Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Rahama wanan bai isa hujja a gareki ba nidai abinda zuciyana yaban game dake shine
kin gaji da halin da nake cikine a yanzu kawai kike nemawa kanki mafita ?
Ohh abinda tunanen ka ya baka ke nan kai to shike nan in haka kake tunane look Rahama idan kin
gama hutun ki dawo nima ina bukatanki a nan tare dani kin sani .
Ashe zaka zauna zaman jirata kuwa don ba zan dawo wanan gidan da baida saiti ba sai abinda kowa
yaga dama yayiwa mutum kuma a hana ka daukan mataki nagaji na hakkura na kashe wayan.
A bangarenshi shiru yayi yana tunane yaushi nake fadawa hakan a gabanshi da farko bai yarda ba
amma yanzu yaji gaskiya da kunnuwanshi.
Maganan mamansu ya zama gaskiya ke nan ba wanan yasani tafiya ba saidai kawai gajiya da halin da
yake ciki din da nayi inbashi ba baiga abinda zaisa nace haka ba shima tunda yasan yana iya kokarinsa
damu ai.
Shigowan mama tudu dakin yasa ya nisa ita ke fadin Jafar yau ina son in koma gida don na shirya zuwa
gida in duba yaya da jikinsa dan uwanta da akace hawan jini ya kayar dashi.
Ya dago yana fadin mama kema tafiya zakiyi ke nan yanzu muka gama magana da diyarki ai tana a
bankanta na cewa ita ba zata dawo gidan nan ba.
Ni abin ya daure min kai mama iya kokari inayi da yarinyar nan amma ace Rahama bata ga hakan a
kaina ba yanzu.
Shiyasa nake tunanen zancen mama gaskiyane da tace kawai dai tagajine take neman hanyan guduwa a
yanzu din.
A kul dinka Jafar na kara jin wanan zance irin haka a bakinka kai yanzu bakaji kunyan furta wai yarinyar
nan ta gajine ba tunda ka fada yanzu a nan nasan zaka iya fadin hakan a gaban kowa Jafaru.
Jafar ka tuna iri alherin yarinyar nan a gareka kana a cikin ciwin kama bata yi haka ba sai yanzu da
Allah ya kawo maka sauki ana gani ?
To mama ni banga abinda nayiwa yarinyar nan bayan wanan da zatace ban mata adalci ba a yanzu
wani irin adalci take so a rayuwa kuma ?
Ehh lalai Jafar da sauranka sosai wanan yasa har ake ganin damanka dana matanka ashe sam baka
tsayawa kayi tunane akan abu ?
Yanzu kai ya dace ace kanwaka da mahaifiyarka suna yiwa yarinyar nan cin mutunci kana kallo amma
baka tsawata ba sai wani cikin yan uwanka yazo shine zai tsawata masu ?
Kaga hakan yayi daidai ke nan a rayuwa don Allah kofa waye akewa hakan a gaban wanda yayi dalilin
zuka gidan baka dauki matakin daya dace ace ka dauka ba a matsayinka na mijinta.
Kayi tunane wanan dalilin kadai dana baka idan kana da tunane zaka gane gaakiyan yarinyar nan nayin
hakan dolene ta kufuleka a zuciyarta.
Sanadinka fa take zaune gidan nan yanzu amma irin hakan yana faruwa baka taba daukan matakin
daya dace ba kan hakan Jafaru ?
Shiru yayi yana sauraren mama din saida ta gama ya nisa yake fadin mama nagode insha Allahu za a
gyara dama gudin nayi magana ace banda ta ido .
Mama kin fa san halin mama sarai mama banyi bama tace nayi akan Rahama ni ina kyalewane don kada
na gogawa Rahama bakin jini amma zan gyara insha Allahu.
Daga wajen suka kara tattaunawa da mama din inda a karshe yake fadin saikin dawo zaki dawo nan ke
nan mama da sauri take bashi amsa da fadin anya kuwa Jafar ?
Shi kuma yace haba mama ki dowo don Allah kinsan zaman ki nan a yanzu yana da amfani sosai a
garemu ta dan dago kai tana murmushi take fadin Allah dai ya dawo damu lafiya ya amsa da amin.
A ranan ta tafi hakan yasa ya koma zama shiru shi kadai a daki sai idan iya tashigo dakin dayake yakan
dan samu abokin hira bata zama kuma take fita.
Makin Asmau tayi amfani da wanan daman ta mami mijin nata sai ya kasance a lokacin ita kuma take
ikirarin wai aiyuka suna mata yawa saidai ta dan lekoshi ita da yaran ta koma .
Hakan yasa ya shiga damuwa mai din bin yawa zaman kadaici ya dinga damunshi a dakin dole yasa
zaisa a fito dashi kofan wajen part din ya zauna yana shan iska.
Gaahi zuwan Yazid ya hana a dinga tayar da injimin da rana sai idan dare yayi ko zafi yayi yawa tun
lokacin da matan yaya Jafar din sukace ai ana cutansu ana cin dukiyan mijinsu ba tare dasu ba don anga
yana kwance baisan abinda yakeyi ba su kuma an mayar dasu mata ba a daukesu a bakin komai ba.
Yazid a mota ya tsaya bai fito ba ya tura aiwa kawu sallama jin hakan yasa kawu ya fito don yaron ya
fada mai wani mai mota ke sallama dashi a waje.
Sai gashi ya fito da sauri yana dan waige waige ya hango motar dake tsaye nisa da gaban gidansa kadan
ganin hakan yasa Yazid din fitowa daga motan dayazo dashi.
A,a Yazid dama kaine ka tura ayi sallama dani baka shiga ba ka tsaya waje ya karaso yana fadin eeh
kawu to bussimillah mana mu shiga daga ciki kawu ya fada.
A,a kawu aiba wani abu ya kawoni ba nazone akan wani zance shiya kawoni to yazid ai da dai mun
dan shiga daga ciki akan ita matar Jafarne daine ko ?
Yaran nan basu jin shawara ai shi jafar tunda yazo min da zancen auren yarinyar nan banso ba naso
hanashi amma ya nuna min yayi niyar hakan na barshi yayi abinsa ko uwarku bai kaunan ta sani.
Dakata kawu ba wanan zance ya kawoni ba ninazo zancen kudinane da mama tace min suna hannun
ka ina bukatan kudin a yanzu don ina son na kara jari ga sana,an dana soma.
Kudi kuma yazid ita uwar taku tasan da zakazo tambayan kudin ka don ba kudinka bane ta ban balle
yanzu kazo tambayana haka kai tsaye ?
Ok hakane to zata zo din da kanta har in kudina yana hannunka ka tabbatar da ka bata kafin mu sake
haduwa irin haka don ina bukatan kudina a yanzu don Allah.
Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar kawu din da mamankishi tsaye yana bin bayanshi da kallon
can Allah ya bashi ikon budan baki yake fadin.
Waiko yazid kan ka daya kuwa koka fara shan wani abune haka jin hakan yasa Yazid din juyowa a cikin
mamaki yake fadin.
Yana nuna kanshi yana fadin ni kawu a hayaci nake don ko goro bana ci balle wani maye nayima kama
da wanda ke shan wani abu makamancin hakan yanzu ko ?
Sai yayi murmushi kafin kawun ya bashi amsa ya juya ya tafi har lokacin kawu din yana tsaye a inda ya
barshi har ya tafi.
Nisawa yayi ya juya yana wasi wasin a zuciyarshi don yasan bai jima da wanan maganan da dubu ba
akan zancen kudin yayi mata maganan da yake ganin hankalinta zai kwanta yadda ya saba .
Yanzu kuma kwatsam saiga Yazid yazo da wanan zancen kudin yadda yaga yaron yazo mashi tsatsaye a
yau shine abinda ya daga mashi hankali.
Yasan inda zai kamo shirinsa ai da uwarsa zaiyi amfani itace logon diyan da ita kawai zai hadashi ya
daina wanan zancen.
Shiko yazid yana tafe yana faman shirya yadda zai fitowa kawu din tunda ya hango rashin gaskiya
tsantsa a idon kawu din zaiko gwada mashi bai isa ba wanan karon.
Tafiyan maman tudu yasa hankalin yaya Jafar komawa gareni ko yaushe zai zauna zugun yana tunane
ta inda zai bullowa zancen tafiyan nawa gida.
Don ya kulla da mama sam bata son wanan maganan haka shima habu yayi shiru da alama yayi fushi
akan rashin dawowana gidan tare dasu lokacin.
A lokacin mama ta shigo dakin ta sameshi hakana a cikin halin tunane ta soma fadin Jafaru na horeka
da zama haka kana faman tunane ?
Kasan jikinka ba lafiya gareka bafa ka daina tunanen yaran nan dukkansu yan banzane don jinyar kane
duk suka gujeka da kuma fitinan su ya koresu idan wani abu ya sake samunka a yanzu ba hasaransu
bane.
Haba mama ki daina zagin yaya mutane haka ita Nusaiba ai kowa yasan abinda ya hadani da ita gidan
nan harta fita haka kuma ita Rahama saboda matsinki da saratu akantane ai yasa ta tafi.
Amma ba don jinyana ba ko za a fadi hakan kuma banda Rahama yarinyar da tayi tsaye a kaina har
Allah yaban lafiya.
Yanzu kuma ace don kada tayi jinyana ko ta gaji da jinyata yasa tabar gidan nan kawai dai irin
maganan da kuke fadi a kantane yasata fushin zuciya ta tafi amma ba,,,,
Wai Jafar kanka daya kuwa yau kake fadin wanan maganan haka kamar wanda wani abu ya sama
shima jafar din katseta yayi da fadin a,a mama maganan Allah udan yazo a yishi don kina gani a gabanki
saratu da Nusaiba suka matsawa yarinyar nan amma ba a tsawata masu ba .
Lalai anyi gaskiya da akace macen bafulatana hatsarice ga mutum don basu shiga gida ba su hada kan
kowa a gidan ba idan basu sami hakan ba kuma sai suyi yadda zasuyi suga sun halaka duk wani wanda ke
gidan ,,,,,,
Wayanta dai daya dauki kara shiyanata karasa zancen datakeyi din ta tsaya daukan wayan a cikin
mamakin dan nata datakewa kallon tababe a ranan kan bafulatanan matarshi din data tafi yasashi
gigicewa hakan.
Ganin layi kawu daya matsa kiranta yasa ta dakatar da zancen ta dauki wayan da sallama tana karawa
a kunnenta ya amsa.
Gaisuwa ta fara mai ya amsa a gagauce ya soma fadin Dubu kina da masaniyar zuwan yaron nan
gidana kuwa ?
Ta mayar mai da tambaya itama da wani yaro ke nan kuma ya amsa da yaron nan Yazid mana wai yazo
tambayana kudinsa da akace suna hammunsa.
Kudinshi kuma shi yazid din yazo tambayanka kudi yaya ya amsa da kwarai yazo shekaran jiya nace
bari dai in kiraki in tambayeki ko kina da masaniya ga hakan ?
Wallahi summa tallahi yaya banda masaniya ga zuwanshi wajeka shi yazid din yaje gidan ka yaya yana
tambayan kudi kuma bayan na fada mai kada yayi wanan maganan a wajenka .
Kwarai kuwa yazo min nan a fitsare wai yazo karban kudinshi a wajena nace yaje sai munyi magana
dake Dubu dama abinda nakewa gudu kenan gashi ko ya faru tun yanzu ?
Har yaushe aka bada kudin nan don Allah dubu da za a dinga matsawa da a bayar dasu bayan an juya
kudin zuwa kaddara yanzu.
Yaya kayi hakkuri dan Allah zan mashi magana sai faman fada yakeyi Jafar yana zaune gefe yana kallon
ikon Allah a tsakaninsu.
Saida ta gama wayan ta dago tana fadin kaji min kuma wai yazid ya samu kawunku yana mashi zancen
kudinshi .
Ok kawune kuke waya dashi yanzu ta juyo a cikin damuwa tana fadin yanzu haka kawai yaron nan
muna zaune lafiya da dan uwana yana son hada tsakanin mu.
A,a mama ku natsu ku bincika kuji meye dalilishi nayin hakan dole yana da dalilin dayasa yayi hakan ai
ba zai tashi haka yaje wajen kawu kai tsaye zancen kudi ba.
Jin abinda Jafar ya fada yasa uwar kallonsa tana fadin barshi ya dawo ai zai sameni bai yarda dani ba ke
nan danace kudin suna hannun yaya yaje da kanshi ya bincikeshi ?
Fada sosai mama din keyi ga yazid din ya fita tun safe bai shigo ba har mama dubu ta fito zuwa part din
don diba jikin jikannata nan ta samu mama din tana fada saidai tana ganin iya taja bakinta tayi shiru.
Don da jafar da yazid suna dasawa sosai da tsohuwar habune kadai suke yawan fada dashi lokaci lokaci
wanan yasa ko yanzuma da yazid ya dawo da iyalinsa suke kadaici itace mai zama dasu tana debe masu
kewa.
Sai bayan la,asar ya dawo gidan part dinsa ya nufa inda ya dan zauna da iyalinsa yaci abinci kafin ya
fito don tun safe bai leka dan uwansa ba.
Ya shigo da yaronshi a hannusa cikin fara,a yana fadin yaya ka ganni sai yanzu na tafi duban masu
aikine can nake tun safe don kada su sake maimaita shirmen da sukayi a baya.
Ya dan rankwafa yana fadin ya karfin jikin naka brother badai matsalan komai ko yake tambayan dan
uwan ?
Ya juyo wajen mahaifiyar tasu a sake yana fadin mama barka da gida yaya gidan kuma da iyali ?
Suna lafiya Yazid yaushe kaje gidan kawun ku tambayansa kudi don dazun ya bugo min waya yana
tambayana ko ina da masaniyar zuwanka wajenshi ?
Ya samu bugo maki kenan naje ina son kudina dake hannunsa akwai abinda zanyi dasu a yanzu don ba
zan tsaya ace sai kawu ya juya min kudina ba mama ?
Yazid ni kake fadawa hakan kai tsaye ko kana son nuna min cewa mu bamu isa rikema abinka ba ke nan
ko ?
A take ya daure fuska yana fadin da karfina mama zan tsaya kawu yana juya min dukiya aban abinna
yadda akabawa kowa nasa in rika don ina da abinda zanyi dasu yanzu .
Yazid kafita min a ido akan kudi kada ka tsaya kana min rashin kunya a gabana yanzu da sauri yazid din
ya katseta yana fadin .
Mama kudina fa nake zance ba wani abu ba ya ban ina da bukatansu tunda hakkinane anbawa kowa
nasa nima ina bukatan nawa a yanzu.
Kudi a yanzu kaddara aka mayar dasu don haka banson jin zancen kudin nan a yanzu ka bari sai ranan
da ya sayar da kaddarorin daya saya ya baku kudin ku.
Ba zai yuyu ba mama kudin nan fa kudinane bance aban na wani nayi amfani dashi ba don haka a ban
abinna don Allah ki fada mashi.
Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar dakin da danshi a hannunsa yana shiga part dinsa ya zauna
yana fada yana fadawa iya abinda ke faruwa .
Karshema ya dauki waya ya dannawa kawu waya yana fadin kawu zancen kudina nake maka ina
bukatansu nan da kwana biyu in Allah ya kaimu yana fadan hakan ya kashe wayar tashi rai bace.
Shima a bangaren kawu bin wayar shi yayi da kallo yana mamaki yadda dan nasa ya kirashi babu ko
sallama yana mashi zancen kudinshi.
Yasan akwai matsala ke nan akan hakan don dole yakai kanshi gidan su zauna a gaban mahsifiyarsu ta
takawa yaron burki don yasan ita kadaice zata iya takawa yaran a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[6/3, 8:58 AM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA[5/14, 10:19 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nayi sati hudu a gidan mijin ummah banda dan damuwa da sabo da zama a dakin aure banda wani
matsala a gidan kamar yadda na fada a baya.
Ganin hakan yasa na kirkiro tafiya Abuja na samu ummah da zancen take fadin anya daddy ku zai yarda
da hakan kuwa ?
Ace kina nan mun barki zuwa kuma abuja amma zan fada mai naji ko zai yarda da hakan idan ya shigo
yanzu ya tafi rigasa wajen abokinshi.
Ina kwance dakinta da yamma sai gashi har dakin ya shigo ya sameni tare da ummah yana saye da
coffe colour din jallabiya mai dogon hannu a jikinshi.
Saida yakai zaune saman kujera ya soma fadin diyata maman ke fada min kina son ki karasa Abuja ?
Nace ko anyi maki wani abune a nan din da sauri na dago kai na dubi ummah kafin na girgiza kai ina
fadin ba komai daddy .
Kawai dai ina son inje can din ne kawai nagansu sai ya gyara mike kafanshi yana fadin ayi haka kuma
Rahama ?
Bayan mijinki da yan uwansa sunsan ki wajen mu yanzu kuma suji cewa kin koma Abuja yaya kike son
su dauki zancen a zuciyarsu ?
Sai na sake kasa da kaina na dukar yacigaba da fadin kinga hakan ba zai masu dadi ba don hakan na
nufin cewa mu nan mun gaza dake hakan ke nufin da sauri na kara dago kai na dubeshi yayi murmushi
yana fadin yes idan mun barki zuwa abuja hakane zancen.
Ba zani ba daddy na fasa yace good girl Allah yayi maki albarka kinji kiyi hakkuri har ki koma dakinki
saiki tafi da bakin mijinki daga can na amsa mashi da toh kawai.
Ya dan min nasiha nayi hakkuri don Allah na saki jiki kuma tunda nasan a yanzu bani kadai banr a jikina
yasan kuma bada jimawa ba mijina zaizo mu koma.
Ya dan jima nayi mai godiya ya mike ya fita daga dakin ummah tabi bayanshi suka fice a hankali na
sauke ajiyan zuciya na koma na kwanta ina tunane.
Sammako kawu ya bugo masu a gidan duk dai akan ya samu yazid din a gida a gaban mama don kada
ya fita suyi sabani donshi yafi bukatan ayi komai a gaban mama din don ya hango rashin mutunci a idon
yaron .
Kamar kullum saida mama tasa yan matanta sukai mashi abin karyawa yanayi yana tambayan kada
Yazid ya fita fa dubu gara a aika a fada mai ana nemashi.
Kada yazo ya fice daga gidan ba tare da sun sani ba kuma yazo daga baya ya bishi gida yayi mai cin
mutumci har wasu suci.
Da mama dubu taga ya matsa yasa ta tayar da salima akan taje part dinsa ta kira matashi suna
nemanshi ita da kawunsu.
Salima taje ta samu har lokacjn basu bude part dinsu ba don yana ciki hakan yasa ta dawo ta fadawa
mahaifiyar nasu cewa basu tashi daga barcin ba.
Karfe nawa yanzu kije ki kwankwasa masu kofa ya bude muna son ganinsa a nan hakan yasa ta koma ta
kwankwasa kofan .
Suna zaune suna karyawa a falon nasu sukaji nocking matarshi ta mike ta bude kofan kamar kullum
fuskanta yana a daure kamar yadda