Chapter 18 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   18 / 101

51K to 54K   out of 302.2K words

shiru shiru bai faye magana ba amma akwai tsayawa ya fadi
gaskiya don hakane ma kowa yake shakunsa a gidan haka kuma na kula Mama Dubu tafi ba Habu din
lokacin ta da daukan sha,aninsa da muhinmanci.

Rayuwa tana ta tafiya a hakan dai inda azumin wanan shekaran ke muna bankwana akwai dadi kuma
akwai wahala wajen aikin abin buda baki ga mata.

Sallah saura sati daya suna zaine ranan dai duk iyalan mama dubu suna zaune a falo misalin karfe hudu
bayan sunyi sallah azahar ina kitchen ina ta hada abin buda baki don yanzu ban tsayawa jira tunda jiran
baida amfani karshe a kaina aikin yake karewa kowa dayasha ruwa zai nemi waje ya labe.

Ka zamo mai zafin nama wani lokacin akan kwari mutum ga hakan kowa saiya sakama ido don amsan
zaka iya din .

Saida hakan bai damuna don da zuciya daya nake hakan, suma kuma sun sani, haka kuma wanan aikin
yafi min aikin gidan baffan mu sauki sau dubu.
Gidan baffa karfe hudu dole mu tashi mu fara surfe idan mun gama gari ya fara haske mu dauki jarkan
diban ruwa muna gamawa da mun dawo zamu cika jallon mu da dan gudun kokon da zamusha wurin
kiwo mu zamu daka amma kuma a hana muna.

Shiyasa nake kallon wanan nagatane tunda ni zan dibarwa kaina iya cina don haka ai wanan ya zamo
gata kuma ga hutun da nake samu nayi na tsawon lokacin.

Rabon kayan sallah Jafar din da Abubakar sukeyi sai mama da iya da kannensu mata dake ta rubutu a
takarda suna mannawa su kuma matan shi suma suna nade kayan.

Mama nifa har yau banji ance ga kayan sallah Ramaah ba salimace ke fadin hakan wa mahaifiyarsu ta
kureta da idanu ?

Kamar ya ba,ace Ramaah ba ba yaya Habu zai mata ba ita da matarshi Saare ta riga uwar bada amsa .

Habu kuma Saare don tana kanwar matar Habu za,ace shi jafar ba zai mata sutura ba kome ?

Cak suka tsaya ga abinda sukeyi gaba dayansu suna kallon mama din da saratu au kece zaki tsara yadda
abin zai kasance ashe ?

Wai akan wa ake magana Jafar ya tambaya da sauri salima tace Rahama ranan full name dina ta fada
kai tsaye.

Ramaah ya juyo ya dan kalli dan uwan nasa yana fadin Rahaam bata da kayan sallah dama kuma baki
fada min ba salima ?.

Yaya na dauka ka sani ai shiyasa ban fada ba da wuri naga kowa kuma baiyi magana a kanta a yanzu ba
yasa nayi magananta ai.

Wai wa kuke zancene bai samu kayan sallah ba cikin mutuwam jiki da jin nauyi mama din tace wanan
yarinyar wallahi .

Ni abin gidan nan yana ban mamaki ta ya yarinyar dake dawainiya daku haka zaku dinga cewa kun
manta da ita don Allah zama baice haka ba wallahi.

Iya ta fadi hakan cikin hasala tana juyawa kafin mama din tace a,a Iya munyi da Jafar tun a waye yace
kayan sallah nace na yaran nan su uku zai sayowa kinji yadda mukayi na dauka harda nata aka hado ai ?

Wai dai wace yarinya ke Asmau dana kawo kaya mena fada maku da aka fitar dasu ?

Nikan kace nasu Saare ko kace mu zaba mu basu saura kuma muka zabi namu muka basu nasu ta
karasa a sanyayye tana dukar da kai.

Toke salima waya baki kayan ki ta amsa da fadin Saarece tashigo min dasu takai dakin mu ko wani
bibiyu ta zaba ta ban nawa shike nan.
A,a ni ban gane ba Saratu ina na wanan yarinyar ya shiga don Allah J is enough idon kayane a barshi
kawai ke salima kuje a sama mata kaya gobe shike nan .

Ya zakace dani shike nan wancan karon ma haka sukayi aka raba abu a gidan nan suka hana mata har
mama taga laifina gashi kuma again ankara yi don haka ina son ina kayan nan suka shiga ?

Suna tsakanin makiran matarka mana ai kaji sunyi shiru ga baki dayan su sunsan yadda sukayi da kayan
ke nan a tsakaninsu tunda suna bakin ciki da zaman boyar Allah nan gidan nan.

Itako bata ko san sunayi ba don basu gabanta sun dauki kiyayyan duniya da kyashi sun dora akan matar
kani banda tsiya harda kanwata zaku saka a kishi.

Ita kanta matar Habu bata san kunayin haukan ku ba hakama yar uwar nata gashi dukkan mu nan gidan
muna moran wanan yarinyar.

Ko wanan aikin da take ga sharan nan ga girki yaci ace yarinyar nan ko albshi ake mata tayi kissa amma
ina tunda suna da wankakken zuciya ba hakan a gareta duk iyace take fadin hakan garesu.

No ba zancen da za ace a kyale bane wanan duk da ba zama nake a garin nan ba nasan irin kokarin da
yarinyar nan takeyi gidan nan kullum.

Ko a fito min da kayan ta inda suka shiga ko kowan ku ya kawo nasa nan yanzu ku har saratu din ban
cireta ba ?

Dama ai tunda koma meye da ita aka hada baki aka kulla hakan tasan komai tunda hanyar data zaba ke
nan bakiji kunyan hakan da kukayi ba don Allah ?

Ina yarinyar nan kamar yadda Iya ta fada duk gidan nan kowa yana cin moriyanta a yanzu ku duba
zuwansu yadda yanzu gidan nan ya koma fes dashi don Allah ?

To mama akan me zai sayo muna kaya iri daya da ita idan su Saare yan uwansane ita kuma meye nasa
don kawai tana kanwar matan Habu ?

A zabure ya tasowa Saiba din dake magana a lokacin, tayi saurin fita don ganin an taresa daga zuwa
gareta ta fita tana maganganu masu zafi game dani.

Hawaye naji sun zubo min don a yanzu kan ba fahinci zancen da sukeyi a kaina sai hukuncin ya Habu ya
burgeni da yace to ai gaskiya ta fada kada kuga laifinta don Allah.

Nine ya kamata in dauki nauyin matana dana yar uwarta dake zama da ita gidan nan ba J ba kowa
yasan albatkacina sukazo gidan nan .

Kai Habu ka bari a fanci inda zancen nan ya dosa dan uwan ya taresa da fadin hakan inda yaci gaba da
fadin kowa dake wanan gidan har gidan kawu nauyin irin hakan akaina ya rataya don hadin kan mu da
kowa namu don me zasu so zarta hukuncin dabani na tsarashi ba .
Yau yarinyar nan kamar kowa take a wajena tunda zamaka takeyi zaman mu kuma a cikin gidan nan to
ai yaya komai za a raba saidai na raba nawa biyun in bata haka akeyi kulum a gidan nan salima ta sake
fada.

Ke ina aka kai kayan yarinyar nan ya kallo Asmau yana tambayanta suna wajen mu ta fada kai tsaye ki
daukosu yanzun nan ya fada.

Kayan nan fa basu gidan nan nake gani Saare ta kara fada a bangareta sai iya dake kallon mamaki take
tambayan .

Nikan me yarinyar nan ta rageku dashine a gidan nan wai ?

Bakin ciki mana Iya amma in aikin karfine kowansu ya iya zuwa nan yace don Allah Rahama kizo ki
taimaka min da kaza amma ba a sonta da karuwa .

To wallahi kuji ni ban raba kan yayana ba a gidan nan ba macen da zata shigo tace zata raba min kan
gida haka yanzu wanan abin dame yayi kamane wai ?

Rikici sosai sukayi a kan kayan ni kan ban kulasu ba na gama miya na dora shinkafa na shige dakin mu
na kwanta don fada sosai ya J yayi ya kuma rantse idan basu fito dashi ba duk kansu ukkun zasuji
mamakin shi wallahi.

Bansan ya akayi ba sai ga kayan an fito dasu da yamma an kawo min mamace ta kirani ta ban na karba
nayi godiya saidai a kasan zuciyana na nasa cewa ko zan tafi tsirara ba zan saka kayan ba don nima ta
fulanin sun hau a lokacin.

Duk da karfi bai kai ba amma zuciyan gado yana nan a jinina aiki kuma idan ba na cikin part din mu
bane na dainashi daga wanan ranan .

Har washegarin da aka ban kayan raina ba dadi da safe na gama shiryawa nace da salima zanje da kaina
asibiti in duba yar uwata dama haka nake bayan kwana bibiyu nake zuwa yanzu tunda aka soma azumi
din nan.

Sam ban fadawa yar uwata komai ba game da abinda ya faru akaina gidan sun dai tambayeni ba komai
konace ba matsalan komai.

Na zauna a nan don na nasa irin zaman da zanyi ban bakin ciki da ko banda Saratu da bansan abinda na
tsare mata ba a rayuwata ?

Don haka nake bakin ciki da in girka taci a raina tunda nima yar adam ne kamar kowa gara in fito masu
a mutum don a zauna lafiya.

Kwatsam saiga anty salma daga Abuja ta bugo waya tana tambayan Yanda karfin jikinta suka dan taba
hira take tambayan ina gida ko tace ina kusa ta mika min wayan .

Mun jima muna hira in tambayi wancan in tambayi wanan har take ce min nazo mata sallah mana
Abuja nace ba za a barni bane .
Tace waye zai hanaki zuwa wajen mu Ramaah ?

Nayi shiru take fadin naba Yanda waya sukai magana na daiji tana fadawa salma din zata fadawa
mijinta idan yashigo insha Allahu zanzo din .

Naji dadin hakan sosai yaushe rabona da Abuja koda Yanda taje da mijinta suka kwana hudu acan da
yai wani zuwa basuje dani ba rabona da mutunen arzikin mu nida mahaifiyar mu tun rasuwan mahaifin
mu da muka koma rugga da zama.

Saida akai Azahar na soma shirin komawa gida na tattara kayan dana kawo mata abincin safe na fito
babu abin hawa hakan yasa na soma shawaran takawa don komawa gida.

Wani mai mota yazo ya tsaya ban kulashi ba yaja motarshi yayi gaba hakan yasa na soma tafiya da
kafa ga kuma kaya niki niki a hannuna dukka biyu.

Saida kyat na samu abin hawa nashiga ya kaini gida abin mamaki ashe mai motan nan yana biye dani a
baya zan bawa dan mashin kudinsa naji yana fadin malam ta barshi kazo ka karba.

Na dago kai na dubeshi shine dai ya tsareni a bakin asibiti na dangwarawa mutumin kudi na shige gida
da sauri.

Gidan kaca kaca ga ganin idona kaina kawar na karasa na shiga falon da sallamata suna zaune suka
amsa min mama ke fadin yar halas yanzun nan nake zance ki fa a raina.

Nadawo mama na tsaya rana yayi sanyi na dawo tace aikuwa yau ana kwada rana da zafi a garin nan
kayan nakai kitchen na aje kayan dana dawo dasu daga asibiti.

Kafin na juya zuwa dakin kwananu suna kwakwance suna barci adakin na tube kayan jikina nashiga
bayi na watsa ruwa na fito na samu waje nima na kwanta.

Sai barci ban tashi ba sai wajajen la,asar da karan wayan anty Salima ya tayar dani alwala nayo na
dawo nayi sallah ina idarwa na fita zuwa part din anty na na gyaro don yaya Habu dake gari baya
dawowa gida sai lokacin shan ruwa ko kuma idan wani abin ya dawo dashi.

Kodana fito kitchen na samesu da mama din sai fada mama keyi tana fadin aiko wani rai yana son hutu
a cikinsa shike nan kun mayar da yarinya yar aikatau din ku kowa ya mike kafa saidai ta girka kuci kuma
babu kyautatawa.

Hakan da tayi yau yai min daidai wallahi aiko shige yanzu ba awa gorin uban don da uban hanya a
zamanin nan balle da gatanta mutuwa yasa kuka ganta nan tare da yar uwanta.

Daga faloma iya na kada nata suna kurum nidai ban fito ba sai dana dan jima a daki na fito na samesu
wanke wanken kwanonin dana gani suna fara daurayewa mama din na fadin ai in bari suyi meye
amfaninsu suna mata dasu ?

Saare tayi girkin a ranan don ita salima tace a raba ai idan hakane nidai ina wanke wanken ina jinsu har
na gama na koma falo na zauna mirsisi da ido kuwa.
Duk da nasan sun fahinceni ko basu bahinta bama nima so nake su fahinceni din zaifi sauki har aka kira
sallah lokacin shan ruwa yayi bata karasa aikin ba.

Sai faman fada da ita mama keyi karshe ma tunda mukaje sallah ni dai ban fito ba na zauna ina jiran ayi
kiran isha,in inyi sallah in kwanta.

Tun a wanjen diban kunun tsamiya dana fito yi nasan akwai matsala ranan don kawai shi nake soma
sha na diba da kyat na sha rabin wanda na dibo din na mayar da saura kitchen.

Na dawo na kwanta ke nan naji muryan su yaya sun shigo shan ruwa shi ya je duk da maganan da
akayi anan part din yake shan ruwa har yanzu.

Ita Saare din ta zubo masu abinci da kanta suna hira ya Habu ya fara kai cibi a bakinsa ya kasa hade
shinkafan.

Yayi shiru sai shi jafar dake magana da iya ya diba yakai shima a bakinsa furzowa yayi da sauri yana
fadin wayayi wanan girkin mama ?

Yana binsu da kallo suma duk kallo suka bishi dashi lokaci guda habu yace na rigaka ji shiru nayi kawai
mama ta nuna saare tana fadin gata nan ita tayisa.

To me girkin nawa yayi kuma tana turo baki zo nan kici kiji abinda yayi jafar din ya fada a hasale yana
fadin shame of you Saratu.

Badai wanan abincin aka kai masu asibiti ba ya habu tambaya yana kallon mama din a sanyaye mama
ke fadin shine mana nina san tsiyan data kwabawa mutane ke nan ?

Ba maggi ba gishiri komai babu a miyan nan fa mama da sauri mama din ta kallota tace na matane kila
ban zuba ba.

Rufe min baki sakariyan banza kamarki saratu zaki kasa dan wanan girkin da baida yawa ina ga mai
yawa ke nan ?

Ina wanan yarinyar ne yau da aka bari tayi wanan shirmen a hasale mama din ta juyo tana fadin yarinya
kan aiba boyansu bace ko ?

Da zata zaman girkawa suna ci kullum yau itama ta hutar da kantane su dandana suji wai shine wanan
sakariyar ta kwaba muna abinci haka ?

Tsam Habu ya fara mikewa yana fafin zai fita bai tsaya saurareb fadan da mama Dubu take yi ba
lokacin da Saare.

Yana fita ya tsaya ya hada wani take away da gasassun kaji biyu da drikis ya nufi asibitin dashi don
yasan ba zasu taba iya cin wanan kwaban ba na saratu ranan.

Hakanne kuwa don koya samesu a zaune sunyi zugun zugun sun gama magana kan abinda ummah
zatayi buda baki da sahur sai gashi ya kawo masu wani abinda zasuci din.
Da bai kawo ba haka zasu zauna da yunwa don ko ba zasuyi magana ba saboda kawaici irin na fulani da
kunya suje tambayab surakansu ya hakan ya faru ?

Shima ya J din fita yayi a hasale yana fadin wanan baki da maraba da girkin wa yancan idan zaki zage ki
koyi girki ki zage har ace karamar yarinyar nan tafiki iya girki ?

A hankali tana gunguni take fadin zaku hadani da yaran da suka bude ido da dafon abinci tunda zaman
aikatau sukayi a abuja har suka iya abubuwa haka ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,



2️⃣0️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Karfe tara na falka ba wanda ya motsa kowa na kwance yana barcin azumi na kewaya bandaki na fito na
kitsa jikina na fito falo.

Ashe iya na zaune a falon ita kadai jin motsina yasa iya juyowa gaida ita na fara yi kafin na juya zuwa
kitchen don in hada kayan wanke wanke.

Yadda naga kayan a wajen bakyau gani yasa na shiga hadasu har falo duk na kwaso cups din akai
amfani dasu da asuba don ranan dai ba wanda yaci abinci zance a gidan.

Saidana hada kayan tas na fara sharan part din nasharo ko ina har dakin Iya da mama dubu dana samu
ta falka don jin motsina da tayi ina aiki.

Falo ta fito ta zauna tare da iya na gama shara na koma kitchen din abincin na tsaya na kalla na tsayin
lokaci kafin na juya zuwa wajen su ina fadin mama ya za ayi da abincin nan me yawa ?

Ta juyo tana fadin kedai Rahama ina nasan yadda zanyi wanan iskacin na Saare aida yawa yake yarinya
ki haramta muna cin abinci haka kiri kiri ?

Ta mike tsaye ta biyuni zuwa kitchen din ina tsaye gefe daya na kura mata idanu ta nisa tana juyowa
gareni tace ki barshi a tukunyan anjima idan Auwalu yazo yakaiwa almajiransu.

Hakan akayi na wanke kayan tas na kara gyara kitchen din ina gab da gamawane naji muryan ya Habu
a part din suna gaisawa na fito ina gaisheshi da kwana ya amsa min har zan wuce naji yana fadin.

Ramaah ashe Abuja zakije sallah jiya suke fada min asibiti danaje da dare murmushi nayi kawai zan tafi
kuma naji yana fadin .

Sai kuje da salima kasuwa ki sayi tsaraba anjima gobe akwai wanda zan hadaku yakaiki Abujan nace
nagode yaya.

Nashige na barsu ina jin mama din tana magana saidai banji abinda tace ba wai ashe tace da alama
yarinyar nan ta dauki zancen nan da zafi don banji tana zancen zuwa Abuja ba ai ?

Sune suke son tazo masu sallah a can ita wace zataje gurinta ta bugo min waya jiya tana rokona Allah
ya kyauta mama din ta fada.

Murna yasa tun a lokacin na fara shirina yan kayan da zan dauka da sauran abubuwan amfanina da
nake bukata na hada saman gado.

Wanka nashiga nayi na fito nashirya zuwa lokacin sun tashi na samu salima zaune tabini da kallo tana
fadin kayan meye haka kika hada ?

Abuja zanje sallah anty Salima cikin mamaki ta maimaita

18 / 101