Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
zakiji itama godiya tayi mai suka rabu ta nufi
tsadadden motanta dake fake a gefe fara sol mai shegen tsada da sai wa yanda suka kafu suke shiga
irinsa.
Juyawa yayi zuwa cikin gidanjen nasu da ake kira da one milleum quaters anan ne kuma suka hadu da
Meabe din wace ta taba fada mai zamanta a nan na dan lokacine ta kusa kammala ginanta da zata koma
cikinsa very son.
Dutse biyu a lokaci daya zancen wanan kafiran zai tsaya nazari ko zancen da Saiba ta kirashi dashi zai
tsaya duba fadawa yayi kan kujera tare da tallabo kanshi yana lumshe ido.
Dolene yaje gida ba zai kira kowa ba don ba zai fahinci gaskiyan meya faru ba gara yaje da kansa ya
ganowa idonsa haka kuma duk wace ya kama da laifi akan mahaifiyarsa zaiyi mumunan sabawa maishi
don ya fada masu wanan duk sun sani kuma.
Ba mama Dubu ba har iya da kawu dauda suna da kwakwaran kashedi ga duk iyayyen nasa daya kafa
masu don bai yuyu a garesa su wullakanta mashi iyayyensa shi bai wullakanta nasu ba.
Haka yake murzan goshinsa da hannuwanshi yana jin wani iri kasan zuciyarshi zancensu da Meambe na
dawo mai akai sam ba zai taba yarda ya jefa kansa cikin halaka ba.
Mafi yawan masu kudinnan na kabilu kudinsu kudin tsafine don haka shikan ba zaiso abinda zai tabfba
martaban gidansu ba.
Gara ya dogara da dan juya kudinsu da yakeyi tunda ko wanan akwai daukaka a cikinsa yana tsoro
matuka da wanan shawaran da Meambe ta kawomashi.
Da haka washegari ya dauki hanyar gida tunda safe yabar lagos din don baijin zai iya daukan lokaci baije
gida yasan abindake faruwa ba.
Karon farko ke nan daya tsani halaiyar matan nasa da irin fitinansu da suka kasa kwantar da hankalisu
su zauna lafiya a tsakaninsu.
Tsuki yaja yana mai ganin laifinsu duk kansu amma na Asmau yafi don me zata canza halinta daya santa
dashi akanshi.
Yasan Nusaiba zata iya jan fitinan da sai Asmau din takai ga tankawa amma meye a ciki idan ta shareta
tayi haukanta tagama yarasa Saiba wace irin yarinyace mara jin magana haka wai ?
Hanya ya tsaya ya sai doya manja jan garin kwaki domin iya dake sonshi sosai saura a can gida yake
saya idan yaje wanan ne kawai yake saya a hanya don yafi sauki da kyau a nan yake tsayawa ya saya.
Baiga Zaria ba duk uban sammakon daya buga sai wajajen karfe tara na dare ya shigo garin zaria kai
tsaye gida ya dosa don dare yayi baijin kuma mama tana tudun wanda a lokacin yafi kyautata zaton dai
tana gidansu yanzu haka .
Haka shima Abubakar sunyi waya da mama take shadai mashi cewa tana unguwarsu wajen iya don
haka shima kai tsaye a can motarshi ya saukeshi da kayanshi ga baki daya daya sayo Sahabi yana ta
mashi sheri akan kayan bai kulashi ba.
Saibace ya sama wajen part dinsu tana waya kala batace dashi ba shima kuma bai kula da ita ba haka
yayi ta jidan kayashi yana kaiwa kofan iya da sukr ciki part din da yarta mama basu sanda isowarshi ba
har yagama jido kayan daga waje cikin wahala ya shigo dasu lokacin ya koma ya kwankwasa kofan iya
din .
Mama Dubu ce ta bude kofan tana ganin danta ta dan murmusa tana fadin ikon Allah kun karaso ke
nan sannuku da hanya.
Daga ciki iya ke tambayan waye tace habu be Allah ya dawo dashi lafiya tasowa iya tayi tana fadin da
daren nan kuke tafe haka Bukar sannunku da hanya .
Karasa fitowa mama dubu tayi tana fadin a,a kaya haka ka zo dasu haka Habu kuma duk bamuji
shigowanka ba sannu da zuwa ta duka ta fara tayashi kwasan kayan zuwa cikin falonsu iya din.
Saida aka gama kwasan kayan kaf mama ta nufi wajen dan karamin fridge tana daukowa dan nata
ruwan leda karba yayi yana fadin bari naje nayi wanka mama indawo.
Ya fada tare da juyawa bai tsaya sauraren iya dake fadin ka zauna kaci abinci kafin kaje wanka mutum
sai kace agwagwa da son wanka dai juyowa yayi ya dubeta ba tare daya tsaya magana ba ya fice.
Yana jin yadda Saiba ta kure kida a gefen part dinta zakice wani sha,anin buki ake a wajanta alkawari
yayiwa kansa zai kawar da ido daga duk wani abinda matan yayan nasa zasuyi a gidan.
Don haka bai tsaya kulata ba ya bude part dinsu dashi da kaninsu dake boarding school anan suke da
dakunoninsu don sunbar can cikin gidan nasu yanzu tun bayan da yayan nasu yai aure.
Yafito dogon rigan jallabiyansa ya zura a jikinsa ya shimfida sallayan sa ya tada sallah saida ya idarne
ya kula da gyaran dakin da akayi wanda yasan ba aikin kowa bane sai mama Allah sarki mama ya fada
yana lumshe ido.
Can yaji sautin buga kofa hakan yasa ya saurara da kyau ba karya kunnuwansa ke masa ba don ko nan
din ake duka hakan yasa ya mike yana duban wayansa dake hannunsa.
Karfe goma saura na dare a lokacin don haka ya nufi get din kai tsaye daga ciki yake tambayan waye .
Aka bashi amsa da Jafar bude min get hakan yasa ya leka yana mamakin yadda akayi yayan nasa yayi
tafiyan dare haka tun daga lagos.
Saida ya tabbatar daya shiga da motan ya mayar da kofan ya rufo ya saka kwado dan basu da maigadi a
lokacin karasawa yayi wajen motan yayan nasa yana mashi sannu da zuwa.
Motar ya bude ya fito yana amsawa kafin ya daga kai ya kalli part din nasa da kida ke faman tashi yana
fadin wanan kuma me suka samu haka yau ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kai Abubakar ya kawar gefe daya alaman baima saureshi ba alokacin nufar part din yayi ya fara dukan
kofan cikin hasala nocking ukku yayi masu kyau cikin hasala hakan yasa Asmau ta daure ta fito tana fadin
ana zuwa kafin ta tsaya tana tambayan waye ?
Ke bude min kofa nine jin muryanshi yasa ta bude kofan da sauri gami dayi masa sannu da zuwa dan
kallon second ya jefa mata ya gane daga barci ta shi a lokacin ke nan har sun shiga barci.
Ciki ya shiga yana fadin wanan kidan haka fa kamar gidan yan kwaya batayi magana ba don haushin da
taji da dan cikinta an hanata shakat yazo kuma zai tsareta da tambaya ?
Wurin fridge ta nufa ta dauko mai goran ruwa ta nufoshi dashi bai tsaya karba ba kai tsaye dakin
Nusaiba ya nufa ya tsaya daga kofa yana daga labule.
Kwance ya hangota tayi rub da ciki tana barci sai kanta gwigwiyye da hula ya zame suman kai yayi wani
tsatsaye tsirma,tsirma dashi yaja tsuki cikin takaici.
Takawa yayi zuwa wajen da kidan ke tashi yakai hannu ya kashe kidan duk da hakan bata motsa ba
hakan yasa ya kai mata mugun maka a tsakiyan bayanta ta tashi firgice tana fadin wani dan ,,,,,,,,
Ganinsa yasa ta soma kame kame tana fadin umm,umm sweet J dama kana hanya ashe shine baka
sanar muna ba ?
Fuska a murtuke yake fadin wanan kidan na meye haka ke wata irin yarinyace Nusaiba baki ganin kina
daukan alhakin sauran jama,an gida ?
Ke shadaniyar inace wai kina yar musulmai da daren nan zaki kwanta min da kida haka a cikin gida
kamar gidan disco don rashin tauhidi a zuciyarki ?
Aiko kira,a kika saka ba zaki kure volume dinsa haka ba don gudun shiga hakkin wani saidai ki kunna
iyake.
Daga hakan ya juya ya fita inda ya hango Asmau a tsaye inda ya barta da ruwa tana jiran fitowarsa
daga dakin abokiyar zaman nata.
Karba yayi kafin yayi niyar zama saman kujeran dake tab da kayan wankin Asmau data nado waje
kwanan su sunkai biyar a wajen bata kwashe ba tana kuma kallon kayan a wajen.
Tsuki yayi ya fasa zama yana maijin wani irin zafi a zuciyar shi ya nufi hanyar fita part din saidai yana
fitane yaga alaman part din duk an kashe wuta ke nan masu part din sun kwanta haka ke nufi hakan yasa
ya juya zuwa wajen motarshi daya bari bude bai dauko komai ba sai rufe ko ina da yayi har gidan ya
duba yana da tabbacin Abubakar ya rufe ko ina a lokacin yasa ya koma part dinshi kai tsaye wurin
iyalinshi.
Kallon takaici ya tsaya yana karewa falon dake hargitse zakice ba mata biyune ke rayuwa a part din ba
babu inda baida miskila don da gani falon nan bai samu shara ba na tsawon kwanaki .
Dama sai ya sanar dasu ranan zuwanshi maigirki takan garje tayi dan kwaskwarima gyaran sama sama
don sunsan sam baya son kazanta yanzune da ya iso zai soma fada balle wanan zuwan dayayi masu na
bazata babu sanarwa.
Don haka babu zancen gyara a wajensu koda ya shigo rasa mai zaiyi a falon yayi ita Asmau itace ta
mike zuwa part dinta ta shiga gyara gado tana kawar da kayan data tula a ko ina dakin.
Don ta dara Saiba kazanta gaskiya ita dai saiba tana da garjewa ta gyara jikinta da inda zata kwanta
amma wanki da sauran aikin gida sune aiki a wajenta.
Baicewa Saiba komai data hakkince saman gujera tana jiran taji me zaice dasu ko kuma taga inda zai
shiga ya kwana duk da tasan in zancen gaskiya za abi wurin Asmauce zai shiga ya kwana tunda itace tayi
girki a ranan sukaci.
Dama ance mai mata fiye da daya kullum a cikin lissafi yake don gudun fadawa ga halaka saidai wanda
baida tsoron Allah zai iya dulmuye gaskiya yayi son ransa.
Donshine Jafar kai tsaye don yabi lissafi tun a hanya ya gano dakin da zai sauka kai tsaye ya nufi
bangaren uwargida Asmau wace ya samu tana shimfida zanin gado don shi.
Sam Saiba bata ji dadin hakan ba yana shiga ganin ko dan zama baiyi sunyi yaya hanya ba bai bata
lokaci ko kadan ba sai taji ba dadi sam a ranta ta mike a cikin fushi zuwa dakin ta.
Yana shiga ya tsaya a kofa ya harde kafan shi a waje daya yana bin Asmau din da take aikin gyaran
gadon a gurguje da kallo a cikin mamaki.
Ta jawo room freshener ta fesa ko ina har zuwa bayi kafin ta juyo gareshi tana dan sakin murmushi
tace dashi bissimillah .
Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya motsa a yadda yake ya tako yana balle aninaiyar rigansa cikin daure
fuska tunawa tayi da tabar towels din da yake amfani dashi a wajenta waje hakan yasa da sauri ta nufi
falon da bakowa sai hasken wuta da aka a kunni ta nemo tawul din ta kashe ta dawo daki tsaye ta
sameshi a bakin bayin tawul din ta mika mashi bai karba sai sunan ta daya kira.
Da Asmau ta yaya zanyi amfani da bayin nan don Allah komai a kazance ke wata irice saboda Allah ace
mace ba tsabta ko kadan kedai baki kaunar ki tsaya ki gyara koda muhalinkine saboda Allah ?
Ai bansan zaka dawo ba shiyasa ban gyara ba ta fada a sanyayye kallon takaici yai mata kafin yace au
sai zan dawo ke nan zaki gyara ashe ?
Bata daiyi magana ba don tasan jafar yana da bala,in hakkuri da halayensu don da wanine yadda yake
dan gayun nan dashi daya anji kansu a kullum amma haka yake shanye takaicin su a zuciyarshi.
Abubakar a bangareshi haushi da takaicin yayan nasa ya juya zuwa dakinsa dashi ya rufo duban lokaci
yayi a jikon wayasa shadaya bai rufe ba a lokacin haka kawai yaji yana son kiran layin Yanda ya gwada ya
gani ko zai shiga.
Saidai ya tsaya yana wasi wasin kasan zuciyashi ya kirane ko yabari da safe baijin zai iya hakan yasa ya
danna kiran Allah da ikonsa kuwa yaji layin ya shiga kai tsaye ta soma kira.
Har ya debe rai da daukanta sai gashi ta daga ta dauka da sallama muryanshi taji yana fadin baki barci
ba ke nan ko kuma nina tayar dake daga barcin yanzu.
Sautin murmushinta yaji tana fadin amincin Allah ya tabba bata a gareka kun sauka lafiya ko kuna
hanya ban zata akwai layinka cikin waya ba ai sai yanzu daka kirani.
Ke nan baki duba wayan taki ba ko gaskiya ban duba ba kasan mun wuni aikin gyaran kaya yau da kula
da dabbobin baffa da suka wahala a wajen tatsansu da mukai tayi a yan kwanakin nan.
Au ashe dabban kayi wahala itama sai yaji tayi murmushi tace halan ba rayuwace da ita ba yadda mu
yan adam muke wahala ai itama rai gareta don haka sai mun kula dasu sosai don ba karamin alheri suka
kawo muna ba a rayuwa.
Sanadin kayan da kuka saye muna na samu baffan mu yau har girki yasa mukayi akaci aka koshi a
gidan ko sallah albarka a yau din nan.
Yadda take maganan yasa bai katseta ba don yana fahintar wasu abu daga cikin zancen datake ta
zubawa din a lokacin duk shi bamai yawan son surutu bane amma sai ya biye mata.
Ya fahinci rayuwan yaran a can yana cikin wahala a hannun yan uwan mahaifinsu da zaman su ya koma
hannunsu.
Suna a cikin matsi da tsangwama babu freedon sam a tare dasu kamar sauran yara karatunsu da sukayi
ya tashi a banza yanzu wace takai matakin karatun Nurse a yanzu ta koma tana tatsan nono a rugga
saboda rashin gata.
Da wanan tunanen ya kwana a ransa har gari ya waye duk da ya dan samu runtsawa kadan saboda
gajiyan dake jikinshi a lokacin na bin dogon hanyan da sukayi tafiyan zuwa da dawowa haka.
Don shine bai fito ba da safe da wuri saboda bayan sun dawo daga sallah ya koma ya kwanta barci sai
zuwa shadaya saura ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da brush din bakinsa ya fito.
Washe gari mama Dubu tana kitchen tana hada masu breakfast sai jin sallaman Jafar din tayi a kofan
kitchen din amsawa tayi tana mashi kallon mamaki da yaushe ya dawo.
Ya fahinci kallon da uwar ke masa yasa yace na dawo tun jiya da dare ai mama kun kwanta a lokacin
Abubakar na samu ya bude min gida na shigo.
Malam meyasa baku tsoron tafiyan darene wai don haka take kiransa da malam Jafar kamar yadda
uwaye da dama sanadin marigayi malam jafar suna kyautata zaton diyansu su samu irin albarkansa suke
kiran yayansu da malam jafar.
Ai ba da dare sosai na shigo ba mama wajajen shigowa kaduna dare yayi min na shigo nan wurin sha
daya saura na darene ai.
Allah ya kyauta nan ya fara gaida ita cikin ladabi kafin muryan iya ya ratso tana fadin wai Jafar ne da
safen nan haka ?
A nan ya kwana Iya mama ta fada ahawaraki shine baka tayar dani na karbi jakkar tsaraban taka ba ka
mikawa marasa hankalin matanka ?
Iya ko allura ban shiga dashi ba gida sai makullin motata kawai ko yanzu kina iya karban jakkar kafinsu
ya fada yana nufar iya din itama juyawa tayi zuwa wajen kujerun falon ta zauna shima haka ya zauna
yana fadin.
Habu bai shigo bane ko har ya fitane zuwa wajen aiki mama ta karaso tana fadin anya yau zai shiga
kaduna kuwa yadda suka kwaso gajiyan nan suma.
Gama tsaraban da yayo muna nan ko kwancewa ban samuyi ba har yanzu Iyace tace badai abinda zai
lalace a ciki ko ?
To ina na sani iya ai kinga baiko tsaya muna bayani ba yafita da sunan zaije ya dawo har yanzu bai shigo
ba kuma karna taba ya kasance ba nasa bane duka naga abinda yawa hakane ?
Ba zai shigo dasu nan ba ai idan ba nasa bane kinsan halin Habu ai mama Jafar ya fada shi nake nema
ya kamin mu fito da kayan danazo dasu ashe ba tashi ba har yanzu.
Kuna da kokarin yaran nan saidai kai Jafar matsalan matan da Allah ya bakane sai addu,a mata ba sanin
ciwon kai ace har yakai don rashin hankalin kishi irin nasu yar nan ta watsawa uwarku abinci a jikinta
abinci mai yawa don wullankaci su wullakantashi haka wuein bakin kishin su na tsiya ?
Abinci kuma suka watsamawa Iya kardai zancen da Nusaiba ta kirani ke nan shekaran jiya take son min
ban saurara ba don dama shiya kawoni garin nan jiya tunda naji ta ambaci sunan mama a cikin zancen ta
hankalina bai kwanta ba na taso.
Kaiko dai akan wanan zaka taso haka zuwa nan iya shegen yaran nan ne kawai don batama san da ina
tafe ba ai kodata jefowa yar uwa abincin sai saman jikina ya dira ya zube banso iya ki fada mashi ba ai
tunda anyi ya wuce ko tun a wanan ranan indai zasu gyara su gyara don ba,a wasa da abinci.
Mama indan iya bata fada min ba waye zai fada min bayan don haka take zaune damu gidan idan suna
abu ba a tsawata masu watarana ai za a samu sun illanta kawunansu a dawo ana ganin laifin ku daga
baya.
Zasu aika tundai wanan mai zubin yan ruwa da take daukan kanta wata tsiya banda karyan banza da ci
mutunci babu abindata koya a duniya na kwarai Iya ke fadan wanan magana a cikin hasala.
Sallaman Abubakar falon yasa suka sake zancen ya shigo suka shiga gaisawa da juna kafin ya sanu wuri
ya zauna mama dubu ta jefo mai tambaya tana fadin kayan can dakazo dasu fa Habu ?
Juyawa tayi ya kalli wajen da mama din ke kallo kafin ya dan bata fuska yace daga can nazo dasu meye
a ciki Jafar ya tambaya ?
Mikewa mama tayi ta isa wajen jarkan da akaiwa