Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
dawo ba nace ta kira da wayar yayanta dazun wai
kumshine basu fara da wuri ba nace tabari sai gobe ta dawo ba matsala.
Jana yayi muka koma falo bayan na rufo kitchen din muna zama kuma ya shiga waya hakan ya ban
daman samu na sulale zuwa daki don lokacin a tsawale nake jin kaina wanka nayi na shirya sosai na
lakace jikina ko ina da humran mama na maiduguri a jikina.
Yana falo kishigide yana waya a cikin natsuwa idonsa yana kaina harna karaso ina fadi a hankali na
kawoma ruwan shayine yanzu ?
Kai ya gurgizamin yace ki bar shayin nan a koshe nake yau Rahamce ashe da yaya Habu yake waya na
dai ga yayi murmushi yana miko min wayan na karba.
Naji muryanshi yana fadin Rahama kina son J yafini kiba ke nan kike faman dura mai abinci haka ?
Murmushi nayi don ban iya wasa haka dashi ba da yake jana dashi a yanzu tunda na zamo matar dan
uwanshi din.
Munkai wani dan lokaci a falo kafin mu koma daki da sai lokacin ya gane fashin sallah da nakeyi tunda
ya fahinci hakan naga mood dinsa ya canza .
Ya lafe yai shiru sai can naji yana ajiyan zuciya yace na dauka cikine dake ai Rahama da sauri na jiyo ina
fadin ciki kuma yaya ?
Kamar ba zai ban amsa ba sai kuma can yace baki son haihuwa yanzu ke nan nayi kasa da kaina ina
fadin ba wai banso bane yaya in Allah ya ban ina so mana .
To Allah ya bamu ni ina son haihuwa sosai wallahi ina son ganin kema kin samu rabonki dani tun ina
raye da raina.
Yaya kana kashe min jiki idan kana wanan maganan dazun ka fada yanzu kuma kana fadan hakan sai
naji yace ana son bawa ya dinga tuna duniya ba matabbata bace a gurinsa ai.
A raina nace lalai akwai abindake damun mutumin nan abin kuma babbane daga Allah saishi saiko kila
yaya habu suka san komeye matsalan don bai fada min ba.
Haka na kwana da damu akanshi washegari zuwan su Salima yasa na dan sake shi kuma ya fita ya
barmu a gidan bai dawo ba ashe yana can gidan da yan uwan saiba suna fafatawa dashi kanta.
Da yamma kuma yan gusau suka dawo zuwan Ibrahim daya dawo da mota yasa muka fahinci hakan sai
gashi shima ya dawo suka zauna tare sukaci abuncin rana dana aje mashi.
Aiki mukayi sosai har dare ba hutawa duk mun hada komai don washegari suna sai dare na samu na
kwanta da asuba kuma muka dora abincine don yan zanen suna da za a fita dashi da safe.
Na aikawa makwabta dashi duk daba shiga gidajensu nakeyi ba kuma sunji dadin hakan da mota su
ibrahim suka jida zuwa family house dinsu.
Muka dora wani kuma da za akai part din mama duk da suna abinci suma a gidan sai wajajen two na
rana suka kwasa suka tafi nace dasu in ya dawo zan samesu daga baya duk da nasan yana da wuya inje.
Koda ya dawo din bai nuna alaman zuwana ba sainice nace dama kai nake jira zancen zuwa can
gidan ?
No ba sai kinje ba tunda kinyi aiki a nan kowa yasan kin gaji ai ban kara maganan ba sai darene mama
takira waya tana tambayan dalilina kin shigowa suna ?
Naji yace shine ya hana don munyi aiki mungaji donshi yace in zauna ba sai naje ba din ni dai nasha jinin
jikina ina mamakin mama da halinta a kaina yanzu ?
Don nice dai bata so da danta har bata iya boye hakan acikin ranta na kula duk abinda zanyi laifi mama
zata kirkiroshi a kaina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/9, 10:26 PM] Zainab Idris Makawa Writer: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Barci nasamu nayi sosai washegari don babu kowa gidan har biba a can ta kwana wajen su anty Salima
dagani sai shine a gidan shi kuma ya fita tunda safe .
Ina kyautata zaton yan uwan saiba ce zasu koma gida a washegarin suna din don haka na samu nayi
barcin gajiya mai isata da yake ina fashin sallah donshi na samu har karfe hudu ina kwance saidai fitsari
ya tayar dani kawai.
Karfe hudu na samu na mike na shiga wanka na fito na shirya na fada kitchen don girka muna abinci
ina gab da kammalawane naji tsayawan motanshi alaman ya dawo ke nan lokacin.
Ko ina na gidan fes yake sai kamshi ke tashi ga kuma na girki dayake dan shigowa ciki lokacin
muryanshi naji yana shigowa a zatona na dauka waya yakeyi ashe shida iyace da habiba suka shigo.
Ina tsaye daga kofan kitchen da niyar gaidashi da dawowa sai ganin iya a bayanshi nayi habiba na biye
da ita da dan jakar kayanta .
Cikin murna na hada ina masu sannu da zuwa na dauka ganin idon iya din zai hanashi yadda yake min
idan ya dawo saidai hakan bai hanashi ba don saida yazo ya rugumeni yana fadin how are you ?
Fine na fada ina dan nokewa ya gane me nake nokemawa din don iyace sai naji yace wai iya ai zataji
dadin ganin yadda kike ban kulawa don itama hakan take son na kasance.
Ni dai na wuceshi ina murmushi zuwa wajen iya din ina kara mata sannu da zuwa na nuna mata kujera
ta zauna a sama tana fadin masha Allah abu yayi kyau sosai wallahi haka ake so a rayuwa dama cigaba
aiba wanda yakishi.
Zonan mu gaisa da kyau tana nuna min gefen da take zaune na zauna kamar yadda ta bukata din ina
fadin iya yaya gida ya taro kuma ?
Taro Alhamdullahi ke dai anyi lafiya an kuma watse lafiya sai abinda ba a rasa ba dai wanan kuma ai an
saba dashi kuma ko ?
Habibace ke gaidani na juya ina fadin biba yan suna nayi ta zuba ido jiya inga dawowanki shiru ta danyi
murmushi tana fadin ban samu wanda zai dawo dani bane har dare yayi na kwanta a can.
To bagashi yau kin dawo ba bata da sabo kin ganta nan taki sakin jiki da kowa amma yanzu kinga tana
zuba kamar ruwan sama.
Mukai dariya na mike kayan da Biba ta aje gefe na dauka zuwa dakin da iya zata zauna wanda a nan
Biba take gyara dakin nayi sosai tare da Biba din na shimfida sabin zanin gado dana dauko daga dakina
na wanke bayin tas duk da dama baida datti sosai amma na kara gyarawa nasa kamshi.
Falo na dawo na sameshi tare da iya yake fadin ina kika shigane haka nace ina gyarawa iya dakine sai
naji tace kaji arziki ba a inda aka santa Allah dai yayi maki albarka kinji.
Kitchen nakoma na kwashe abinci na hada miya ina tsaye biba ta shigo ta sameni zata kama nace jeki
huta aina kammala tun dazun kafin ku iso.
Ke kuma ai da gajiya a jikin ki tace banyi komai ba a can wai anty ai gara da bakije ba wallahi ana ta
fada dasu anty salima da matan uncle wai ta aiko a dibi abinci mummy salima ta hana shine tashigo tana
ta zaginsu harda ke da bakije ba din.
Maman tudun wada kuma ta farwa mummy salima din da fada har ta kira uncle shima tace wai an
kawo abincin mai kyau gidanki andafa ba akai can ba gashi kuma yanzu abincin ya hada fada.
Ikon Allah nafada cikin mama sai tace ai uncle yace duk abinda ya sawo nan gidan shiya saya a can
kuma na can din yafi yawa tace dai ya dinga adalci.
Bayan haka kuma aka zauna da yan uwanta akaita fada da uncle din tana ta kuka shine mama tudun
wada tace wai in tashi in fita na koma part dinsu Abba na zauna.
Biba irin hakan dama dole zaki gani tunda kina tare dani ko kingani kibar damuwa saivyarinyar tace
Allah mama tudun wanda bata sonkine anty haka shima uncle ya fada yace me kikai masu meye
matsalansu dake ne wai ?
Muryanshi naji yana kirana nazo yake fadin to bakuwanki zaki kai daki zatayi alwala na amsa da to iya
muje dakin kiyi ko ?
Tafiyan nata daine yasa dole nima na taka a hankali muka shiga har dakin sai fadi take masha Allah
kinga arziki dole ai yarinyar nan tayi hauka sunzo jiya da yan uwanta sai koke koke suke muna wai Jafaru
ya fita batunta ya maida ita bora a gida.
Uwarku kuma kamar sun gama da ita sai wani noke noke takeyi makin ta fada masu gaskiya ta tsaya
marawa karya gindi ita da yar nan saratu mara hankali.
Duk abinda dubu keyi da zugin saratu takeyinsa ni yaushe zan zauna yaro karami yana min wanan
shegantaka in dauka yarinyar dako auren fari batayi ba.
Kinga ki daure kibi mijinki yadda yake yabon nan naki karki yarda ki canza halinki ko gaba haka nake
fadawa yar uwarki wanan zancen don yadda suke hattaranta a yanzu gidan.
Dan dama wanan Asmau din naga kamar ta fita wanan shirmen nasu tunda tasan Allah dayane taba da
kai bori ya hau har abin suna naga ta hado akawo maki amma uwarku ta rabewa mutane duka.
Naman daine na suna nayiwa Jafar magana tasa a debo maku har muka fito bata bayar ba nace iya
nagode ba komai wallahi Allah dai yabashi lafiya tace amin kafin kuma tace dani.
Wai har yanzu dai jikin nasane kome ni naga yana rama a tsaye nake tambayanshi yace min damuwane
kawai da abubuwa da sukai mai yawa kuma.
Haka yake fada iya idan anyi magana baidai fada maki gaskiya bane amma da abinda ke damunsa
gaskiya sai kin zauna dashi kila zai sanar dake damuwansa din .
Jam jam Allah kaza gata a garemu shiko abu na cinsa bai fada tun abu bai baci ba ni yaron nan tausayi
yake ban don da kurciyarsa nauyi ya hau kansa haka ?
Na dai nuna mata ban daki ta shiga tana mita na fito na samu biba ta kammala komai a kitchen din
dakina nanufa na zauna ina azzakar na yamma.
Ban fito ba saida akai isha,i na fito na dauki abincin nakaiwa iya din har ruwan sha dana wanke hannu
duk na aje mata a nan inda take sallah din.
Na koma gefe muka zauna da biba muna hira ta gama addu,a ta shafa ta juyo tana fadin shi dai
mutunci gadarsa akeyi haka yar uwarki take faman dawainiya dani kullum gashi na fito ban samu sallama
da ita ba.
Ayya bari na kira maki ita kuyi sallama din tace hakan shiyafi kada taga rashin hankalina nasan yanzu
ta shigo bata sameni ba.
Itama uwar naku naji tana fadin gobe zata gida ai saigashi Jafar yazo yace dani ai in shirya muzo nan in
kwana biyu daku in huta hakan yai min dadi sosai wallahi.
Kwana biyu kuma iya nida nasha kinzo ke nan baki komawa a nan zamu zauna dake tace haba ina haka
zai yuyu ai sai a zageni nazo nan na tare don kwadayi kamar yadda ake zagin yar nan salima tunda na
saratun nan ba mai ido a tsakar kai.
Na fadawa dubu ai tayi mata aure ta huta da ita yafi zaman ta sai gulma tsakanin yayyun ta da hadin
hasumi da takeyi a gida.
Aure lokacine iya idan yazo koba shiri sai anyi nata harda ruwan ido kinji aiba maneman ne ta rasa ba
ruwan idone kawai ta dafewa yaron nan da akace baida kirki sai karya yake masi ko yaushe gashi turo
magabatanshi ayi zancen aure.
Ina ji masu tsoron irin na barakha ta fada hannun baragurbi azo ana dana sani daga baya ido ya raina
fata shine ya dawo yasa namike zan fito sai gashi ya shigo yana fadin kina nan ashe ?
Na amsa da ehh yake miko min goran ruwan dake cike da ruwa nabi goran da kallo kafin na karba don
ruwan ciki bai min kama da ruwan goran ba.
Ganin na karba da mamaki yake dan wuceni yace ruwan da akace a samo na hadin maganine ai nace
au ruwan doki ko ?
Ya amsa shine Auwal ya samo min a gidan makwabcin su yanzu ya kawo minshi daga inda iya ke zaune
take fadin ruwan doki kuma ?
Yace iya banjin dadin jikin nan nawa wallahi shine wani yace mu samo ruwan a hada magani dashi ina
jin kamar wancan ciwon yake son ya dawo min kuma a yanzu.
Muna ga rasulu ni yar mutum biyu kaga abinda nake fadawa uwarku ko amma ta kasa fahintana sai
shirme ta tsaya yi ita da wanan shashan dan uwan nata.
Wai yanzu ace kamar dauda zai kara aure don jaraba mace tazo ma da goyo har da yayyu a gida ka wani
haukace kana sabari kamar karamin yaro ?
Jiya nan hafsatun take ai tana muna kuka wai dauda ya juya mata baya kan ya kara mata da yaya ko
yaushe yana rugume da dan da akazo mai agolanci dashi.
Har yana batun sabawa Hafsatun da yaranta kaji min abin kunya waya saura wanan auren kazantan
yanzu banda shi mara hankali ?
Ba rashin hankali bane iya abinda yake ra,ayine kinsan mu maza idan muka hangi abinda muke so sai
aga rashin hankalin mu kan abin da zuciyarmu ya zaba.
Kaiya ba irin haka bane wanan yarunyar daya kwaso yar duniyace kaji banda duniyanci da samun waje
zakizo aure da yaya ukku ?
Sai kace wani attajiri dashi a zamanin nan da kowa keta kansa ina dai dan dukiyan nan daya kwamsa na
uwarku da yan uwakane ya ke rudansa har yake ganin shiya isa a yanzu baijin has ?
Kawu aiya canza gaba daya iya ni har abin nasa yana ban mamaki wallahi zai baka kuwa kaida kasan
kanka amma dama ai haka dauda yake kune baku ganesa ba dai sai yanzu.
Kaga matar nan nasa hansatu to makiran matace tun aurensu gaba daya lamarinsa ya canza bari naga
abu zama da wanan yarinyar.
Don akanta nasan dan kauye bala,ine duk abinda ake fadawa bakauye gaskiyane ko wanan zancen
auren naka waya zuzutashi ga uwarku haka banda ita da mijin nata ?
Duk wani makirci da aka kulla nasan ga hansatu ya fito kallon su nakeyi kawai sai ranan da dubu ta
gano gaskiyan zancen da idonta.
Don yanzu kowa baida kima ko mutunci a idanunta banda dauda a duniyan nan ko kara dauda ya gitta
dubu bata iya ketara mashi shi a yanzu na dauka zumuncine na tsakani da Allah sai yanzu na fahinci
makircin hansatune hakan.
Habiba taso muje falo na fada don wani zancen da suka somayi ba jin Biba bane harni wanan yasa na
fadi hakan muka fito don mu basu waje su samuyin zancen da kyau.
Aikuwa dai sun samu kuma har ya amaryar mata da abinda ke damunsa din inda yace mama taki
fahinta a tsaya ai bincike kan zancen gashi duk inda yaje magana daya ake fada mashi.
Jikin iyar yayi sanyi cikin damuwa tace Jafaru kasan da wanan maganan baka fada min tuntuni ba ta ina
yanzu zan somashi dole a zauna dasu muji yadda abin yake ?
Ka bari nasan yadda zan bullowa wanan zance din dauda dauda na fada maku kune baku san dauda ba
ai komai dauda zai iya idan akace tunda yana rayuwa da muguwa.
Kirikiri kaika sani saida Allah ya kawo rabuwan muna dawo gidanku da zama na samu sa,ida da kaidin
wanan yarinyar duk da hakan ta riga tayi min illa a rayuwa saidai aina musulinci kawai a zauna lafiya.
Abincinsa nan nakai masa yaci don har biba tayi barci a nan falo da muke kallo saida ya fito daga dakin
na tayar da ita taje ta kwanta na rufo masu kofan dakin nina na sameshi a dakinsa.
Washegari dole zan fita school ga kuma iya a gidan donshi tun karfe biyar natashi na fara aiki kafin
gari ya haska na hada mata abinci har na rana na samu nashiga wanka saidana shirya na shiga mu gaisa
da ita.
Inda na sameta zaune a kasa tafi ganewa zaman kasan nake gani muka gaisa nake fadin zan shiga
makaranta iya gashi zamu barki ke daya na wani lokaci a gidan .
Allah dai ya tsare ya kare tayi min na koma kitchen na kwaso kayan abincin ta na kawo mata dakin na
jera take fadin duk yaushe aikai wanan aikin haka yar nan ?
Murmushi nayi ina fadin yanzu da safe nan na girka ai har na rana don kada infita in jima a can din ban
dawo da wuri ba.
Allah yai maku albarka ta fada tace kwarai magananki gaskiyane mijinku yana cikin damuwa yar nan
jiya mun zauna dashi ya fada min komai kuma hankalina ya tashi.
Tun za a ke shiri ba sai an dawo ba habu nake son yazo garin nan ina gidan nan ya tara min iyayyenku
muyi zancen dasu muna kallo yaro zai halaka ba a dauki mataki ba ?
Sam basu da tunane wallahi dan nan shine jigo a garemu kaf amma sun kasa tsayawz su fahinci gudun
kada in makavjqra nace ina zuwa don ina biyewa zancen iya ba zan samu class ba ranan.
Dakinsa naje na sameshi yana barci na fito wayan yaya ibrahin na kira shi yazo ya kaimu school ranan
din ban tayar da shiba muna tsaka da lectures ya kirani yana fada na bashi hakkuri na kashe wayan nawa
gaba daya.
A gidan kawu fadane sosai sukayi ashe ranan da iya tazo gidan mu har saida mama dubu ta kaiga zuwa
gidan don sulhuntasu inda take fada sosai kan yadda abubuwa suke taso mata a yanzu .
Cikin fada take fadin abin yayi yawa mana zaman lafiya yana nema ya kaurace muna ayanzu shigowan
yarinyar nan cikin mu ni bai min dadi ba wallahi.
Na kula da zance nan nason zama gaskiya