Chapter 83 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   83 / 101

246K to 249K   out of 302.2K words

a kanmu ummah tanayin ne kuma don kawai an sakata tayi
muna hakan kada mu mamaye masu gida kamar yadda dan uwanta ya fada.

Dan murmushin yake ummah din tayi tana fadin kaiya ta makaro wallahi ai tunda ta haifa sai an mora
din yadda bata so.

Yanzu dai ki karbi kudin nan ki shirya din gobe ku fita da antyn naki don jibi zasu mai dake dakinki in
sha Allahu.

Jibi kuma ummah na tambaya da sauri ta mike tana fadin me zaki zauna nan kiyi Rahama ga mijinki
can yana bukatanki a kusa dake.

Ta juya ta tafi nabi kudin dake hannuna da kallo zasu kai dari biyu kila da dan kai don nauyinsu da naji a
hannuna din.

Koda na shiga daki na samu wayata dake makale a caji tana ta rigin na duba shine a kan layi yake
kirana har yayi min three mis called a lokacin ina waje.
Kamar zan share sai kuma na daga da sallama ya amsa yake fadin ina ta kira baki picking ba tun dazun
dama nace in tura habibane ta gyara maki daki ?

Ai Key din suna wajena na bashi amsa da hakan yace saida nayi tunanen hakan saidai falon da sauran
dakuna ko nacewa Yazid a kawo maki kayan abinci fresh a kwashe wa yan nan tunda sun dade .

Nagode kawai na fada a darare yake fadin please Rahama kiyi hakkuri kada kice baki dawowa yanzu
rayuwana tana bukatanki a kusa dani wallahi.

Da sauri nace dashi aiba ni kadai bane bayan haka akwai yan uwa kaida kake cikin gatanka ga kowa
naka a kusa zakace kana cikin wani hali a yanzu ?

Haka dai kikace idan kika wuce satin ban Allah saidai in dawo kaduna daddy ya bamu daki a nan mu
tare baki dayan mu.

Kit na kashe layin cikin takaicinsa don ni dai shine ya jefani a wanan halin da ya barni yadda muke da
shike nan yanzu muna zaman mu lafiya da kowa a gida yaje ya kawo zancen aure a tsakanin mu daya
jawo min bakin jini a cikinsu yanzu.

Zama nayi ina tagumi a bakin gado tunanen abinda zan koma in tarar yanzu kuma a gidan nakeyi duk
da nasha alwashin cewa ba zan kara kulasu ba duk abinda zasuyi min nasan wanan karyane muje dai din
don dole wata rana in kula.

Nusaiba kuwa daga ranan da suka shigo kaduna din zuwa wanan ranan tashiga tashin hankalin dayafi a
girka duk iya shige shigenta bukata bai biya ba yadda malamta suke mata karyan zai faru din.

Don gashi har kaduna suka shigo amma ba wanda ya kula da lamarinta har waya da tayi da mama ta
fahinci maman batayi na,am da hakan ba.

Koda basu zo donta ba ai zasu shigo su duba yarsu dake tare da ita amma kememe tayi ta jiransu sai
sakon Saratu data samu cewa sunma kusa shiga zaria ai.

Hakan yasa ta kasa hakkuri ta dinga tura masu sakon bakar magana a cikin bacin rai tana kara dasa
kiyayarta a zuciyarsu wanda ta dauka hakan gwanintane a wajenta ai.

Abinda nake son mata su kulla a nan shine matukar kina shuka gaskiya cikin lamarin ki ubangij Allah
yana tare dake a ko wani hali saidai idan kece kika raina abinda kika gani din a kanki.

Ban taba zato ko tsamanin cewa zasu shigo haka kamar yadda daddy ya bukaci ganinsu ba amma sai
gashi Allah yayi ikonshi dole sunzo din har gaban su ummah suna bada hakkuri.

Washegari anty Nuratu tazo gidan ta daukeni farko wajen wata mata muka tafi yar maiduguri ina dai
kallonta a raina nace nu dake da mummy a abuja ana gwada min wanan abin ?

Saidai lokacin da matar ta fara fitar da kayanta na fahinci kowa da nasa sabin ashe ita anty Nuratu din
ta biya da kudinta muka fito daga gida.
Muna mota take fadin ni naga no need asai maki wasu sutura a yanzu haka zaifi kyau bayan kin haihu
muyi wanan shirin .

Nima ban ra,ayin wasu sutura wanda aka dinka a baya suna nan cushe ta juyo tana fadin wallahi ki
dingawa mijinki kwaliya kanwata.

Kada ki yarda ki saje da wa yan nan matar nasa marasa kan gado ga miji tsab tsab aje aga matansa
kamar rainon kauye ba kyau gani .

Ni tun a nan na raina masu wayau wallahi suna ganin don yana kwance yana jinya ba zaiji dadi bane
idan sun gyara jikinsu ?

Krdai abinda nake so dake ysnzu Rahama shine kada ki yarda ku zama daya dasu don Allah ki
bambanta kanki dasu ta wajen kwalliya abinci da gyaran gida.

You are lucky ma ba a gida daya kuke rayuwa da kazantannan ba don wallahi dazaki sha wuya ga hakan
don haka ya kasance ya zamo yana mararin dawowa gareki ko yaushe wanan ne kishin zamani ai ba
zama ana hauka ba.

Haka kuma zancen yan uwansa daddy ya fada min komai kada ki kara damuwa da lamarin su don Allah
shi dan uwa marfin jallone basuyi saida shi haka kuma shi bayayi saida yan uwansa.

Ki dai dauki matakin zama da kowa don Allah kada ki kara bada daman da zasu rainaki kuma ki daina
cacan baki dasu haka ko yaushe.

Sufa yanzu takaicinki sukeyi sister suna ganin kece star din gidan duk wani shawaransa dake yakeyi so
kinga dole suyi bakin ciki dake haka ?

Yaushe zaki wuce servuce dinki jn haka yasa na gyara zama ina nsawa nace zuwa next month ne in sha
Allahu.

To ki mayar da hankali don Allah Rahama ki dage sosai ki zamo wata a cikin family dinku don Allah
kece Allah ya zabo kila da zaki tallafi kowa.

Ki daina yawan shiga cikinsu sai un wani abu mai muhinmanci ya faru ke leka kada ki jima ki fito sosai
zaki dauki girmanki fa Rahama .

Ita wanan kanwar tashi ba komai bane illa zallan hassadanki da takeyi tunda taga kin tsaya kinyi
karatunki tasan zaki zama wata abu nan gaba a cikinsu.

So ina son ko baki dauki shawarana dukka ba Rahama kiyi amfani da wasu don Allah a karshe takaini
wajen gyaran jiki aka lugudeni tas na fito kamar bani ba .

Anan take fadin ki kula ki dinga shigowa kina gyara jikinki ko nan ko kano din duk da nasan zarian ma ba
za a rasa ba amma ba zaikai nan dinba ai.
Kamar yadda ummah ta sheda min wanan sister din daddy da muke kira da gwaggo Laraba itace dasu
anty Nuratu suka mai dani gidana na kaduna ranan jumma,a .

Nayi mamaki kwarai yadda naga yan sauye sauye a gidan anyi min hakama wajen gidam anyi sabbin
abubuwa na zamani a haraban wajen gidan.

Saida aka fito daga jumma,a sukai shirin komawa kaduna a lokacin kuma ya bugo min waya yana min
barka da jummah yake fadin sun fito daga sallah yanzu ya dora da fadin.

Watau har satin nan ya shige Rahama bakiji tausayina kin dawo ba ke nan Allah ina wahala rashinki a
kusa dani sosai Rahama goben nan zaki ganni a kaduna ai.

Idan kaje ka gaidasu nikan ina zaria yanzu haka tun karfe shadayan rana muka shigo garin nan nidasu
anty Nuraru.

Kina ina yanzu na sameku nace gidana a takaice sai naji yace wasa kike min dai ki dawo garin nan ace
ban sani ba Rahama ?

Duk da ina daurewa a yanzu don fada da nasihan danasha a kanshi na dan daina jin haushinsa da nake
ji kamar farko amma hakan bai hana na dankara mashi magana ba.

Don Allah wai da gaske kin dawone ya sake tambaya nace kazo ka gani mana yanzun nan ma su anty
ke shirin komawa kaduna su.

Ina jin yana fadin kai mu gani koda gaske takeyi ya kashe wayan tashi da sauri muna falo suna batun
fita suka shigo shida Yazid.

Har yanzu dai saida dabara tafiyan nasa haka kuma kallon daya zakiyi mai ki fahinci yana sauran jin
jikin nasa karfin haline kawai yakeyi irin na dan adam.

Fuskamshi kyam a nawa yake fadin wallahi na dauka wasane kike min baki dawo ba suka shiga
gaisawa dashi gwaggo tayi mai nasiha sosai kafin ta mike tana fadin Allah ya bamu alheri.

Sun tafi Yazid ya rakasu har gidan mai ya kara cika masu tanki da mai ya kuma basu tukwaicin kamar
yadda dan uwan nasa ya umurceshi dayi garesu.

Muna falo zaune dashi mama ta kira wayansa tana fadin wai ina kuka tsayane baku dawo kunci ahinci
ba kasha magani ga wanan mutumin yazo fa ?

Ina nan gidana mama gidanka naji ta tambaya da mamaki yace eeh wajen Rahama data dawo yau
nazo daga masallacin inyiwa wa yanda suka rakota godiya.

Ta dawo fa shine zata wuce can gidan don ta raina mutane muryan Saratu ce karara a wayan take
fadan wanan magana ga uwar.

Kallon juna mukayi dashi kafin muryan mahaifiyar tasu race dashi ke nan basu kawota nan ba sai can
gidan suka ajeta wai ko sun manta kana da uwane wai ?
Kit naji ya kashe wayan ya kalleni yi nayi kamar ban fahinci me hakan ke nufi ba yana nan zaune muna
dan hira jefi jefi har yazid ya dawo ya daukeshi nake fadin.

Ya kira yaya Ai ya sheda masu na dawo a turo min Biba yace nayi tunanen hakan nima anji zan zo da ita
insha Allahu suka fice a gidan sai annashuwa yakeyi da kaninsa yazid.

Bandai nuna a gabanshi zancen saratu yaci min rai ba da alama kuma har mama ta hau zancen saidai
na share kawai na nuna ba komai a fili kamar ma banji ba.

Ya zama dole a matsayina na diya mace in kara hakkuri in daure in dinga shanye duk wani bacin rai da
iskamcinsu yanzu tunda nasan manufarsu a kaina yanzu matukar ina son zama da mijina lafiya.

Wanda su basu ko iya boyon hakan har salima din da muke dan shiri wani lokacin bata iya boye
hassadanta a kaina saita fada a cikin wasa.

To tunda na fahinci Basu da wani guri saidai suga an samu matsala a tsakanina dashi ke nan tunda na
fahinta zanko tura masu haushinsu akai a yanzu zan nuna masu kan mage ya waye ashe ?

Duk da bansa a raina zai dawo gidan ba a ranan don yadda naji kalamin mama da nayi sallah la,asar na
fito na gyara gidan tsab duk da ba wani datti na feshe ko ina na rufe window da kofa tunda sanyi akeyi
tuwo kawai na dora don ummah tasa saudi tayi min miya mai yawa nazo dashi .

Ga kuma soyayyen nama da sauran abin bukata don haka aikin ya rage min a lokacin ina kwance falo
muna waya naji horn din motarshi gidan yazid ya kawoshi.

Bibace ta fara shigowa sai su a baya da gudu tazo gareni tana rugumana nayi murmushi don naji
kewam yarinyar sosai dan rabuwan da mukayi din.

Nan yazid ya zauna yake muna sheri donshi akwai son barkwanci damu haka don koda su Asmau
nakanga yana dan taba hakan saidai ba kamarni ba da sosai yake wasa din dani.

To ni zan tafi yau akwai sanyi wallahi ga sahiba na barta ba lafiya na fito yau dai za a barni na huta
tunda madam ta dawo yaya .

Zaka koma ka samu jidalin mama kuwa don dai nasan yau kokai ba za a barka ba wajen fada haba dai
ina jira ai sai kaji na balla yarinyar nan saratu zuwa gobe idan tayi wani rubishi akaina zanci kaniyarta
sosai wallahi.

Biba je kitchen ki debi abinci kici nace don basar da zancensu nan yazid din ke fadin what dama iya ta
fada ai ko jiki ka mayar a yanzu.

Don Allah Yazid idan ka koma iya ta shiga cikin gida ta kwanta don kada a barta a nan ita kadai kwanan
nan duk bata kwana da dadi wallahi zazzabi yake damunta a cikin dare haka muke kwana da ita.

Abinci fa na fada ga yazid din yake fasin naso in zauna naci abincin nan amma kuma ina gudun makara
me kika dafa mai nasan yau ai sai didima a gidan nan.
Murmushi nayi ina fadin tuwone kawai donshi nake so shi kuma nayi yace a zubo mai yaje dashi hakan
yasa na mike na hado mashi tuwon ya tafi.

Saida na zauna nake fadin iya ba lafiyane kuma yace wallahi takai kwana biyar a hakan kafin yaci gaba
wayanshi ya dauki ringing lokaci guda ya dauka yana dubawa.

Mamace take fadin Jafar ina ka fita da sanyin nan kuma nazo baka shiyanka mana ya bata amsa da
fasin gani nan yazid ya kawoni gidam Rahama.

Sai naji tace dashi gidan Rahama kuma da daren nan wai kanka daya kuwa daka je can din maganin
kafa da sanyin nan ka kwashi kafa zuwa gidanta don kawai ta dawo a yau kome ?

Mama wanan ba abinda ya shafeki bane fa ni hakan ya shafa Rahama matatace kuma dole inzo gidanta
tunda Allah ya ban lafiya a yanzu.

Anzo inda ba a son azo din ranan da zai fara ba mama amsa irin haka dama daddy ya fada a karshe zata
gusar da wanan biyayyan da yake mata ita da kanta lokacun daya fara hakan kuma ba zataji dadin shi ba
kuma.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/21, 9:28 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



8️⃣4️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




A cikin zancensu da mama a wayan na fahinvci baida niyar komawa gidansu a ranan yana nufin a nan
wajena zai kwana ke nan.

Banyi magana ba a lolacin saida yayi sallah duk a nan falo na bashi abinci yaci an dan jima nake fadin
Yazid din bai dawo ba har yanzu ga dare nayi kuma baka sha maganin ka ba kuma !?

Kin ce ya dawone ya kawo mj magani ya tambayeni cikin tsureni da idanuwanshi da sukayi mugun
fadawa a yanzu saboda raman daya karayi kuma yana son jin amsan tambayansa a gareni.

Saida na sada kaina kasa nake fadin ni bamuyi hakan dashi ba naga dai kana shan maganine bai kamata
a kyatare ba kuma ?

Rahama ko kema gudana kika farayi yanzune kamar wa yan can dama da wanan maganan yakanci
galabata idan irin haka ya taso a tsakanin mu.

Gudunka kuma ban guje ka ba a baya sai yanzu na fada ina daure fuskata to ba inda zan tafi yau nazo
ke nan dama ai kece mai jinyata din suka koreki ko ?

Ka daiyi kwanakinka ka koma ni kada ka jawo min wata magana kuma a sakani a faufai ana tallah na
bayan wannan da nake cikinsa.

Suyi tayi mana waya damu da zancen mutu ni yanzu ban kara jin nauyi ko idon mutane a irin haka
abinda zai fitar dani zanyi idan sun damu dani su biyoni nan su dubani ai.

Wani kallon mamaki na sake mashi amma ban furta komai ba saboda gudun rashin fahinta amma
nasan hakan ba abu bane da zai yuyu a garemu a yanzu.

Bayan hakan nima ai ina bukatan hutu don haka ba zan sake wahal da kaina ba irin danayi a baya koma
yace din zai zauna a nan nasan mama ba zata taba barinshi ya zauna din ba.

Mikewa nayi na shiga bedroom dinsa har lokacin banyi magana ba ya bini da kallo na jima a ciki na
gyaro mai ko ina na sauya zanin gadon nasa mai duhu saboda maganin da ake bursune masa jiki dashi .
Ruwan wanka na hada mai na fito na samu yana waya na wuce zuwa kitchen na dan kawar da kaya na
fito na samu ya gama wayan nake fadin ga ruwan wanka can na hada ma saidai ban sani ba ko saida
magani kakeyi har yanzu.

Yanzu da ba maganin a kusafa ba sai in watsa hakana ba yaushema rabona da wankan dare tun
tafiyanki ai sai inkai kwana uku ma yanzu ko wankan maganin banyi ba.

Da sauri nace saboda kaji sauki ko ka daina magani bayan ciwon bai gama fita a jikinka ba har yanzu ?

Saida ya langabe kai yake fadin bari kawai Rahama shiyasa manya ke fadin Allah ya kawar da ranan
yabo ga mutum aini naga abu dan tafiyan nan naki saidai kawai a kyale kawai ba a cewa komai.

Amma ai yanzu na fahinci kowa a duniyan nan ki bari kawai Rahama sosai zakiga halai yana ya canza a
yanzu don darasin dana samu a kwanciyar nan da nayi.

Zance da bansan dawa yakeyi ba don haka ban yarda na zake sosai ba illama cewa da nayi ka tashi ka
watsa ruwan kada dare yayi.

Yai shiru kamar yana tunane kafin naga yana kokarin mikewa tsayen daga inda nake nake fadin kona
taimaka makane ka mike ?

Yace bari na dafa kujeran ai yanzu dole na koyi hakan tunda ba mai zama dani sai iya, iya kuma aiba
zan bata karfina ba tunda itama ta kanta takeyi yanzu.

Haka dai ya samu ya mike ina bashin a baya a dakin daya kai saida ya zauna yana ajiyan zuciya nice na
taimaka mashi ya mike tsaye zuwa ban dakin nayi set up din komai don har kujara da zai zauna saida na
cudashi na fito na barshi ya kara din.

Daki na koma na jawo goran ruwan zam zam din da anty Nuratu ta bani na diba na fito zuwa dakin shi
na samu har lokacin bai fito ba nayi magana ina fadin har yanzu baka fito ba ashe ?

Sai naji ya amsa da fadin ina kara zubawa jikina ruwan zafinne don sunyi min dadi sosai a jikin zama
nayi na fara jero adduan data koya min .

Wanda kowa ya sani ga sauki ga falala ga musulmi shine suratul fatiha da ikilas sai la,ilaha illah anta
subba hannaka innin kummtu minal zallimin kafa 41 da daya data kira shi da raina kama kaga

83 / 101