Chapter 36 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   36 / 101

105K to 108K   out of 302.2K words

Sun dai tsaya an sulhuta inda shi Jafar ya roka da cewa suyi shawara sai a sayi wajen a gina ma gwaggo
din tunda bayi za a yi mata zama ba bayi kuma baiyi a gareta.

Daga gefe Habu ke fadin wai tsaya Isah yaushe aka raba gidan nan bamu da labari sai wanda aka kira da
isah din yace ba dole sai kayi labari ba ai tunda ita mama dubu tasan kowa akan bangaresa yake ai gidan
nan tun baba na da rai kuwa.

To ban yarda ba yasa kai ya shiga yabarsu ana wani hayaniyan a wajen kuma iya gaskiyarsa ke nan akan
bai yarda ba din a lokacin.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/7, 9:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
3️⃣8️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Zaune suka samu mama Dubu da Saare a kasan kafet din falon suna cin shikafa da miya da aka zuba
salad a gefe daya sai goran zobo a gefen kowansu da ruwa na leda.

Mama ruwan ya kare ke nan ko kun koma shan na gora kuma Habu ya fada yana zama mama dake
kokarin kawar da goran gabansa don ya zauna da kyau tace.

To Habu a zauna ba abinyi sai shan ruwa a gora wanan ma ai samunsa gatane wasu na can suna neman
irinsa basu samu ba ba kuma lafiya muka fisu dashi ba.

Sanabene kawai irin na zamani da wani ruwa iyayyen mu samu kanmu muka sha muka rayuwa cikin
sallaman ubangiji kuma.

To ai yanayi yana saka ayi taka tsantsan mama Jafar ya fada daga gefe daya sun zauna aka gaisa take
fadin saiga Rakiya hankali tashe wai kawunku yai tafiya bataji duriyansa ba ?

Ai har nan tazo ashe Habu ya tambaya mama take fadin har nan take ai hankali tashe bataga mijinta ba
ni abin na Rakiya har yana ban kunya kuma wallahi ?.

Koda yake shiya saba mata ai dole ta damu don daya dawo baya numfasawa sai ya zube mata kaf
abinda ya nemo ta lissafe itace mai tsara yadda za a kashe a tsakanin su.

Ita har yanzu tana wanan halin natane wai Jafar ya tambaya tome zata fasa haline fa kuma ya daukar
mata hakan ai kaga bata da laifi ke nan.
Wayan mama din dake saman kujera a gefenta yayi kara ta dauka tana fadin kaga yar halak itace ma ke
kirana ashe yanzu kuma .

Habu ya dubi dan uwansa yana fadin Isah bai san halina amma zamu hadu wanan karon dashi rainin
wayyon da sukeyi a gidan nan yayi yawa sai kace su kadaine yaya baba ?

No saka masu ido duk abinda zasuyi suyi gida dai a yanzu kafi karfin tsayawa kana fada a kansa Habu
suda suka tsaya jiran gado sai suyi ta zaman cinsa mu dai mun gode Allah munfi karfin hakan a yanzu.

Lokacin mama ke fadin ai gasu gabana yanzun nan suka shigo amma basu fada min har can suke ba ai
sai kuma tayi shiru tana sauraren bayanin da Rakiya keyi kafinta tace wai wani Jafar kike nufi dai ?

Jafar yayi aure haka kowa bai sanda zancen ba jin hakan yasa su zubawa mama din ido lokaci guda
suna saurarensu .

Don Allah Rakiya ki bar zancen nan mana Jafar fa yai aure har yaushe ya taso daga ciwo da za a kakaba
mashi aure a yanzu haba dai don Allah nawa Jafar yake da zai zauna da mata ukku biyun nan ma yaushe
ya iya dasu balle yaje karo wani auren kuma ?

Saare ta kafe mama da ido don bata fahinci takamaiman zancen mama din ba akwai mamaki ace
yayanta J yayi aure haka basu da masaniya a kai.

Mama wani masaniya zakiyi a zancen banda ki saka masu Albarka tunda Allah ya nufa dai matarsace
daga zuwa nema aka sauwaka muna komai don nisa aka daura auren lokaci guda ai kinga anyi muna
halarci a nan.

Kai dakata min da wanan zancen banza don Allah ban haifi dana don wasu ba don haka babu wata
gaiyan tsiya da za,a sake kwaso min kuma wanan aure bai dauru ba a wajena.

Haba mama wani irin zance kikeyi hakane aure kan an riga da an daura yarinya na zamasa a yanzu
saidai kiyi hakkuri da fatan alheri a garesu kuma.

Habu wai meya hau kankane haka ina fada kana fada zan gani idan kaine ka haifa min jafar din waima
wayaje har wanan gari ya auro banda labarin komai ?

Shiru sukayi gaba dayansu sun kasa bata amsa don yadda ta birkice a lokaci daya a hankali habu dake
mikewa yake fadin you have to be strong for dis issue if not ,,,,,

Ai da ka zageni da hausa habu abin zaifi maka sauki da wanan yaren nasaran da kakeyi a yanzu ko
bamu son jafar zamu so lafiyanshi ba tashin hankali a kansa ba.

Tsam ta mike zata shige daki cikin wani tsaya yayi magana yana fadin ke dawo munafuka kawai ina zaki
ana magana zaki daukan rahoto ki samu na yadawa ko ?

Ai ka barta ta yada din duk uban da zata kira ta fadawa taje ta kira idan wani ya aura min matar mama
ba kowa na aura ba sai Rahama dai da kika sani kanwar marian habu itace na aura zargi ya kare.
Anty Nafisa dake shigowa don ta gaidasu taja ta tsaya a cikin mamaki tana bin yan uwan nata da kallo
tace yaya J ka auri Rahama ?

Tabbas Rahama ce na aura don wanke zargin da aka soma min iya matakin da zan dauka ke nan tunda
ance dama farkatace ita dole in mata gatan hakan a idon kowa.

Yanzu na gaskanta zancen da ake fadin fillo kakan sheri yau sherin nasu a kaina kuma ya dawo ke nan
an fada masu ni na haifa masu diyana donsu ne ?

Haba mama bai kamata aji hakan daga bakinki ba ai na dauka wanan abin da nayi albarka zaki saka min
kan yadda nayi din ba irin maganganun nan ba ?

Rahama dai kowa yasanta yasan halinta balle ta zama bakuwa a cikin mu ni kuma na ganta nace ina so
ba wanda ya tilasta min yin hakan.

Ni dai naga dacewan hakan da nayi duk da yarinyar bata sona ga hakan asalima daga ita har maria har
kawo yanzu basu sanda zancen auren ba.

Don bata ban hadin kai yadda naso ba hakama wa yanda take wajensu can basu bani goyon baya akan
nufina ba yasa na dauki kawu da Habu da Nasir muka tafi tare dasu aka kumayi mai gaba daya.

Kiran wayansa da akayi ya katse masu zancen ya mike yana fadin yana zuwa ya barsu a zaune zugun
zugun kafin yasawa Habu kira ya mike shima ya fito daga dakin.

Fada mama dubu ta soma tana fadin yau za ayita ta kare ba sai gobe ba wanan ai tada zaune tsayene
yaushe aka taba yin hakan kagani.

Kanin ka yana auren ya kai kuma kaje ka daura aure da kanwa don shashanci kana babba a garesa ka
koma ka auri kanwa kuma ? wanan wani irin komawa bayane wai ?

Ba kowa bane maria ce keda kisisinan nan mama tunda tana ganin ta samu waje bari ta cusa yar
uwarta itama da hadin bakinta hakan ya faru .

A,a Saratu ki kama bakinki wanan zancen manyace bata yara bace kin dai san halin yaya habu yanzune
yaji abinda kike fada akan matarshi zai latsa ki wajen nan.

Ai sai yazo gata tunda hauka yayi ya kara dukan mi ya kan matarshi wanan karon ba zan raga mashi ba .

Mama ta daiyi shiru shine alheri ta kama bakinta tunda ba zancen ta bane gashi kuma sun fada daga
maria har Rahaman basu sanda zancen ba ?

Dazun nan muka gama waya da Rahama da safe a dakin nan mamakinji metace ai danace hutunsu ya
kare tace saita kara lokaci zata dawo .

Nafisa rabu da yaudara inda kika gansu sunsan komai maganan saratuce da gamin bakin maria akai
hakan don haka ko ita ba zan kyaleta ba gidan nan yanzu.
Ya jima a unguwar saidai bai yadda ya kara shiga cikin gidan nasu ba don habu ya fita tun bayan
fitowansu ya nufi kaduna.

A lokacin ya kira anty Salma yayi mata bayanin komai tare da rokonta zai turo mata kudi ta hado mashi
laife.

Hakan akayi ina daki kwance duk da ba barci nakeyi balokacin don haka kawai nake jin raina ba dadi
aranan.

Kafana taja tana fadin lazy tashi ki rakani outing wani ya ban aiki daga maiduguri haka na tashi na shiri
muka fito ganin harda Samuel driver da yunusa zamu fita yasa nasan babban abu zamu fitayi kfaruwa
lokacin.

Bayanin da takewa yunusa yasa na fahinci meke faruwa a takaice dai wani ya sakata hada lefe na
gagawa wanan sana,an mamace mahaifiyarsu anty salma.

Donshi banyi mamaki ko kawo wani abu kasan zuciyata ba nakance alfahari da neman suna yake sa
wasu fita waje don banjinta da daukakansuna.

Amma komai da zaka sayo waje akwaishi a nan gida Nageria dan bambanci kudi kuma kadanne a
tsakani don muda kan mu muke raina arzikin kasan mu da kan mu amma gaskiya matasan masu kudin
Nageria suna iya kokarinsu wajen cigaban kasan nan saidai mu yan kasan ne bamu bada goyon bayan
cigabansu.

Don munfi ganewa alfahari da bajinta a koda yaushe wanan na kara durkusar damu a cigaban kasa da
zamu samu.

Tayani zaba Ramaah kada ki damu da kudin kayan ki duba qualities dinsu kawai ki dauka duk abinda
yai maki kyau a zuciya.

Nasan wanan akidar tasu tun muna kananuwa mama kanzo damu mu tayata zaben kayan da take
hadawa din da gyaran wajen event dinsu da suke bada haya.

Jin hakan yasa na zage na tayata zaben abinda nake ganin na fita kunya saboda furcinta sosai muka
hada kusan akwati ukku da kaya na gani na fada a ko ina a fadin kasan nan a wanan shagon na el,samad
kafin mu fito zuwa Sahad.

Bamu shigo gida ba sai bayan ish,i akan washe gari za a koma a karasa sayan kayan tunda na shige
nayiwa wanka da alwala nayi sallah na kwanta.

Bandamu da neman abinci ba a ranan saboda gajiya dana debo har nake dariyan kaina ashe ko wani jiki
yana son hutu a duniya ?

Dan kwana biyun da nayi ina samun hutu a yanzu dan abu kadan yake wahal dani da gajiya kamar bani
bace nake yawan aiyuka a yan watanin baya ba.
Zaune suke dukansu a falin iya din da mama ta daga masu hankali saidai shi Jafar bai wajen don ya
wuce a ranan ya bar gari zuwa kano zaibi jirgi da zai kaishi lagos .

Sai habu da ya tsaya shima yace da safe zaibar gari zai tafi maiduguri mama ta nisa tana fadin na dai
gane kuna son mayar dani mutumiyar banza habu ?

Na fada maku hakan ba zai yuyu ba dole Jafaru yasan yadda ya walwale auren nan dayaje aka daura
masa da yarinyar nan.

Ko kuma har naka auren shima ya samu matsala akan wanan zancen da kukeson jawo min a yanzu ?

Saida ya dan gyara zama ya shafo kansa ya sauke wani shu,umin murmushi a fuskanshi kafin habun ya
kallo iya yana fadin a dai tsaya gana J shida yasawa kansa son yarinyar nan da karfi da yaji.

Don dai Rahama Allah ya gani bata bada son ranta ko ra,ayin yar uwarta aka daura auren nan da Jafar
ba tunda baiyi soyayya da ita ko ya nemeta wajen wani ba.

Allah ne kadai ya nufa akwai hakan a tsakaninsu shawaran na zuwa mashi muka yanke shawaran
daukan kawu muje wajen yan uwansu ko hakan yana yuyuwa sai gashi munyi sa,a muna zuwa har auren
aka dauro lokaci guda saboda nisan waje.

Asalin zancema wallahi duk kansu har yanzu basu sanda zancen auren nan ba don banji ita maria tayi
min magana a kan zance ba kunga ke nan bata sanda labadin auren ba itama ?

Ikon Allah abin farin ciki ashe yana zama na tsiya Dubu ?

Na dauka wanan zance ke zakifi kowa farin ciki da alfaharin faruwan hakan a cikin mu ai don kece kika
san halinda danki yake ciki na bukatan abokiyar zama tagari da zata bashi kulawa da kwanciyar hankali?

Amma kaiyya dai abin takaici sai gashi kece tafarko da kike nuna halin uwayen zamani akan danki don
kawai ya zabawa kansa farin cikin rayuwansa .

Iya ba wai naki zancen nan bane sai duban irin yadda za a fassara wanan zancen a waje yar uwarta fa
tana gidan nan tana aure iya yanzu kuma ace shi jafar ya auri kanwarta ?

Zargin matansa saiya tabbata tunda dama sunce yana kula yarinyar har a gabansu bai son ranta kona
yar uwata ya baci inaga yanzu ace ya aurota ?

Dubu ban soki da wanan rayuwan ba a cikin yayanki kada ki manta ke dai ba ayi maki irin haka ba
dagani har mahaifinku bamu takurawa rayuwan ku ba a baya.

Yanzu ki duba bayanin yaron nan Habu yaran nan basu san da zancen nan ba daga tambaya akai masu
halarci aka dauro auren nan ko wanan abin bai isa ki gane Allah dayane ba dubu ?

Iya ina son ki tuna Jafaru hakkin yan uwansane a hannunshi yake juyawa suma yaran nan suna da
bukata akan dukiyan su .
Nina tauyesu na bashi dukiyan nan ya juya yau iya yana ta faman aure aure yaran nan bai aurar da kowa
a cikinsu ba banda shi habu su sauran basu bukatan dukiyansune iya ?

Kina kallo ko abu zaiyiwa yaran nan daidai dana matansa zai basu hakan fa ina kyaleshine kawai iya
amma a gaskiya raina yana sosuwa da hakan wani lokaci.

Au tanan kuma zaki fitowa dan naki kice min tun farko bakin ciki dashi kikeyi ko kuma yar kice ta zugaki
akan hakan yanzu ?

Wanan ma mai saukine ai mama in dai dukiyansu suke so nasan ko yau din nan aka bukata Jafar zaiba
kowa kasonshi in sha Allahu iya ta amsawa habu da kwarai kuwa dan nan.

Iya rabu da wanan tunda an kashe masa baki a yanzu komai zai fadi game da dan uwan nasa don
bakinsu daya akan zancen.

Amma gaskiya mama duk wanda ya canza maki ra,ayi akan yaya jafar zai iya cutan mu da dukiyan mu
yayi maki mumunan hudu ba arayuwa.

Ni sam ban taba wanan zargin akanshi ba mutumin da yake tsaye a kan mu da komai namu gidan nan
shine za ace yana facaka da dukiya yanzu ?

Rufe min baki salima tun ranki bai baciba wajen nan idan an tashi zance ki hana mutum yai magana don
wani ra,ayi naki na daban.

Gaskiya take fada maki mama don kuskuren da kike nema ki tabka a yanzu babbane da nan gaba zai
dame mu bake bama don duk ranan da Jafar yaji zancen nan ba za asha da dadi ba.

Kai dukiyan nan dai ina nina danka masa da hannuna ko nayi shawara dakai da zan bashi don haka ka
kyaleni ba zan yarda Allah ya tambayeni kan hakan ba.

To shike nan mama a samu lokaci a zauna dashi kan hakan amma ina bukatan ku cireni cikin zancen
nan don Allah .

Daga hakan ya mike ya fita daga dakin cike da bacin rai part dinsa ya koma cike da tunanen yadda zai
tafi yabar yanda a cikin wanan cakwakiyar hakan yasa ya daga tafiyansa a ranan.

Zama yayi da matanshi ya fara fada mata abinda ke faruwa tiryan tiryan inda ta kasa fahintar abin don
a zatonta yana nufin yaya J yana son ya nemi Rahama da aure yake nufi.

Inda ta fara fadin haba dai yaya habu ina hakan zai yuyu don Allah kabar zancen nan kafin ya kai ga
zancen har an daura aure don haka Rahama a yanzu tana matsayin zaman matar J ce a gidan nan.

Cikin tashin hankali ta fashe da wani irin kuka tana fadin amma bakuyi muna adalci ba yaya habu haba
dai Rahama fa ?

Rahama za,ace ta auri yaya Jafar don Allah ku daina wanan zancen saboda Allah don ba abu bane da
zai yuyu garesu shima ya sani.
Duk yadda yaso ta fahinci zancen ta kasa sai kukan tashin hankali da takeyi tana neman layin Rahaman
data kasa samun layin.

A lokacin wayan na wajen anty na barshi don haka bansan duk wainar da ake toyawa ba a kaina
lokacin.

Bai san ya akayi ba ya daifi zargin Saarece ta fada har matan J sukaji sai ashar yaji yana tashi muryan
Saiba na zunduma zagi daga wajen part din tana kiran su da munafukai.

Abinda yake gudu ke nan har ya hanashi tafiya a ranan dama yasan sai hakan ya faru a gidan idan labari
yaje garesu duk da mama ta bar gidan a ranan da yarta saare .

Sai iyace tayi karfin halin fitowa tana tambayan meke faruwane haka suke daga murya ?

Kaji tsohuwar nan zakice baki san makircin da aka kulla bane gidan nan don kawai aga an tozarta mu ?

To ai gamu gani idan gidan nan na shiguwa ga Rahama tazo gamu wanan kuma yanzu meye idan ance
zarginsu mukeyi a baya ?.

Jin yadda take fadawa Iya magana yasa ya bude kofa ya fito ya tsaya yana fadin iya ki koma daga ciki ki
zauna.

Suje suyi abinda zasu iya anyi aure da Rahama in ma baki sani bane ki sani an daura aure a shekaran
jiyan nan kuma aure ya tabbata mai zama ta zauna .

Wallahi baka isa ba idan ma nufinka kenan dama ka aurawa kanwar matarkashi kayi kuskure yin hakan
habu gara tun wuri ku rufawa kanku asiri kawai zaifi sauki.

Koki rufawa kanki asiriba a yanzu mijin dake da cuta kike gudun ya kamaki Nusaiba don yanzu ya samu
wace bata gudunsa kome ke gareshi har zaki tsaya kina kumfar baki akansa yanzu.

Sai hakkuri don aikin gama ya gama faruwa saidai ina son ki sani duk kika sake kika zageni

36 / 101