Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
kira ukku na dauka da sallama
muryan yazid ne yake fadin Amaryan J kina ina don Allah ?
Hanyar garin mu na bashi amsa na kashe wayan ban tsaya saurara mashi ba don ban son yawan
magana tunda mun kwasa da ummah tun isowana.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/1, 10:49 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ban san ya akayi ba ummah ta kira Maria ta sheda mata ina kuduna wurinsu nace daga nan kasan mu
zan tafi amma sun hanani tafiya gida.
Hakan yasa hankali a tashe maria din ta dinga lalubar wayana ina ganin kiranta na shigo min naki dauka
a karshema na kashe wayan nawa gaba daya.
Ina nan dakin ummah kwance sai gata da waya tana fada min in karba yar uwatace a layin, fuska na
bata ina fadin banyin magana da ita a yanzu ummah.
Kina da kafuwa Annini ita meye hadinta dasu da zaki ki fada mata damuwanki kuma ko baki fada ba ki
karba ku gaisa mana da ita.
Dole na mika hannu na karba ummah ta juya ta fita daga dakin ta batmu muna waya ina dauka a dakile
nace hello naji tana fadin Ramaah baki kyauta min ba yaya zakisa kafa ki fito gidan mijinki bayan kinsan
yana kwance ba lafiya.
Kin kuma san yadda ya samu dake a zuciyarsa dole in kikai hakan ya shiga damu gashi ko ya shiga
damuwa din don ana kokarin boye masa tafiyan ki har yanzu ya gane abinda ke _fa_ ruwa.
To ya gane mana Maria ke kika damu da hakan ni yanzu ta kaina nakeyi bata shi ba don gara dashi yana
gaban kowa nasa a gabanshi kuma akeyi min abinda akaga dama bai dauki mataki ba kin kuma sani.
Haba Rahama wani mataki kike son ya dauka shida yake kwance bayan haka kinfi kowa sanin yadda
suke tsoron mahaifiyarsu ai dukkansu mazan matan ne dai basu faye tsoronta bama nake gani.
To suje can suyi ta jin tsoron ta ni ban sake komawa gidan nan wallahi da sauri naji tace ki daina
rantsuwa don Allah haka Rahama idan baki koma ba yaya zakiyi da cikin jikinki ke nan kuma ?
Nace ciki ciki ai zubarda shi zanyi don ba zan yarda in haifi cikin da zaizo duniya yan uwan ubansa na
kirasa da shege ba .
Ke Rahama wanan magana ina ya fito kuma nace a bakin Saratu don tace ba a shege waje sai a gidan
miji macen data hada kwanan yan uwanta tayi ciki wanan dan ake kira da shege.
Innalillahi ta fara ambata tana fadin ita Saare din ta fadi hakan gareki lalai kuwa inta fada akwai magana
ke nan gaskiya amma don Allah ina rokonki da kada ki taba cikin nan don Allah saina kashe wayan don
takaici daya rufe min zuciya.
Sam ya J da kowa nasa har maria dake tare dasu a yanzu sai naji gaba daya sun fice min rai lokaci guda
ina dana sanin saninsu ma baki daya don yadda nake ji din.
Zuciyana ya dake sosai ba wani zancen kuka a gareni yanzu kawai solution nake nemawa kaina a yanzu
wanda kuma zuciyana yafi yarda da in zubar da wanan cikin kaddaran dake jikina lokacin.
Kwanciya nayi na lafe muryan ummah yasani dagowa don tashigo tana fadin ki tashi ki saka wani abu a
cikinki tun dazun kina daki dunkule.
Wayarta na miko mata na dago daga kwancen da nake ina jingina da gado ga abincin nan falo ki fito
kici ki watsa ruwa ta fada a cikin tsigar umurni a gareni.
Bin bayan ummah din nayi da kallo ina son in fahinci fushi takeyi ko goyon bayana don tunda nazo
bata furta min komai ba.
Kuma tana falon nayiwa mijinta bayanin zuwana din mikewa nayi zuwa falon inda na hango abinci a
kuloli tsakiyan falonta waya takeyi daga kofan dakin ta juyo tana kallona kafin ta karasa fita daga falon
gabaki daya.
Abincin na bude inda naga shimkafane da miya sai ganyen salad amma miyar na kifine ko ta manta
cewa ni bafulatanan asalice ban damu da kifi ba oho ?
Su sun iya ci a gidan daddy Abuja tun wani ciki da tayi a yadda take fada muna a baya saini da Abban
mune bama son kifi dan gara danima nakanci miyar kifi din wani lokaci ba tare da nayi amanshi ba .
Shiko mahaifin mu har ya rasu sam baya cin kifi a rayuwansa na gwada ci din duk da budewana naji
yana hawa min kai amma haka na daure na kai a bakina.
Kamar kada ya sauka a cikina da sauri na mike zuwa waje dakin inda keda kasa da fulawowi na duka na
fara shega amai na fitan hayaci.
Sai mai aikinsu ummah dince tazo tana faman yi min sannu daga inda ummah din take taji kakarin
aman nawa ta fito da sauri tana tambayan yaya haka kuma ?
Na kasa bata amsa a lokacin don yanayin aman da nakeyi din saida ya dan sarara min suna tsaye kaina
don har mijin nata ya fito yana tambayan ba,asin aman ?
Na lalaba na koma zuwa daki na zauna a falo ina maida numfashi ummah ta shigo ta zauna takara min
sannu kafin ta dora da fadin kardai wani abu kika sha don sakarcin da kikeson yiwa kanki ?
Idona na kasa ina karewa jan lalen hausa dake kafanta yayi kyau ya karbi kafan nata da kyau na dago a
cikin mamaki ina binta da kallo.
Sake maimaita tambayan tayi daidai mijin nata yana shigowa dakin ga yar aikinsu a bayanshi dauke da
ruwan sanyi ta kawo min shiya cabe tambayan da bata amsa .
Yana fadin haba dai har me zata iya yi yanzu kinsan mai karamin ciki da jin tashin zuciya ai na sauke
kaina kasa a ciki kunya na nuna mata abincin dake cikin plate din tabi da kallo.
Kafin tace abincin bai maki bane in badon ummah bace sai ince tayi min ba daidai ba wallahi wanan
tambayan don tafi kowa sanin bancin kifi tun fil azal a rayuwata tundai wanan na tekun mai bakin karnin
nan haka ?
Bai mata bane nasan tsohon ya fada yanawa kansa matsuguni a daya daga cikin kujerun falon a
kasalance na basu amsa da KIFI ?
Kifi ta fada a cikin mamaki tana bina da kallo muryan na gwada mamakin hakan tace dama har yanzu
ke baki cin kifine Rahama ?
Kaina gyada mata tace sam na manta wallahi na zata ai ta daina wanan matsalan na rashin cin kifi a
yanzu tunda naga an dade ai ashe matsalanta guda da mahaifinta.
Ai dama na fada maki akwai dai wasu sam basa son kifi a rayuwan yanzu me zataci ke nan ko akwai
abincin da ba kifi a bata taci ?
Yanzu aka dora abincin dare ummah ta fada sai tsohon ya mike zuwa part dinsa ya dan jima sai gashi
da furan gora mai sanyi ya kawo min yana fadib ko zata sha wanan din a gwada a gani ko zai tsaya mata.
Shina karba nasha na gama na koma daki na kwanta ina lumshe idanuwana rayuwa ke nan rayuwan
yanzu sai a hankali yau wai ummah ce zatace ta manta da wasu halaiyan mu na baya data san mu dashi.
Ina jin muryansu a falon da alama waya takeyi don naji shima tsohon ya karbi wayan yana fadin haba
dai ta dai fadane ai akan me zata zubar da cikin dake da ubansa ?
Bacin raine kawai yasa ta furta hakan amma ai Rahama yarinya ce mai hankali kawai dai sun tabatane
take son ta rama abinda sukai mata din.
Can naji ya koma fadin haba dai ba inda zamu barta ta tafi tunda tazo nan ai shike nan ku barta din ta
huta hankalinta ya dawo daidai kawai ?
Hawayene suka gangaro min a idanuwana naji wani bakin ciki ya tokare min zuciya da niyata shine in
samu da safe in karasa inda na nufa don banda niyar zama wanan gidan gaskiya.
Saidai nasan wa yan nan kattan sojojin dake gadin get din gidan yana dawuya in fice wani baiga fitana
ba a cikinsu don haka na fara lalubo hanyar da zan gudu nan din don bansan illan daya kaini tsayawa a
nan din bama da har na tsaya.
Wana furan dana nasha ya rike min cikina bayan nayi sallah magaribane ummah ta shigo tana fadin
kada inyi barci fa in tashi inci abinci nakoshi nace daga kwancen da sauri ta kalloni tana fadin me kikaci
bayan furan dazun ?
Shiru nayi ta koma fadin ki tashi ga Saudi nan tayi maki miyarki daban na nama kici abincin dole na
tashi zuwa falon nata.
Tuwon shimkafane miyar kuku yaji daddawa da kayan yaji kamshi shi kawai zai sanarma da hakan tsaye
tayi a kaina tana fadin ko bai maki bane miyar ?
Na dago a hankali ina kallonta a sanyayye na bata ama da yayi min ina lasan miyan tace to kici don
Allah kada ki zauna da yunwa don Allah kinsan yanzu bake kadai bane.
Ki kula sosai ko baki son abinci ki daure kici don Allah kada lafiyan ku ya tabu daga ke har abin cikin
cikin naki kai kawai na iya gyada mata ban iya amsawa .
Har zata fita sai kuma ta dawo ta zauna tana fadin ke banda abinki Rahama me zaisa ki bar gidan mijin
ki saboda wasu yan uwansa can ke baki ga yadda yar uwarki ta koma masu kurma bane tunda ta
fahincesu.
Nasan ba haliku daya da ita ba duk da hakan ya kamata ace kin koyi hakkuri hawaye suka soma zubo
min ga loman tuwo a hannuna.
Falon yayi shiru zuwa can ta mike ta fita tana kiran saudi mai aikinta wai tazo ta zauna dani zata duba
tsohon mijinta abinsu a yanzu ya daina ban mamaki.
Nasan sauyi rayuwane Allah ya kawowa ummah a yanzu yadda tasha wahala rayuwa a baya saudi din
tazo ta zauna dani a falon tana dan jana da fira sai dai ban saki jiki ba.
Ta soma fadin wa yan zaria ai ai kasan halinsu kake iya zama dasu kina ganinsu kamar gidadawa sai kin
zauna dasu zaki fahinci bakin kishi dasuke dashi ga sakar da haibaici ga mutum Allah ma yayi maku
gyadan dogo mazan naku suna son ku ai da baku kai labari ba.
Haka suke da sa ido ga abinda yayansu keyi da matayensu su koma kamar kishiyo dasu saidai ba a taru
an zama daya ba don wayayyun basa haka gaskiya.
Banda murmushi ba abinda nakeyi kawai na gama na wanke hannuna ta koma fadin kai gaskiya mijinku
dai yaji jiki wallahi wasa wasa fa yakai shekara da rabi yanzu ai nace za a kai gaskiya ciwon ya dade a
jikinsane .
Tace balle abu ya kasance na jifa ai sai yawancin rai irin hakan son ma dai suna tsayene suma ba a
samu yadda ake so ba dashi.
Hamma na soma yi hakan yasa take fadin tashi kije ki kwanta ki samu hutu yar nan nima bari na
kwashe kayan nan zuwa kitchen hakan ya rabamu da ita ranan na fahinci tana da son surutu gaskiya.
Washegari kodana tashi nayi sallah na koma na kwanta abinda ban sababa nayi barcin safe mafarkin
da nayine ma ya tayat dani misalin tara da rabi na safe sai nake ganin ai rana yayi sosai lokacin.
Mikewa nayi zuwa bandaki ban fito ba saida nayi wanka na tsabatace jikina nafito na shirya zuwa falo
ina neman abin karyawa.
A falon na samu ummah zaune tana karyawa itama tana waya tun kan na karaso na fahinci wayar dai a
kainane har lokacin gaida ita nayi da kwana ta amsa tana fadin.
Yanzu nake zancen na tayar dake ashe ki dade da falkawa ga abin karyawa nan ki zauna kici ta fada
tana nuna min abincin a bakin table nakai zaune kamar zan bude sai kuma nace daddy fa ya fitane ?
A,a manjo ai bai fita ko ina shi indai baya kama ba ko ina bai zuwa shi ko yaushe yana gidan nan dan
dama da yamma yana zama ta wajen gidan nan da mutanen unguwa.
Balle yau da yasan yana da baki koda fitan ya kamashi ai bai zuwa ko ina sai sunzo sun wuce ban
tambaya suwaye bakin ba tunda ba abinda ya shafeni bane.
Sai misalin karfe sha biyun rana saiga sallaman mama da iya tare da yazid maria da habu suna bayansu
suka shigo gabana ya fadi daki na tashi na koma da sauri don a falo nake kwance ina kallo abinda na
dade banyi ba ke nan a rayuwata.
Ummah ta kunna min wai in rage rana a nan din tunda ni kadaine bata san hakan baya damuna ba don
na saba ko a gidana wani lokacin ni kadai ke zama ai.
Sun shigo naji ana gaisawa dasu suna tambayan ina inane tace ina ciki maria ta mike zuwa uwar dakin
ta sameni ko kallonta banyi ba a wajen .
Take fadin yanzu ke haka yayi maki ai gashi saratu taji dadin hakan can yazid ya kamata tana waya tana
fadawa Nusaiba yai mata dan kareb duka jiya ya hade mata haushi biyun ta da yake ji.
Dama nayine taji dadin ai abinda bakina ya fada ke nan nace kinga saita dawo da nusaiba din tazo tayi
ta haifa masu yayan halas a gidan.
Ki bar wanan zancen don Allah jiya aita kwammace da bata fada ba din don yadda akai mata dukka yan
uwa kuma sunce wata daya suka bata ta fito da mijin ko suyi sadaka sa ita.
Ke jiyafa da yaya J ya mutu wallahi don faduwa yayi harda jin ciwo wai abarshi ya biyo ki ko yanzu ma
dakyat aka samu ya zauna don mama tayi mai alkawarin dawowa dake yau din.
Cab aiko tayi kaffara don wallahi ba inda zani barin fada maki wanan gidan har shi sun fita raina wallahi
suyi da wata kuma badai Rahama ba kuma ?
Wasa dai kikeyi kina son bawan Allah nan ya shudene Rahama baki ganshi bafa mama tayi fada duk da
bata so laifin Saratu amma tun jiya take kan zaginta gidan nan akace.
Su wanan ya shafa ko ince ku amma ni na fada maki ba zan koma ba gaskiya nagaji wallahi neman
sanadin abinda zai zubar da cikin nan nasa nakeyi yanzu a jikina na daina tuna komai nasa ga baki daya.
Wai kanki daya kuwa Rahama kodai kema din Nusaiban ta hada da kene wajen mallaka ta yamutsa
maki hankali baki komawa kamar yaya ?
Nusaiba fa kikace Yanda in an fada maki nusaiba zata iya min wani abu ya kamani a duniyan nan baki
mussawa ko kin manta dani yar baffa ne ?
Saidai ta Allah bata mutum ba kin sani amma mutum ya gwada idan yana ganin haka sai kace ba diyar
fulanin asali nake ba muryan ummah ne dake kirana tana fada akan banji zuwansu bane naki fitowa mu
gaisa dasu.
A daidai lokacin kuma mijinta ya shigo falon suke gaisawa dashi na fito na gaidasu duk sun kura min ido
suna bina da kallo ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/3, 10:07 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ya kasance mun shigo falon a tare da daddy muka gaisa nan mama ta soma fadin haba diyata don me
zakiyi min haka duk hakkurin da nake baki ?
Dukar da kai nayi kasa a cikin jin nauyinta ina wasa da yatsuna ta cigaba da fadin kin kamo hanya kibar
min dana a cikin tashin hankali jiya ?
Gaba daya jiya sam bamu gane kansa a gidan nan don ya rikice muna ciwo yana kokarin ya dawo saba
a jiyan Allah dai ya gyara.
Alh ayi hakkuri a bamu yar mu mu yafi da ita don Allah ko zamu samu ya kara kwantar da hankalinsa
don in ba komawa tayi ya ganta ba gaskiya yana iya samun matsala.
Murmushi daddy yayi ya gyara zama yana fadin ai hjy banki ta takiba don babu iyayyen dake son yarsu
ta taso daga gidan aurenta ai gata nan zaune idan tace zata biku din wa,lillahi hamdu udan kuma tace a,a
to ba dole don ni banwa yaro dole akan rayuwansa.
A,a Alh kada kace haka adaiyi hakkuri shima ya tareta da fadin yes iya gaskiyata na fada don yarana kaf
banwa kowansu dole akan matsalan aurensu.
Don bani ke zama dasu ba a can amma ba inda za ace asa ido yarinyat dako auren farko batayi ba tana
kokarin sheganta jinin dan uwanta amma ba a dauki wani kwakwaran mataki a kanta ba.
Inaga idan dan yazo duniya sai abinda taso zatayi mai na wullakanci ke nan don tun jiya datazo da
zancen nan da ace nine na haifeta da wanan yar ta kwana a cell .
Taje can ta koyi ladabi da kama baki na kwana biyu kafin a sakota saidai za ace don banina haifi
Rahama ba a yanzu idan nayi hakan.
Alh dan yaune kanayi kamar bakayi in bashi ina wanan zancen zai fito haka a bakin yaro adaiyi hakkuri
don Allah an tsawata mata ai.
Nan Habu ya tsoma baki yana fadin daddy yarinyar kamar wata mai motsi a kai don tsaban iskancin da
takeyiwa matan mu saida na taka mata burki a gidana.
To kagani kai kayi mata iyaka da naka gidan gidan dan uwanka ke nan ta koma ashe gaskiya zancen
yayi muni ace