Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
a cikin kara aure don ya kara aure saiba ?
Wai ina labarin Asmy ne har yanzu kuna tare kuwa ta bata rai tana fadin muna nan tana zaria muna
nan muna bugawa da ita.
Murmushi tayi tace kema Nusaiba kinsan ai dole ayi hakan kema kawarki ta kut da kut fa kika ciwa
amana kina tunanen Allah zai barki haka ba jerabawane ?
To amma ai naji ance kuna cikin rufin asirin ku don ina da labarin ku mijin ku bai rageku da komau ba
na rayuwa.
Naga tun haduwan ku kin kwacewa Asmy shi yana kuma yi maki yadda kike so to me kike bukata kuma
ina ruwanki da kara aurensa ?
Wallahi Sa,ade ba zaki gane bane ni yanzu ai nayi nadaman aurenshi uwarshi da yan uwanshine fa suke
juya shi har mu .
Haka basu kaunarmu ko kadan tundai ni basu sona musanman mahaifiyarshi da kaninshi wai shine
yanzu don cin amana kanin nasa yasa ya auri kanwar matarshi fa.
Ni kuma nace bai isa ba wallahi don ubansa sai naga yadda shegiya zata zauna a gidan nan ?
Umm,umm subbahanallah Nusaiba har yanzu haka kike da wanan halin naki ashe wallahi gara tun wuri
ki bari zaifi.
Ni dai shawarata gaskiya dolene ki sauke wanan girman kan naki da wani jiji da kai har in kina son gane
kan mijiki dole kiyi masa biyayya kamar yadda Allah yace ki kuma zauna lafiya da abokan zaman ki.
Abincinsa shimfidansa da komai nasa hakama yan uwansa sai kiga kun zauna dashi lafiya amma idan
kikace ba hakaba sai abinda kikaga dama zakiyi kinsan wallahi ko yar gwal kike ba zaku shirya ba ita
Asmau fa da kika sama ?
Na tabbatar ba haka take ba ita saidai yanayin zama dake sauya mutum wani lokaci don dai zuwa
yanzu,,,,
Bari kiji Sa,ade wallahi kinsan tun ba yau ba daga shi har Asmau basu isa su sake min halina ba don
bawani mutuncin da zan tsayayi akan kishiya.
Ke kika dauki wata tsiya wai biyayyan aure irin na matan da da suke wahala akan aure haka kawai in
zauna ana juyani.
Aure kuma nace bai isa ba wallahi kuma wallahi bai isan bane falon yayi tsit ana sauraronta a lokacin.
Sai Sa,adatun tace waike hanashi auren zakiyi inace sai yaso zai zauna dake dai tunda ragamar auren
yana a hannusa.
Ai sai idan ya raga makine zai barki ki zauna har ki daga mashi hankali dashi da sauran matan nasa
yanzu idan kin tada hankali yace ki bar masa gida fa ?
Gabantane ya fadi sam ta mace zai iya yin hakan ta lamkwashe a waje daya tana tunane Sa,ade ta
kalleta tana murmushi tace wallahi don haka kibi sannu.
Gara kiyiwa kanki fada don namiji zai kara aure zaki tsaya kina wanan daga hankali haka duk gatan
mace yau akace ta koma bazawara an gama dake.
Don haka kibi sannu ku zauna lafiya kibar wanan cika bakin kada zance ya koma a kunnensa daga gefe
halisa yarta tace shi nake fada mata.
Shiyasa na kawota nan wajen anty ta dai dan bata dabarun mu na mata itama tayi kaddari kada dai ta
koma baya a cikin kishiyoyi.
Mafalki ke nan anty Halisa ai in banyi gaba ba babu shegiyar da zata shigo tayi gaba a wajensa bari dai
in koma kawai ki gani.
Haka dai suka zauna suna bata shawara amma a banza don ko daya bata dauka a cikin shawaran nasu
ba lokacin har Saaden tayi masu sallama ta tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[2/10, 10:11 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN
TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Tun bayan wayan ya habu da Jafar inda ya Habu ya fadawa Jafar cewa idan ya gama ya kamata ya dawo
gida don har yakai mama ta tutseye maria ta kira Rahama tana tambayanta ina kake.
Which means tana zargin cewa kuna tare da Rahama din tunda ana kiran wayanka bai shiga so kada su
takurawa yar mutane da zargi a kanka .
Wai meke damuwan mamane Habu ?
Saida Habu ya dan fura iska a bakon shi yace da dan uwan zargina shine su kawu da yar iskan yarinyar
nan Saratu.
Saratu tana daga cikin wanda suke dagawa mama hankali akan zancen nan son basu shiri da Rahama
tun farko kasani irin halin nan yasa nayi mata duka kwanaki ai.
Ga yar iska taki karatu wai wanan mayaudarin mansur ta kwallafawa rai yanzu ni kuma nasan mansur
bata isheshi kallo ba banda ya yaudareta kawai.
Mansur kuma wani mansur kake nufi yace mansur dai naka mana ai tare suke dashi haka kawu ni sai
yanzu nake tuna abubuwa da dama da mutumin nan yakeyi muna J.
Amma mama bata gane hakan idan anyi magana tace ana son rabata da dan uwanta tillo sai ta nemi
sabawa mutum a kansa.
Ok wanan karon ku barni dashi nida kaina zan dauki mataki a kansa ai ba sai anyi wani magana dashi ba
kawai nasan inda zan kamashi.
Ka kyale kowa banson ka fadi wani zance daya shafi auren nan nawa don Allah Habu ka barsu duk
abinda za a fada suyi ta fada a kaina.
Kudi kuma na shirya tsab ranan da duk na dawo washegari in Allah ya yarda zan gabatar masu da kudin
don haka ka lalabasu har in dawo don Allah.
Ok zaka dawo kwanan ke nan ?
Ehh saboda karatun yarinyar nan Rahama banson karatunta ya tsaya sun kirani sunzo sun gyara gidan
sun saka mata abinda babu .
Maria ta kirani tans fada min mutanen suyi masu kokari sosai sai godiyan Allah gaskiya mutanen arziki
Allah ya hadasu dasu ba kowane zai rike amana haka ba ?
Ya halakansu yake dasune Jafar ya tambayi kanin nasa yake fadi just mahaifinsune yayi aiki a karkashin
Alh har ya rasu shi kuma tun yana raye Alh ya rikesu tankar yan uwanshi shine har yanzu suke halaka
bayan ranshi.
Kai Habu na dauka ai yan uwansu na jinine wallahi a,a fa kawai haduwan jinine duk da halakan ai ta
zama ta jini yanzu ido ya lumshe yana raya abubuwa a zuciyan shi.
Don sam bai taba zaton cewa ba halaka tajini bane tsakanin mu dasu ya dai dauka akwai zumuncin da
muka rike akansu suma suka rikemu din.
Sun dan kara tataunawa kan wani zancen kafin suyi sallama su kashe wayan kowa da irin abin dake
cikin zuciyan shi a lokacin .
ABUJA
Ni mamaki nakeyi yadda anty salma take faman rawan kai a kaina haka sai kudi take kashi ga gyaran jiki
da sauransu duk saboda zancen tarewana wanda nake sa rai bai wuce karshen satin nan da za a shiga.
Duk da naji tana waya bayan mama tayi min buki a nan Abuja sai a koma can kaduna kuma ummah ta
hada min walima daga can za a kaini gidan miji .
Tankar ban wajen a lokacin saida ta gama wayantane ta kallo tana fadin waike haka zakita zama da
angon nakine ba magana ?
Shirun kifa ya fara ban tsoro Rahama aita magana kina zaune baki furta komai wanan wace irin
amaryace wai ?
To na dai bada dinkunan ki da zakiyi amfani dasu idan kinje kada ki fara idan kinje kice zakiyi amfani
dako daya daga cikin tsofin kayan ki da aka sanki dashi gidan nan.
Haka kuma kada ki yarda ki zauna gida ba kamshi ko jikin ki kwaliya ko baya gari ki kasance mai gyara
Rahama don yana daga cikin abinda mazan yanzu ke so gyaran jiki.
Abinci kuma nau,in daban daban zaki dinga dafawa kada kiyi rowa Rahama don haka duk wanda zaizo
gidan ki ya kasance kin dan bashi wani abin sakawa a baki don Allah.
Ban son ki da dogon hurda da kowansu a yanzu don kada ki yarda dayansu tace zata shige maki ki
yarda sam irin hakan yana kawo matsala daga baya don haka ki kama kanki da kowa don Allah.
Gidan ki babbane amma akwai maigadi kina kuma da makwabta makwabci ba kowane kake saurin
yarda dashi ba balle nasan baki da matsala a wanan wajen don ke din kurace dama baki da saurin yarda
da mutane.
Rahama don Allah ki sauke komai a zuciyar ki kiba mutumin nan sallama abinda ya kawoshi gareki ke
nan neman rayuwan inganci kada ki yarda a samu matsala a wajen ki Rahama.
Kin daiji abinda mama ke fada muna kullum kada mu yarda mazajen mu su kuka damu a zuciyarsu idan
muna son riban aure.
Maza tankar magene sunfi taushi a inda aka san darajansu ko mutuntasu bawai ladabi da biyayya kawai
ke kai mace da zama mowa ba sai mace ta iya kissa da na kwatar miji maza suna son haka kin dai gani
da Alan,guguro yadda sai nayi dakyat yake barin gidan nan mu din kada ki manta da rainon mamace fa.
Ya kama ace tun akan mama mun koyi rayuwa basai wani ya tsaya yi muna nasiha irin haka ba don
mama a gaban mu kike ganin yadda takeyi da daddy bata hada komai da daddy ba a duniyan nan.
Shiru nayi har ta gama ina saurarenta ni ina zan iya wanan abubuwan ga Jafar mutumin da ban wani
saba dashi ina ma nasan abinda yake so da wanda baiso ?.
Nikan dai ganinan zaki iya kirana da amaryan danko amaryan da aure yanzo mata kwatsam ba shiri
shine wai ake so kuma naje na ririta mijin a hakan ?
Kumshi ni kaina naji mamakin yadda kayan hadinshi ke kamshi kai mutanen maiduguri Allah ya hore
masu sanin sirin kamshi a rayuwansu.
Wallahi tun kamshi na damuna har nazo na saba don dole na wanka daban dana fito ga na tsuguni
yana jirana haka za a yafa min wani bakin zani na zauna sai na bushe a hakan.
Ina mikewa zata ban wanda zan fara murzawa a matse matse da kataruna hardasu hammata ni kaina
saida na koma kamar zanyi kuka wani lokaci har kai akwai wanda tsohuwar zata rufe iya kaina da kasko
tana turaramin kai in gajarce maki jin kaina nake kamar bani bace tundai da akai min gyaran kai din.
Inda sumana na fulan ya samu gyara yayi baki wulk dashi sai kamshi ke tashi ga wani kasala dana zauna
naji sanyi yanzune zan fara gyangyadi a wajen.
Zan iya cewa Alhamdullahi Alhamdullah gaskiya dan irin ni,iman da Allah yai min lokaci guda na fahinci
gaskiyan maganan da hausawa keyi na dare daya Allah kanyi bature wanan gaskiyane hakan.
Cikin dan taki ubangiji yai min wani irin baiwa da ban taba sanin ina dashi ba sai a wanan lokacin gidan
daddy na kwana ana gobe zamu tafi nan mukayi wani ganawan siri da mama da anty Salma mu biyu irin
abinda da suka fada min a ranan yasa na kwana gabana yana faduwa.
Washe gari da wuri muka dauki hanyan kaduna cikin tsalalun motocin gidan daddy dana mijin anty
Salma mota hudu mukai tafiya dasu zuwa gidan mahaifiyata kaduna.
Bisa rakiyan mama da yan uwa da abokan arziki data fadawa ni din yar dan uwansune daya rasu
yabarmu .
Manyan mata kanuri mazauna Abuja su shidda sai kawayen anty salma da ita kanta sune sukayi min
rakiya mun sauka a gidan ummah anyi walima .
Ni saida naji mamakin ummah ta waye ta zama yar kaduna a haraban gidansu akai walima ana gab da
tashi saiga dagin ango sun iso suna bada hakkurin makaran da sukayi din.
Wai ashe sai a na gobe yaya habu ya fada masu zancen tarewan wasu ma a ranan sukaji amma sunyi
kokarin zuwa din duk da saida akai dan rigima don mama ta hau kawu ya samu ya lalabata tabada bakin
azo din daga nan a dauki amarya.
Nafisa tace yanzu mama tana can ta hake sosai taga inda za a ajekine Rahama don basu san da zancen
gidan ki ba sai idan mun koma ko innata ban fadawa ba kinsan inna da surutu.
Nayi murmushin yake zakice ba wani abu mai muhinmanci muke tataunawa ba da ita a lokacin don ko
motsi banyi ba ina kallon yadda suka zuba min ido suna kallon sauyawata lokaci guda haka.
Anzo da Salima da Saratu da sauran yan uwansu da suke uba guda karfe hudu bayan anci ansha aka
dunguma zuwa zaria wajen kai amarya .
Koda muka isa direct family house dinsu muka nufa saisu mama muka sama a gidan duk da
gwargwado dangi sun dan taru lokacin.
Wai mama tana can gidan Iya ita da wasu na kusa da ita nayi mamakin ganin harda anty Barakan
zamfara ta samu zuwa bukin donni ban zata zasu yi hakan bama sai ina ganin komai makare akeyinsa ai.
Hjy Yabi yar uwa kuma kawa ga mama tace akwasa a sameta can gidan daga nan a ba uwargidayena
girman su kusan magariba muka kwasa zuwa gidan .
A falon iya aka taru aka shiga gaisawa mama tana kallon bazata ko hajiyoyin ai abin kallone da
kawayen salma.
Taji mamakin ganin Salma nayi min yare ina dan amsawa a cikin kanuri iya sai haba haba takeyi damu
tana kokarin ganin fuskana na boye.
Tace yar fillo wayau kikai min haka kika kwace min angona ko da ina da ja amma yanzu na sake ance
mai waje yazo mai aro ya tashi don haka nasake na barki da Jafar na kara noke kaina kasa cikin kunya.
Hjy Yabi take tambaya ina kishiyoyin nata suke sai matar kawu ke fadin suna bangarensu ya fada maku
inda za a sauke amaryan ?
Basu fahinci me take nufi da zancenta ba hakan yasa sukace a gidanta mana ko ko a wani wajen ake
fara sauka don su basu sani ba ko ana wani al,adane a nan ?
Au ashe ya fada maku inda zaku ajeta din ai shike nan idan mun tashi daga nan gidanta zamu wuce da
ita ai dama mama muka biyo nan din mu kawo mata amarya anty Salma ta fada.
Basu wani tsaya ba suka mike duk da lokacin sallah yayi muka kwasa zuwa part din uwayen gidan nawa
matan yaya jafar.
Da irin kudansu na kanuri mai kada zuciya ya yamutsa hankalin wanda akaiwa girshi muka nufi part din
matan yaya jafar din.
Zakice basu san da zancen ba suna falo dukkansu muka shigo ita Asmau wani rigar abayane a jikinta sai
ita saiba data saka wasu lace haka baki da adon golden jikinshi.
Asmau kan tayi muna sannu da zuwa amma ita saiba ko kallo bamu isheta ba ba wani dogon gaisuwa
hjy yabi ta fara fadin amaryace muka kawo kamar yadda al,ada yake .
Da fatan samun zaman lafiya a tsakanin ku kuyi hakkuri da junan ku a zauna lafiya kwarai kuwa inji
matar kawu ta dora da fadin amarya aiba bakuwarsu bace sun santa ta sansu.
Matar kawu karma tazo da zaman lafiya mana mune dai ba wasu ba ai ta san mu mun kuma santa sai a
dora inda aka tsaya.
Mikewa anty salma tayi tana fadin su tashi zuje kada dare yayi muna aka barta nan tare da wasu yan
gulma tana fada kamar karya.
Bamu koma dakin iya ba muka nufi wajen motocinsu muka shiga ni dai kaina na rufe gwaggo Yatu
najana duk abinda akeyi dai ina jinsune.
Muna zama motan naji an soma fadin wai dama basu sanda zancen gidan bane anty salma na fadin bar
yan iska idan basuyi hankali ba mace gidansu zata kwana ai wallahi.
Sai gudan su hjy yabi ke tashi da karan motoci muka bar gidan na sauke ajiyan zuciya ina dan bude
fuskana anty salma na fadin akara fesa turare wai zarni falon su Asmau keyi yasin da kyat idan batayi
amai ba lokacin.
Tare da matar kawu aka zo kawoni gidan dasu inna da anty Baraka basu jima ba suka tafi nan muka
samu su Salima da Nafisa da maria an kawo abinci da abinsha kala kala gidan don taron baki wanda
salima da Nafisa suka kai kwangilan dahuwan don fita kunya.
Hjy Dubu yaron yau kaji tsoronsa kinga gida hjy dubu gida ai iyakar Aljannan duniya ke nan wannan gida
ke kinga gida kuwa ?
Kai lalai dan yau ka barshi inda ka ganshi ni sai ince wanan abu an dade ana shiryashi mune dai aka
rufewa hakan.
Kya fada kema hafsatu aisu salima na can ana sakin hanci kiji wai kamshin yar nan har yanzu dakin
nan keyi don Allah kamar tana zaune wajen nan.
Ga dai magana nan yana fitowa fili shine za ace wai a kyaleshi kada ai magana kada zumunci ya lalace
zumunci ya dade bai lalace ba ya fito muna da hakkin mu ya bamu abin mu.
In ma ya kama a saida wanan kayan karyan da yayine a sayar abawa kowa hakkinsa mu rike abin mu ai
abin yayi yawa wallahi.
Barshi kawai dai Allah ya kawoshi lafiya ai yazo yai bayani zamuji mai zai fada iya dake addua ta shafa ta
juyo tana fadin.
Kaiya Hafsatu shi babba gyara aka sanshi dashi ba barna ba kina fadin zancen nan kawai don ki tunzara
yar uwar mijinki ta saba da danta.
Baki tunanen kema kin haifa ai hafasatu na rasa dalilin da yasa kuke son a tozarta yaron nan yau ko ace
yaron nan da dukiyan nan yayi auren nan aiba zakuyi masa haka a bainan jama,a ba dai.
Jidalin nan tun daren jiya kuna abu daya a kansa har mutanen nan sunzo sun tafi yanzu ko hakan da
kuka gani baku tunanen wani abu akan yaron nan Jafaru.
Kuna nan kun kasa kun tsare kuba zai zauna wa dan uwasa wajeba tunda kusan babu waje a
sashenshi ?
Amma ya gwatsale ku ya nuna maku shi dan yaune ya riga ya tanadi inda zaisa matarshi ko ya barku
nan zube da takaici.
Naso ace yadda kuka shirya mashi ya faru da sai ince ke hafsatu da mijin ki ku fita min a gidana shi jafar
ya gyara gidan su zauna sai Allah ya gyara hakan.
Iya saboda jafar sai ki kori su yaya gida iya waya saka yaje yai auren da zakice su tashi su bashi