Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
warewa
kowa nasa kaso a yanzu don ta kula Jafar ya salwantar da dukiyan nasu.
Bai tashi ganin sakon salima ba sai da dare bayan ya gama abinda yakeyi ya bude data yaga sakon
mutane lokacin ya kula da sakon kanwar tashi.
Ya bude yaga sakon muryane kusan guda hudu daya bayan daya yake bin sakon yana saurare a ranan
kasa barci yayi don zullumi da tunane.
Habu ya fara nema akan zancen ya nuna mashi yasan da zancen shima an fara a gabanshi amma ya
nuna rashin dacewan hakan sai aka baryi dashi.
Haba dai Habu shine ka kasa fada min komai a cikin lokaci tun tuni idan nasani da ban fitar da kudin nan
an raba a bawa kowa nasa ba ?
Yake tambayansa waya turo mashi wanan murmushi yayi shi habun yace salimace don ra,ayin mu daya
da ita tun a waje ta fada masu gaskiya abar nata a wajeka kome zakayi dasu kayi.
Sun dan jima suna zancen tun bayan kashe wayansa ya kira nura da yunusa abokansa da suke
kasuwance a asirce ya bukaci da su hada mashi kan kudin a waje daya.
Ya kuma kara umartan Nura da ya mayar da hankali wajen ginan daya saka suna gama waya ya kira
wani ya bashi cigiyan gida.
Allah sarki da ace mama tasan abinda ta haifa da bata yarda har kawu yayi amfani da damanta ya bata
wanan shawaran ba duk da bai kyautata zaton shawaran kawune shi kadai dole akwai wasu yan uwa
dake kwadayin dukiyansu a hannunsu.
A lokacin kuma ya kara yarda da maganan hardo kalai kawu ya dade yana bin duduniyarsu ba tare da
sanin hakan garesu ba duk da alama Habu yasan wani abu shikan dip yake banda kasuwanci baisa komai
a gabanshi ba.
Bayan kwana biyu ya bar kasan zuwa South Africa da niyar sati daya amma saida ya share sati ukku a
can wanan yasa mama dake ta neman layinsa dare da rana ta kasa samun shi .
Ta kira Habu shike fada masu baya kasan nan Saaratu ke fadin kin gani ko mama da kudin yake ta
facaka ya dauki yarinyar nan sun fita ke nan yawon amarci ya barmu nan ko Lagos bamu taba zuwa ba.
Shi kuma kawu cewa yayi dubu na fada maki yaron nan yana dawowa a kwace komai na hannusa a
rabawa yan uwa ko gida in bai tsira da komai ba dole ya sayarwa yan uwa da part dinshi a basu hakkin
su.
Mama da bata data cewa sai kara hasala da zancen ke sakata a kan danta takeyi haka yasa ido rufe
ranan data zo gidan ta shiga part din habu .
Yanda na kwance sai ganinta tayi ta mike tana gaida ita cikin rashin walwala take fadin yar uwarki tana
inane Maria ?
Ta dan sasauta murya tana fadin tana Abuja mama tace kira min ita yanzun nan a waya hakan yasa
yanda daga wayan takira layina na dauka na fara mata yarenmu na fullanci tace bani ita nan ta mika
mata wayan.
Naji muryanta a lokacin yasa tana karban wayan tace hello Rahama ina jafar yake ne ?
Na maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin mama bansan inda yake ba don rabona dashi tun dana
barshi gida nazo abuja ban kara ganinsa ba sai naji ta kashe wayan.
ZAINAB IDRIS MAKAWAMURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kwana biyu a cikin zazzabi na samu sauki har lokacin ina gidan mama saidai anty salma takan zo ta
dubani lokaci lokaci amma ba wanda ya kara min zancen auren Jafar dake kaina yanzu.
Saina dauki hakan da kila gwadani sukayi ko zan yarda da zancen amma ganin ban yarda ba yasa aka
fita zancen nasa.
Hakan ya bani karfin gwiwan sakin jiki da har na fara fitowa falo muna dan hira da mama satina daya
cur a gidan anty salma tazo a wani yammaci zata tafi na mike nima nace tare zamu tafi ai.
Ta juya ta dubi mama mama din tace kuje mana duk da daddy bayanan idan ya dawo zan fada mashi ta
koma gidan ki hakan yasa muka tattaro muka dawo gidan anty salma din.
Sai a ranan kuma ta ban wayana dake hannunta duk da ina son wayan a tare dani ganin bata ban ba
nima ban tambayeta ba saina share zancen wayar tawa din.
Sai gashi ta mika min abina ba tare da kona tambayeta din ba wayan da cajin shi full haka yasa na
kunna don a kashe take nayi tunanen mutane da yawa zasu nemeni sujita a kashe.
Data na kunna na aje saman gado inda sakonni suketa shigo min kai tsaye bandaki na shiga nayi alwala
don magariba daya kawo jiki idan na biyewa wayan za a samu matsala dani lokaci don shedan zai
rinjayeni in shagala da zancen sallah.
Na idar nayi addu a na shafa naji wayar tana sauti alaman kira yake shigo min lokacin na mika hannu
na duba anty Nafisa ce akan layin.
Ina dauka tayi sallama na amsa naji tana fadin haba matar yayana duk sallon amatcin ne haka ko waya
baki dagawa sai kinga dama halan angon ya fitane.
Ke kuma shike nan ko buki kinki fada muna muzo musha wallahi Ramaah ban zaci hakan daga gareki
ba sam na dauka kome ke nan nice ta farko da zaki fadawa ai.
Anty Nafisa ke nan nida ke kwance banda lafiya mezan fada maki satina daya ina gidan mama banda
lafiya wallahi sai yau na dawo gidan anty salma dazun nan taban wayan na kunna kece ta farkon kirana
yanzu.
Haka madam Maria ta fada min cewa baki da lafiya to yaya jikin naki nace da sauki anty Alhamdullahi
ya kuke ya su mama dasu inna ?
Lafiyansu kalau Ramaah ga inna ma tana gaidake da jiki sai naji taba inna wayan ta soma fadin halo
Rahama yaya jikin ya mutanen wajan ku ?
Lafiya kalau inna na fada take fadin to kiyi hakkuri da kaddara kinji auren jafar alherine a gareki in sha
Allahu ki fita zancen kowa ki kama mijin ki.
Kada ki damu da zancen su yaya Dubu duk bari zasuyi tunda mijin ki yana kaunan ki kowa tasa ta
fisheshi haka zaman gidan miji yake dama.
Kada ki kula kowa kiyi abinda zaki burge mijinki dashi Ramatu ita wanan da tayi yaji karma ki tsaya kula
ta ki zage ki nuna masu akwai banbanci a tsakanin ku.
Barta can ko Allah yayi dawowan ta gidan kada ki yarda ki biyewa shirmensu na rashin hankali kin daiga
yadda yar uwarki take dasu.
Jafar mutumin kirkine yasan ya kamata kwanciyan hankali da kulawa yake bukata in sha Allahu zaki
alfahari da hakan na gode inna na iya furtawa a cikin kyarmar murya.
Na sake jin tana fadin na fada maki ki fita zancen su yaya dubu da sukeyi na asiri kikaiwa Jafaru keda
yar uwarki har ya aureki.
Lokacin naji muryan Nafisa tana fadin nikan inna zaki cinye min kudin waya bamuyi magana ba ta
amshi wayanta badon inna ta gama zubanta ba.
Naji tace min Ramaah to yaya jikin naki nace lafiya kalau anty Nafisa ta sake fadan yaushene tarewan
naki koda yake ai kamar ba yanzu ba ko don ance yaya baya Nageria ya tafi kasan waje.
Wallahi ban sani ba na fada maki ai dazun nan na dawo gidan anty sallma bansam komai a kai da suke
shiryawa ba.
To bari na barki saina sake kira mukayi sallama ta barni da waya a hannu ina mamaki a raina nace
watau zancen auren dai yana nan a kaina ke nan ?
Ni Rahama yaya zan iya rayuwa da yaya Jafar a matsayin mijina da fitinan gidansa ta ina zam soma
wanan badakal auren da ya hau kaina yanzu kuma ?
Har nayi sallah isha,i na koma saman gado na kwanta maganganun inna kemin yawa a kai na kasa
hadasu a waje daya.
Ni Rahama nice zanwa yaya Jafar asiri don ya soni ba yaya Jafar mai mata ba ko wani irin namiji ba zan
iyawa a siri don na mallakeshi ba a ina ma zan samo asirin da zan masa din ?
Zancen maganin na dashi ya fado min a rai gabana naji ya fadi na furta na shiga ukku shiyasa taimako
yake da wuya a zamanin nan.
Ko dai sun dauka maganin na asirine da zaisa ya soni nayi mashi a lokacin harwa yasan da zance haka
banda nafisa da ya habu sai shi jafar din.
Shigowan anty Salma ya katse min tunanane ta shigo tana fadin ke abinci fa bakya jin yunwa ne kika
kwanta ,?
A hankali na dago idona da sukai ja duk da ba kuka nayi ba a lokacin amma bacin rai yasa idanuwana
sun sauya min lokaci guda ba yadda na dawo daga gidan mama ba.
Meya faru kuma take tambayana muryan can kasan makoshi nake fadin ba komai anty tace ok ga
abinciki nan nace jummai ta sako maki a kawo maki nan baki jin dadi ba lalai bane ki fito.
Allah sarki anty salma ba abinda ya dameta ita hankalin ta kwance komai nata cikin gata ba
tsamgwaman rayuwa nake fada a kasan zuciyana sai naji tace ke Ramaah ?
Jafar din nan naki wani irin mutum ne shi gaskiya mutumin arzikine sosai wallahi a cikin matansa akwai
mai cikine ashe ?
Kai na gyada bata jira cewata ba taci gaba da fadin dazun nan ya turo min da kudi da za aiwa mai jego
da jariri sayaya har daku daba haihuwan kukayu ba bayan lefe da na tausan gaba daya saka aka hada
mashi.
In wanine yana zancen aure a gabanshi aiba zai tsaya tuna hakan ba har ya tsaya hada kayan haihuwa
kan wa yan nan yan iskan matan nasa.
Ni wallahi Ramaah tun bangasu ba bakiji yadda na tsani halaiyansu ba haka kawai su hana bawan Allah
shakat a rayuwansa don iskanci da samun waje wai meyasa matan hausawa akasarinsu suke hakane ?
Naji ance wai ita dayan matar nasa tayi yaji tana gidansu tun ranan da taji zancen auren shi kuma yace
a barta can ba inda zaije tunda bashi ya turata ba.
Kala bance da ita ba akan zancen har jummai tashigo tana jera min abincin ta gaidani da jiki ta fice a
dakin kallona tayi tana fadin ki tashi kici abinci kisha maganin ki.
Kada mijinki ya dawo ya samu kin fada yace amanan daya ban ke nan na bari kika koma haka nidai
banyi magana ba ta kare ta fita tana jaddada min da inci abinci fa.
Sannu a hankali cikin hiran anty Salma nake ta tsuntar magana wai ashe har kudi yaya Jafar ya bayar a
saya min wasu abubuwan da nake bukata.
Saidai tace kudin suna hannuta don ita dasu mama sun hada min kayan daki komai daddy yaba da kudi
a saya min gwargwadon hali ta kara ta sai min moderate din kayan kitchen na zamani dasu.
Da anty Salma tasan zancen aurena akan jafar yana daga min hankalu da sam zata dingayi min zancen
ba amma bamu zama bata sako min zancen shi a gabana duk dade gyarane irin ta yayyu take min a
lokacin.
Ina kuma karuwa sosai ga wasu abu da take ban duk da tare muke faman dirka da ita wani lokaci kuma
ni kadai zata ba in shanye tas a gabanta.
Training din rayuwan gidan miji aiko zama tsakanin mama da daddy dole kayi course sun tsufa amma
rayuwansu zakice yarane har yanzu su balle anty salma dake cikin ganuwan kurciya a lokacin tana
shanawa da mijinta.
A cikin hakan muna waya da yar uwata har da mama saidai suyi ta kwantar min da hankali sam ban
tsamaci hakan ga yar uwata ba na dauka zata shiga damuwa fiye dani sai gashi naga akasin hakan gareta.
Ranan da mama ta kirani tana tambayana jafar ta kashe wayan ta barni da mamakin ta don dai ban
taba tsamanin hakan wajenta ba yadda takeyi min maganan .
Itace fa mai min addua Rahama Allah ya baki miji nagari inda zaki huta kema sai gashi a yanzu lokaci
daya ta sauya min.
Yandace ta kirani take fada min abinda ya faru har mama din tazo ta karbi wayan wai suna tuhuma
Jafar ya daukeni ne mun fita tare dashi shine yasa tazo ta tabbatar da hakan a kaina.
Bayan ta tambayi Nafisa tace da ita muna waya ina Abuja har yanzu amma hakan baisa ta yarda ba a
yadda nake ji a bakin anty salma zancen tarewana wani satine insha Allah.
Hakan ya kara saukar min da faduwan gaba ta ina zan fara ina zan kama yaya zanyi in zauna wanan gida
da sunan auren jafar a kaina.
Har wata zuciya tana ban shawara da ingudu in koma garin mu sai na tuna ai can aka daura min auren
alkakan a kaina dole dai na tsurawa sarautan Allah ido.
Sunje Zaria kwana su daya suka dawo saidai kaduna tace min zata ashe zaria sukaje gyara min daki
saida ta dawo tana santin gidan take fada min ai sunje sun yimin jerene a zaria .
Gaskiya Rahama kinyi sa,a sosai gidan ki ke kadai ba wani hayaniya ko saka idon da wani zai maki irin ta
maria ke kadaice a babban gidan saidai gaskiya gidan nada girma sosai.
Mun samu ya gyara gidan ya saka komai amma muka saka kayanshi a falonshi Kayanki da akai maki nan
muka gyara maki naki falon hakama daki biyu muka gyara maki sai muka bar wancan a matsayin turakan
maigida.
Ni ba tsayawa saurarenta nakeyi ba ba don duk abinda zata fada ba burgeni yakeyi ba saukinsa ma
yanzu da naji cewa ba a gida daya zan zauna da matansa ba .
Sai abin ya dan min dadi a raina koba komai wanan zullumin da fargaba zai rage min akan ace muna
zaune waje daya dasu.
Nasamu training fiye da zaton ki mai karatu dan zaman da nayi da anty salma ta bude min ido ta wayar
dani banda tsoro ko fargaba a baya har ina jin idan na koma zaria zamu kwashi yan kallo dasu.
Sai gashi zancen auren nan na yaya Jafar a kaina yanzu ya jawo min cikas ga duk plan dina nima yanzu
dole ta kaina nakeyi yadda zan kasance dasu .
Balle nace zan taya yar uwata danayi niyar tayata zama da fitinansu yanzu kam nasan a kaina abin zai
dawo gaba daya tunda dole in zauna kamar yadda daddy da mama suka roka a gareni.
Shi kishi ko zaman aure ga ya mace halittane garemu mata wanda bamu san muna da baiwanshi ba sai
in mun gwada.
Haka kawai mace ke tsuntar kanta da iya irin rayuwan data zabawa kanta zatayi dma gidan miji don
haka a bangarena idan na zauna ni kadai abinda nake tunane shine ta ina zan fara a gidan ?
Da bangaren shi yaya Jafarne ko bangaren matanshi ko kuma bangaren mama da yaranta duk da nasan
banda matsala dasu saida Saare amma yadda anty Nafisa ke fada min a yanzu mama ta canza sosai game
dani.
Nikan an sakani cikin tsaka mai wuya a wanan auren an tauye min rayuwata da yawa me zangane a
wanan gida hakan ya zamo sonkai ga yaya Jafar duk da bansan ainihin manufanshi na zarga min abinda
bai shafeni ba.
KD
Cikinta mahaifiyarta tayi da fada akan ta shirya ta dawo dakinta kafin tayiwa kanta aikin dana sani haka
kawai zaki kwaso kafa kin dawo gida kin zauna don mijinki kawai ya kara aure ?
Har uwar ta gama batace kalla ba don sai take daukan uwar bata damu da itaba yasa a kullum take
nuna mata ta saita koma haka zikau ba wani magana akan shanmatan sa Jafar din yai mata.
Saidai Halisa yarta ta shigone suka kebe tana fada mata irin matsin da uwarsu ke mata akan ta koma
zaria din .
Yaya takan fara magananta ke nan fa don me zaki koma zaria Jafar baizo ba ita bata tsayawa ta
kwatowa mutum hakkinsa idan kuma za a kwato mashi ta hana,.
Yanzu dai muje gidan anty Sabi,a muji kota samu aika sakon don nafi bukatan sai kin rikeshi zaki koma
har in zaki koma din ne yar ta fada hakan yasa Nusaiba ta mike ta shirya suka fita ita da yar uwarta.
Da kafa suka taka zuwa unguwar don ba nisa gidan Sabi,a din da alaman matar gidan tana da baki don
motar da suka gani a kofan gidan.
Sun shiga da sallama suna falo zaune suke amsa masu an fara gaisawa bakuwar Sabi,a ke fadin waiba
Saiba umar bace ?
Nice ta fada tana kallon mai maganan kafin tace sa,ade yakubu ko suka kwashe da dariya son tun
barinsu makaranta rabon da su hadu don haka da murna suka rungume juna.
Saiba ta kalli Sa,adatu tana fadin wai Sa,ade kece haka kinyi wani fresh dake kamar wata matar
gwauna ?
Murmushi wace aka kira din tayi tana fadin kaji ki dai da wani zance Nusaiba har yanzu dai halinki yana
nan na zolaya ko ?
Wallahi kina inane wai yanzu nusaiba ta kara tambayanta tace ina nan gefe daya ba kun manta da
kowa ba yanzu haba dai ai kema kinsan hakan bai yuyuwa nakan tambayeki wallahi.
Har yanzu kuna tare da mustapha ko haba dai daram kuwa muna calarba yanzu kinsan a can yake
aikinsa .
Kice min mutumiyar kinyi nisa da garin nan gaskiya na daina jin ki gaba daya wallahi lalai mustapha ya
iya rikon aure kinga yadda kika koma wata babban mace ?
Gaskiya da ganin ki kin samu kan mustaphan nan a hannu Sa,ade murmushin kasaita tayi tana fadin
Saiba ke nan wani samunshi nayi kuma ?
Takai zaune a gefenta tana fadin wallahi sa,ade kin kara hadewa ba irin mu ba nan ni gani wanan dan
iskan zai kasheni wai wata kishiyar kuma ya kara auro muna yanzu .
Cikin mamaki Sa,ade take kallonta tace saiba kanki daya kuwa da hankalinki kuwa ?
Mijin naki kike zagi da dan iska meye