Chapter 19 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   19 / 101

54K to 57K   out of 302.2K words

da Abuja wurin wa nace anty Salma kinsan
mutumiyatace sosai yanzun nan da safe ya Habu ke fada min ta bugo waya tana son inzo inyi sallah
wajenta.
Shiru tayi na dan lokaci kafin ta tashi ta mike ta fita daga dakin nagama shirina na fito falon na samesu
suna zaune zama nayi gefe daya ba tare da magana da kowansu ba.

Sai iyace ke fadin yar fullo ina za a hakane naga kinyi kwaliya kamar bakya jin azumin nan ke ?

Murmushi nayi ina fadin asibiti naso inje iya inyi ,,,,,,, ina jiya kinje Rahama ku koyayyi zuwa asibitin
nan fa kuna kanana daku mama ta fada.

Naso naje kan tafiyan da yaya yace zanyi gobene kada in wuce banyi sallama dasu ba daidai lokacin ya J
ya shigo yana fadin mama kinko ga gidan nan yadda yayi kaca kaca don Allah ?

Inda nake mama ta kallo nayi kamar ina kallon tv da wani malami ke wa,azi akan zakkan fidda kai da
za,ayi idan ansha ruwa.

Sai naji tana fadin ato ita daice me sharan gidan ai tunda tazo gidan nan take wanan aikin bayan ita ba
maiyi a cikinsu tana nuna yaranta mata.

Suma matanka ba zasu iya komai bane wai Jafaru saidai suci su sha su kwanta su a dole ga bazan ta
samu garesu yau da gobefa sai Allah jiki da jini kuma ?

Yarinyar nan ta gajine fisasbillah kunga abin nan da yar nan keyi ba a banza zai tafi ba hakan duk gidan
da tayi aure nakab fada ince sun huta wallahi.

Mijin da zai aureta ya dace mace ba son jiki ba keta ba algus gako wani aiki ta saka kanta yi zata tsaya
tayisa tsakani da Allah yarinya ce karama data san ciwon kanta.

Haka zakuyi kuma a gidajen ku muddin baku gyara kada ku dauki hakan kamar wayewane kanku kuke
cutarwa wallahi.

Iya ta karasa fada a cikin takaici tana maida fuskanta wajen tv dake aiki balle dan mutum rana garesa
ai, .

Yau yarinyar nan bata kimu ba ta yaya zaku nuna baku kaunata kiri kiri haka ba kunya dan zanin da duk
dadewansa yan shekaru a jikinta kuce ta kasa ramawa ?

Itama fa rayuwane a jikinta kamar kowa yadda kuka rufe ido aka tozarta ta a gidan kowaye dole yaji ba
dadin hakan don sai ince duk da sanin ku aikai hakan idan na debe shi namiji a cikin ku da bai bibiyan me
ake ciki.

Wallahi iya bansan da wanan shirin ba Rahama ai diyatace a yanzu bata da banbanci dasu Salima a
wajena don itama a karkashina take rayuwa.

Munafunci daine irin ta yaran nan da suka shirya komai da sanin saare aka hadashi a gidan nan
makircin nan kuma yana gindinta.

Kuka Saare din ta fara tana fadin mama ni ya zanyi tunda sunce ba zasu bayar ba kamar Ramaah zata
saka kaya irin wanan tare dasu ?
Dama Saiba har ta raba kayan a tsakaninsu ai lace din nan ne suke rigima a kansa jifa wai rigima don
Allah akan abinda baku da hakki kansa mama ta fada.

Ban raba daya biyu don ko rantsuwa nayi ban kaffara akan wanan zancen yarinyar nan zata tafi Abuja
gobe aiba yau take gidan nan ba bataje Abuja ba saida haka ya faru.

Wayan da yakeyi ya dakatar yana fadin Abuja kuma me zata tafiyi Abuja gab da sallah haka kuma ?

Wai mutanen Abuja din sukace dashi ya bari tazo nan tayi sallah a wajensu niko nasan don wanan
zancen suka fadi haka.

Shi Habu kuma ya yarda da tafi din ya yarda mana tunda har yazo da safen nan yana fada mata ta
shirya gobe akwai wanda zata bi su tafi.

Ai nima goben insha Allahu zan shiga Abuja amma bai fada min ba yanzu muka gama magana dashi na
shigo nan .

Ku barta taje don Allah kada kuce zaku hana yarinyar nan tafiyanta iya ta juyo tana fadan hakan garesu
mama dubu tace ai ba zance kartaje ba iya.

Sam baiji dadin yadda abin ya kasance ba haka ya fita gidan da bacin rai wani kauye da ake kira da
kinkinau suka nufa shida kawu .

Wasu filaye ya saya a wajen sai daga baya kuma mai filin yake son ya tayar da ciniki don wani yazo ya
kara masa kudi.

Kudin da yaya ya ban ba wani sayayya nayi ba na dai sayi kayan kwaliya saura kuma na dunkule abina a
jikina don banga wani tsaraba da zan kaiwa anty Salma ba daga bangarena.

Sai traveling bag dana saya mai kyau don shi nake kwadayi dama na dawo gida na shirya kayana tsab
ina jiran washe gari tafiya idan Allah ya kai mu.

Ina barci naji Saare na kirana da dan karfi da in tashi yaya yace in fito mu tafi gabana ya fadi ina duban
lokaci shida da wasu yan mintuna na safe.

Da sauri na mike tsaye na shiga shiri Allah ya taimaka nayi wanka da asuba hakan dabi,atace watsa
ruwa kafin na fara aiki don in samu kuzarin aiki da kyau.

Simple dress nayi dogon riga sai hijab a jikina saboda sanyin safiya na fito da yar jakkata da zanyi tafiya
nan na samesu falo har da yaya Habu a cikinsu suna magana da dan uwasa.

Na gaidasu da kwana suka amsa min mikewa Jafar din yayi yana fadin ka barni dashi Habu nasan yadda
zanyi maganinsa ai.

Ramaah kin shirya ga yaya zaije Abuja yau shi zai wuce dake don shi wancan sai da karfe biyu wai zai
tafi banyi magana ba shiru nayi.
Rahaman ta fito kuwa mama dake fitowa kitchen ta fada na amsa da eeh mama tace toga wanan din
tsarabarce da zaki dashi ki gaida muna su son Allah a kula da kai kuma aje lafiya a dawo lafiya.

Na amsa da insha Allahu mama su har sun kai bakin mota a lokacin suna tsaye suna cigaba da magana
da gani dai magana ce mai muhinmanci a garesu.

Nida salima iya sai mama suka rakoni har bakin motan da kayana salima tayi mai magana ya bude
bayan motan muka saka kayana a ciki.

Kafin na zagaya na tsaya ina jiransa a gefe daya salima na min sheri da indai yaya ne yanzune zaku kai
Abuja don gudu yake da mota sosai wallahi.

Ai shine matsalansa ranan da ya kaimu kaduna ai fada nayi dashi sosai kamar wanda zai tashi sama
damu mama ke fadan hakan nidai ina kurum sai ya Habune ya dago yana fadin bude mana ki shiga
Ramaah .

Baya na bude da zumar shiga naji yace a,a gaba zaki bude mana ai ina ganin kamar ba wanda zai tafi
dashi ko ?

Ta shiga mana ni kadai zan tafi ya fada daga mama har iya kudi suka dunkula suka ban suna min a
dawo lafiya saiga ya Habu ya kara min kudi daya miko min wana rike a hannuna.

Nayi masu godiya ya shiga motar suka juya don komawa cikin gida ya fara ribas da motar sai naga yaja
ya tsaya.

Ta karaso bakin motar rike da yarta a hannu tana fadin wacece kuma tare dakai naji yace ki fadi meye
don Allah kada in makara banson rana yayi min a hanya.

Lekowa tayi ta ganni kamar in shareta saidai nace da ita ina kwana anty Saiba bata tsaya amsani ba sai
cewa ita kuma ina zata ?

Tsuki yaja yana fadin gata nan ai ki tambayeta ya fisgi motar da karfi don maigadi na tsaye yana jiransa
da get a hannunsa rike.

Amma ai ka tsaya dai muyi magana sweet J bai saurareta ba ya fice yanawa maigadi horn da mota na
lumshe idanuna na hankali a yadda nasan halinta zasuyi rikici sosai da daukata da yayi a motarshi yau.

Ban ko kai karshen zancen zuci ba wayanshi ya katseni naji ya dauka yana fafin umm,humm ina jiki ta
fara fada Jafar ina zaka da yarinyar nan baka fada muna ba ?

What ki shiga hankalinki wallahi Nusaiba kina wuce gona da iri fa a rayuwata dolene sai na fada maki
inda zani da ita ki je ki tambaya idan kin damu ?

Naji ya kashe wayan yana tsoki dama nasan za a rina yadda take da zafi akanshi tunda Salima ta tayar
dani tace dashi zamu tafi gaba saida ya fadi nayi wanan tunanen da sai wani abu ya faru kan hakan gashi
kuwa.
Tsuki ya kara ja yana lalubo wayan daga inda ya jefata da farko ya dauko yana tuki yana neman lamban
da yake nema a lokacin.

Can naji yace mama wallahi idan Nusaiba bata yi hankali ba yau din nan saina saketa kafin ta bata min
suna a banza.

Banji me uwar tace dashi ba naga ya kashe wayan nasa a hasale yana faman jan tsuki akai kai saida
muka tsaya gida mai a kaduna ya tsaya magana da wani kafin ya dan sake.

Hanya muka kama sosai inda barcin azumi yake dan dibana a wajen lokaci lokaci saboda sanyin AC
motan nasa daya sake .

Maganan Salima ya tabbata don ganin mun shigo Abuja ga signboard din THIS ABUJA baro baro a
jikin allon shiga iyakar Niger da Abuja din.

Wani unguwa zakije ya tambayeni ba tare daya kalloni ba na amsa da maitama kinsan gidan ke nan
zaki gane na amsa da ehh .

Har yayi shiru naji ya kara fadin idan ba zaki gane ba ki kirasu a waya suyi maki kwantace nace banda
waya amma zan gane gidan.

Cikin mamaki ya juyo da kyau ya dubeni yana fadin baki da waya fa shi Habu yana me da basu saya
maki waya ba ?

Shiru nayi don ko da zan taso saida mukai zancen waya da yayata da salima kuma har Salima tace zata
ban karamin wayanta bansan meyasa kuma ta fasa ba.

Shiga wanan lungin fada wanan muka isa wani katafareb shago yaja ya tsaya ya dauki abu naji yana
fadin ina zuwa jirani kadan in dawo don Allah .

Ya fita lokacin na sauke ajiyan zuciya a hankali ina bin wajen da kallo shagone babba don jama,a sai
shiga da fita sukeyi a wajen.

Can na hangoshi da ledoji kusan ukku rike a hannunsa ya nufo inda motarsa yake ya bude ya baya yana
aje lodejin aciki kafin ya juya zuwa gaba wurin driver ya bude ya shiga.

Sorry na dan dade a ciki na barki zaune bakomai yaya saida ya zauna da kyau ya dauki hanya muka bar
wajen hanyan maitama naga ya dauka kai tsaye.

Ajiyan zuciya na dan sauke an karaso gida ko naji ya fada na danyi murmushi ban dauka yana da saukin
kai irin haka ba.

Wancan layin na fada ya mike zuwa layin dana fada muka shiga dab tafiya kadan nace wanan gidan mai
bakin get nan din gidansu hjy mamace daga waje ya tsaya ya juya yana dauko ledab a bayan mota naga
ya fitar da waya sabo dal a kwalinsa ya fara duba lambobi a cikin wayansa yana lodawa kafin ya miko
min wayar yana fadin layin mama dana Salima saina habu suna saka maki .
Saida na dan dubeshi nayi kasa da murya ina mika hannu nace nagode yaya Allah ya kara arziki amin
yace a uzurce da alama sauri yakeyi a lokacin.

Horn yayi sai ga wani dogon sauriya ya leko yana duban mu kafin naji yace daga Zaria ko nace ehh
sorry duk basu gida sun tafi umura last week amma anty salma tace idan kin iso a kaiki gidansu .

Sai lokacin naji zuciyana ya dan sake da har nashiga vibration inane gidan nata yake naji yaya ya fada
tana Aso rock muje ka nuna min ya fada.

Saurin yace ga mota nan da tace in kai ta sai naji yace.

No muje dai ka kai,mu naga gidan na ajeta baiki ba naga ya juya ya fito da mota muka bi bayanshi har
gidan anty Salma din.

Duk wanda yaji ance gida a Aso yasan ba karamin gida bane ke nan za a gidan ya hadu iya haduwa
mijinta wani babban dan kwangilane mutumin maiduguri.

Gaeinsu daya asalima yan uwa suke dashi itace matarshi ta biyu yanzu anty salma yaranta biyu dashi
bayan barin mune akai aurensu dashi mun dai sanda zancen auren kafin Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa
mu koma gida.

Ko kuma Allah na tuba ka yafe min inji mata gashi kuma zan fada ince Baffa ya cinyeshi don shi yai
sanadin barinsa duniya duk da lokaci yayi dama.

Tsayar da motar yayi yana fadin kice min gidan manya kikazo dama murmushi kawai nayi ina mashi
godiy.

Ledan ya dauko daga bayan mota ya cusa kudi a ciki ya miko min yana fadin rike wanan inda matsala ki
kira gida a zo a daukeki .

Na amsa da godiyana na fito daga motan ya fito ya bude baya aka fito min da kayana zuwa ciki ban
shiga ba saida na kara mashi godiya naga tafiyansa na sa kai zuwa cikin gidan.

Ina shiga saiga anty salma da gudun ta muka rugume juna da ita a cikin murna kafin ta sakeni tana fadin
wai Ramaah tace nan haka ta zama yan mata ?

Nayi murmushi ina fadin nice anty muka kwasa zuwa cikin gidan nasu tana nuna min kauna don haka
muke da ita tun ina karamata .

A zaria motarmu na dagawa ta juya zuwa part din su mama a hasale take babu ko sallama ta fado masu
a falon ta samu kowa a falon zaune.

Mama tana ganinta hakan hankali tashi ta soma fadin Nusaiba lafiya kuwa na ganki a haka hankali
tashe ko wani abu ya faru ?

Babu komai mama dama karan J na kawo maki mama ta dan sake kallonta tana fadin jafar kuma me
kuma ya hadaku dashi ?
Mama din ta tambaya cikin kulawa don ta kwantar da hankalinta tayi mata bayani yadda zasu fahinci
abinda ya hadasu .

Mama don ya dauki yarinyar nan Ramaah ina tsayar dashi zanyi magana amma J ya daka min tsawa ?

Bai saurareni ba ina ruwana da inda zai tafi da ita tunda da ai an,san ya dauke ba a hanashi ba saboda
ita zai dinga muna wullakanci haka mama ?

Haba yar nan ki saurara mana kada kiyi furci irin haka ga mijinki don Allah koda kika ganshi da yarinyar
nan Rahama hanya ya rage mata ai.

To don me ina tsayar dashi in fada mai yarinyar nan jikinta yana zafi amma yaki tsayawa saboda
Ramaah zai min wullakanci mama ?

Point of correction ki gyara zancen ki kwarai da sanin su ya dauki Ramaah zuwa Abuja kada ki tsaya
boyewa don kinj zafi ya dauki wata a tare dashi salima ta fada a hasale.

Ki barta tayi maganan ta mana ke ina ruwan ki salima wajen mama tazo fa ba wajen ki ba Saare ke
fadin hakan .

Dole inyi magana don mu ba yan iska bane da kike son fadan hakan a gaban mama tana fadin wai
saboda Ramaah ?

Kinzo nan ne kiji dai ina zai tafi da ita to Abujan daya nufa can zai kaita gidan yan uwanta a can zatayi
sallah

In kuma ya Habu daya bashi ita yakai yaji an juya wanan zancen wallahi mama rai zai baci sosai a gidan
nan don sai yaba kowa mamaki matakin da zai dauka kowa kuma yasan hakan .

Kada inyi magana ita din muharamince halan da zai dauketa daga shi sai ita a mota da zakice kada
inyi magana mijinane fa J dole inji dalili ?

Mijin kwace ba da kika kwace wa kawarki mijin har zakizo nan kina kokarin karantawa mutane hauka
kega mara kunya don ana kyaleki ?

Wai Salima me kike nufi da bazanyi magana ba naga kamar dama kina jirace dani ashe ?

Jinan Nusaiba tunda kinji abinda ke nan sallah yarinyar nan zata Abuja tayi gidan yan uwansu shine
habu ya hadashi sa ita ya sauketa banga abin hayaniya ba a nan ?

Mama niba hayaniya nazoyi ba kawai dai nazone in fada maki abinda yai min akan Ramaah saiya dinga
nunawa mutane banza muke mu ?

Wasa wasa zancen dai ya koma na Salima data gaji da halin Nusaiba fada sosai sukayi a gaban mama
tana zagin Salima din don me zata hanata magana a kan gaskiyarta.
Hayaniyan su ya fito da ya Habu daga part dinshi yashigo yana fadin wai meke faruwa hakane meye
haka ga mama zaune ga iya kuke wanan abu haka ?

Sam bata san yana gidan ba ta dauka ya fita ko bai gari ta don basu sani idan ba sun gashi ba tasan
waye Habu din bai dariya da kowa a gidan balle aje ga wasa .

Nace meya faru duk sukai shiru ya juya wajen Saratu yana fadin ke Saare meya hadasu fada da safen
nan haka ?

Bafa fada bane ita Nusaiba tazo wajen mamane da magana shine ,,,,

Yaya zakice ba fada bane ita mama din sa,artace da zatazo tana fada akan ya J ya dauki Ramaah a
motarsa salima ta tare Saare dake kwana kwana da zancen tana kokarin dora mata laifi.

Kai ya girgiza cikin takaici yana fadin don J ya dauki Rahama shine abin fitina ba dan uwana bane J
Rahama kuma tana zama kanwar matatace a gidan nan .

So baki da right din da zakice kada ya dauketa wai ma a gaban mama kika zo kina wanan haukan ke
yanzu bakiji kunyar wanan abinda kikeyi ba don Allah.

Assuming nine yanzu zani kaduna saiga kanwanki zata sai ince ban daukanta don ina tsoron Maria kada
ta shakeni ko ranta ya baci kome ?

Ai yau naga mamaki ga yarinyar nan gara da Allah yasa kana gida ka ganewa idonka irin cin kashin da
sukewa uwarku a gabanta ba zagin da yar nan bataiwa Salima ba yau don ta raina arzikin uwarku
balleni ?

Bazan ce komai ba sai mijinki ya dawo daga Abuja shida ya ajeki zanwa iyaka da shigowa part din nan
idan ba alheri ke kawoki ba dama ?

Fice kafin na canza zuciyana koda yake banganin laifin ku gaskiya waje kuka samu nayin hakan ni akwai
matar da ta isa tayi min haka ko yar wacece ita kuwa an dauki wata a mota idan ya dawo yau ki kasheshi
don Allah.

Amma ke kan kibar wanan halin wallahi salima ta dubi yar uwarta ta fada tana mikewa don barin
wajen.

Mama duk hakan da laifin ki wallahi idan mutum

19 / 101