Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
gane kayan da mukai ta jida zuwa cikin gida shi take nufi nikan ko kusz ban kawo da rabona a
cikin kayan ba don haka ban tsoma masu baki ba nasan dai shima yaya Habu idan ya tashi saya zai sayo
dani donshi ba zaice ya manta dani ba .
Tunda sanadinsa nake zaune a gidan wanda kiri kiri matan dan uwansa suka nuna suna kyashin zaman
mu a gidan mu kuma da muka fisu iya miskilanci muka nuna bamu san sunayi ba ma.
Ruwan shayi kadai nake sahur dashi in kwanta ko ranan inga gama sha na shige daki na kwanta da
yake azumi na kai bakwai ban fito yin shara ba saida gari ya kara haskawa na fito nayi shara da wanke
wanke na koma na kwanta.
Yanzu mama tana gida kamar yadda yayanta sukace ta dawo gida da azumi sai ummah mu da yar
uwata ke asibitin gashi ita Yanda sai an hada mata abinci don ba halin tayi azumi din a lokacin.
Abincinta na dora wanda a yanzu sau daya akeyi da ankai abin karyawa sai kuma na dare donshi
nakeyin wanda ba zai lalace da wuri ba akai mata.
Ina gamawa na koma daki na kwanta ban fito ba sai da azahar daidai lokacin kuma muke fara shirin
abin buda baki a kullum.
Saman gado naga kaya saidai ban tsaya ba na shige ban daki dana fitone na kula laces ne saman gadon
ajiye a cikin leda ban kuma tsaya budewa ba na tayar da sallah ina gamawa na dauko dogon rigan da
anty Salima ta ban nasaka dogon rigar atamface dinkin pitted ya dan matse min jikina kadan don zan fita
kurman jiki.
Falon na fito na samu mama tana gyaran kullum masa da za ayi ranan nayi mamaki ganin hakan gaida
ita nayi ta amsa tana fadin Rahama kin tashi ashe yanzu nake zancen zuci a kanki ai.
Natashi mama na kara fada masa zamuyiwa yayan ku yau tun da safe nake aikinsa na barkine ki huta
tunda kin samu barci yanzu don Allah fitar min da kayan miyan can daga waje mu dora murhu zaifi sauki
ba zan iya yin wanan aikin a saman gas ba .
Na juya na dauki kayan miyan mai yawa a wani baho nauyin sa ya ban mamaki ina fita nake jin mama
na kwalawa yan matan ta kira da su fito su sameta waje.
Icen na hada da komao yadda ya dace a wajen gidan wajen wani dan innuwa kujera na dora mata sai
na nufi wajen famfon waje da kayan miyan .
Alokacin naga ashe naman kaine na saniya guda aka sare yasa roban nauyi sai kayan miya da aka zuba
sama ya rufe wanan din.
Mama ta fito tana fadin kinsan Jafar da hauka yace masa yake so ayi mai yau yasha ruwa da abokansa
na lissafa mai tare da sako tun safe a hada mun wan kullum yanzu buhari ya kawo minshi daga can gidan
da aka niko min.
Nagane me take nufi yasa naci gaba da mamaki miyan muka fara hadawa tunda miyan naman kaine
bamu tsaya sai markaden ya soyo ba irin miyan shinkafa.
Wanda a lokacin mukai mashi hadin gaba daya bayan mun soya mai daban muka lema a saman
markaden dake tafasa a wuta kayan kamshi da komai aka zuba muka shiga gyara wuta idan ya jaye.
Saida mukai sallah la,asar ta fara suya da kanta a zatonta ban iya ba tunda ni bafulatanan dajice ai don
a daji suka dauko mu.
Sukan manta da kaddaran mutuwa ya mayar damu dajin da suka ganmu a ciki din amma komai na
rayuwan bahaushe shine akidar mu.
Saboda iya na koma ciki don tace ita sai an dafa mata shimkafa da miyan da zataci da ganyen salad kai
azumi bakaci ganye ba aiba yi bane.
Har nagama miya na dora shimkafa na fito anty Saare na samu saman tanda tana tuyar waina nace ta
kawo in gwada wutan na gyara na bajeshi da kyau kafin na fara zuba man suyar cikin yan mintuna na
tara waina karshe dai nice na karasa suyan mama tana ta masu kwakwazon hakan .
Tace komai yar nan ta iya duk abinda kasa kanka a duniya zaka iya amma shiririta ya hana ku tsaya ku
koyi girki da zakuyiwa mazajen ku nan gaba.
Su wa yancan mashiririta kuna dai gani mijinsu yana son abincin gargajiya amma basu iya ba sai shirme
daga taliya sai indomi wanan girkin macen arzikine ?
Sai gashi kuma ya shigo da kayan shan ruwa niki niki aka jibgesu a nan inda muken yana fadin ke Saratu
don shi da sunanta na yanka yake kiranta dashi.
Ki gyara muna kiyi fruit salad a jefa kankara ta kalleshi tana bata fuska alaman itafa ta gaji lokacin
mama din tace wai kai don me ba zaka kaiwa matanka wanan wahalan daka jajibowa mutane ba ?
Ya dan marairaice yace mama ai sai naji kunya wa yan nan me suka iya don Allah banda shirme aida su
fito su kama a samu a hada da wuri kada a makara.
No please mama son Allah barsu a can suna zuwa wajen nan aikin zai tsaya ko su tafkawa mutane
shirme yanzu dai a kara da ferfesun kifi irin na ranan da kika bani da safe.
Ga wace ta hada can ai tana nuna mashi ni ta kara da fadin indai kaci abincin arziki a gidan nan itace ta
hadashi ko yar uwarta .
Mama wanda nace dake kamar hadin restaurants din nan fa itace na fada maka ko masa yanzu data
karba tayi bakaga yadda ya fita gwanin ban sha,awa ba shine ma nasa su zuba maka.
Ya juyo ya dan kalloni yana fadin don Allah ki taimaka kiyi min irinsa ga kifi nan a leda an wanke anyi
komai sai ayi yadda ya dace ya miko kudi yana fadin gashi idan za a sai wani abune akara a ciki ?
Da sauri anty Saare ta karbe kudin daga hannunsa uwar tace nan kikaci rani har damina ya sameki
wajen son kudi tandan masan na sauke na shiga ciki dauko kayan hadin .
Dan attah kadan da albasa sai kayan yajin mu na hausa da citta yafi yawa da tafarnuwa da species
kadan na dauka daka na fito sharp sharp don lokacin daya karato na shan ruwa har na gama hadawa ina
jiran ya tafasa.
Naga suna shirme na karba uwar tagumi tayi ta zuba min ido tana kallon ikon Allah tsab na hada fruit
salad din da yaji madara da kankanran da zai sakashi sanyi sai flavour don yayi kamshi.
Tabarama manya guda biyu anty salima ta shimfida masu saman barandan part dinshi data share sai
aka shiga jera kayan abincin harda shimkafan da miyan da mukayi da kunun tsamiya duk aka fita masu
dashi wajen shan ruwan da alale da mama ta hada.
Nikan tun da aka soma kiran sallah nashige ban fito ba sai suke kai da komo akan abokan yayan nasu
abincin asibiti da za a kaiwa ummah na buda baki na fito dashi don dama na damu banji ana zancen
kaiwa uwata abinci ba gashi lokaci ya shige wanda aka dauka don hakan yanzo lokacin dauka.
Sai lokacin naga motoci zasu kai biyar a wajen nasan ashe yawa garesu don abokanshi na kurciyane
dama haka suka taso sunayi a tsakaninsu.
Ummah dataga har lokacin shan ruwa yayi ba a kawo masu abinci ba ranan yadda aka saba saita dan
fita don tasayo dabino da ruwan sanyi a wajen asibiti.
Ganinta yasa wata mace da suka saba take fadin hafsatu yanzu nake zancen yau banga an shigo maki
da abinci ba kizo mu zauna mu buda baki kafin a kawo maki.
Da kunya ummah tace da matar a,a ki barshi zasu kawo akwai abinda ya tsayar dasu ai kila amma suna
tafe nasani haba hafsatu .
Aiko ba sabo haka tsakanin mu akwai na musulunci don Allah zo ko dabino da lemu kisha ga ruwan
sanyi kada kice a,a ki hana min ladan hakan ?
Dole ta zauna suka sha ruwan tare saidai dabinon nan da lemon da ruwa kawai taci daga garesu suka
mike don yin alwala.
Nan suka zauna bayan sun idar suna dan hira matar tana buda bakinta tunda tasan baci ummah zatayi
ba kota matsa mata.
Ruwan sanyi ma gashi ranan tana ganinsu dashi amma haka taje gurin sayarwa ta sayo saida matar
tagani take maganan bata kyauta mata ba meye amfanin zama taren da sukeyi kuma ?
Irin halaiyan ummah na kama kai yasa matar sha,awan ummah din sosai gashi ita kome aka kawo mata
saita nemi matar ta bata koda abin dan kadan ne amma ita bata saka ido ga kowa sai abinda ya kawota.
Har mu dake zuwa mun san da shakuwar ummah da matar don bamu shiga mu fita sai muje mun gaida
mara lafiyan su da matar a duk inda take.
Ainihi matar daga kaduna sukazo ba a cikin garin zaria suke ba saidai suna da yan uwa sosai a garin don
haka gidane masu zaria din.
Tana zaune ta hango yaron yana nemanta ta kirashi yazo da basket da ledan poly bag yana gaisheta
bai bata kayan a nan ba saida suka shiga ciki ya aje.
Ya gaida yanda da ba,a bari su fita ko ina sai idan su suka bada umurnin mutum ya fita daga dakin zai
dan fita yasha iska ya dawo ciki.
Kai bawa ya godewa Allah aduk halin daya samu kansa a ciki rahamace hakan garesa daga Allah wata
zatayi cikinta lafiya har ta dauka ta haife bata taka asibiti ba .
Saiga wasu kuma don son haihuwan za a rikesu gun likita harsai sun haife cikin saboda tsaro irin
hakane sa,an jahiliya mace tayi ta daukan ciki tana samun mata har mahaifa yazo a karshe ya kasa
daukan cikin don wahala.
Ita kuma yanda abinda Allah ya jerabeta ke nan dashi a rayuwanta har wasu naganin hakan samun
wajena kawai da jin dadi irin na wasu matan da sukeyi da gangan.
Bayan na idar da sallolina na shiga wanka na fito na zauna na gyara jikina ina dakin nake jin muryan
Saiba a falo wai tazo idan masa da miyar sun rage a zuba masu su kara wanda aka kai masu sun cinyeshi
gaba daya.
Naji muryan mama tana fadin ba za a rasa masa da miya ba ai fruits salad din daine ban zata yaran nan
sun rage ba ?
Muryan Salimace ke fadin mama kinsan fa nida Ramaah bamuci komai ba sai anjima kada ki kwashe ki
basu duka bamuci ba.
Salima meyasa kike hakane masan nan mai yawa ina zaki kaishi don Allah azumi akeyi balle kice da safe
zaki shi .
Mama meyasa basu fito anyi aikin dasu ba aimu ba bayinsu bane da mukayi tunda aikin mijinsune ?
Sai abin yaso ya zamo kamar fada a tsakaninsu da anty Salima din har Saiba na fadin ai dai mijin su ya
kawo ai masu dole kuma suci ko bata so ai itama zata gidan wasu za a rama masu abinda take masu can.
Muryan ya Habu naji sai lokacin nasan ya shigo gari ashe shima yana garin tunda yamma tare dashi
akasha ruwa.
Shigowanshi gaida su mama shine kashe fitinan da saboda sanyin hali irin na mama ta kasa kashewa a
lokacin.
Saida naji fitan ta na fito ina gaidashi da dawowa ya amsa min kamar kullum ba yabo ba fallasa a
fuskanshi yana tambayan ya gida ?
Na amsa da lafiya kalau nan dai muka zauna suna hira dasu mama wanda hiran akan saiba ce data fadi
maganan banza.
Naji ya habu din yace da mama daga yau duk abinda ya kawo ki barshi yakai masu can kome za ayi suyi
masa da kansu sune dolensa ai tunda shiya ajesu.
Nima dai a raina haka nagani mutum mai mata biyu kamar yaya jafar sai ya tsaya yana wahal da
mahaifiyarsa da kannesa kuma ko kuma ya dauko yar aikin da yace zai dauka mana a baya ya dinga
biyanta duk wata.
Ina zama na debo masa kwara biyu da miya sai gashi ya shigo part din daga rakiyan abokan nasa ya
ajewa mama leda yana fadin.
Kai mama yau kun fitar dani kunya da bakin yan sherin nan kinji yadda Anwar yake santi kuwa ?
Gata nan dai itace zaka godewa yanzu haka zancen ka samu munayi a nan matar ka tazo nan kan
wanan abin tana fadan abinda bai dace ba.
J don Allah daga yau din nan duk abinda ka samu na laluranka ka dinga bar masu can suyi ai suma
matane kamar kowa ?
Me zai gagaresu iyawa da har zata shigo nan gaban mama tana fadin magana haka komai na gidan nan
suna zaton nakane don haka yaran nan basu da daman magana a kai ?
Me tazo tayi nan Habu ba naga Saratu ta shiga masu da nasu ba dazun kafin a sha ruwa ?
Koma dai meye sun din suke da alhakin irin wanan aikin gareka basu mama ba da yaran nan don a
kaucewa fitina irin haka.
Kuma ka kyaleta tunda nayi mata magana ba sai kaje kayi fada da ita ba ita wanan halintane gori da
rashin kunya So ka barta don Allah.
Ranshi dai ya baci amma ya kasa magana don yasan halin matan nasa sarai kome akace tazo tayi zata
iya don yar rainin hankalice ita.
Bai jima ba ya fice daga falon zuwa part dinshi shima ya Habu din ya fita saida mama ta tambayeshi
koya leka asibiti ?
Naji yace ai can ya jima daya shigo gari can ya fara zuwa ya dubasu kafin yanzo gida nan yake fada mata
cewa likitocin sunce jibi zasu shiga da ita suyi mata scaning a duba lafiyan cikin ta din.
Washegari kamar kullum ban fito da wuri ba kamar jiya daine kodana fito a falo na samesu ana ta
kasafin kayan shayi da abubuwan more rayuwa na dan adam a falon .
Nagaidasu nashiga kitchen har lokacin kayan da akaci ya rage suna wajen ba a samu wace ta saka a
cikin fridge ba dole na tsaya tunda miyar baiyi komai ba na adanasu a cikon fridge din.
Rahama ku karbi key kukai min kayan nan a part dina ya habu ya fada nida salima muka kwashe kayan
a hanya take fada min wai ashe ?
Jiya ya J sunyi fitana sosai da Saiba har ya mamareta yana fadin sai ya sake ta don ta isheshi tana son
jawo mai matsala da yan uwansa.
Ina gyaran falon take fadin ai har Saare yau mama taci mata mutunci sosai da safe tace ta daina shiga
part din ya J din tunda duk tsegumi ya taso da sunanta a ciki.
Wayanta da mama ta kira tana tambayanta ina muka tsaya gashi tana jiran mu mu mikawa makwabta
munje can mun zauna take fada mata Ramaah ke gyarawa yaya part din.
Bayan mun dawo muka dauki kayan da aka warewa makwabtansu niki niki muka shiga gidajen muka
bayar ba hutu kuma muka dauki na tudun wanda wanan ya habune ya kai mu da motarshi muka ba
kowa nasa ana saka albarka muka fito daga unguwar.
Ranan kan bamu iya komai ba sai mace tayi muna abincin buda baki ita da Saare saboda mun gaji sosai
a ranan wajen raba abin buda bakin da ya J ya rabawa yan uwa da abokan arzkin su tunda mune kamar
yara a gidan.
Sai bayan shan ruwa a buda baki iya ta soma magana tana fadin gidan nan kan ranan da yarinyar nan
ta barmu zamuji daban .
Yau kadai har munyi kewan girkin yar nan to iya kina nufin ni bam iya girki ba ke nan shiyasa bakici ba
saiga mama kuma na fadin ke salima jeki kitchen ki dumama muna miyar jiya wanan kan ina zai ciyo ga
yaji ga gishirin tsiya miya kamar an wanke kan mahaukaciya haka ?
Fushi anty Saare din tayi tana fadin ita shiya bata zama duk abinda tayi yanzu sai ace bai yi ba Ramaah
ta fisu iya komai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,1
1️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Idan suna gida bamu da hutu sai sun bar garin zamu dan dafa abu mai sauki da zamu bude baki dashi a
irin hakan na fahinci abubuwa da dama a rayuwa.
Na farko komai arzikin ka a waje idan akwai wanda ya daraka naka sai ya zamo babu mai ganinsa saidai
wa yanda suka zama dolen ka su gane maka hakan.
Don yanzu da mai lokaci ake zamani harda wasu uwayen suna nuna irin wanan bambanci a cikjn
iyalansu da suka duka suka haifa.
Zakiga uwa kamar tana shakkar danta don kawai yana da hali shike daukan dawainiyar ahalinsu sai a
koma jin tsoronsa shiya zama kamar bakece kika haifishi ba.
Da yawa a yanzu ana samun hakan ga iyayye saidai akwai jijirtattun iyayye da har gobe suna a
maysayinsu na iyayye din komai mutum ya zama kuwa.
Zaki suma sauran diya suna nasu kokarin amma ba a ganin hakan da sukeyi hankali sai ya koma a waje
daya anfi ba bangaren dake da maiko muhinmancin.
Saidai gaskiya a nan din ina kallon abin kamar da dama sosai don dukka yaran nata biyu tana basu
kulawa irin yadda ya dace uwata gari tayi din.
Don ko shima ya Habu yana tsaye da dawainiya dasu sosai duk da kamar karfinsa baikai na jafar ba da
akewa kallon maikudi a cikin dangi .
Dan kowa ya tashi dai jafaru dai jafaru dai nazo a roka min jafaru abu kaza da yawa haka suke zuwa a
cikin dangi wajen mahaifiyar nasa tunda Jafar din baida tsayayyar matar da yan uwa zasu buga gaba da
ita.
Zakiga abin mamaki a babban gida da abin haushi har dana takaici shi jafar dai ya kasance mutum mai
ujula yanzune zaizo kuna magana sai kuma wani uzuri ya kamashi ya barka wajen.
Ya Habu kuma akwai tsare gida gashi