Chapter 90 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   90 / 101

267K to 270K   out of 302.2K words

kula da rufe gida.

Kasan nan yanzu ba wani sequrity kwarai a yanzu Aminu muke jira ya shigo ya dauki abincinsa na bashi
amsa.

Idan yazo ya kwankwasa mana ko a aje mashi daga waje ana ruwan nan sai mugu yayi amfani da daman
yazo ya cuta maku a raina nace cuta yafi naku kuma ?

Na dan dago nayi mai sannu da zuwa ya amsa yana fadin ya kuke Alhamdullahi na fada a cikin basarwa
ya juya ya fita mai karatu har zuwa lokacin ba wani sakewa a tsakanina dashi irin baya qda muka dan
shaki yanzu duk na daina hakan duk da shawaran da mutane ke ban wai yana sona don haka kada in
nuna abin ya dameni a bamgarena.

Dole in nuna don yiwa dan cikina gata baka sanin halin mutum ka zauna ya shanmaceka nasan waye
Saiba da Saratu hakama mama da danta.

Don haka ban sanyaya a wanan zance ba gaba daya na kara dagula mashi lissafi idan ya dauka ni ruwan
sanyice zan nuna mashi kalan tafasana a yanzu.

Bafulatana fa nake ta asali ba muna fulani ba zuciya gadan shi mukayi a jinin mu yake ba ara min akayi
ba idan kayi min sai nayima don bamu yafiya kona kara balle na fili.
Ki tashi idan ya fita saiki rufe kofan nacewa Biba daga inda nake kwance jin hakan yasa ya dan juyo
yana fadin idan na fita ina ?

Nina rufe kofan aidana shigo ko Aminu din bai dauki abincinsa bane baya gidanne har wanan lokacin
biba data mike don barin dakin take fadin ina ganin yana nan don da aka fara yayyafi yana falo yana cin
abincinsa.

Tana fita shima ya fita hakan yasa na mike zuwa kitchen na shirya mai abinci na kawo falo na dauko
ruwa na samu ya fito yana waya naji yana fadin na dawo mana tun dazun ina nan gidan wajen Rahama.

Yadda ya tsaya sauraren wayar yasa nasan maishi na koro mashi zancene a ciki na juya naji yana fadin
mama wanan kuma ra,ayinane fa bansan da dawowanta a jiya bani ?

Kai kai kai su mama dubu dai anga lagwai da tsohuwar nan nada ikon kasheni na tabbatar data
halakani ta gama a duniyan nan.

Yanzu uwace ke fada da danta haka akan matarsa a fahintana sunyi mai bazata shima ya mayar masu
da hakan idan Saiba ta dawo a ranan girkina don su nuna min isa to Allah ya hau dani kansu ga baki daya
yanzu.

Da wayan yayi yawa bayan ya kashe aka kara kira naga ya dauka yana fadin na dawo ina gidan
Rahama.

Karshema yaja tsuki ya kashe wayan tashi baki daya ya aje gefe daya yacigaba da cin abincinsa ba dai
wani hiran da mukeyi na zauna ya gama in kwashe kayan a wajen.

Ina zaune kamar ban fahinci meke faruwa ba a lokacin har ya gama na kwashe kayan bance dashi uffan
ba shima haka baiyi magana ba.

Na fito kitchen yake fadin maganina fa da ruwan addu,an da kike ban ban hada ba na bashi amsa na
shige daki na barshi a falon zaune .

Kayan kwanciya na sauya a jikina na kwanta can dare wajajen sha biyu da rabi barci ya soma daukana
sai gashi a dakin yana tayar dani.

A cikin idon barci na bude ido na sauke a kanshi yana tsaye kaina saye da farar jallabiyansa mai dan
hannu yake fadin wai meye haka Rahama kinfa san ina jiran ki kinzo nan kin kwanta kuma ?

Ido na mayar na lumshe kamar ban san yana tsaye a wajen ba sai jinsa nayi ya fita daga dakin na soma
barci ya dawo ya kwanta a bayana don jaraban maza daya motsa mai ya kasa rike fushinsa da yakeyi
dani ko dai wani abu.

Washegari da safe har muka zauna karyawa bai kunna wayansa ba saida ya fito ya zauna naga yana
kunna wayan kamar ana jiransa a lokacin kira ya shigo.

Tarr naji me take fada lokacin don kusa dashi nake zaune lokacin saibace take fadin ba sai ka nuna min
kafi jin dadin abu kazan yar fulani ba zakai min haka.
Yace ashe kin sani to tunda kin sani kisan matsayinki yanzu kada ki hada kanki da ita don ita din ba
tsaran yinki bace look Saiba mena fada maki game da yarinyar nan kafin in yarda ki dawo ?

To udan bakiji ba kada kiyi mamaki yau din nan ki kwana gidanku na har abada ba dai kinga na kyaleku
ba kada ki dauka bokan da kike bine aikinsa yaci a kaina karr nake kallon ku wallahi.

To in kwana mana sai me dama ban saba kwana bane a gidan namu wallahi akan wanan yar dajin
matar taka ba zakai min wullakanci in kyaleka ba Jafar.

Tunda banga abinda tafini dashi ba da zan dawo ka dauki kwanana kakai mata don ita tafi ko wace
mace a idonka yanzu kome ?.

Kwanafa kikace gashi kin ba kanki amsa tafiki komai ke nan ashe kin gane hakan keda kukace zaki
dawo ki zauna zaman yarki ina ruwanki da kwanan da nakeyi da matana yanzu kuma ?

Zaka dawo gidan ai ta fada a hasale kamar wace idan ya koma zata dukeshi a ranan ta kashe waya yaja
tsuki ya dauki plate din abincin dake gabanshi yana fadin mahaukaciya kawai wanan ba zata taba
canzawa ba tayi hankali ba wallahi.

Wacece na samu kaina da tambayar karya tankar banji me sukeyi a wayan ba da ita ya dan kawar da
kai kafin ya ban amsa da Nusaibace mana mahaukaciyar banza da wofi.

Naja bakina nayi shiru don ba abinda ya shafeni bane zancen har ya gama kamar kurame haka muka
zaune a wajen ba wanda ya kara magana a cikon mu.

Saida ya dan jima ya mike yana fadin bari na leka gidan in dawo ina yaron ki yakene nace ya fita school
tunda safe ok yana da lectures ke nan ko ?

Ban tsaya bashi amsa ba don zuciyana dake famam sake sake a lokacin ko don wanan mahaukaciyar zan
daure in biye masa mu kara haukatata kafin nasan abinyi.

Lokacin kuma na fahinci dole akwai wata a kasa cikin zancen dawowanta gidan dole a kaina ta dawo ko
wani abu amma yadda naji magananta haka a tsaye bawai irin na wacce tayi nadama bace gaskiya.

Koda ya isa gidan ya samu mama ta hau ta cika don me yayiwa matarshi haka da wanan zancen ta
tareshi da fada ga matarshi ta dawo don ya nuna masu iyakarsu yaje gidan wata ya kwana ya barta nan ?

Amma dai mama gidan matana na kwana ko da zata dawo wa kuka fadawa dawowanta ga shekaran
jiya din ?

So tunda banda amfani ga da zata sanar min zata dawo ai gara inje inda akasan darajana ko kai ji nan
malam naga yarinyar nan gaba daya ta juyema kai to ka natsu kasan abinda kakeyi yanzu.

Rahamace zata juye min kai kuma mama ya tambaya fuskanshi dauke da murmushin mamaki ga
maganan mahaifiyar nasa.
Inda mama din tace ba dole ince haka ba tunda kai baka san me kakeyi ba ta ina ka taba jin anyi hakan
itama inba makira bace ai tana da labarin matarka ta dawo data karbe ka .

Ina ruwanta da zancen dawowan Nusaiba mama tunda ba a unguwar nan take ba ina zata sani koma
dai ta sani ko bata sani ba dai tunda tasa kayiwa wata wullakanci itama ta saurarinata ai yana tafe.

Mama wai meyasa kike saka kanki cikin irin shirmen nan bafa dake ake zancen nan ba banga abinda
zaisa kina saka kanki irin wanan maganan ba girman ki na zubewa ?

Ooh yanzu don na tsaya gyaran gidanka shine girmana ke zubewa malam to ya tude karshen zubewa
ke nan badai ga yar gwal din matarka zai zube ba kawai to aida sauki tunda iya nan zai zube din.

Mikewa yayi yana tambaya iya tana can bangaren ne har yanzu salima ya samu ta amsa mai da tana
can yau ta tashi bata jin dadin jikinta tun jiya.

Subbahanallahi ya fada ya dakata yana tambayan ta meke damun iya din take fadin gudawa tayi sai
jikinta ya mutu .

Shine baku kaita asibiti ba mama kuka barta a gida haka amma haka baiyi ba wallahi ya fada ya fita da
sauri zuwa part din da iyan ke ciki.

A kwance ya samu tsohuwar cikin wani hali na ban tausayi da sauri ya kamota zuwa asibiti shida
salima da mama din akaje asibitin dole aka kwantar da ita aka saka mata ruwa.

Lokacin ya kira yazid a waya ya haushi da fada kan rashin kula tsohuwar da baiyi ba kuma yana gari
fada sosai yayi da kanin nasa yana bashi hakkuri.

Sai lokacin jikin mama yayi sanyi ta shiga kame kame tana fadin wallahi na dauka irin yadda yakan dan
bugeta ta mikene kawai.

Mama bidon Allah yayi iya da tsawon rai mai lafiya ba jikin iya a yanzu ba komai zaku bata taci ba ya
kamata ace ana duba irin abincin da zataci tunda tana da gatan hakan a yanzu.

Ya bugo min waya a gabansu yana fadin in shirya abinci gasu nan asibiti da iya an basu gado hankalina
ya daga anyi dace nagama abincin rana ke nan na kwashe na cika kula Aminu yakai masu.

Wanan ciwon na iya ya kwantar da fitinan da akaso tayar mashi wanda shima a hake yake dasu ashe
kan hakan da dare tare mukaje dashi duba jikin iya din don yazid ya kawo wa yancan da zaizo da
matarshi sun duba iya din.

Akwai haske tar a lokacin duk da shigana ba wani shiga nayi ba a lokacin amma hakan ya tsonewa
mama da iyalinta idanu .

Duk dago kai zanyi zan samu dayansu yana satan kallona a cikinsu bamu jima ba ya soma fadin wa zai
kwana a nan din nida Dubu zamu kwana Hafsatun kawu ta fada.
A,a mama ki koma gida abar mama ta kwana don ko maman tudu taso tazo ta kwana sukace basu son
mutane da yawa a nan din.

Da dai ka barmu mun kwana mu biyu din tunda ba a san me dare zaiyi ba a hankali na fara takawa don
barin dakin cike da mamakin hali irin na mama din .

Ke nan tana nufin jinyar mahaifiyarta sai wani ya saka mata hannu a cikinsa bayan tasan ba shiri bane a
tsakaninsu ko banza.

Ya jima a tsaye kan iya ya dago yana fadin bari nakai yarinyar can gida indawo bai tsaya ba ya fito
zuwa wajena ina tsaye na dafa mota ya iso yana fadin muje ko ?

Saida muka soma hanya nake tambaya yaushe iya ta soma ciwo duk ta rame haka yace waya sani ko
yanzu ai salimace dana shiga take fada min da haka zata halaka a daki ita kadai.

Daga asibiti idan an sallamota nan gidan zan kawo maki ita don ta samu kula mai kyau don Allah ace
abar tsoho da yunwa ga tsufa ga ciwo sai lokacin da akaga dama za a bata abin karyawa taci ?

Ni dai banyi magana ba har muka isa gida duk abinda zan fada idan ba zagin mahaifiyarsa zanyi a
gabansa ba me zance don laifin duk natane game da hakan gaskiyaa.

Tunda ya dawo bai koma ba kamar yadda yace don har mama ta bugo waya wai in zai dawo yazo masu
da ruwan zafi a flask.

Yace gaskiya ba zai samu dawo ba don har ya kwanta saboda yana jin rashi dadin jikinsa.

Hakan yasa tayi fushi ta fara zage zage tana fadin Jafaru baida ta ido akan wanan yarinyar don in yana
gabanta tankar yana gaban Allahnshi ne

Haba dai dubu kada kice hakan kawai dai zuciyace take kaunan mai kyautata mata duba ga irin kokarin
yarinyar nan gareshi ba tsoro bane hakan kyautatawace kawai a tsakaninsu.

Kin dai tsani yarce har baki ganin kirkinta a yanzu amma ai tayi kokarin da ba kowa zai daure yayisa ba
kinga ko dole yaso abarshi a yanzu yadda tayi fama din nan a baya kanshi

Na kula kema hafsatu a yanzu kamar kin fara shakku da tsoron yar nan koda yake ba laifinki bane koda
kinyi hakan don kanki kikewa yaki hakana din.

Kwanan iya biyu ta samu lafiya kamar yadda yace yaso ya wuto da ita gidan mu sai iyan tace dashi a
bari agama bukin Saratu in muna raye sai tazo ta zauna dani har in haihu shiyasa yayi na,am da hakan ya
barta.

Sun fara shirin buki gadan gadan har lokacin ana neman abinda ake nema din na wasu abubuwa ga yan
uwan duk kowa yaja bakin aljihunsa ya tsuke yana kallo.

Shine mai saukin da suke saka ran zai fitar dasu kunya shi kuma din ya nuna yanzu Habu ma ya fishi
karfi don dukiyanshi da aka wawashe yana kwance bai gane komai ba.
Ga karyan da take sonyi ta burge mutane a wajen bukin nata ba abinda ya kamkama daga wajenta
shima angon ta rasa gane kanshi a yanzu datayi magana zaice ba kudi bai son karya a sha,ani.

Tana sonshi kamar me don haka saita kyale ta kasa tambayansa komai abu yayi yawa ya taru masu
lokaci guda.




ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



9️⃣1️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Banda niyar zuwa ko wani event a cikin sha,anin bukin donshi ko gyaran jiki ban tsaya nayi ba amma da
nayi tunanen kada ai min girshi naje amin kumshi da kitso da gyaran jiki don haka a wahalce na wuni a
ranan.
Yana can gidan da ake jiransa bayan yayi min kwana biyuna da zaiyi gidan sannan ya koma can gidan
don haka an fara sha,anin bukin yana gidan nasu a karshene zai dawo gidana har a daura aure yana
gidan.

Duk da iya ta dawo gida daga asibiti amma bamu daina saka mata abinci daga nan ana kai mata ba don
surfan tsufa tace abincina kawai take iya ci hakan yasa na dage ina girkawa da ita ko yaushe.

Kwance nake ina barcin gajiya lokacin da maman tudu ta bugo min waya da basu ganni gidan wajen
taro ba na rasa abinda zance mata karshe dai na fito fili na fada mata gaskiya cewa ina gudun fitina yasa
na zauna gida.

Kada ki hakan yar uwar mijinkice fa ko meye ki shiga koda ba duka ba ki daije a ganki yafi kice kin zauna
gida baki tafi ba ba zaiji dadin hakan da kike nufin yi ba gaskiya.

Nayi mata godiya barcin da ban koma ba ke nan a lokacin tunda ranan kamune don haka zanje da
yamma ayi kamun dani ke nan sunsa a kofan gidansu na cikin gari za a hadu zuwa dan wani wajen event
a unguwar.

A makare naje wajen don ban fita ba saida na gama har abincin dare don gudun yamma na fito shiya
turo da motarshi aka daukemu na samu a cika wajen sosai amma ana ganin zuwan duk wanda yazo
taron a yadda tsarin wajen yake.

Aminu ne ya jawoni zuwa wajen don haka ya shiga dani sosai inda za a ga fitowana daga motan ya
tsaya kafin na saka kafa na fito a hankali.

Tankar ba ciki a jikina irin kwaliyan dana caba duk da nauyin cikin da nake ji yana hanani sukuni wanan
ban yarda na biyewa hakan ba na lalace don ban bari an barni baya ba gaskiya.

Yar uwar Asmauce ta fara tabata tana nuna matani kafin saiba ta farga da abinda suke kallo a wajen.

Nida Biba munsha kwaliyan mu muna fita ya juya ya nemi waje yayi packing a can nisa kadan da wajen
nan gulma ya dan fara tashi ga matan dake wajen wasu na magana da nice amaryan jafar ai.

Wasu kuma suna zance akan cikin jikina yadda na sameshi a cikin jinya yayin da wasu ke fadin yanzu ya
fisheni daban a cikin matansa nice ke yadda naga dama a gidan.

Kamar Aminu ya sani yana fitowa ya kawo min key din motan ya mika min don yaron akwaishi da
gudun zuciya sosai bai yarda ace yayi laifi ta bangaren kawun nasa yana da taka tsantsan sosai wallahi.

Sai a wanan wajen muka hadu da mahaifiyarshi ya fada min tazo kwana ukku ke nan a lokacin don
haka ta taso daga inda take zaune muka gaisa a cikin mutunci da ita.

Wanda nasan ba komai bane yaron nata ya fada mata yadda muke zaune dasu a gidan ya kawo hakan
a yanzu.

Salimace ta taso ta kamani tana min sheri wai ciki ya boyeni ya hanani shiga mutane koda yake ita ai
kyau taga cikin ya kara min na dan harareta ina murmushi.
Wajen zama ta sama min daga inda yan gidan suke ban zauna ba saida nabi matan yayyunshi su yaya
Auwal na gaidasu na dawo na zauna.

Nida biba muna kallon abinda akeyi a wajen hango yar uwata da nayine yasa na kara mikewa zuwa
wajenta muka gaisa take fadin yanzu take cewa idan bata ganni ba saita biya ta gidan mu ta dubani.

Share zancen nayi na basar ina fadin ina yaran tace suna gidan makwaciyarta ta barsu duk a cikin filanci
muke maganan da ita lokacin.

Na hango Saiba a cikin wani dogon riga tana kai kawo a wajen taron kafin can na hango tana magana
da Aminu sai naga ya nuna matani tana magana kamar da tsawa dashi.

Wai ashe cewa tayi ya bata key din mota zasuje wani waje su dauko abu yace makullin yana hannuna
kuma uncle yace kada abawa kowa motanshi bayan ni.

Shine take fada kamar ya yace kada a bawa kowa motarshi ita din tafimune data shiga sai gashi yazo
yace in bashi key inji saiba yake mayar min dame tace nace ta kira mai motan ta fada mashi sannan na
bata key din.

A shirye nake dasu nasan hakan plan ne yasa ban bata key din kai tsaye ba da ace akwai girma da arziki
a tsakanin mu

90 / 101