Chapter 93 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   93 / 101

276K to 279K   out of 302.2K words

wajen irin halin nan.

Mutane sukan manta da arziki na Allah ne duk akace mutum mai arzikine daga Allah bana haye irin na
zamanin nan ba kabar maishi kawai kada ka jefa hassadanka akanshi.

Ire iren halin rayuwan da bawan Allah nan yake fuskanta suna da yawa gana yan uwa a gida don wasu
har yanzu basu san da baida hali irun na baya ba gani suke shi maishine akoda yaushe.

Ga fitinan iyali a kullym sai anyi ance ya samu ya shiga wani hali balle yanzu da abu biyu zuwa ukku
sune a gabanshi na farko zancen haihuwana daya nuna damuwa akai sosai tun anan nasan lalai bada
kudi kamar da.

Sai zancen jikin iya da shine tsaye a kai yana bata kulawa sai kuma salima dake kula da ita din da mama
sai kuma zancen jikinshi da halin rayuwan matsi dake tunkaronshi.
Cikin haka dai ranan na tashi da nakuda gashi ba a gidan mu yake ba gashi saboda alkunyan mu ta
filani na kasa kiranshi in fada mashi duk da jaddada min da takeyi tunda watana ya kama akan in naji
wani abu in buga mashi.

Kasa zama dakina nayi na koma wanan dayan dakin da babu kowa ina sintiri ina gudun wani yazo ya
ganni aga gazawana.

Ya kira waya tun asuba kamar yadda ya saba ban daga ba har rana ya fito gashi hankalinshi yaki kwanci
hakan yasa ya fito zuwa gidan namu.

Kofa na rufe har lokacin ban bude ba yayi ta nocking saida kyat na iya zuwa na bude kofan kafin ma ya
shigo na duka a inda nake don taso min da abin yayi a lokacin sanadin dan tafiyan da nayi din.

Salati ya sake yana tambayan meya faru meyasa ban kirashi ba shi haka kawai jikinsa ya bashi akwai
abinda ke faruwa dani tun dare.

Tashi maza muje asibiti ya fada a gigice na dago ido da kyat na dubeshi ina zufa nake fasin zan iya ai ?

Zaki iya me kin taba sanin haihuwane common tashi don Allah muje asibiti jin hayaniyarsa yasa Biba
dake ta sharan barci fitowa daga daki.

Turus taja ta tsaya tana kare muna kallo tace baki da lafiyane anty ya juya wajenta yana fadin ke dauko
mata wani zani daki da sauri ko kuma tsaya in kira mama dai tazo.

Maman tudu ya kira ya sheda mata ta shirya gamu nan zuwa a dauketa zamu asibiti take fadin a,a yau
abin yazo ke nan ubangiji Allah ya raba lafiya ya amsa da amin take fadin ai a shirye take.

Saidai ka dauko zannuwa kamar uku da kayan jariri a je dashi ya amsa tare da kashe wayan a cikin sauri
yama rude ya dannawa yaya Ai kira kuma.

Yake tambayana ina zanga zani din da kayan baby akwaisu kaina na dago da kyar na dubeshi ina gyada
masa kai alaman akwai.

Ina zamu dauko zanin suna a cikin kasan closter dina don yakai sati dana hada komai don gudun irin
girshi haka nayi wanan dabaran gashi yayi amfani yanzu.

Da kyat muka kai wajen motanshi a nasa yaso ya daukeni naki hakan dole ya barni na taka zuwa bakin
motan muka shiga yake fadawa biba ta kula da gida da kanta.

A hanya muka saida ya tsaya saboda wani yunkuri da nayi kamar zan rike mai hannunsa da yake jan
motan ban tsanmanin ya taba ganin matarsa tana nakuda urin hakan yasa ya gigice sosai a lokacin duk
da dauriyan da nakeyi kuwa.

Saidai tunda mama ta shiga motan dole na daure ga duk abinda nake jin din saboda alknyan mu ta
fulani ban yarda nayi koda dogon motsi ba sai shine ke dan juyowa yana fadin sannu ya lafa ko saidai in
gurgiza mashi kai kawai ban iya magana a lokacin don mama kada taga raunina a cewan mu.
Sun karbeni sun duba kiran da likita yayi mai ya kara daga mashi hankalinsa inda likita ke fada dashi
kan cewa yasan matanshi nada matsala meyasa basu zuwa awo ?

Tana zuwa awo saidai asibitin can na mata take zuwa a dubata likita yace to yallabai gaskiya matarka ba
zata iya haihuwa da kanta ba saboda yaro nason fitowa amma ba hanya.

Anyi arziki ma da yaron yake da rai har yanzu bai mutu ba don haka dole sai munyi mata aiki an cire
abin dake cikin nata.

Zufane ya karyo mashi son haka yanzu idan ka shirya sai ka saka hannu ga takardan nan a nemo muna
jini da wanan maganin muyi shirin aikin yanzu dole sai aiki za ayi mata a cetosu ita da dan nata.

Zufane ya karyowa yaya din lokaci guda yacewa likitan go ahead ya mika hannu aka miko mashi
takardan aikin yasa hannu sai kudin magani da sauran abubuwan da zai sayo din na aikin.

Lokacin daya kira gida yana sheda masu mama na zaune dasu iya tana jin ance aiki tace jam kukan
yaran nan kun daukowa kanku jamgwangwan ace mace bata iya haihuwa sai anyi aiki wanan wani irin
masifa suka jajibo haka wai ?

Assha dubu asha abin naki har yakaiki ga rashin tausayi akwai macen da son kai zai kaita ga askan likita
inba dole ba wata mace ke fatan a fede ta don Allah ?

Kema fa uwace dubu kin haifa kuma za a haifar maki ki tuna kina da yayan nan gasu nan maki har
yanzu a gaban ki kike irin wanan magana.

Keda ya kamata aji furcin alheri na Allah ya tashesu lafiya kike wanan maganan haka nasan ko agaban
yaran nan zaki iya fadan hakan cikin rashin damuwa da abinda kika fada.

Haba iya ace ga yadda yarta take ita kuma yanzu ace sai anyi aiki wanan idan an samu mai karamin
karfi don Allah yaya ke nan za ayi kullum kashin kudi kan mace ?

Rufa min baki don Allah mara imani da tausayi kawai Allah yana nuna maki abinki hakan baisa kin
saduda kin koma gareshi ba har yanzu ?

Da kike aibanrta yaran nan haka yasa mazajen nasu sun tsanesu ko sun rage son da suke masu din ke
dai ki kama girman ki tun bai bare ba kin kasa kwasa.

Balle yanzu ai mama wayewane ga mata mace taje asibiti ko tana iya haihuwa a fedeta don kada tayi
saurin tsufa a idon mijinta balle wanan da nasu yake da dalili salima ta fada.

To iya kinji ko nikan nace haba gaskiya dai a yanzu yawan aikin ga mata ya yawanta wanan wani irin
zamanine muke cikinsa wai tsufan banza da komai wayau ki sai kinyishi.

Ki daiji dashi idan kayane kada ki bari don Allah ki matsa kinji har su gane kina kishi dasu irin haka raini
ya shiga.
Kishi kuma Iyaa su zan tsaya kishi akan me zan tsaya kishi dasu suna yayana da sauri iyan tace, a,a
dubu kowa yasan kina kishi da yaran nan akan yayanki maza waye gwanarki cikin sarankanki kaf ?

Babu gaba dayansu kishi kikeyi dasu kowa yasani ko don ba,a iya fada maki a gabanki ?

Ta mike tsaye da kyat tana fadin salima tashi ki kaini asibitin don Allah kada mu barsu su kadai a can
gashi ance aiki za ayi.

Ke iya ina kuma zaki keda ke fama da kanki tashi nace ki kaini ta fada da tsawa bata tsaya kallon mama
da mamakin furcinta ya kashe a zaune.

Duba min Yazidu idan yana nan ya kaimu in kuma bai nan mu samu motar haya mu tafi salima dai ta
mike tasan mai iya hana Iya tafiya asibitin wanan lokacin sai Allah.

Dole salima ta mike ta shirya suka fito duk da safiyane matan yaya na waje da yaransu suma kansu don
tsamin shiyan basu faye son zama a cikin part din nasu ba wani lokacin.

Yanzun ma ruwan wake da Saiba tayi alale shine bata zubar ba part din ya dauki wari su kuma basu
gane kome ke wanan wari ba saboda kazanta suka fito daga waje suka zauna.

Ganin su iya sun fito yasa Asmau tambayan yau iya fita za ayi ke nan tunda safen nan ta juyo tana fadin
asibiti zamu abokiyar zamanki aka kai asibiti haihuwa za ayi mata aiki.

Aiki kuma har abin yakai can ne shi sani gaibu aisai Allah yanzu Jafaru ya bugo waya yana sanar damu
hakan suna can aaibitin dai tun dazun.

Allah ya raba lafiya ya kawo rayayye Asmau ta fada samun waje itama bata iya haihuwan ke nan da
kanta ko irin na yar uwarta ?

Aikan tunda akace aiki za ayi kema kinsan hakane to shine don munafunci ya fita bai fadawa kowa ko
yana tsamanin wani abune ?

Wa zai tsaya yin wani sheri a kanta ko yar da zata haifa Nusaiba ke fadan hakan cikin hasala tana fadin
shiyasa ake jin mu ni banson harka da munafunci wallahi ?

Kila shima baisan aiki za ayi mata ba Asmau ta fada ta juyo tana fadin kamar ya baisan aiki za ayi ba
tunda haka ta zaba wai ita wayewa oho dai su suka sani ta fada cikin bacin rai.

Allah akbar kishin ke nan fa mata kishiya idan ba ta daina ganin numfashin kishiya ba ko taji an fasa ihu
shine kawai zata numfasa amma wani ciwo ko wani kakanakayi bai hana kishi ga wasu.

Asibitin kuma habu ya fara kira yake cewa dashi muna asibiti da Rahama idan akwai kudi a wajenka
don Allah turo min an rubuta min magani.

Yana hamma don barci yakeyi yace kudi gaskiya ba wasu kudi a hannuna sosai yanzu amma bari in
duba yace ba matsala.
Shiru yayi bayan sun gama wayan ranshi a bace ya kira abokinsa na nan dake juya mai kudin Salima
yace dubu dari biyu yake so don Allah ina asibiti da matana aiki za ayi mata yanzu.

Subbahanallahi aiki kuma gani nan zuwa amma ai sha,anin asibiti dari biyu baiyi gaskiya bari dai in
karaso yanzun nan zan watsa ruwa in sameka kuna wani asibitin ne a ciki ?

Ya fada mai yace gashi tafe har yazo aka shiga aikin bayan ya kawo mai dari hudu duk wani zirga zirgan
asibitin akayi dashi saida aka fito mai da jariri ya tambaya akace za a fito dani yanzu yayi godiya ga Allah.

Mama da Salimace suka tafi gida da yaron don ai mashi wanka suka bar iya da inna data biyo mu daga
baya ita da Nafisa.

Duk abinda yakeyi hankalinsa yana ga dan uwansa yana mamaki furucin yaya habu din don mamaki
shi kwarai yake a zuciyarshi.

Yana aiyana lalai kudi sune rufin asirin bawa yau shine dan uwansa na jini yayiwa hakan gara yazid ya
san baida kudin amma ya turo mashi da abinda ke akwai a lokacin.

Haka yayi ta sintiri da yunwa a cikinsa sai karfe biyu ya koma gida don ya watsa ruwa ya samu abinda
yaci lokacin abokin nasa shima zai tafi yace dashi zaka jini insha Allahu sulaiman nagode kwarai da
taimakonka.

Haba dai dole muyi maka ai J waye silan zaman mu hakan a yau i bamuyi ma ai Allah zai tambaye mu ni
wallahi ba wancan kudin bane kyauta na baka wa yan nan din.

Abinda bai tsamata ba hakan ya sama don koda ya shigo gidan da saiba ya fara cin karo tana shayi a
wajen haraban gidan har ya aje mota ya fito ko kallo bai isheta ba.

Saida ya shiga ciki ga wari ga komai ya fara kwalawa Asmau kira da ita yana fadin wanan warin fa tun
safe nake jinshi a part din nan ?

Asmau ta fito da danta a hannu tana fadin kadawo ashe yaya mai jikin kuma yace da sauki ashe an
sauka Allah raya ya amsa da amin yana fadin.

Wanan warin fa na meye do Allah yaya zaku zauna cikin warin nan kuna ji zai iya illanraku amma kun
kasa duba kome ke wari haka don Allah ya fada yana bin falon da kallo.

A,a warin ruwan waken da Saiba tayi alale dashi jiyane na fada mata yana wari ta dauke taki to
munafuka kina fada mashine don ya dakeni kome ?

Hauka nayi da har na fara duka waike Nusaiba wace irin macece da baki son zaman lafiyane komai naki
nacin mutuncine ke ?

Yanzu ina shigowa asibiti na fito amma kika bini da kallon wullakanci din kina yar rainin wayau ko ke
gaki issasa ki shiga ki dauke ruwan nan yanzun nan kafin na fito.
Ina ruwana da ka fito asibiti tunda ban aike ba asibiti wanan ruwanka kai ya shafa bani ba name zaka
kuma dafa min wai nayima mugun kallo ?

Ai nasan ruwana tunda bai shafeki ba niko daya shafa ai kinga naje har kuma kin gune da hakan ni
yanzu na gane ki sarai kanki kawai kika sani ke saukin abin kowa dai na ciwo aiko ?

Wata sabuwa za a dora min laifin da banji ba bangani ba akai kaje kaji da wace ta jaka zuwa asibiti ta
kwanta don samun waje bani ba ?

Ai kinji nace niya shafa kuma naje ba sai kinyi hakan zaki nuna min ranki a bace yake ba ai dani taje ta
kwanta kuma naje na tsaya din anyi mata aiki ina shike nan koda kudinki nakai ta asibitin ?

Meye nawa malam mu dai da aka raina idan munyi magana ace damu babu kudi gashi yanzu anyi kudin
kai mata asibiti ai tunda tana yar gwal.

Au bakin cikinki ke nan ashe na samu kudin dana kaita asibiti akai mata aiki to kije ki kwanta kema
asibitin sai in kashe maki kudin ko ?

Kai kai kai wai haniyar meye kukeyi hakane kai da kake da mara lafiya kazo nan kana wanan hayaniya
haka kuma kuna saida hali ?

Yarinyar nan mama yar rainin wayauce ya juya yana fadawa mama din yace har da asibiti mutum ya
dawo ba zata barshi ya huta ba nina gaji wallahi tunda bata da ranan gyara halinta ?

To ka gaji mana sai me keko kikan fara halinki ke nan wallahi tunda kinsan hankalinshi na a kwance
yake ba baki kyaleshi koma meye ?

Mama kodaya fita gidan nan bai fada muna matarshi tana asibiti ba ko zai kaita asibiti don ina
tsoronsu yanzu sai ince mashi yaya jikinta ko an haihu ?

Kallon mama din yayi cikin mamaki yaji abinda zata fada sai yaji tace towa ya fadawa ga abinda ke nan
muma saida yaga za ayi aikin aiya kiramu tunda bamu da amfani a zancen ?

Ina dai fadama kayi hankali da mace balle irin shu,umar yarinyar nan data iya kisisina iri iri tun bata kai
nan ba.

Mama kin goyi bayanta ke nan fa zancenki ke nufi ba zancen goyon baya a nan tsoranka akeji daba za a
fada maka gaskiya ba tunda an nayar daku shanun tatsa ko yaushe kuke nan cikin wahalan mata ?

Yarta ta kwanta tace bata iya daukan ciki balle haihuwa yanzu gashi itama ta tsiri hakan farawa da
iyawa saika koma kaita kashe jiki ana tatsanka kaiga mata asibiti.

Ballema ita bata haifo a sa,a ba tunda taszo da kissan ba kudin ta gaji da kwanci ta taso don kanta idan
taga ba abinda sukewa din ta makara wajen wanan kissan.
Kai ya girgiza ya juya zuwa dakinsa ya rufo ya barsu tsaye cirko cirko a wajen sai nusaibance ta kawar
da shirun take fadin wallahi Asmau muna fukace ta karshe wai mutum bai fada muna komai ba take
mashi wani kashe murya yanzu .

Wanka yayi ya koma asibitin Nafisa ya kira yake fada mata taje can gidanmu ta shiryo abinci a
kawowasu mama nan ya bata kudin mota ta tafi.

Koda ya shiga dakin ya samu na farfado ina ina kwance mama tana gefe da jaririn a hannunta tare da
sauran yan family house dinsu da sukazo ya shigo suna gaisawa dashi suke mashi barka da arzikin fitan
kai lafiya.

Ya amsa kafin ya aje masu ledan daya riko dan abinda zasuci a lokacin ya nufi wajen gadon yana min
yaya jiki na lumshe ido cikin gajiya tare da amsawa da kyat nace da sauki.

Ya juya gurin mama yana tambaya yace wai kuwa matar habu tazo mama mama din tace yanzu na kare
zancenta a raina da ban ganta ba nima.

Waya ya dauko yana bugawa habu din wayan ta kusa katsewa ya dauka yana dauka yake fadin sorry J
wallahi kudin ne basu samu ba kajini shiru.

Yace nerve mind nace ka fadawa Matarka cewa muna asibiti anyiwa kanwarta CS an cire da dazun ?

Wai dama aiki za ayiwa Rahama din na zata kunje ganin likitane kawai fa ya katseshi da fadin don Allah
fada mata anyi aikin an cire da tun dazun muna nan Royal da ita ya kashe wayan .

Ya juyo gareni nake fadi a hankali dama ka kyaleta ai yace No a dai fada mata din kada ayi laifi donshi
bai fada ba wai baisan aiki za ai maki ba.

Shigowa likita yasa sauran fita aka bar mama dashi a dakin likitan na fita mama ta soma fadin matanka
fa da dubu koda yake ga iya ai da salima sunzo ba zance basu sani ba.

Sun sani mama ya fada a cikin wani irin yanayi na bacin rai kafin ya juya zancen da fadin yaron yanzu
mai za a bashi ga dai ruwan zamzam nan na sayo da dabino a leda.

Nagani salima zata bashi likita ya shigo barci ma yakeyi tun dazun dai yayi dan kuka kuma aka
lalasheshi yayi barci.

Likitan yace ya gaji da yawa hutu yake so ai an auna arzikine aka sameshi raye yarinyar nan tana da
taurin kai mama tana nakuda tun cikin dare amma bata kirani ta sheda min ba ?

Murmushi mama tayi tana fadin bafulatancefa Malam aiko inba ta zama bafulatanan zamani ba baka
taba jin ta bude baki tacema ga matsalan ta wanan halinsune alkunya da kawaici shi mutane suke dauka
rashin wayewa nan ko alkunyace irin tasu ta fulani da akasani.

To mama kana cikin wanan cindition din baka kikirana kunya hardani zata hada mama haba mama tayi
murmushi tana fadin daga ita har matan habu ai basu yarda akidojinsu na fulani ba.
Mama ni yau ai ina a cikin mamaki sosai wallahi ashe idan baka dashi ba kowa kake a wajen ko yan
uwanka ba mama ni habu zauwa haka.

Ban gama mamaki ba kuma naje gida na samu wanda yafi wanan abin mamaki ace maman

93 / 101