Chapter 33 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   33 / 101

96K to 99K   out of 302.2K words

babban mutum ya zamo yaro a gabanka.

Akwai wayewan kai a yar fahintan da naiwa rayuwan mutum biyu a yanzu ma,ana miji da mata ko
saurayi da budurwa.

A tsakaninsu akwai kyautatawa da burge juna a lokacin taraina koda akwai sabanin hankali idan Allah
ya hada wanan burgewan yana nan a zukatansu.

Jin nayi shiru na shiga dogon tunane yasa yake fadin kina jina Rahama ina son dana dawo wanan
tafiyan in sha Allahu za ayi komai a tsakanin mu.

Fatana ki kwantar da hankalinki ki cire wani shakku da tsoro a zuciyar ki kada ki tsaya duban rayuwan
wani ki duba tamu da nake kokarin ginawa a yanzu.

Sam ban yarda da tsarin anty Salma na cewa ki zauna a hostel ko a kama campus ba nafi bukatan kai
tsaye ki dawo Zaria a matsayin matar jafar.

Gabana naji ya fadi da wanan kalman da sauri na tareshi da fadin a,a yaya don Allah kayi hakkuri ban
taba wanan tunanen ba kuma ba zanyi a yanzu ba.

Kai din a yayyuna nake daukanku yaya ba irin wanan zancen a tsakanin mu don Allah kamar yadda ka
fada a baya ba a daukan hukunci a cikin fushi yaya.

Haka kuma matanka basuyi karya ba yaya kaidin ba tsaran aurena bane sun fadi gaskiya da sukace naje
na nemi daidai dani dan daji.

Nima ai daga dajin asalina yake ko habu bai fada maku asalin mu daga kauye mahaifin mu ya fito yazo
nan zaria ba.

Sun san kin fisu da komai Rahama hassadan hakan yasa suka sakaki a gaba har sherinsu ya haska min
hanyan da ban gani da farko saida kalamansu ya haska min hanya sun kwakwasa min kofa da zan bude
sabon shafi a rayuwata.

Don haka a cikin kalamina Rahama ba gudu ba ja da baya don a shirye na fito da makamaina kan mai
uwa da wabi zanyi lokaci guda.
Kasake nayi ga bugun zuciya dake harba min lokaci guda tunane barkatai suka taru min a kasan
zuciyana .

Tabbas idan na samu yaya a miji na more a rayuwata saidai bahaushe yace ana barin halas don kunya
dolene naki karban tayin yaya a kaina don tsira da mutuncin yar uwata dake aure a gidansu .

Yau badon hakan ba kai tsaye zan amsa tayin nasa sai dai wani sashe na zuciyana yana mai ban shawara
da mai zai hana inbi shawaran anty salma ko girgiza imanin su indanyi.

Muryanshi naji yana fadin zan barki Rahama an fara sanar muna da mu karaso kusa jirgin mu yana kan
layi.

Saina samu muryata da fadin to yaya Allah ya kaika lafiya ya bada sa,ab tafiya amin Rahamata in kuma
dawo lafiya in sameki a shirye da tarona.

Muka kashe wayan da karfin gaske nake jin zuciyata ta bugawa hakan yasa na sauke ajiyan zuciya ina
lumshe idanuwa tunane barkatai nayisa a lokacin kan in yarda ko kada in yarda .

Washegari da safe haka na tashi ina jin zuciyana tayi min nauyi don kwana tunanen dana zaunayi
dogon riga dinkin dinkin atamfa mai A sharp na saka a jikina sai dan karamin gyale dana dora a kaina .

Abujane fa birnin taraiya Abuja ko dame kazo anfika saidai kayi naka banjintar ka bari wani yazo da tasa
kalan .

A falo na samu anty Salma zaune tana ba yaranta abinci tun daga fitowana take fadin oya zo na zata ai
kina kwancene wanan dan naki dan rigima wai ba zaici abinci ba haka zai tafi school da yunwa.

Murmushi nayi na karasa na karbi abincin a hannunta ina lalashin yaron kafin ya soma karba yaci daga
hannuna har suka gama na rakasu har bakin mota suka tafi.

Falon na dawo don sai goma zan fita tana waya na kwashe kayan zuwa kitchen nakai na fito bayan mun
gaisa da yan aikinta dake dauka ni din yar uwatarcen ta jini kamar yadda take fada a kaina din

Don haka suke kirana da small hjy zama nayi a gefenta din ta juyo tana fadin kai Ramaah wai kinga
yadda kikayi wani fresh dake kuwa wanan aiko yau kika koma zaria ba zasu ganeki ba

Waini kan ya zancen mutumin nakine kwana biyu banji zancensa ko kin fita batunsane wai gaskiya
Rahama ina sonki da guy din nan.




ZAINAB IDRIS MAKAWA[2/4, 10:18 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,



3️⃣5️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Bayan sati biyu da hakan shigan bazata yayi masu don da safe yashigo gidan wanda ke nuna a garin ya
kwana ke nan don duk wanda yagashi a zaria karfe takwas na safe haka yasan a cikin garin ya kwana.

An kasa samun wanda zai tambayeshi ina ya kwana sai iyace take fadin amma a garin nan ka kwana
Jafaru.

Ya bata amsa da eh iya cikin gari na kwana nashigi da darene sai kawai na sauka wancan gidan nawa.

Kana da wani gidane dama Jafar ban taba sani ba kowama bai sani ba iya idan ba yanzun din da nake
fada maki ba amma na dade da ginasa ai komai kuma na saka a cikin gidan.

Ina son in kai amaryata can ta zauna ita kadai sai masu tayata aiki kawai a gidan kinga na samu gidan
hutu ke nan .

Can zai zama Abuja kenan yaya nan kuma gidan kwamacala ya zama lagos ko don lagos shike daukan
duk wani kwaram da amma.
Salimace take fadin hakan a cikin barkwanci ga dan uwan nata data dauka zolayan iya yakeyi ya fadi
hakan.

Saiba dake zaune ta tsoma bakiga zancen da fadin babu wata shegiyan da zata shigo muna gida iyamu,
mun isheka rayuwa muma din ya aka iya damu balle aje dauko wata.

Ta fada tana turo baki dake nuna tana cike dashi har lokacin gashi ya sharesu kusan wata daya ke nan
yanzu ya dawo kuma ba wace ya tsaya kulawa a cikinsu.

Itako Asmau sai cewa tayi ai lagos din ma ba laifi indai zaka zauna lafiya ko a lagos ai akwai more
rayuwa sosai ma don yafi wani wajen sau dubu.

Salima tace amma ai kusan cewa Villa shiyafi dadi ko ?

Don gaka ga gidan kudi kullum kana jin kamshin bugunsu haka kuma shine headquater da kowa ya sani
dai dole yaya ya tare da amaryansa Villar ku kuma kuna nan da yara kuna kwamacalan ku.

Dadin abin dai ba a canzawa tuwo suna haka kuma baka zama da miya ba tuwo don shine abokin
hadinsa mu din dai mune dai ba wata yar banzan da zata sake shigowa gidan nan da sunan matan aure a
part din nan sai dai can gaba kuma .

Wayanshi dake kusa dashi ya dauka cikin rashin damuwa da zantukan da sukeyi lokacin can a ka daga
yake fadin kai Habu kana inane wai gani gida zaria ?

Ina nan kano tun shekaran jiya ana karasa sauke maine har yanzu to idan an gama kazo gida don ba
dadewa zanyi ba zan koma .

Ina tafe yau din nan in sha Allahu zuwa yamma Habu din ya fada yace Allah ya kawo ka lafiya yana
kashe wayar tasa ya aje gefe daya.

Sai lokacin iya ke fadin da alama dai wani tafiyan zakayi ke nan kuma Allah ya tsare muna ku Jafar a
duk inda kuka nufa din ya amsa da amin iya.

Yanzuma akwai abinda nashigo yi a nan zaria don da baku ganni maza ba saboda aiyukan da suka taso
sosai a yanzu sai iyan ta karba da madalla haka muke son ji ko yaushe aiki ai alherine.

Ta juya ta kalli salima data rakota tana fadin to ke zaki zauna nan ne kuna cika baki ko zaki maidani
wajena don naga baku karasa cacan bakin naku ba har yanzu.

Ehh lalai ma Iya cacan baki kika dauki zancen mu ashe yanzu akwai wata wace zatayi gigin shigo muna
gidan nan da sunan kishiya ?

Au kina wasa wuka a gaban doki ne don yaji tsoro ko to jafaru ba raggon maza bane yana da ikon
cikawa da biyu a rana daya.

Yadda aka auroki kika shigo kika hana wata rawan hantsi kema haka za a dauko wata a kawo bayanki
don ba a haifi namiji don mace daya ba dama.
Tashi muje yar nan ta dubi Salima bayan ta gama maganan daya harzuka Saiba din data gane nufinta ta
zata asirin da take bankawa jikan nata yana tasiri akansane da har bai iya daukan wani kwakwaran
mataki akansu.

Jafar yasha yiwa iya korafi akan Saiba ko ince ya kawo mata karan sai ba din kan barbade barbade ga
abinci ko cusa abu a gabanta bayab sun gama sunna ya ga abin tun yana mata fadan hakan dagashi sai
ita har yagane hakan yabi jikinta ba zai iya lamuntan hakan gareta ba yakai karanta wajen iyan akan a
tsawata mata ta daina wanan halin.

Wanan yasa ciwon sa na farko harda zargin saiba din saida sukayi wanda dama hakane ga mace mai
hadawa da surukulle wata rana har abata abinda zai cutawa abokin zamanta cikin rashin sani da sunan
taimako a gareta.

Ya Habu bai shigo gari ba sai wajajen la,asar ya dan gauta ya iso tun shigowansa gidan ya hango motan
dan uwansa a kofan part dinsa.

Nasa part din ya tsayar da motarsa ya shiga ciki inda ya samu matarsa da dansa don ita ba ma,abociyar
son shiga jama,a bace wanan ya kara mata bakin jini a gidan suka kara tsanarta.

Don sun dauka daukan kai take masu don tana ganin kamar ta fisu wanda ba haka bane haline saika
zauna da ita na wani lokaci batace dakai kalla ba saika gaji kayi mata magana.

A part din iya suka hadu da dan uwan nasa sun dan zauna na lokaci kafin suka mike da sunan zuwa
wajen mama dake can tudun wada family house dinsu ita da Saare da Nafisa.

Tun zuwa sunan matar yaya sani basu dawo gidan ba suka zauna can din wanda ita Saare bata so
hakan ba amma mama Dubu tace ba zata koma gidan yayyun taba sai tare da ita wanan zaman takuran
Saare take cikinsa duk kwanakin.

Motar Habu sukai amfani dashi suka fice gidan a hanya Habu daya kula da rashin sakin jikin dan uwan
nasa yake fadin kace kana son ganina J ?

Haka kuma tun shigowana part din iya na kula da dan fadawan da kayi don kayi rama sosai a yadda na
barka wani abin ya farune kuma ?

Ya dan juyo daga barin kallon titin da yake yana mai dan tsurawa dan uwan nasa idanu na dan lokaci
kafin ya mayar a hanya yaci gaba da tukin da yakeyi.

Yayi wanan magananne don yadda yaga damuwa karara a fuskan dan uwan nasa don bai saba ganinsa
a hakaba ko da yaushe yana a yanayin nishadi da walwala .

A hankali J din ya kwantar da kansa jikin kujeran mota yana sauke ajiyan zuciya tare da lumshe
idanunsa yace.

Bari Habu ina cikin wani dan cakwakiyane a kwanakin nan duk da kaima nasan abin zai shafe ka duk
yadda ka kauce kuwa .
Subbahanallahi mene wanan abin J jikin nakane ya kara tashi kuma again ya girgiza kai yana fadin ba
jikin bane Habu rigima dai na fada a ciki lokaci guda.

Habu ya jinjina kanshi yace ina saurareb ka nasan dai duk rigiman da zaka jawo ba wanda zaiyi kasa da
martaban mu bane a idon mutane in sha Allahu.

In Allah ya yarda ba irin wanan da kake nufi bane habu rigiman soyayya na fada lokaci guda ka kangani
a haka na rasa wanda zan fara tunkara da zancen nan saikai habu don nasan zaka sama min mafita in sha
Allah.

Soyayya kuma J kana da mata biyu fa a gida me zaisa ka fada tarkon wani soyayya kuma a yanzu
again ?

Nima abinda nake duba ke nan Habu abin mamaki ban taba tunanen zan fada tarkon soyayya irin haka
ba lokaci guda sai gashi Allah ya jarebeni da hakan .

Lokaci guda habu Allah ya jarabeni da matukar son yarinyar da kowa zaiyi mamakin hakan a gareni
amma ubangiji cikin hikimarsa da buwayansa da masifan sonta haka lokaci guda.

Guntun tsuki Habu ya saka lokaci guda yana fadin wanan ai baikai na tashin hankali haka ba ni harka
firgitani wallahi .

Aure a yanzu gareka ai wata mafitace ga wanan matan naka da basu san ciwon kansu ba Allah yasa dai
ita wanan din ta kwaraice da zata fiddakai kunyan abokanka.

Kaifa Habu dadina da kai ke nan ba sai kajira kaji ko wacece yarinyar ba a yanzu kana zaton zan yarda
in kara jefa kaina a duhu irin hakane ?

Wa yan nan ka dauka auren kaddara da kurciya nayi dasu yanzu ko aure nake so na kece raini a kaina
wai kasan yadda nake zaman kaddara da kazaman matan nan kuwa ?

Ankai fa nida part dina habu har gudunsa nake wani lokaci ka dai sanni da kyankyamin tsiya tun farko
sai gashi ubangiji yai min wanan jerabawan kazantar akansu.

Ankai habu ko ruwa na dauka koda a gora ina jin kyankyaminsa haka inda zan kwanta sain kakabe da
kaina in samu in raba in kwanta sabo tarin jakkanci irin nasu.

Ni nakance ashe shiyasa suke abokai tun farko haline yazo daya ashe babu wace zata gyara wata a
cikinsu ranan ina jin kannen Asmau suna mata fada wai har yanzu ashe tana nan da kazantar ta suna
ganin kokarina da nake iya rayuwa cikin wanan bolar dasu haka ka duba fa Habu yan uwanta ma sun
shedeta da kazantan tanan ashe haka.

Habu yayi kasake yana sauren dan uwan nasa tare da kara tausayawa irin rayuwan daya tsunci kanshi a
ciki da matan nasa don zai iya cewa dan uwan nasa sam bai morewa aure ba.

Haka kuma wanan zancen da dan uwansa ke son fada mashi a yanzu matsalace babba don abin bai
tsaya akan soyayya kadai ba game da yarinyar da yake son ya aura din .
Yaji J din yayi huci gumi yana dan tartso mashi saman goshinsa tankar wanda yake cikin mumunan
yanayi da sauri ya kara waigo dan uwan nasa yace.

J wai meke farune dakai haka nifa gaba daya ka rudani ma ka wani sauya kamar ba kai ba wanan wace
yarinyace haka wai take son baka wahala ?

Ko kuma ita din ba musulma bace kake tunanen abinda zai biyo bayan zancen ga iyayyen mu ko kuwa
sun hana maka itace an samu matsala daga iyayyen yarinyar ne ?

Murmushin karfin hali J din yayi yace haba Habu ba wata bace fa yarinyar da sonta ya rikitani min tulin
tunane illah Rahama dai kanwar matarka da matana sukai min zargin kulata wanan abinda sukai min
kamar sun ingizanine ko haske min hanya akan wanan yarinyar Rahama a yanzu.

Saida Habu yaja wani uban burki a saman titi Allah ya taimaka hanya ba wasu motoci a cikinsa sosai ya
juyo yana kallon dan uwan nasa yace.

Rahama dai Ramaah ta wajen maria matana kake nufi J ?

J din ya marairaice murya tamkar zaiyi kuka cikin yanayi na kyarmar murya yace Habu mafita nake so
da zancen nan don har nakai kaina gareta garesu da ita yayan nasu nacan .

Ban samu matasala ga yar uwar tasu ba saiga Rahama din ita ta nuna kaduwa da jin zancen saidai nasan
yar uwar nata tasa yanzu ta soma saurarena.

Shiru Habu yayi yana wasu tunane da baisan iya adadinsu ba lokaci guda kafin yaji muryan dan uwan
nasa yana fadin .

Habu ina son auren yarinyar nan a yanzu don irin halaiyansu nagari dako wani namiji ke fatan samun
mace ta kasance a hakan.

Bani barci da dadi akan tunanen yarinyar nan a yanzu duk abinda nake wanan abin ne yanzu a gabana
na rasa ta ina zan fara nasan akwai cakwakiya sosai da rigimar auren nan idan hakan ya tabbata din
saidai na matana mai saukine tunda ba waje daya zan ajiyesu ba don gudun fitina kuma ga yarta a gidan
hakan ba zai yuyu garesu ba.

Ina matukar jirkita akan zancen nan Habu rasa Rahama a wajena tankar rasa rayuwatane habu ban kara
furgicewa ba saida naji ita wanan yar uwar tasu tana fadin.

Koda Rahama zata dawo zaria school ba dai a gidan mu ba saidai ta zauna hostel ko kuma ta kama mata
campus ta zauna ina hakan zai yuyu gamu habu ?

Habu ya nisa yana fadin ni a ganina wanan ba matsala bane babba haka J matsala dai dayace shine ka
samu yardan yarinyar wanda nasan da wuya gaskiya hakan ya faru a cikin sauki.

Duk da haka idan matanka sunji wanan zancen yaya zasu dauki hasashen su akanka na baya zaka iya
jure kalubalin da zai biyo bayan zancen.
Idan har zaka iya ninasan hanyar da zamu bullowa ita Rahaman da yarta dama wani da zai iya kawo
cikas a cikin zancen mafita dayace shine muje muga hardo bakin mu a laikum in yaso daga baya sai a
baiyana wa kowa yasani.

Amma kuma ni dai shawaran da zan baka shine idan kasan matanka zasu kawowa yarinyar nan nakasu
a rayuwan ku gara tun wuri kayi hakkuri ka cire wanan zancen Rahaman a cikin zuciyar ka don na fahinci
har da gaiya kake son aikata hakan.

A harzuke ya soma fadin wai Habu su suka ajeni koni na ajesu dubaiya nakeyi nake zaune dasu kasani
amma kuma yanzu kana fada min in hakkura da Rahama ?

Kai Habu ya girgiza yana fadin J kayi hakkuri ba wai bani sonka da Rahama bane nima na dade inawa
wani dan uwana samun wanan yarinyar Rahama saboda halaiyanta dayayi min.

Amma yanzu kai daka bullo da wanan zancen akwai babban aiki nake hango maka agabanka don fitina
kake son janyowa kanka a ganin ka ita Rahama yanzu bata da wanda take sone ?

Haka kuma matan ka kana ganin zasu kyaleku ku zauna lafiyane wanan abubuwan nake hango maka J
don tasu mama mai saukine matukar muka samu kan kawu ai an gama zancen.

Wayan J din yayi kara amma ya kasa dagawa har saida

33 / 101