magana da zata tafine nake fada mata damuwana akan yan uwan namu maza tunda
ba wasu manya bane dai.

Shine take fadin mijinta ya soma maganan hakan yana son su dawo wajenta don suci gaba da karatunsu
itace bata bada goyon bayan hakan ba kada yan uwansa suce tana son mamaye masa gida.

Ummah ai yasan kina da yara ya yarda ya aureki don haka a taimaka masu su samu suyi karatun nan
suma bata dai ban amsa ba har ta tafi gashi ko wayansu muka kira ba,a samun su wasan dadi suna daji
inda ba service.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,



2️⃣7️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wai habune aka fada a bayanshi jin hakan yasa ya tsaya cak yana dube dube ko zaiga wani fuskan sani ya
kirashi.

Saidai ba alaman wanda ya sanshi a wajen hakan yasa ya dauka bashi ake nufi ba ya kara yunkurawa zai
shiga motan.

A daidai lokacin ta karaso tana fadin Garba sadauki garaba gagare Abu bakari mazan fama baka shedani
ba ko ?

Yanzu kan yasan dashi take magana a lokacin don haka ya dakata tare da juyowa gareta duk da
baudaden halinsa dabiansune gaida nagaba dasu.

Ina wuni yayi mata cikin ladabi ta amsa tare da fadin kwana biyu shekaru da yawa Habu ba zaka
shedani ba duk ku din kuna a raina don abinda na hango a zurian ku.

Uwarku tana da yawan sakaci ga mantuwa habu tun a lokacin naso tazo na fada mata abinda ke faruwa
bata zoba har nabar garin ku.

Banfa ganeki ba boyar Allah ya fada yana kara kallonta sai tayi dan dariyan manya tace kagani na
ganeka kuwa ni mutum ce da bani raina alheri komai kankantarsa idan anyi min.

Balle alherin ka dakai da uwarka yasa naji ina dai son in taimake ku duk da nasan abin ya faru ko dan
uwaka yanzu.

Don yanzu haka yana kwance a gida rai a hannun Allah kuna shiga kuna fita kuna bata kudin ku a banza.

Duk da kamar warkansa yana hannunka a yanzu amma baku san da hakan ba don mantuwa irin naku.

Haka kuma cutarshi na jikin ku habu yana biye daku sauda kafa ako yaushe matukar ba wanan sadakan
aka bada ba.

Duk da akwai hannun maki don abune da yayi yawa a tare dashi shiya nasa ya kaishi kwance amma ko
ku baku tsira ba gaba dayan ku matukar ba wanan sadakan aka biya ba.

Ba na fada maka a ranan tafiyan ka a kofar gidanku ba na fadama alherin ka da nasara yana inda ka
dosa a lokacin tabbas nasan zaka hadu da wani abin alheri a can da zai iya fin karfin abinda ke bibiyan ku.

Wanan kawun naku yasan komai kuskuren daga gareshine shiyasa yake jin nauyi a yanzu yadda zai
gyara kuskuren nasa.

Haka kuma ku din kuna da kariya daga Allah don kuna da alheri sosai kaida dan uwanka harma ince
shiya fika.

Cikin yardan ubangiji kuma kayi nasara a nan Habu don baka bar alherin naka ya salwanta maka, ba a
lokacin don a yanzu haka kana tare dasu a hannu .
Matsalan saidai kada ka yarda kai sakaci irin na dan adam kamar yadda iyayyen ku sukayi a baya11q.

Kallonta yayi kafin ya katseta da fadin Mama kece matar nan mai maciji da tazo gidan mu a baya ko ya
tambayi matar cikin mamaki ?

Sai yaga tayi murmushi tana fadin nice naso fada maku komai a lokacin tun hakan ba faru ba amma
mahaifiyar ka bata maida hankalinta ba.

Zanso kubar yarinyar nan ta bashi maganin hannunta don mai gaba daya akai mashi itace zata iya
kwatoshi ba tare da komai ya sameta ba koya sameshi.

Amma bayan ita duk wanda zaice zai taimaka maku akan matsalarsa karyane hakan saidai maishi yaci
kudin ku kawai.

Nata dai din shine maganinsa don shi wanda ya bata makarin bai san iya amfanin shiba dabai bata ba
itama tayi arziki dauko wanan abin daga wata kasa zuwa wajen ku.

Ka tambayi dan uwanka dake kwance zai fada maka komai don yasani a yanzu babu maganin da yake
sha da yake mai amfani kamar wanan da take bashi a boye.

Mahaifiyar ku kuma ka fada mata nace inda ta nemo haihuwata tayi gagawan zuwa ta biyansu
sadakansu idan ba haka ba an dinga bibiyan ku a cikin sauki sauki ana halaka ku.

Su kuma wa,yan nan yaran dake cikin ku a yanzu sune saukinku dob kamar kariyane a wajenku.

Saboda abinda ke bibiyan naku basu iya masu komai akwai alkawari a tsakanin su dasu tun na asali
amma suma basu sani ba akwai dafa,i a jikinsu dashi kuma ake haifansu .

Ko wani mahaluki daka gani a duniyan nan akwai wani sirin rayuwa a baya a tare dashi tun na
kakaninsa saidai yai ta mafalkin abin ya dauka mafalkine kawai.

Saidai mutanen yanzu basu sanshi ba kamar na da saboda wayewan kai da suke amfani dashi a yanzu
sun watsar da komai na baya.

Wanan yasa kaga ciwo yayi yawa ga dan adam naba gaira ba dalili da asibiti saidai su camfa kawai don
su lalaba mutum.

Don haka kuma muddin suna tare daku a gida daya wani mugun abu ba zai taba cin maku ba sai alheri
saiko idan aka samu akasin hakan kamar yadda ya samu dan uwaka din.

Falkawa yayi yana zufa duk da sanyin AC dake dakin amma zufa yakejin yana tsiyayya mashi abinda ya
gani a mafalkin nasane ke dawo masa wace yarinya ke nan wai ake nufi ?

Amma zai gwada tambayan J din kamar yadda ta fada yaji idan da wata yarinya dake bashi magani
basu sani ba ?
Idan har hakan gaskiyane dole ya fadawa mama dubu wanan magana asan abinyi shi wanan maimagini
na Niger abinda ya fada masu ke nan duk yadda akayi wanan abin yana da salsala daga mama din ke
nan.

Allah Allah yake gari ya waye ya nufo gida don yana katsina yai wanan mafalki duk da ya dauka karyan
mafalkine hakan don dadin barci amma zai gwada tambayan J din kamar yadda matar mafalkinsa ta
fada.

Abinda ya faru tun haduwansu da matar ya kama dawo mashi sabo gashi kuma shi J wani lokaci saiya
kama salinta jikinshi na saba irin na macizai.

Abinda da daure kai a cikinsa duk yadda mutum yai tunane abin ya wuce hakan gareshi Allah dai ya
bada lafiya kawai za ace.

Watau akidar nan ta mutanen baya kakannin kakannin mu da sukai ta shirka wa yan nan abubuwa suke
bibiya wani lokaci don suna biye da zuri,a har karshen duniya don alkawarin da aka dauka a kansu.

Shine zakiji ana fadan wani nada iska ko wance iskansu na gadone ai ko wani ciwo ya kamashi ba a san
takamaimain ciwon ba Allah dai ya kyauta kawai za ace.

Mafi A,a lah shine bawa ya koma ga Allah a kula da addua da sadaka da taimakawa bukata nakasa dakai
komai kankantan alheri wata rana sai hakan yai maka rana.

Da irin wanan tunanen a zuciyarshi ya shigo garin zaria kai tsaye gidansu yaiwa tsunke inda maigadi ya
bude mashi get yai arba da kawu dake tsaye yana waya.

Suma ido suka zubo mashi suna mamakin dawowanshi a ranan don ya fada masu sati daya zaiyi a can
saiya tsaya yaga komai ya kankama ga aikin gidan man nasu da akeyi.

Sai gashi kwana guda sunga ya dawo garin kuma koda ya fito mota wajensu ya nufa suna mai barka da
hanya ya runsuna ya gaishesu.

Lafiya dai ka juyo yau kawu ke tambayansa yace lafiya kawu wasu takarda zan dauka kuma sai an
bincika yasa na dawo da kaina.

To aida sauki hakan sannu da hanya na dai dauka don jikin dan uwan naka kajuyo kuma ince Jafar kan
jikinshi Alhamdullahi jiki a na samun sauki sosai ai.

Mikewa yayi zuwa part din ya J din inda ya samu Nafisa na shara ni kuma ina mopping a bayanta ya
shigo muna gaidashi da hanya.

Ya amsa muna tare da shigewa dakin da dan uwan nasa yake kwance da sallama dan juyowa yayi yana
kallonshi yace Habu ka dawone ?

Na dawo J ya fada yakai zaune saman kujeran dake gaban kadon yana fuskantarshi yayi mai ya jiki shi
kuma yana tambayanshi hanya ?
Jiki da sauki ya fada a hankali cikin yanayin ciwo ya dan kura mashi ido na dan lokaci kafin yace J akwai
wata yarinya dake baka maganine bayan su mama ?

A hankali ya juyo kanshi ya kurawa dan uwansa ido yana nazarin fuskansa da tambayan daya jefa
mashi kafin ya mirgina kai gefe daya yana fadin .

Meyasa kake tambayana hakan ina son in tabbatar ne kawai don wanan zancen na dawo garin nan
amsa kawai nake son ka bani ?

Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin ya furu iska daga bakinshi bayan dogon nazarin daya gama a kasan
zuciyar shi don bai san dalilin tambayan da dan uwan nasa ke mashi ba ?

Akwai ya fada a takaice yana kawar da kansa gefe daya don sauraren abinda zai fada din game da
zance.

Wacece ita J ya kara jefa mai tambayan shiru na dan lokaci kafin J din ya juyo gareshi cikin tsare gida
yana fadin kai inda aka fadama basu sanar dakai ko wacece ba.

A,a sun daice in tambayeka kasan hakan zaka fada min ina son sanine don a tsaya ga magani daya ba
tare da dora wani ba akan hakan.

Ok to Rahama ce ta wajen ka tace daga gida aka bata makarune amma sirine bata son wani yasan da
tana min amfani dashi kada a fahinceta ta bai bai amma gaban Nafisa ta fada min don kafa hujja koda
wani abu ka iya tasowa.

Rahama dai Rahama kanwar maria Rahaman nan dai dake waje na itace kuma naji sauki sosai don
tunda na fara shanshi gabban jikina suka daina ciwo hakama kaina .

Da wanan abin dake rike min makogorona duk yanzu na daina jinshi sosai a jikina karfin jikin ne dai da
banda.

Rahama ikon Allah Rahama dai dama abinda ake yawan nuna min ke nan akansune shine alherin da
ake nufi tabbas hakan ne kuwa don a wanan tafiyan na hadu da maria.

Kana yawan mafalkin ke nan kai ma ban taba dauka ita bace amma ina yawan ganin rabin fuskan maishi
tana neman taimako a waje.

Idan nazo in taimaka mata sai kuma inga nita taimaka saidai ban dauki wanan mafalkin da ma,ana ba
sai yanzu da kake wanan maganan .

Amma idan Rahama ce kuwa ,,,,,,,

Me Rahaman tayi muryan mama dake shigowa ya baiyana a dakin da sauri ya habu ya dago yana fasin
zancen aikin da yaran nan keyi mukeyi mama .

Ki duba yadda cikin yan kwanakin nan yaran nan biyu kacal sun gyara wajen nan haka gwani ban
sha,awa dashi wallahi.
Ai kaidai bari kawin kuma saida yai wanan maganan jiya ni yaran nan na rasa irin haukan kurciyan su
yanzuma kawun ku a kansu yake min magana waje.

Wai mahaifin ita Asmau ya matsa da zuwa gidansa akan ya ban hakkuri kaga dai rashin su yasa munyi
magani a tsanake so nake kowacen su takoyi hankali a gidansu.

Duk da ita wanan Nusaiban da alama ba hankalin zata koya ba tunda ta saba zuwa gida ta zauna shiyasa
wanan karon nake son su dauki lokaci a gidajen nasu har iyayyensu su fahnci rayuwan da sukeyi a
dakunan su.

Mata ku zauna baku iya komai ba sai kazantar tsiya da sherin duniya kala kala bayan wanan basu iya
komai ba sai daukan kai su wata tsiyace.

Aiko yanzu sun horu mama ki barsu su dawo hakana don Allah abinda takaici shi bai gujesu ba don
halinsa sai sune suke kyamatarshi habu ?

A gaban mu wanan yarinyar ta nuna hakan fa haba dai don kwatoshi cikin bari a horasu tunda ba
tsoron su akeji ba mana abin yayi yawa shege da hauka.

Idan dai zasu dawone su dawo kawai duniyace ai zata gyarasu gaba ina kawu ya tafine habu ke wanan
maganan shi jafar yana kurum baice uffan ba a lokacin tunda aka dauko zancen matan nashi.

Ya tafi kaidai wai yana da daurin aure bayan sallah kuma muka tsaya muna magana bai fargaba har
lokacin ya dan shige.

Ok mama wai nace ba don Allah wani tambaya nake son nayi maki kuma kada ki damu tambayane
kawai jin hakan yasa ta zauna tana kallon dan nata.

Nace mama ko a baya kin taba yawon neman haihuwa haka ko amsan wani magani kan haihuwa a
wajen wani ?

Magani kuma gaskiya kona taba ba zan iya tuna hakan ba wani abune akace game da hakan eeh to
ance gaskiya.

Don yadda aka fada min kamar kin karbo maganin bisa ga sharadin cewa idan bukata ya biya zaki koma
ki kai masu wani abu .

Sai kuma da bukatan ya biya mama baki koma ba wanan yana daga cikin abubuwan dake damun J a
yanzu in ma ba ai hankali gaba dayan mu wanan matsalan zai iya shafan mu.

A ina kaji wanan zancen Habu tana tambayan dan nata cikin zuba mata idanuwanta don jin amsan da
zai bata don zancen ya taba mata zuciya sosai.

A baya kan lokacin da bata haihu ba anyi neman magani duk wanda ya kawo kuma tana gwadawa ita
yanzu yaya zata iya tuna hakan.
Mama ina son ki tuno kafin kiji yadda zancen nan yake san nan kuma zancen maganin da J yake sha a
yanzu duk za a dainasu akwai wani wanda zan ba Rahama ta kawo maki yana a mota shi kadai za,a dinga
amfani dashi har kwana biyu a gani.

Ko me kikace mama shiru tayi kafin tace a sanyayye a gwada din aiba a ki ta magani ba sai an gwada
akansan na kwarai inji ba haushe .

Yanzun ai lalube mukeyi a cikin duhu Allah yasa a dace din ya bashi lafiya shida sauran al,umman
Annabi baki daya suka amsa da amin.

Sai aiwa kawu bayani ya dan tsagaita zuwa wajen karbe karben da yakeyi din yanzu a gwada wanan din
sosai a gani ta amsa da insha Allahu.

Sun dan jima kafin ya mike zuwa part dinshi a gajiye anan ya sameni dauke da Abbati dakinsa ya shige
matarshi ta bishi hakan yasa na fito zuwa part dinsu iya don nasan anty nafisa tana part din.

Ina shiga na samu Saare tazo nasan kuma a nan zatayi weekend tunda alhamisce Allah ya gani duk da
gidansune banyi maraba da ganinta ba.

Haka na gaida ita a darare ina kokarin zama take fadin kai dan fillo miko minshi nan kafin na kaiga
mika mata iya ta karbe da fadin dan fillo kuma kun basune ?

Ai dole mu basu dan nema baisan kowa ba sai uwayenshi bakin kiuyane dashi iya baya yarda da kowa
a gidan nan.

Ki daina fadan hakan ran mahaifisa ba zaiyi dadi ba ranan dayajiki da aida gidan ubansa aka san asalinsa
ba fannin uwa ba.

Ai fulanin basu kadai bane ko ita Asmau asalinta ai fulanine saidai sun zama yan garin nan yanzu don
ko yare basu iya ba gidan su.

Nafisace ta fito daga daki tana fadin Ramaah mamace kadai a wurin yaya wallahi ban sani ba anty
nafisa tunda na fito ban koma part din ba ina shiyan mu.

Saida ta mede baki take fadin yanzu kune kuma masu kula da ya j din duniya tai maku dadi matanshi
sun tafi kun maye gurbi.

Haba dai Saare wanan wani irin maganan banzane zaki fada haka idan munyiwa yaya hidima laifine
yaya mukaiwa ko kan mu ?

Shike nan don matansa ba zamu kulashi ba ko suna nan ai dole mu kulashi tunda lalura ya kama na
hakan kin taba gani mutum ya guji dan uwansa ?

Zaki mayar min da zance wani abin kuma niba nufina ke nan ba gani nayi dai bai dace ba inda baku
kulawa din ai mama ba zata iya ita kadai ba ?
Oky hakan laifine ko to ba don wani abu mukayi ba don Allah da mama dashi ya J din mukayi inma kina
zaton wani abune.

Ta mike tana fadin nifa Nafisa ba wani abu nake nufi ba ato shiyasa ban damu da zuwa ba son gudun
hakan da kayi magana ayi kokarin juya maka zance zuwa wani daban.

Kallon mamaki nake mata nasan dai sabodani take wanan zancen a kofa suka hadu da mama dake
shigowa tana fadin hayaniyar me nake ji haka wai ?

Banda wanan figagiyar mai zubin yan ruwa kinsan ita bata rabo da abin fitina na rasa yadda yar nan ta
koyi tsegumi a gidan nan.

Meya faru Nafisa tace ba komai mama ba zaki fada ba kina tsoronta ne tace wai cewa tayi munji dadi
an sallami matan yaya mun maye gurbinsu da mu barki ke kadai da kika koresu kiyi jinyar yaya din .

Allah sarki ke kan kinyi hasara wallahi baki san takaici ba sun maye din sai ki dawo dasu dakunan su
insan kin cika yar nema mara hankali.

Daga zuwanki kina son ki haddasa min bacin rai abinda yaran

26 / 101