Chapter 8 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   8 / 101

21K to 24K   out of 302.2K words

naki na fahinci wasu abubuwa daga bakinsa.

Wanan baida matsala don yana Nageria yanzu haka kaga bari na nemesa sai muji time din da zamu
samesa don gaskiya mr handsome ina sonka da wanan business din don ba karamin samu zakayi a
cikinsa ba yafi wanan buga buga din da kukeyi a yanzu.

Tana magana tana dauko wayanta a cikin handbag dinta a lokacin ta soma dialing din number dan
uwan nata kira kusan zai katse ya daga yana fadin sorry sister ina meetinga ne a yanzu.

Dama broda guy din nan danayi ma zancenshi shine yake son ka bamu time da zai gana dakai yake fada
mata zai shigo lagos next tomorrow idan ya shigo by 4 pm zasu iya ganawa dashi a ranan.

Suka danyi yaresu inda take kara rokawa mr handsome dinta alfarma a wajen yayan nata tana yabawa
har yayan ke fadin tabari din yazo din da alama guy din yasan kansa tunda har ya nemi su fara ganawa
dashi.

Abinda baiso shine cuta da cin amana idan haka ya faru ba zai dubi alakansu ba zai dauki mataki mai
muni akan ko waye.
Tace by god grace hakan ba zai faru ba son ta yaba da halinsa sosai sun dade suna business dashi ta
fada mai hakan don ya yarda.

Kai ta dag ta saukewa Jafar kallo tana fadin munyi sa,a basai muje can ba zai shigo lagos banda gobe
kaga zamu sameshi 4 o,clock ku gana dashi don forget with d time ta kara fada suka taka zuwa bakin
motarta tashiga ta wuce.

Shima motanshi dayazo da ita wajen ya nufa ya shiga ya nufi inda zai tafi tare da tunanen yadda abin
nasu zai kaya saboda zuciyarshi ta shiga wasi, wasin don imani da tauhidi dake yawo ajinsa na adduan
iyayye.

Kamar yadda suka aje time karfe biyu yana fitowa sallah ya kirata karo na farko yana tambayanta ko
brother din nata ya samu shigowa lagos din tace zata kira ta tambaya taji.

Ba a dauki wani lokaci ba ta turo mai sakon wajen da zasu hadu zuwa wajen yayan nata yaci gaba da
harkokinsa na yau da kulum a lokacin.

Sai bayan ya fito sallah a masallaci mafi kusa ya shiga mota ya sameta tana jiran sa hakkuri ya bata
daya tsaya sallah ne a masallaci tace ba matsala tana gaba motanshi nabin nata a baya har gidan dan
uwan nata dake wani unguwar masu kudi anan kusa da ruwa.

Kai tsaye ganinta security suka barsu suka shiga gidan don tayi masu bayanin tare suke yaji mamakin
girman wanan gidan haka yasashi nasa wanan yayan nata ba karamin mai kudi bane ashe.

Sun samu waje sun faka motocinsu wajen suka fito zuwa cikin gidan shidai yana dauke da addu,a a
bakinshi don zuwa yanzu sai tsoron zuwa shi kadai ya darsu mashi a zuciya yana tuna addua shine mafita
koda yazo da wani din ba zai iya mai abinda Allah zai yi mai ba ya fara jero duk abinda ya sani a bakinsa.

Wasu kulka kulkan mutanene ta gani suna gadin gidan bai damu ba saboda addua yasa ya daina jin
tsoro a yanzu.

Sun samu yana meeting da wasu yan kabilansu kana ganinsu kaga manyan matasan arnakun kasan nan
ya fake da waya da wani abokinshi a lokacin.

Ya fahinci duk wanda ya fito yaga Meiarbe sai yayi mata kirari da bata girma irin tasu na iyamurai da
sukeyi bayan sun fitone akai masu iso zuwa ciki don yayan nata ya hangota daga waje yasan sun iso ke
nan.

Addu,an da Jafar ya doshi wajen dashi yasa suna shiga yaga mutumin aiba wani babba bane can yanda
ya zata don irin matasan daya ganine a waje yanzu.

Hannu ya mikawa Jafar din su gaisa baiki ba ya mika masa yaga zalla nagartan jafar daya hango a
yaron lokaci guda.

Bayan sun gaisa yake tambayanshi daga ina yake ya fada mai kai tsaye daga zaria yake yana zaune nan
lagos.
Ya dan kara kallon Jafar din dake zaune a cikin ladabi kafin ya soma magana yana fadin quity sure kayi
min haka nake son dama matashi mai lokacinsa wanda zai iya bada karfinsa ga aikin mu ba ya zauna ya
tura ai masa ba.

Saidai kota fadama harkan mai zamu soma a yanzu mutane da dama daga arewanku suna son wanan
harkan ban basu daman hakan ba don ina jin tsoron hurda hausawan ku saboda basu da amana.

Kai jafar ya dago ya kalleshi yacewa Jafar din gaskiya na fada nagwada aiki da mutanen ku a baya banji
dadin hakan bane.

Allah sarki malam bahaushe da abaya iyamuri ko bayerabe suke tsoron koyi masa kallon banza balle
fada a yanzu zamani yazo da iyamuri zai fito fili ya fadi magana akan bahaushe sune ke fadin basu yarda
da bahaushe ba suda muke kyama sosai.

Saida wasu marasa zuciyan bahaushe da suka batamu a wajensu sun ari rigan bahaushe sun yafawa
kansu suna yaudara suna batawa hausa asali suna da akidarsu ta yaudara a yanzu.

Kada ka damu you are lucky tunda autace ta kawo ka nasan idan bata yarda dakai ba zata kawoka har
wajena ba zan barka hakan don nasan tunda kace kana son ganina kaima kana da abinda kake son fada a
kaina.

Zama Jafar din ya gyara ya soma fadin najo duk abinda ka fada saidai ina son jin ainihin yadda kake son
sana,an naka ya kasance a arewa idan zan iya zan karba da hannu biyu inma godiya idan kuma naga ba
zan iya ba zan fada tun a wajen nan ka neme wani don addini mu bai yadda da wasu tsare,tsare ba a
cikin sana,an mutum.

Kallon guy din chibuza yayi yaro karami yasan kansa akan addininsa abinda bai taba jin manyasu sun
fada ba Allah Allah ma suke ai signing din contract dinsu su farawa mutum yaudara shi gashi yazo masa
da nasa tsarin akan addininsa yanzu.

Ehh to ba wani abu bane ya soma mai bayani akan yana bukatan gina gidajen mai a arewacin Nageria
din shi Jafar duk zai kula da wanan bayan haka akwai motoci da zasu shigo wa yanda zasu dinga sintiri
kai mai kuma duk zasu tsayane akarkashin kulawan jafar din da komai illa iyaka shi nasa balancen zasuyi
yana turo mai kudi a wajensa eather shekara ko bayan duk wasu watanni haka yadda dai abin ya samu
karbuwa a wajensa.

Ajiyan zuciya Jafar ya sauke don jin ba wani abinda zai soki addininsa ko rayuwansa nan gaba donshine
ya amince suka tsara yadda abin zai kasance tare da musayan secret number da zasu dinga magana a
tsakaninsu.

Ya gargadi Jafar sosai da bai son yawan magana inda yace koda ba,a aka sunan yadda za a fahinci nasa
bane shi wanan ba matsalan shi bane kada dai a samu kuskure a cikin harkan .

Budan bakin Jafar yace wanan kada muyi fatan haka mu nemi sa,a a wurin ubangiji ya dafa muna kan
lamarin da muka dosa .
Iyawan mutum ko kwazon mutum baiyi kamar na Allah ba da komai yake a hannunsa kai chibuza ya
daga yana yaba nagartan Jafar a zuciyarsa.

Dafa Jafar din yayi yana fadin idan ka rike gaskiya zamuji dadin juna sosai dani dakai don a wanam
harkan kadai zamu tsaya ba a sannu zanyima hanyar international business .

Sun rabu cikin jin dadi da fatan nasara a tsakaninsu sukai sallama akan in Jafar yagama nazari zai
nemesa yaji inda za a fara.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f




MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kamar yadda yake dan adam bai gani bai tofa nasa ruwan a cikin lamarin da bai shafeshi ba shike faruwa
yanzu akan Jafar .

Wanda yasan jafar yasan mutumne daya taso da kwazon nema saidai ganin rufin asirin da ubangiji yai
masa lokaci guda yasa mutane nata tofa albarkacin bakinsu akan cigaban daya samu inda a yanzu ya
gyara gidansu da suke zaune a cikinsa don haihuwan matansa yaiwa kowa part dinta amma falo na
tsakiya babba haka bangaren Abubakar da zancen Aurenshi yanzu kowa ya san da yana neman aure a
Cameroon .

Don har manya su kawu sun shiga zancen zuwan farko baffa yake amincewa da zancen saida suka biyu
ta Alh can abuja ya fito masu ta bayan gida a dan Nageria ya hadasu da hakimin garinsu shiya aika masu
da sammaci aka nemosu har can inda suke zama akan human right tayi karan baffa din.

Tsoro da gudun wahala yasa baffa cewa ya yafe yaran su koma nan kauyen su gidan hardonsu don
zaman kaka yake ga yaran.

Yace su zauna anan tunda shi baida iko dasu dama taimakonsu yakeyi ai tunda naggen da ubansu
yabari a yanzu sun zama nasa tunda shekaru ya kora shike kula dasu.

Hardo yaso yayi magana amma sai su Abubakar sukace ya kyaleshi daha baya za,ayi wanan zancen
yanzu zancen yarane da uwarsu su samu freedom ayanzu akeyi.

Abubakar bai tsaya dogon nema ba irin na barna lokaci a dade da budurwa ana shan soyayya daga
shiga rayuwansa ya fito da zancen aure.

Inda mama Dubu ta kama mashi tana kuma tayashi da addua da shawara wanda a yanzu kowa yasan
da zancen bafulatanan ruggace yake son ya aura.

Inda wasu ke ganin ya rago kamarshi dan boko dan gaye mai jin lokacinsa zai buge ga auren yar daji
jahila mara boko wace bata waye ba ?

Sun manta kida Jahilace haka Allah ya tsara idan itace matar da zai aure din ba (makawa ) inkiyan
kauyen zee makawa) sai ya aureta.

Allah yayi za ai abin a gabar da dan uwansa ke cikin tashen Naira Allah da yardansa yadda aka saka
watan auren lokaci yayi akasha buki.

Bukina mai kama da dunkula irun ta fulani ba wani shagali aure kawai aka daura aka dunkulo amarya
sai yan rakiya da hardo yabayar mutum biyu sai kanwata da zatazo zama da ita don ta samu wani a kusa
da ita cikin garin da bata san kowa ba .
Hardo ya roka kuma anyarda mai da hakan gidan su Abubakar din mama tace dama tana da niyar hakan
a zuciyarta don ta samu na gida a kusa da ita.

A bangaren matan yaya jafar kuma sai dariya sukewa Abubakar a fakaice tunda Saiba dake fadin duk
bakin ransa da jiji dakai a bafulatan daji ya kare ashe.

Ga mata birjit a gari amma ruwan ido ya kaishi daji auro bafulatana saidai basu fadi a gabanshi saidai a
bayanshi basu kadai ke wanan zancen ba harda matan gidansu gidan mahaifinshi.

Suma sunata sakin irin zancen nan da fadin magana akan fulani abindai kamar yadda aka saba tsegumi
akan ko wani irin aure wanan ma a tofa iya tofawa da za a iya.

Mutum dai bai isa ya hana abunda Allah ya nufa ga bawa ba saidai gajin hakkuri namu na yan adam
yakansa mu daukanwa kanmu zunubi a cikin rashin sani.

Ita kanta maria bata taba zato ko tsamani haka zata samu gidan Abubakar din ba don ya nuna mata shi
baida komai a lokacin nemasa da ita.

Sai gashi hadaden gidan dataga an kawota ciki ya tsinka mata zuciya ta kara godewa Allah daya duba
mairaicinsu ya fitar da ita daga kuncin bautan da sukeyiwa baffa.

Sai addiua take wanan auren ya zamo mai dorewa a gareta don baffa yai mata baki da cewa indai
auren kado ne taje ya bata shekara tasan baffa mugune na bugawa a jarida.

Don ko yan uwansu kaf fulani tsoronsa sukeyi abu dayane ke razana baffa shine hukuma baison abinda
ya dangantashi da hukuma.

Don bai kaunan ya cire nagge daya balle fiye da dayan a cikin garkenshi ko yaushe a cikin lissafin
garensa yake a tsakar dare bai barci nan zaita sintiri yana kidayan shanun dake garken sa.

Yana kuma surukullensa a ciki yanawa mutane aiken shirin daya saba wanan tunane data shigane yasa
har bataji sallaman su saiba ba da suka shigo ganin amarya da safe.

Sai da yar uwarta ke fada mata a cikin hausa anty Yanda ana maki sallama fa ta zabura tana fadin
wa ,alaikis sallam.

Kallon juna sukayi suna fadin tubarkallah amaryan ke nan ta fito tana masu sannu da zuwa sai yar
budurwan dake tare dasune da ba zata gime mata sosai ba take fadin.

Anty maria wanan matan Yaya J ne ana suke gidan suma ina kin gane yaya J babban yayan mu na dakin
mu sune matansa.

Cikin fara,a da yar kunya ta sake dago kai tana masu sannu da zuwa tare da gaidasu tana dan kare
fuskanta don kallon kurullah da suke mata.
Ba zakace ita din bafulatan daji bane yadda suke fada don dinkin da anty fadila tayo mata daga Abuja
sune jikinta a lokacin dinkin dakosu basu saka irinsa ba dogon rigace da yaji duwatsu kamar sarka ya
danne a jikinta sai dogon gashin kanta daya sha gyara an daureshi a waje daya yana kyalli a jikinta.

Mikewa tayi tana fadin bari tazo taji saiba ta juya harshe a cikin turanci tana fadin muje mana me zamu
tsaya yi kuma ta juya tana fadin excuse me please a cikin sallon turancin dake bakinta.

Kallon juna sukayi tun lokacin suka fara mamakin anya bafulatan dajice wanan kuwa suke tambayan
kansu cikin zuciyarsu.

Bana fada maku ba babu inda tai kama da yar daji yadda kuke fada yaya Habu fa duniyane dama nasan
za a rina kallon kowa yakeyi kar a gidan nan.

Leda ta kawo masu shake da kayan buki ta mikawa Sare data santa tun jiya tasan kanwarsu Abubakar
dintane ita.

Ke wanan kuwa anya yar dajice wayewanta yayi yawa ko fuskanta kagani kasan wanan ba yar kauye
bace.

Ai ba wayewa ko kauyanci akajawa a aure ba hali ya kasance tana da halin kwarai shine zaman lafiya ga
ko Asmau ta fada.

A harzuke ta juyo tana fadin to me kike nufi da zancen ki da bani wanan amsan a yanzu Asmau nifa irin
zancen nan naki na gugar zana kin san shike hadani dake Asmau.

Nan fada yaso ya fara a tsakaninsu Sare ce ta dakatar dasu da take fadin wanan ai saiku nuna mata irin
zaman da kukeyi a nan itama ta fara.

Jin hakan yasa Asmau tayi gaba ta barsu a baya son ita dai bataga abin laifi a cikin zancenta ba kawai
dai Saiban ce kamar a jirace take da ita lokacin.

Fitowan Ramah daga wajensu mama dubu yasa su duk binta da kallo suna mamakin yaran don wanan
koba a fada ba kanwar wanan amaryam Abubakar dince da suka fito wajenta.

Ya Allah wa yan nan diya akwai halitta dole yaya Habu ya rude a kansu ji wanan karamar don Allah
zakice itace ta halicci kanta wajen kyau.

A can wajensu mama dubu baki yan kawo amarya suka sauka don iya tace ba mai zama a wajensu a
bata masu part din don akwai dakuna a wajenta shine aka gyara masu daki guda suka sauka a ciki.

Babu wani laifi a nan din don ina aka saka ake faman yi dasu tun jiya da suka iso garin abincine iri iri
kafin su bude wanan wanan ya iso sun rasa wani zasu taba a ciki.

Karasawa rama tayi cikin dakin tana fadin a cikin fulanci anty Yanda baffa yace ki fito kiyo hakan ne ya
basu dariya ita da kanwar nata lokaci guda suka zauna suna hiran baffa Buga da shu,umancin daya nuna
masu a baya.
Allah ne ya kwatomu Ramah don babu da amanan baffa Abban mu baici amananshi ba a rayuwansa
amma ya azabantar damu haka a gidansa.

Kinga matan gidan nan da suka fita yanzu matan yayan Abubakar ne sune abokan zamana a gidan nan
saidai na fahinci kamar akwai zaman lafiya a tsakaninsu don suna fita nan suka soma fada.

Tsoro nake ji Ramaah zama da irin matan nan akwai fitina da barazana irinsu ba zasu barka ka huta a
rayuwanka ba da ace ba gida daya muke a zaune dasu ba hakan yana da sauki.

Babu ruwanki dasu tunda ba a bangare daya kuke zaune ba suyi harkansu a can muyi namu a nan dani
dake.

Murmushi tayi tana bin kanwar nata da kallo tasan Ramaah da iya fadin zance kalma daya zata fada ya
wadatar da abokin zancen ta.

Kwana biyu yan rakiya sukayi suka juya bayan nasiha da kuma jan kunne da sukaiwa yaran nasu da
sanadin aure ya rabosu dasu zuwa nan yanzu.

A dan zaman da sukayine suka har sun fahinci wasu abubuwan dake faruwa a gidan wanda suke son
natsuwa da gyara a kansu donshi suka tsawatawa ita Yanda din.

Sun tafi a ranan kuma Yanda ta fara girki a gidan bisa umurnin mama data bata baki data dora abincin
darewa mijinta.

Hakan ya bata daman zagewa ta dora girki tare da amfani da sanadaran da sukasa gidan gaba daya ya
dauki kamshin dake tashi a girkin.

Tuwon shimkafane da ya tuku yayi laushi kamar ba shimkafa aka sarrafa ba ga danko ga leda fara data
kwashe a ciki daga nan suka kara mayar da hankali ga miyan da suka dora wanda kowa ke son ya
dandana yaji dadinsa.

Miyan bindin saniyace ta dora sai miyan yauki na agwano da dan karkashi kadan yaji daddawa da
kayan kamshi a gargajiye.

Tayi hakanne don hiran da sukaji iya nayi cewa mama ta huta da tambayan tuwo yau maciyi tuwo yakai
ga matar da zata tuka masa tuwo yadda yake so yaci sai ya koshi.

Sun kammala an zuba waje uku suka shige yin wanka don itace kusan karshen shiga wanka a lokacin.

A falon ya J Saiba ce ta fito rugume da yarta tana fadin yau kamshin meke tashi hakane a gidan nan ?

Asmau dake zaune ta dago tana fadin nima tun dazun nake jin kamshin nan yana shigo min wata kila a
part din iyace kamshin ke tashi.

Baki saiba ta tabe ta gyara zama tana fadin kamshi kamar wani girkin kwarai ina bafulatana ta iya girki
banda tatsan nonon shanu.
Badai gyaran gyaran ba tayi mai wanan

8 / 101