Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ba akace munyi.
Zancen da abakin yan uwanka mukaji suna fadin ga ciwon dake jikinka shine laifin ka dauka ka dora
muna a kai yanzu ?
Na fada maki ai zaki girbi abinki koban fada ba yan uwana da suka fada din banji a bakinsu ba sai naki.
Badai dadi haka yakai yamma dasu a gidan yabasu kudin cefane dana sauran bukata yayi masu sallama
ya tafi ya barsu nan.
Ranan da ta sauka gida tayi mamakin ganin gidan a share tsab komai an gyara ba yadda ta saba tafiya
ta dawo ta samu gidan kaca kaca ba wanan karon har da abinci aka aje mata shimkafa da miya da salad .
Tabarma suka baza a tsakar gida tare da yaranta dake jiran ta bude jakkar tsaraban data dawo dashi ta
bude jakka ta mikawa yaro guda kudi tana fadin amso min coca colan kwalba bata gora ba mai sanyi
zakace a baka yaron ya karbi dari biyar din ya fita sai gashi ya dawo da kwalban cock din dake nason
sanyi a hannunshi.
Ya mika mata ta karba tasa baki ta balle murfin ta kafa kai tana zuka gyatsan da yazo matane yasa ta
sauke kwalban a bakinta.
Ta saki wani uban gyatsa tana hamdallah ta ture abincin gefe daya Aliyu dake gefe zaune ya zubawa
uwar ido tun bayan shigowanta gidan yake nazarin abubuwa da dama game da mahaifiyar nasu.
Daki ya shiga yasa mata kira take amsawa tare da juyowa ta hangoshi zaune saman kujera yana dakon
shigowanta dakin.
Saidai bata da niyar tashi daga inda take zaune din don sai hiranta take zubawa tana bada labarin
abinda ta gano da wanda akayi saidai ba zancen rabon gadonsu da sukayi da yan uwanta a cikin hiran
nata.
Daga daki yaron ya kara fadin mama fa sai kanwarsa ke fadin mama yayana magana dake a dakifa
tundazun kallon yar tayi tana fadin ina jinsa me zanshigo daki in mashi ?
Muna nan zai shige daki yace inzo idan bai iya fadan abinda zai fadi a nan ya bari har lokacin dana taso
yaron yana jin hakan ya mike tsaye ya fito daga dakin daidai lokacin mahaifinsu ya shigo gidan shima
cikin murna da ganinta yana fadin wai baya batada kada ?
Yanzun nan na fita fa ashe har kun iso mun iso malam mun mun sameku lafiya yaya gida da al,amura
kuma ?
Yana washe baki ya samu waje ya zauna a gefenta yana fadin kunsha zaria dai kam daga tafiyan kwana
ukku gaku sai yau din nan muka ganku ?
Tafiyane ya kama haka mun tsaya saida akai komai a gaban mu na samu na taso Aliyu dake tsaye dan
nisa kadan da bayan mahaifinsu yana mata alama da ido sau daya ta kalloshi ta dukar da kai ta cigaba da
magana da mahaifin nasu.
Ganin bata kula dashi ba yasa ya fice daga gidan kofan gida ya koma ya zauna yana dakon fitowan
mahaifin nasa .
Saidai mahaifin nasa yakubu kamar yasan da hakan a lokacin yaki fitowa daga gidan suna can matarsa
baraka na mashi hiran yadda zama nasu ya kaya a lokacin.
Ya gyada kai yana fadin mena fada maki a baya malamin da naje wajen kafin ki wuce aiya fada muna
zai bayar da kudin ba tare da yayi gardama ba.
Yanzu dai aikin gane gaskiyan da nake fada maki cewa kune mata aka tauye su suna amfana da kudin
ku sun gina kansu sun bunkasa sun barku a cikin wahala.
Idan ba yasan ya samu ba wanan kudin za ace an tarawa wanan uban riban haka mai yawa ya dade
yana moriyan abinsa shi kadai ba tare da kowan ku ba.
Hakane ai kafin naje na samu saratu ta zuga mama sosai har mama ta yarda da zancenta cewa da
dukiyan mu yake wanan abubuwan tunda ba binkcike akeyi kansu ba.
Shima kawu daya zo haka yace da mama din shiya bada karfin gwiwan da har aka samu aka zauna
komai kudin kowa ya fito a cikin mu.
Yanzu kuma ai sai ya samu wanda zaiyi facaka dashi da yake dauka yafi kowa yaron nan baida kirki ina
fada maki baki yarda yanzu ai gashi kin gani dama kyautan rufe baki yake maku don kada a tambayeshi
kudin nan.
Jafaru fa kafansa ya dafa kasa malam har kyautan gidaje naji yayiwa Habu da Yazid a wajen kufa ya
tambaya da sauri tace mu ai matane ba zai bamu gida haka bakatan ba.
A,a lalai dole ya kawo maku kudi haka masu yawa ya toshewa kowa baki amma ki rubuta ki aje zai
dawo daga baya yana maku dadin baki ku hada kai a bashi yacigaba da juyawa .
Cabdi yana da wuya hakan don yadda akayi din nan banjin zai karbi kudi a hannun wani kuma nasa
kason ma jiya muke ji da dare wai yace a buge massalacim kofan gidan mu din nan a tayar da wani Allah
ya kai ladan hakan ga baba.
Kaji dan duniya ya fada yana mikewa yau kuma ina mota saratu ta kirani take fada min cewa wai
yayiwa matansa akwatuna da mama dasu har iya na tausan gaba din nan da maza keyi.
To shi sana,an me yake hakane wai indai ba smogal ko safara yajefa kansa a ciki ba yake wandaka da
kudi haka ya kamata a buncikeshi dai gaskiya.
Ance sana,an mai sukeyi yanzu kuma naji yana fadawa iya cewa yana kai kayan ma,adaine kasan waje
akwai samu sosai ga hakan .
Ni yamace yana son ganina kafin na wuce ban tsaya jiranshi ba na taho abina to me zai min yanzu tunda
hakkina ya fito a hannusa ba abinda ya rage kuma ai ?
Mena fada maki dama kudin nan yake son ya biyoki ya karbe yace ki bashi tunda yaga kamar kece mai
taushi a cikin ku.
Kofa ya nufa yana fadin ni zan fita me za a zo maki dashi a daidai lokacin wayanta ke haske bata dauka
ba take bashi amsa da ba komai saidai dan abu mai maiko haka dai ?
Tana duba wayan take fadin ikon Allah jafar dinne fa ke kirana yace aina fada maki zai saka rai ga taki
dukiyan ta dauka da sallama tana fadin bari muji me zaice ai.
Jafar ta ambaci sunanshi yake fadi a bangarenshi Anty baraka kin tafine ban sani ba ashe saida nazo
ake fada min ai kin wuce naso muyi wata magana dake wallahi.
Cabdi nikan gani Gusau ai jafaru da yake tunda safe na taso kasan malam bai son inyi tafiyan dare yace
hakane to an isa lafiya yaya su malam iliya din suke ?
Ta amsa da lafiya yanzu yaya akayi jafaru yace leter on zamuyi magana ai dama zancen Aliyu naso muyi
jin hakan mijin nata yayi murmushi yasa kai ya fice Aliyu dake kofa ya fado dakin yana fadin uncle Jafar
ne mama abani shi don Allah ?
Ya mika hannu ya karbi wayan yana fadin Uncle ina wuni fita yayi da wayan a hannunsa sukai magana
ya gamsu da maganan kawun nasa a lokaci.
Ya dawo da wayan ya mikawa maman nasa yana fadin yace zakuyi magana dashi ya samu waje ya
zauna a gefenta yana fadin.
Mama ina ta maki kwantance da kada ki yarda da duk wani dadin bakin da baba zai maki kada ki yarda
da baba don Allah .
Yana fadin hakan tace babangida banson rainin wayau banson rashin kunya kaine zaka fada min
zancen mahaifinka dana zauna dashi.
Dana zauna dashi da farko har na haifeku kaine kake zuwa ka koya min dabarun zama dashi din ?
Babangida ka fita min a ido tun ban saba maka rai a wajen nan ba wallahi ina ruwanka da sha,anina da
mahaifinka ?
Kallon mamaki ya bita dashi kafin ya mike baki a laikum ya fice daga dakin har ya nufi wajen fridge
dinsu sai kuma ya fasa ya fice daga gidan baki daya
Alkawari ya daukarwa kanshi ba zai karawa uwar tasa maganan komai ba dangene da abinda ya hango
yana tunkarota kan mahaifin nasu.
Yasan tabbas mahaifinsu dabara irin ta miji da mata yake sonyiwa mahaifiyarsu gashi kuma maman
nasu ta kasa saurareb shi .
Idan ya mata hankaline zai tashi a banza don ba fahinta zatayi ba lokacin saboda dadin bakon mahaifin
nasu daya inma bakinshi wajen tsara mutum don haka yin shiru da bakinsa yana kallon irin bidirin da
suke zubawa a gidan
Tun dawowan mahaifiyan nasu aka tsiro cin dadi a gidan nasu inda baraka sai barin kudi takeyi shiko
malam yana manne da ita yana mata dadin baki.
Alkawari iri iri da labarai sai fitowa sukeyi a bakin mahaifinsu donshi yanzu Aliyu ya zama kamar
makiyinsune a gidan don tun ranan da mahaifinsu yai mashi tas yana fadin ya facin Aliyu din yana bakin
ciki da lamarinsa a gidan don haka zai dauki mataki mai karfi akansa yaja bakinsa yai shiru tare da saka
masu ido ga duk abinda sukeyi.
Babu zancen za a bashi kudin jari ko wanda akai mai alkawarin in an samu za a sai mashi offer wajen
aiki da mata garin ma,aikantan gwaunati ke sayarwa.
Hakan yasa ya nemi laban kawunsa Jafar ya kirashi yace yazo Zaria ya samu habu sun riga da sunyi
magana a kanshi don haka daya taso daga gidan bai fadawa kowa ba sai kanwarsu da yace da ita zai tafi
ya nemo kudi ya bar garin.
Zarian ya nufo amma kuma ya samu ance Habu don yayi tafiya dole ya juya ya dawo gida ba tare da
bukata ya biya ba.
Inda Habu yana sane yaki bari ya gana da yaron a lokacin cewan Habu idan anyiwa yaron ai kamar ita
Baraka akaiwa don haka taje taci barnan ta a yanzu tunda tace su diya mazan dakin su basu da taimako
ko amfani a garesu.
Don har matayesu sun fisu dara don akan matansu suke mutuwa ya dawo ya samu mahaifiyar nasu
baraka ta dauki kudin daya rage taba mijin nata don ya juya matasu .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/23, 10:15 AM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Da dare bayan sallah sallah isha,i ina zaune dakina naji dawowan yaya J hakan yasa dana tabbatar da
yashigo na mike na nufo fallo in mashi sannu da zuwa.
Ashe sai lokacin yake shigowa gidan da wata yarinya a bayanshi bayan nagaidashi na kurwa yarinyar
ido ina mamakin in ya fito da ita ?
Shiko ya juya yana fadin shigo mana daga ciki habiba ga maman takima ta fito ai a sanyayye na furta
mai sannu da dawowa yaya ?
Yauwa Rahama an wuni lafiya ya gida wanan yar yaya Ai ce Habiba na dauko maki rikonta zaku zauna
tare a gidan nan.
Na daga kai na kara ksllon yarinyar ina fadin Allah sarki sannu da zuwa biba ko don ina jin sunnanta a
bakin su anty Nafisa.
Ta gyada min kai nace karaso ki zauna mana ina zuwa na mike ruwan sha na dauko mashi nata a
babban gora sai ita dana daukowa karamin gora na hado masu da cups na kawo masu.
Saidana zuba mai na mika mashi ya amsa yana godiya na mika mata karamin gora da cup itama tayi
godiya ya kurbe ruwan yana lumshe ido.
Zama nayi daga gefenshi ya kallo Habiba din yana fadin to Rahama ga habiba nan na karbo rikonta a
hannun yaya Ai daga yau din nan zamanta ya dawo a karkashina dake zata zauna nan gidan tare dake da
fatan zaki tayani rikonta cikin aminci.
Ya kara maida hankalinshi a kaina kasa nayi da kaina ina fadin Allah ya tayamu riko yace amin ke kuma
habiba ina son ki zauna damu a cikin amana banda wuce gona da iri banson ko kadan inji wani abu ya
fito daga gareki don Allah.
Idan kina da damuwa ki fadawa Rahama ko menene zata sanar dani ba sai kin fada a gida ba tun yanzu
idan kinsan ba zaki zauna damu ki fada in mayar dake in samo mata wata da zasu zauna anan tare din
don banson abinda zai taba min zumuncina da yar uwata.
Tayi kasa da kai tana fadin zan zauna Uncle yace to madallah sai ki nuna mata inda zata zauna ya
kasance shine dakinta a cikin daku nan can biyu.
Ya mike ya nufi dakinsa na sauke ajiyan zuciya tare da kallon yarinyar nace taso muje dai kiga dakin duk
biyu na bude mata donta zaba ta zabi daya ta dauko kayanta dake falo zuwa dakin.
Wajenshi na koma yana tsaye yaba kofa baya yana waje na karaso a hankali sai na fahinci da daya
daga cikin matansa yake waya a lokacin.
Ban tsaya ba na nufi bandakinsa na hada mashi ruwan wanka da kara tsabtace wajen na fito a zaune
yake yayi shiru ya kurawa kasa ido.
Ya dago kai ya kalleni nake fadin ga ruwan wanka can na hada maka yake fadin yana kaiwa kwance
yace kina shagwabani da yawa fa Rahama ?
Zan ji daban daga gobe idan ban kusa dake kwana biyun nan kin shagawabani ina jin nima namijine a
yanzu gidansa.
Ko ruwan wanka da nasha sai an bani har kinsa na fara zullumin tafiyan nan da zanyi in barki duk daga
yarinyar nan dana kawo maki amma nasan hakan ba zai tare komai ba.
Daga inda nake tsaye din na danyi murmushi ina fadin ai gara dai a tafi din a nemawa iyali abinci yafi
zama a gida ko yaushe.
Wallahi har kin tuna min da mahaifin yarinyar nan Habiba ban yake ban labarin su da taimaka masu
da yake sonyi ya kara da fadin yana daga cikin dalilin dana dauko yar nan don a rage mata wahala.
Idan Allah ya dawo dani lafiya don Allah Rahama ki tuna min a san abinda za a taimaka masu dashi da
zai tallafawa rayuwansu na amsa da insha Allah.
Ya dan yun kura kamar zai mike sai kuma ya koma ya zauna yana fadin ina ganin dai yanzu ansai duk
wani abinda zaki bukata a gidan nan can ma na gama dasu saidai sun bugo waya yanzu suna min korafi
wai ban sayo masu gas ba nace Nura zai zo ya dauka yakai masu refilling .
Ko har da naku zai dauka din yayo nace nan kan ina ganin ba yanzu ba dan banyi komai dashi ba idan
dai ya kusa karewa ayi min magana yazo ya kai maku koda yake bari kawai ya sayo exctra ya kawo maku
in case .
A take ya bugawa Nura din daya karo mashi exctra a aje ako wani gida har wajensu mama ya mike yana
cire tufafin jikinshi na dukar da kaina kasa cikin kunya ina mamakin yadda sam bai kunyana shi sai kice
mun jima dashi da aure ko mun jima da sabawa.
Ganin ya shiga yasa na tsunce kayan daya cire na adana a gurguje na gyaro dakin na fito falo abinci na
jera mashi nakaiwa Habiba nata a dakin.
Itama na samu harta sauya tufafin jikinta ta saka wani kodaden rigan barci haka a jikinta sai hula tana
zaune tayi shiru nashigo dakin ina fadin har kinyi shirin kwanciya ashe ?
Toga abinci nan kici kada ki kwana da yunwa na fito na koma dakina inda na dan zauna in huta yakai
kamar awa daya sai gashi ya shigo dakin.
Yana fadin badai har kin kwanta ke nan ba Rahama ?
Na dan mike ina fadin a,a ina jiran kafito kaci abincine kai nake jiran ka gama sai in kwanta din yace
kinci abincin ke nan ke kai na girgiza alaman a,a.
Ki tashi muje muci abincin ya fada yana miko min hannun shi dolena na kama muka fito falo duk a
tsarge nake kada habiba ta fito ta samemu taga abinda yakeyi din.
Wayarshi daya zamo mai kamar rabin rayuce ta shiga ruri ya dauka yana tsoki yake fadin ibrahim ya
akayine naji wanda ya kira da ibrahim din yana mashi bayani.
Lokacin na samu daman mikewa zuwa kitchen da kayan dana kwashe na abincin da mukaci din dashi .
Don dole yake sani gaba sai naci abinci kusan rabin ledan da nake sakawa don shine a yanzu nayi
dabaran rage hannu wajen saka abincin.
Har ns fito yana kan wayan a cikin dan fada fada yake bayani inda naji yana fadin wai me isa yake
nufine haka lokacin na fito ya ya futoni da hannu alaman inzo gareshi.
Dole na nufishi hannuna ya kama ya zaunar dani tsakankaninsa yaci gaba da wayansa yana wasa da
sumar kaina wanda ni kaina kitson ya fara isata lokacin.
Amma shi kuma hakan naga bai dameshi ba illa dadin hakan yake masa gaskiya gyara wani abune dake
karawa ma,arauta daraja a idanun junansu wanda sai a yanzu na fahinci hakan.
Don yana gama wayan ya kara kai kanshi saman wuyana yana shakan kamshin jikina da ko yaushe ban
rabuwa da hakan yake fadin zanyi missing din kamshin nan naki Rahama.
Jin hakan yasa na kara narkewa a jikinshi ina murmushi don nidai din na kasa sakewa dashi irin yadda
yake min Allah yagani ban san ya zan iya daga ido nace nayi mai hakan ba a lokacin.
Monday zaki fara fita school nayi magana da Auwal namu kanin Nafisa shine zai dinga zuwa ya dauke
ku har yarinyar nan yana sauke ku a school idan an tashi ya dauko ku ya dawo daku gida saiki karbi key a
hannunsa sai kuma washegari ya dawo ya daukeku din.
Nagode na fada ya dan yunkura yana fadin ban accout number dinki zan tura maki kudin komai har na
man mota da zaki rike a wajen ki.
Tafiyan safiya sukayi inda yaya Habune yazo ya daukeshi na fito ganinsu zaune tare suna cika wani
takarda yasa na dan koma da baya na lebe a cikin labule ina gaidashi da kwana.
Lokacin ya dago yana fadin a,a Rahama antashi lafiya ya gida na amsa a kunyace da lafiya ina su anty
Yanda ?
Baki barin kira min mata da yanda ko aikece yanda din yanzu ba Maria