Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ina ruwanki
da kawoshi yanzu ki daina bana so don Allah.
Shiru falon yayi na dan lokaci sai can iyan ke fadin kinji tarbiyan kwarai haka ake son ya kasance
kanayi kana kwabon bakin yaro ko yaushe baka kyale yaro na tsoma baki a zancen manya ba shine
matsalan dake damun uwarku.
Kada ki kara bayan haka duk uwa tace bata kwaba yaro duk abinda ya fada shine daidai a wajenta to
itako da zaman lafiya sunyi ban hannun makafi ke nan.
Ki bari gaskiya ta fada maki ko ita da zancen ya shafa inkin kula bata fadan kallal kahu a ciki idan anayi
don haka kada ki kara kinji.
Iya idan na kyaleta watarana a kaina zatayi kuma ta dauka ai hakan daidaine ban taba zama dake ba
habiba ina maki zancen wata a gidan don haka ki daina don Allah hakan ba halin kwarai bane kinji.
Bazan karaba anty ko yanzu ma subutan bakine mamanmu ta kwabeni da hakan kullum naje kuma sai
tayi min fadan hakan ta fada a dan maraice.
Saida mukaci muka sha donshi bai tsaya yaci abin kwarai ba na kwashe kayan tare da biba kafin mu fito
iyan ta shiga dakinta na leka ina fadin har zata kwanta ke nan ?
Tace meya rage min kuma yar nan baku barni da komai ba sai godiya ga Allah Allah dai ya tashe mu
lafiya kuma ya karawa mai nemowa dake mai dafawa lafiya na amsa da amin na kalli biba ina fadin saura
ki kwanta da kayan nan baki sauya ba don har yanzu kina da matsalan haka biba kije ki watsa ruwa kiji
dadin kwanciya don Allah.
Akwance na sameshi yayi shiru jin motsina ya kalloni na karaso ina fadin a hadoma ruwan shayine naga
bakaci komai ba kai ?
Naci abinci da habu a wajenshi ya dawo da yamman nan anfito da abinci ya matsa sai naci shiyasa
banjin yunwa.
Ashe ya dawo ke nan yace ya dawo dazun ashe maria din bata jin dadin jikinta shine ya dawo da sauri
nace bata fada min ba kuma munyi waya da yamman nan tana fada min zancen haihuwan yar mijin
ummah a kaduna.
Ta boye makine gobe sai ki shiga ki dubata idan zaki dawo school amma taji sauki don naga tana aiki
da kanta ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[3/17, 11:45 PM] Zainab Idris Makawa Writer: Follow this link to join my
WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu
Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Rayuwa kenan haka take tafiya da dadi ba dadi ga dan adam amma idan ka saka hakkuri ka dauki komai
a saukake sai Allah ubangiji yasa abubuwa su dinga zuwama a cikin sauki ta yaddama baka zata ba.
Haka shima rayuwan aure ya kumsa garemu mata idan kina tausan zuciyarki akan kishi zakiga
abubuwan suna zo maki a cikin sauki matuka zaki daure ki ba komai baya ki dauka a ranki cewa aure
bautan ubangijine a gareki.
Hakan ya kasance a rayuwan auren dana tsunci kaina a cikinsa na yaya Jafar auren da bantaba zato ba
ko tsamani nasa akaina.
Haka kuma nake daurewa da duk wani abinda zasuyi min dashi da matanshi ina nuna ba komai bane
hakan a wajena.
Idan yazo wajena mijina idan ya koma gidan matansa kuma mijinsune ban damu da irin rayuwan da
sukeyi a can ba dasu din zan kawar da kaina ba tare da son sanin yaya yake ciki dasu ba can ?
Duk da yan tsegumin da nakan tsunta nasu abakunan dangin miji cikin zance hakan ban yarda na
sakawa zuciyana damuwa akansu ba.
Bazance bamu haduwa ba mukan hadu can ba a rasa ba don ina zuwa ganin yar uwata a gidan kuma
saiba bata daina kawo muna hari ba da sunan kishi.
Balle yadda na dauki lokaci ban samu ciki ba shima wanan din ya zamo kamar abin gorine a wajenta
don takan sakar min magana a kansa wani lokaci.
Yau,ma daga school nan na nufo don in duba yar uwata dake fama da laulayin ciki a cikin yan kwanakin
wanda hakan ya zamo mata dabi,an da zaran ta samu ciki babu zaman lafiya a rayuwanta ke nan.
Don ko yanzu likita yace dole sai tayi zaman asibiti irin wancan din da tayi a baya donshine nazo gidan
muyi shawara da ita don ni ta fara nema da zancen hankali tashe.
Yunwar dake cina yasa ina shiga na fara neman abinda zan aikawa cikina agaji dashi tace na duba
fridge dinsu ko zan samu abinda zanci a ciki .
Yoghout din Rufaida na dauko da cake na dawo saman kujera na zauna na bude ke nan yaran su saiba
din suka shigo part din.
Sun biyo dan wajen Yanda suna wasa ba zance yaran basu sanni ba saidai babu sabone yanzu sosai
tsakanina dasu kamar da amma don sani sun sanni ai.
Haka kuma kowa yasan yaro da daukan ido idan yaga wani abinci a hannun wani hakan yasa na rasa
yadda zanyi saboda idon da suka zuba min din ga Rufaidan dake hannuna ina sha.
Banda kyakyamin yara donshi nake diba ina basu a baki wanda hakan yayi daidai da shigowan Saratu
part din tazo amsan hairdryer a wajen yar uwata din.
Haka kuma bata sanda na shigo gidan ba sai a lokacin don banshiga wajensu ba tukunna na nufo wajen
yar uwata din.
Har ta karba zata fita sai kuma ta dawo baya tana fadin jimun yan iskan yara da saka idon tsiya me
kuka rasa a wajenku da zaku dawo nan ku rufawa wanan abin ido haka ?
Tsawa tayiwa yaran suka fice a cikin kuka nace da kin barsu ai munsha tare aini na basu bata ko tsaya
kallona ba ta fita a fusace ta tasa yaran gaba.
Sai bayan sun fita naji maria tana fadin yanzu wanan abin ya isa uwayensu jidali bansan meyasa saratu
take halin nan ba ko shigowa yaran nan sukayi sai tayi masu jan ido akan su fita zakice ina masu wani
mugun abune a nan.
Kyaleta kawai neman maganane irin nata idan da sabo ai yaci ki saba da halinta bata so a zauna lafiya
ita ko kadan dama.
Na mikawa Abbanta roban gaba daya na gyara zama ina fadin yanzu yanda dolene sai asibiti zaki
zauna ?
Ba zaki zauna gida a dauko maki wace zata kula dake ba ninaga kamar hakan zaifi sauki da zaman
asibitin nan tunda kinga dole wancan karon ummah ta zauna dake yanzu ko ummah tana da aure.
Idan ance tazo ta zauna akwai takura acikin hakan yana da wuya mijin nan nata ya yarda da hakan
gaskiya.
Tace Ramaah abinda nake tunane ke nan mama dai yanzu kinsa ba dadi a tsakanin mu don tunda ta
kula da cikina samu nake wanan wahala naji tana fadin.
Ai hakan ya zama takura ace duk ciki sai an wahala dama abinda akewa yaran nan gudu kenan kaje ka
daukowa kanka wahala yanzu gashi abu ya zamo fitina wa zai iya wanan wahala ace duk ciki sai mace
taje tayi kwance ta mike kafa asibiti.
Dama ai kinsan zata fadi har abinda yafi hakan ai tunda ba yan sonta bane sukayi hakan kofan da aka
turo a fusace yasa duk muka juya lokaci guda.
Ita kanta a yadda ta shigo din ta samemu saida ta raina kanta don jikinta saye yake da wani dogon riga
na atamfa baki daya kode.
Roban youghot din dake hannun Abba yana sha ta kalla ta soma fadin ai dama nasani akan wanan
tarkacen kwadayin zaki mayar muna da yara kamar marasa galihu ?
Haba dai anty Saiba meya kawo wanan maganan kuma anty Maria ta fada cikin tsawa take fadin don
Allah rufa min baki kinji malama.
Shi Rufaida din inba abin yaro ba nawa suka sha da zasuzo nan ana yan masu a hannu kamar wasu
almajirai dasu ?
Ku ya zamawa bakon abu har kuke kwadayinsa koda yake ba abin mamaki bane don ba asaba ganin
hakan ba sai a nan din ake samu kuma dai kudin ubansune dai ake ci ko saukin abin ke nan dai daga yau
bance wata ta kula yata ba balle a bata wani mugun abinda za a sabauta min ya in rasa gane kanta yadda
akaiwa ubansu.
Wanan kuma ke kika sansa ai don bamu gaji mugun abuba balle muyiwa yarki don baki tsarewa kowa
komai ba balle yarki
To mara kunya nasan idan ita bata tanka ba dama ke zaki tanka ai nace kwarai tunda ba tsoronki nakeji
ba kuwa baki da wuta baki da aljannan sakani akan me zanji tsoronki Saiba ?
Kazan uba nice ma Saiba haka gatsau a bakinki nace kina da wani suna da yafi hakan ne a bakin mutane
Nusaiba.
Na fahinci sanyin da yar uwata keyi masu ya jawo raini a tsakaninsu tun ina gidan wanan yasa a
yanzuma nake son in kakabe hakan a tsakanin mu tun a yanzu din.
Idonta ya fifito na masifa ta soma jefa muna zagi na wullakanci ina rama abinda take fada min din cikin
hikima da nasa mata bakin ciki a rayuwanta dama ance magana zaran bunu.
Nasam karshe tace zata dora min hannu a jikina don haka takewa kishiyarta a baya nasani kuma hakan
yasa tunda naga tana nufoni na mike tsaye cikin masifa nima ina jiran karasowanta a kaina.
Sai fadi take yau zan murji rashin kunyar nan taki da kyau dana jima ina jiran wanan ranan zan gwada
maki nafiki iskanci ke karamar yarinyace wallahi .
Yariya ai tana bayan uwarta kin sani nikan ai daidai nake dake saiba kafin hannunta ya sauka jikina don
yanda data shiga tsakanin mu hakan yaban daman samun shammatarta nakai mata wawan mari a
tsakiyar fuska tauuuu.
Saida ta duka kasa kokarin kare yar uwata don kada mu illantata nayi nakai gareta muka hade ana
gwadawa yar filo mai kiwo a daji kokawa ?
Ai kunya garemu badai tsoro ba sai gashi Allah yaban sa,a na dagata sama na zuba saman kujera nabi
na danneta ina aikawa fuskanta naushi a iya karfina da bansan na saura dashi ba har lokacin .
Ihun yanda ya fito da mutanen gidan mama a rude babu kallani akanta tana rige rige da yayanta suka
nufo part din cikin tashin hankali.
Salimace ta soma fadin ayya girma ya fadi ke Rahama daga mata hakana don Allah garin yaya haka ya
faru kuma yaushe kika shigo gidan nan ma inji mama ?
Jin abinda suke fadi din yasa na daga akanta ga idanuwanta sun firfito waje tana haki ta soma fadin
wallahi ba zan yarda ba yau gidan nan za ayi bala,in da ba a taba yiba kuwa kun tarar min ke nan ?
Da keda yar uwarki ko nace kunji munafuka har me za a tarwa anan mace haka kamar faifai ba nauyin
komai nidai din da kikace zaki murza na murjeki son raina yau din.
Tayi kukan kura akaina tana fadin wallahi baki isa ba kizo har gidan nan kice zakiyi min haka karyane
wallahi na tattare bujena zuwa gwiwa don kada ya takura min nako here hannuna nakai mata wani
naushi sai a gefen fuska duk suka jaye baya dama salima da Asmauce ke rikeni mu din don sunfi kusa
damu.
Na kara samun sa,anta na taushe a kasa amma wanan ai zaluncine ku dagata mana tunda kunga bata
in mata kun tsaya kuna lallonsu kuma tana dukanta ?
Saarece ke fadan hakan cikin hasala tayi kaina wai zata dagani jinta kasa yasa ta kai min duka nako juyo
na aza mata duka iya karfina saida ta saka ihu tana fadin kika dukeni Rahama ?
Keda kika dukeni fa ina can ina bata amsa ta samu sa,ana ta kai min cizo a hannu tana dagowa na
koma na kaimata shaka a makogoranta ta soma kakarin kamar zata shude.
Haka na zama masu yar daban gaske a gidan inkaiwa saratu duka inkaiwa saiba maria ta dora hannu
akai tana kuka duk da suma suna dukan nawa amma Allah bai basu sa,ata ba yadda suke so don na
fitarwa kowa da jini .
Saida kyat mama da su salima suka samu rabamu fadan salima ke fadin an daiji kunya yau tunda har
kuka tararwa mutum daya ke Saare meya kaiki shiga fadan su don Allah ?
Ke rufa mana baki mama ta fada a cikin tsawa tana fadin mara zuciya kawai da iya fadan tsiya ki tsaya
kina kallo kin kasa rabasu daga rabon fada zata hau yar uwarki da duka haka kina tsaye ?
To mama so kike mu zama daya meyasa takai mata duka haka ake raba fada kakaiwa mutum duka
muko muna can muna aikawa juna zagi na tashin hankali ido a rufe duk a gabab mama din data kasa
komai .
Sai ranan na fahinci waye mama da kyat suka samu na fito daga part din cikin masifa don banson na bar
gidan su mayar da abin akan yar uwata dake fama da kanta aiki daba kan ranan sungashi wajena don
ban raga masu ba.
Asmau tazo har inda nake tana fadin kizo ki bar gidan nan don Allah don in baki tafi ba fadan nan ba
karewa zaiyi ba wallahi.
Na budawa idona yaji nace ba inda zan tafi saina tashi so nake tazo ta murjeni kamar filawan datace an
fada mata shiru shiru tsorone dama niba maria bace da take kyalesu duk wanda yai min zan mashi nima
ban kaunar a zauna lafiya din.
Kawune ya soma zuwa cikin wanda mama ta kira tun a get ya soma fadin asshaaa subahanallahi garin
yaya haka ya faru kuma ke dubu ?
To kadai gani ace yarinyar nan ta biyosu da masifa har gida irin haka don ta rainawa mutane wayau
komai ?
A,a mama inda ita ta biyosu ai part din mu zata nufa ko amma a wajen yar uwarta fa ta sameta saida
nace kada Saiba ta fito don Rahama taba yaran nan abu shine wani abu don Allah ai,,,,,,,
Kaji munafunci ko zaki juya zancen yanzu Saiba datace taje ta shirya tafito da wani bakin dogon wando
da t,shirt ajikinta take fada ta nufoni kawu yana mata tsawa.
A lokacin kuma motan su yaya ibrahim ya tsaya suka shigo gidan ankira mazajen mu an fada masu
abinda ke faru shine yace yan uwansa din suzo gidan.
Tare dasu na koma gida inda suka jawa kowa kunne kan duk wanda ya kara tayar da zancen wallahi su
zasu dauki mataki mumuna akan mutum.
Jin hakan yasa na yarda na bisu badon naso barin yar uwata ba da naga suna da niyar illanta muna ita
haka kuma mijinta dake kusa ya kamo hanya zuwa zaria hankali a tashe kar wani abu ya samu matarshi
din.
Gaba dayan su na barsu da tabona a jikinsu zakice ko wani abu na samu nayi masu illa haka dashi duko
hannunane yayi masu wanan aikin haka ?
Ana gwadawa bafulatani hanyar keta muda in muje daji muke gwada karfin mu da juna don gudun ta
taso a garemu .
Kodana koma gida daki nashiga bance da iya komai ba jin hannuna yana son takura min da tsami yasa
na gasa jikina da ruwan dumi na shafa rob na sauya tufafina wajajen karfe biyar na fito falon.
A lokacin kuma kawu ya shigo gidan shida mama sukayi sallama sai lokacin iya kejin abinda ya faru a
bakinsu don irin fadan da mama din take min akan me zan hada har saratu don tana rabamu ?
Dakata Dubu ban fa fahinciki ba shin da saratu akai fadan nan koda yar nan Nusaiba don zancenki yana
nuna da mutum biyu akai fadan nan haka ?
Iya dasu biyun nefa duka tayi fada haka daga maganar fatan baki zaki dinga kai masu duka kamar kina
jirace dasu dama ?
Kaiya iyan ta fada ta kara fadin nace kaiya dubu ina hankalinki ya shigane wai har hakan yakai ga
faruwa ?
Ba yau ba kinsan halin yaran nan haka suke wanan dabi,an takaiwa yar uwarta duka daga magana
kadan sai duka ita saratu ya akayi ta shiga zancen shine ban gane ba ?
Wai rabasu takeyi shine kawai ta,,,, dakata muji daga bakinta ai tana da hujjan yin hakan tunda ba
hauka tayi ba ko ?
Jin abinda iya ta fada yasa na soma magana banji nauyi ko tsoron idon mama ba don zuciyana daya
bushe a lokacin komai zai faru ya faru shike nan nace.
Ina school Maria ta kirani tana fada min zancen rashin lafiyanta shine na kira yaya nace zanje na ganta
dana isa ina jin yunwa na dauki youghout ina sha nan dai na fada masu komai tas har dukan da saratu
din takai min.
Kaiya iyan ta fada a hasale ta kara da kin min daidai gobe ta koma in halintane tunda bata da mutunci
ita a fakaice ta shigarwa masoyiyarta fadan ko saita hadu da fulani sukai mata maigaba daya.
Ta dauka ta hada fada zataci bulus ko tunda ta zata irin sakarancan ne da suka saba tauyewa su
zalunceta tayi ta kuka ana dariya gobe su kara in halinsune iyan ta fada.
Amma iya wanan abu yayi yawa ta yaya zata bisu har gida tayi masu wanan aikin kamar an turota tayi
masu hakan sai iya ta dubi mama tace kila nice na turata tayi masu hakan ko ?
Bakiji kunyar wanko kafa zuwa gidan nan kina wanan maganan ba dubu aure fa ba bauta bane dubu
duk abinda ya faru dama an shirya a tozarta yarinyar nan ne sai Allahnta yafi nasu ya dorata kansu duka
shine kuma yanzu don an daki yarki data saya aka sayar mata kikazo fadan haka ?
To ki bari mijinta ya dawo dubu sai kisa a ranan ya saketa ina shike nan tunda kina da power hakan a
hannun ki idan bashi ba wanan abin kunyan ina na taba jin haka ?
Fada ya hadata da abokiyar zamarta yarki ta shiga ta saya an mata dukan tsiya yanzu kinji haushin
hakan tunda ba ita bace aka samu sa,anta akaiwa hakan ?
Iya na