Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
gyaya .
Koda ya fito ya samu ina sauke falaki da nas da kulluhullahu kafa uku uku ina tofawa yana zuwa ya
zauna na mika mashi ya sha .
Saukin abin sam baida gardama shi kam ya karba daga hannuna yana bissimillah ya kafa kai ya fara zuka
nace ka dan rage in shafama ya amsa da kai ba tare da yayi magana ba.
Saida ya shaye ya miko min na karba na fara shafa mai a jikinsa ko ina sai faman ajiyan zuciya da yake
saukewa ana son ya bushe a jikin mutu don haka na barshi nace kada ya rufa sai ya sha iska.
Na leka dakin Biba na samu tayi barci nayi mataa addua na fito a yanzu in shha Allah ban sakaci da
addu,a abakina tunda aka tunatar dani hakan..
Na kashe mata wuuta na fito daga dakin nawa dakin na koma na kimtsa kaina tsab na rufo kofan zuwa
dakonshi na saami ya kwanta shima a bakon gadon na zauna ina karanto addu,oin dake bakina na
neman tsari daga Allah.
Shina fara tofawa kafin ni nabi bayanshi na kwanta a hankali ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya jefi
jefi zakice yayi zuciya akan wani abune ?
Shigowan mijin nata ta gaidashi ya amsa yana tambayan yaranshi ta bashi amsa da sunyi barci abinci ta
mike ta kawo mashi saida ta hada mai komai ta samu waje ta zauna tana fadin.
Dazun su anty Nuratu sunzo daga kadun wai sun dawo da Rahamane yau har ya dauki kofin ruwa zai
kai a baki ya dakata yana kallonta kafin yace.
Dama yau zata dawo ashe ta bashi amsa da ban sani ba nima saida suka biyo nan ni suna min fada wai
ina nuna ban damu da Rahama ba yanzu?
Ni yaya suke son nayi don Allah kowa yana ta ganin laifina akan Rahama yanzu shiyasa wallahi ban so
auren nam nata da yaya ba tun fatko don gudun irin haka.
Kai baka gama daukan naka laluran ba ace sai ka dauki laluran wani ita Rahama ai tunkan ta auri yaya
tasan abinda dake cikin gidansa.
Kuma ta yarda ta zauna dashi shiya tare ta da fadin kanki daya kuwa kalau kike kike fadan wanan
maganan ko so kike ta bijirewa iyayyen ku da suka bada goyon bayan hakan ?
In ma laifine su hardo suvkeda laifin ai da suda basu binckeki ba suka daura mata auren dashi amma ita
Rahama umurni tabi ta zauna dashi.
To ni dai wanan auren a yanzu yasani tsakiya gaskiya nan yan uwanku naganin laifina cewa dani na
hada komai nayi sheri data auri yaya .
Can kuma gida sun koma ganin laifina a yanzu kan naki tsayawa yar uwata in mara mata baya
murmushin da mijin yayi yaci gaba da zuba abincinshi shiya katse mata magana.
Sai binshi da kallo da tayi a cikin tuhuma saboda me yayi murmushi bai tsaya kulata ba ya soma cin
abinsa falon yayi shiru na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin.
Yanzu dai na fahince ki so kike ta kashe auren ko ?
Ko kuma bakiyi na,am yanzu da dawowan datayi gidansa bane da sauri ta tare da fadin ka rufa min asiri
don Allah ni ba haka nake nufi ba kawai dai gani nayi a yanzu kowa ya dora laifin hakan a kaina.
Ko anyi hakan daidaine Maria ja rasa irin halinki nako in kula har yar uwarki da kika san kece sanadin
zuwanta gidan nan kina nuna halin ko in kula irin naki a kamta.
Dolene Rahama tayi fushi dake ta nuna bacin ranta duk abubuwan nan dake faruwa kin taba tsayawa
kika nuna damuwanki a kai ?
Rahama ce fa ku kenan ku biyu ga mahaifiyar ku sai yam uwanku maza amma zurin ciki ya hanaki fitowa
ki kare yar uwarki don kada a zargeki ?
Nima nazo daga baya nayi tunanen rashin kyautawa yarinyar nan mu ya kamata ace mun tsaya mata
ba sai tabar dakinta zuwa wajen ummah ba.
Nasan Saratu yar banzan yarinyace sosai idan ta saka abu a gaba daki sai taga bayan abin wanan yasa
nayi mata iyaka daku tun farko .
Wanan kuma yanzu ni ba mai zama bane balle insan abindake gudana ke kuma baki kirana ki fada min
to yanzu gashi ta gane hakan ta dauki zafi dake kuma abin ya dawo ya dameki.
Tana da gaskiya idan tayi hakan don mu muka fara nuna mata rashin kullawan mu su kuma aiba fushi
sukayi dake ba tunda har sun biyo nan sun duba lafiyan ku.
To amma baban ,,,,,, dakata haka maria don Allah wanan zance ya isheni ki barni inji da wanda ke
gabana a yanzu don Allah yaci gaba da cin abincin kafin ya daga ya barta tana kuka a wajen.
Nima haka na kwana ina tunane akanta don tun bayan zuwan da sukayi gida bamuyi waya nida ita ba
saboda ta hau fushi dani wai naki girmama mijinta indawo a lokacin.
Kiran sallah asuba na farko na tashi zuwa bandaki na dauro alwala na dawo na fara nafila saidai
saidana dubashi yana barci har lokacin cikin kwanciyan hankali hakan yasa banyi dogon motsi ba kada
yaji ya tashi a lokacin.
Don a lokacin barci ake son ya samu issashe a rayuwansa idan ba hakan ba daya tashi shima tunkan na
tashi din din na shedeshi gaskiya akan addini sosai.
Shi mutum ne da aiyukanshi basu hana mashi tsayawa bautan ubangiji hakan kuma yana raya dare
wajen bautan Allah saidai ba kullum ba.
Muryan ladabin unguwar na kira na biyu naga ya falka ina zaune ina lazumi a inda nayi sallah nasan
idan ma ba yanzun daya dan ji sauki ba bai iya dagawa da kanshi ko alwala a baya saina kawo wani tasa
mai fadi nayi mashi kafin naje gida dana koma gidana kuma maman tudu ce ke taimaka mashi.
Zance hakan kamar shagwabane wanda ba hakana bane saukin daine kawai ke shiga a hankali lokacin
don yanzu yakai yana dan lalabawa yaje da kansa.
Saidai ina ganin hakan na mike zama ya fara yi ina gaidashi da mashi sannu da jiki ya amsa yana fadin
koya makarane nace ba a tayar da sallah ba ai a lokacin.
Yana kokarin mikewa tsaye ganin yanayinsa yasa na tuna da zancen likitoci da suke fadin idan mutum
ya tashi da dare koda safe daga barci ba a son ya mike farat daya sai ya dan zauna jininsa ya sauka don
gujewa faruwan sturk a gareshi balle wanan dake halin ciwo a yanzu.
Daka zauna tukun na bashi amsa yake fadin wallahi naso tashi kuma na kasa kinga yanzu abin dake
damuna shine duk ilahirin jikina sai na dinga jin yana min majirya wani lokacin.
Wani lokaci kuma sam banjin hakan a tare dani amma hakan yafi faruwa gareni da safe haka ko da
yamma idan na dade a inda nake fitowa insha iska.
Kinsan yanzu sun daina tayar min da injin don kawai Asmau tayi magana ranan kan an jima ba a tayar
da injin din ba wanan yan iskan yaran suka fadawa mama shine tace samun wajene ai ?
Ko gidan ubanta ana tayar da injine haka balle ta kawowa mutane iskanci to injin din ma an daina tayar
dashi idan akwai wutan nepa aga haske din.
Idan babu kuma kowa ya zauna hakana kinga ni basu damu dani ba koda mutuwa zanyi ke nan Rahama
kansu kawai suka sani sai naga yayi murmushi yana hada hannayesa a waje daya.
Kafin ya dago kai yace amma kinsan me kuma duk sati sai ansaka kudin mai a cikin buget din da za a
fitar nidai kawai kallonsu nakeyi fatana a yanzu shine.
Idan ina da rabon tashi a ciwon nan Allah yaban lafiya mai amfani gareni da iyalina idan kuma hanyar
tafiyanane hakan Allah ubangiji yasa na cika da imani Rahama.
Tausayi sosai ya ban a zuciyana wanda nagane maza da yawa ashe in sun kwanta ciwo suna ganin
takaicin duniya a kan iyalinsu ban ji tsoro ba saida naji yana fadin kinsan me kuma ?
Nace a,a yace duk basu zata Allah zai ban lafiya da zan mike kamar haka bama a yanzu ba karamin illa
sukaiwa dukiyana ba Rahama zancen dai kawai ayi shiru tun Habu yana hanawa yazo ya fada min har
yakai yanzu shima ya soma nasa hada hada a ciki saidai nayi kamar ban fahinci hakan ba garesu.
Yau dan uwakane yayi ma hakan da mahaifiyarka to don wani yayima me zakace mamafa wai har cewa
tayi a ware wasu kudi don auren yaran nan kada nazo na mutu kudin su shiga cikin magadana ?
Ki duba wanan zancen don Allah Rahama wai mahaifiyace takewa danta hakan me zan fada a yanzu
suyi min hakam waye ba zai min ba nasan wanan shirin kawune sarai shike turata duk wanan
abubuwan .
Bansam lokacin da bakina ya furta to wai ku baku iya maganin kawu din nan ne mutum yana cutan ku
kun sani amma kuna taushewa don Allah ?
Bai ban amsa ba sai murmushin da yayi yana fadin kamani inje inyi alwala kada mu makara ga sallah
lokaci naja hakan yasa na kamashi ya mike tsaye zuwa bandaki.
Bamu fito ba saida yayi komai ya fito na gyara mashi inda zai zauna yayi sallah na koma na dauro
alwala na fito nazo na don har an tayar da sallah a lokacin.
Na idan na dan zauna nayi addua kafin na mike zuwa kitchen tea mai kauri na hado mashi nazo dashi
dakin yana zaune a wajen har lokacin.
Na mika mashi bayan na fifita ya karba ya shanye yana min godiya ruwan dana tofe da addua na mika
mai ya dora a sama bayan yasha na shafe mai jiki dasu tsaba na kamashi zuwa gado ya kwanta.
Na gyara mai kwanciya yadda zaiji dadin samun barci zan mike yake fadin ki kwanta mana ki huta nace
ina zuwa kawai na fice daga dakin zuwa dakin biba na tayar da ita don tayi sallah.
Duk aikin da nakeyi zancen mu dashine na dazun ya tsaya min a rai na na fahinci wanan abin sai an
koyawa mutanen nan wayau a rayuwansu.
Wani abin ko baka da niyar yi mutane suke sakaka yinsa don fansan kai matsala guda kishiyoyina haka
take garesu duk inda aka juya mu can suke.
Haka kuma ba zamu taba rabuwa da wanan matsalan bafa matukar talikin nan yana raye sai mun rabu
da mutanen nan kamar yadda yaya habu ya tsame kansa cikinsu a yanzu.
Dan zama da igiyar auren Jafar yasa na fahinci abubuwa da dama game da zaman gidan wanda a baya
ban kai fahintar hakan ba a lokacin don abune dabai shafeni ba lokacin.
Don haka ya zama dole na fito da halin fulatanci na mugunta da nuna wayau wawaye yanzu garesu
don tsirar da mutuncin mu ga baki daya.
Mama ko a gaban mu da yar uwata idan abinta ya tashi zatace ita makircin fulani ai duk ta sanshi ita da
tayi zama da inna amarya ana gwada mata fulatanci ?
A yanzu zata fahinci fulantanci ba komai bane sai zalla wayau da kissa da iya duniyanci akauyance
muke shammatan mutum.
Abinci lafiyayye na shirya mashi wanda nasan zai kara gina masa jiki ya samu lafiya don ramansa tayi
yawa a yanzu ba son nakai zuciya nesa ba saima na zargi zama a kusa dashi din.
Kamar yadda saudi ta ban shawara na zage in kula dashi idan yana wajena ta yadda ba zai iya boye
komawansa wancan gida ba a fili ta hanyar bashi kula ta musanman.
Don ita saudi irin mantan nan ne da suka kare rayuwan kurciya a bariki har lokaci ya kare masu basu
sani ba sai a koma yan kame kame saboda girma.
Wanan ya kaita ga aiki gidansu ummah ita din ance wata yar uwar su daddyne ta haifeta gashi tana
bala,in jin tsoron daddy wanan yasa a yanzu ma don ta natsu ya zaunar da ita a gidansa yana kuma yi
mata albashi.
Alhamdullahi din ta natsu kamar yadda yan uwa suke mata fatan hakan wanan yasa bata da shamaki a
gidan din nasu yazo daya da ummah sosai saboda bata takura mata ko kadan.
Itace kuma a irin hiran mu ta kara min haske akan zama da irin su mama da iyalanta wanda wanan
huduban hakan yai min tasiri sosai a cikin zuciyana a lokacin.
Na lekashi a dakin na samu ya samu barcinsa sosai har baisan inda yake ba a raina nace har yunwa a
cikin lamarinsa na fito falo na tsaya muka gyara da biba don gudun girshi a gareni azo a samu gida ba
shiri wanan kesa macen kwarai ke gyara gida tunda safe kazama kuma malakaciya itace ke zama har
wani lokaci gida ba gyara ko jikinta nakoma dakina nayi wanka.
Bayan na fito na zauna na shafe jikina da mai sosai na zauna nayi kwaliya kafin na fito daga gidan har
jikin mu duk ya dauki kamshi yadda nake so .
Ina cikin irin mutanen dake son kamshi a rayuwansu don hakane ban wasa da kamshi a lamarina ko
don tashi a wajen mummy Abujace na kasance a hakan oho ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/22, 9:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A gaskiya zamuce ba laifi don amarya ba zata gwadawa anty barakha komai ba na rayuwa saidaima anty
barakha din ta gwada mata don ta fita komai na zamanin nan.
Hakan yasa da farko anty barakha daga kai tana ganin cewa ba wani abinda amaryan zata gane aiga
mijin nasu don haka ta shiga aika yan dabarrun data iya na kisa don kawai ta sace zuciyar miji a
bangarenta.
Saidai kash ta manta da haljn da namiji a lokacin dayayi aure idonsa gaba daya makancewa yakeyi wani
lokacin ya koma akan amaryan ke uwargida duk gwanintaki ba a ganar maki hakan.
Bature yana fadin don,t mind the body mind the engyne matukar gidan aikin na kalau ba a damu da
kyau jiki ba.
Don kuwa maigida illiya kan amaryansa datayo masa tsaraban kayan hadin matanmu na hausa na
gargajiya sune suka haukatashi har yakai yana fitar da sabon rayuwa da ba a sanshi dasu ba a gidan.
Mutumin da aka sani yana fita sallah asuba yanzu duk ranan girkin amarya babu mai ganinsa wajen
jam,i sai rana ya fito kiri kiri zasu fito yin wanka da ita dashi a cikin bayi daya duk kuwa da yan matan da
yake dasu sakwa sakwa baya kunyar hakan.
Haka kuma zasu fito zuwa daki don shakiyanci wani lokacin amaryance ke goyashi a baya tana fadin shi
babyntane wai a cikin shakiyanci suna wasa da dariya a tsakaninsu.
Dare kuwa karfe takwas da rabi sun kargame kofan daki sai kuma safiya idan sun fito ga yaran
makwabta kawayen yayansu dake shigowa gidan kallon tv.
Amma bawan Allah nan ba kunya haka zasu shige daki su rufe da magariban fari ido na ganin ido ba
tare da yaji nautin diyansa ba ko matarshi.
Ire iren wanan halin yasa ko yaushe waya yana manne a kunnen anty din tana kai karan mijin a gurin
mahaifiyarta ko kanninta.
Gashi duk wani kissa da akace tayi tana kokarin yi amma ga banza randama ya dawo dakinta zai tsiri
fushin banza da ita da yaranta dan abu kadan ya hausu da fada da cin mutunci.
A ranan kuma sai dare bayan sha biyu zai shigo gida ya kwanta da safe kuma inya fita sallah asuba ba
zai shigo gida ba sai wajajen tara da rabi na safe ko goma daya shigo ya karya zai fice idan ya fita kuma
sai karfe hudun yamma zai dawo gidan.
Allah sarki macen bahaushe don mata da yawa suna fuskanta wanan sauyin a wajen mazajensu yayin
da akace miji ya kara masu abokiyar zama .
Wanan yasa matan mu na hausawa a yanzu saboda halin maza basu kaunar ace miji zaiyi aure sai su
dauka abinda ya samu waccan shine zai samesu suma ?
Tun tana magana har yanzu ta jinginashi ga Allah ita da yaranta ga wani sabin doka dayasawa yaranshi
zuwa kasan layinsu don su dibowa amaryansu ruwan bohol wai bata shan ruwan rijiya tace.
Haka zasu fita da safe suje bun layin ruwan bohol din da take so din shiko suna daki kargame da ita sai
lokacin da sukaga dama su bude su fito.
Zuwanta duban jikin jafar data dan jima acan zaria din ta danyi dabarun ta irin na mata ta dawo dashi
amma halin bai canza ba saima wasu sabbin sallon data dawo ta sama a gidan lokacin.
Wanan yasa ta rame ta lalace ta fita hayacinta don yanzu ta gaji da kiran gida tana fada masu halinda
take ciki saida a yanzu ta daina wahalan kashe kudin da takeyi na gyara girkinta a ranan da yake wajenta
haka iya abinda ya bayar kawai take girkawa kowa yaci.
Wanan kuma ya kara haddasa fitina a tsakaninta da maugidan ya sako wani bakin kiyayya da yake mata
a gaban kowa saidai abokiyar wayarta saratu tace ta daure ta fita batun dan iska kada ta bashi komai
nata har yaran ta barsu ai diyanshine.
Yanzu kan fitina sosai sukeyi da mijin akan hakan har yakai ana bugaiya tsakaninshi da anty barakha
din zai dirke ta a gaban kowa a taru a gidan suna tonon asiri.
Tun mama na boyon wanan abin har yakai ga ta fara sakin magana tana jawa surikin nata Allah ya isa a
baina.
Na samu ya falka dana shigo yana kwance ya zuba min ido har na karaso gaban gadon Allah kadai
yasan tunanen da yakeyi a lokacin.
Gaidashi na sakeyi da kwana ina fadin da zaka lalaba ka tashi kai wanka sai kaci abinci zaifi ya dubeni
yana murmushi kawai yace bayan karyawan da nayi dazun din ?
Awa uku da dan kaifa yanzu naso ka yi wanka sai kasha wancan maganin dakazp dashi jiya haka dai na
samu yaje yayi wanka ya fito na