Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
an karbe wayan ne don yadda yake tunanen suna cikin
matsi akan hakan.
Dafashi sanusi yayi yana fadin lafiya kake kuwa abokina naga kamar kana cikin damuwa niko naso na
gama baka labari in fada ma riban da aka samu bayan tafiyan ka.
Barshi kawai zuwa gobe idan nashigo ya fada ya juya ya soma tafiya hankali tashe har lokacin yana
gwada sa,anshi ga kira ko zai shiga.
Garba sadauki garba gagare Abubakar mazan fama irin ku biyu ke gyara gari kwana biyu ashe ka dawo
daga tafiyan ?
Kai ya daga a hankali ya kurawa matar ido yana son tuno ta kwalan kanta yasa yayi saurin ganeta ita
matar ranan da sukai tafiya data shiga da maciji gidansu.
Fuska ya tsuke a waje daya sai dai duk da hakan saida yaji kawai ya gaida ita don baisan wacece ita din
ba da take faman bibiyan shi tambayan daya fara yiwa kansa kenan a zuciyarsa.
Baabba ina wuni ya fada sai tayi murmushi tace dashi kada kaga na kulama yarona akwai abinda nake
son ka sani game da rayuwanku na fadama ka fada wa mahaifiyarku inda nake ko baka fada bane yasa
bata zo ba ?
Yanzu haka naga hankalin ka a tashe yake don baka samu mutumiyar ka bako kada ka damu zuwa
yamma insha Allahu ka gwada zaka sameta.
Saidai ka kula da amana taraiyanku akwai nasara don kusan ince ka tsira daga sherin magautanka
habu.
Saidai yan uwanka amma a gaskiya in mahaifiyar ku batayi da gaske ba za,a dukar daku gaba dayan ku .
Ka maida hankali akwai alheri da nasara daga wanan yarinyar daka hadu da ita acan saidai iyayyenta
mutanen banzane shine kadai matsalan da zaka dan fuskanta.
Habu yau fiye da sati fa ina cigiyan ka garin nan muryan Sabi,une abokin shi yake fadan hakan ya juya
yana cewa sabi,u yaya nima ai naso ganin ka sai na danyi tafiya ina zuwa ya fada ya juya girin wanan
matar don yace yagode.
Saidai wayau baiga kowa a wajen ba cikon mamaki ya juyo ga abokin nasa sabi,u yana fadin ina wanan
matar tabine sabi,u ?
Wace mata ke nan fa sabi,un ya tambaya matar daka samemu mana magana a nan mana naga kamar
nan tabi ya fada suka juya gaba dayansu har sabi,un suna kallon hanyar cike da mamakin ta.
Ikon Allah kasantane ya girgiza kai alaman a,a amma dai ranan tashiga gidan mu anan taji sunana ta
rike sai ya canza topic din don ba zaiso ya matsa mai da tambayan daya fara ba yasan halinsa bakinsa
baida sirin rike magana.
Yanzune ma zai iya juya zaicen zuwa wani tsiga ta daban ya dauko mashi zancen magana da soka soma
dashi a ranan zasu hada kudi su sayi wani shago anan cikin unguwa suba da haya.
Ire iren hakan yanayi sosai da abokansa na kut da kut dama yan zaria basu da wasa wajen sana,a rigima
da naci kawai kanawa suka fisu 😍.
Har suka rabu da Sabi,u a wajen sallah yana tunanen zancensu da wanan matar dake yawo da kwalla
tana tallan maciji a cewarshi.
Saidai abinda ya daure masa kai shine zancen data soma ta katse ta yaya tasan cewa yana gwada kiran
layin Yanda tun safe bai samu ba.
Gabanshine ya fadi lokaci guda wanan wata irin matace take kokarin bibiyan rayuwatane wai meyasa
ta lake min hakane ?
A iya tunanesa baiga alaman tana nemam wani abu a wajensa ba tunda bata tsaya karban komai
garesa ba yauma amma kuma me take son fadawa mamane wai ?
Data matsa tana son yin magana da mama me zata fadawa mama din akan shi shirme ya dauki zancen
da sallon yaudara irin na mutane.
Wata zuciyace ta bashi shawara ya gwada abinda tace mana ya gani idan hakan gaskiya har yakira
yanda ya sameta da yamma to akwai kamshin gaskiya a cikin zancen ta ke nan yake fadawa kansa.
Zama ya gyara yana fadin abu sai kace almara meye hadina da wanan matar da take son shiga min
rayuwa ya akayi tasan dana hadu da Yanda ?
Gaskiya dole ya sanarwa mama barazsn matar nan a kanshi kada sai abu yazo ya faru dashi ba yadda za
ayi a lokacin yace zai sanar da ita daga baya.
Anan cikin unguwar yai sallah magariba da isha,i yana fitowa kuma suka dauki hanya da sanusi daketa
kokarin masa bayani kan shagon nasu na saida waya da kayan wayoyi din wanda ba kowane yasan da
kudin habu a cikon shagon nan ba sai iyayyensu kadai suka sanda wanan.
Kusan lokaci guda suka iso gida da yayansa do zakice tafiyarsu gudane yadda suka shigo din shi jafar
part dinsa ya nufa shi kuma habu ya tsaya nan jikin motar yayansa yana gwada kiran layin Yanda da son
ya kure karyan wanan matar don ya samu madugaran yi mata kashedi akansa.
Ga mamakinsa yana kira kiran ya shiga mamakine karara a fuskanshi yaji ta dauka tana sallama da
muryantan nan mai nuna sanyi hali irin nata.
Kamar kullan yadda take fadan amincin Allah ya tabbata a gareka hakane ko lokacin ta fada gareshi a
cikin sanyin murya daya sakashi cikin wani irin yanayi shauki.
Tare dake sahibata ya fada ba tare da yashirya furta hakan agareta ba sai yaji sautin murmushinta na
jin dadin abinda ya fada a gareta da Sahibata.
Tun safe nake gwada kiranki baya shiga da fatan dai lafiya hakan ko take bashi amsa da fadin lafiya
kalau kasan da zaran bakwai yayi muna daji muna kiyon dabbobin baffan mu nida sister .
Duk da kuwa a kwai maza da yakamata suje kiyo amma mu baffa ya zaba da mu dinga fita mashi da
shanunsa wajen kiyo acewarsa don mu koyi wahalan ruga da bamu taso a cikinsa ba a baya.
Shi wani irin mutum ne da zai yanke hukuncin hakan yasan abinda gobe zatayi a kanku hira dai sukayi
sosai dashi wanda a cikin irin hiran yake tsuntan wani abu daya shafi rayuwansu na baya ita da yan
uwanta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yanda wace akafi sani da maria kamar yadda aka rada mata zanen sunnanta tun haihuwanta inda sunan
nata ya samo asaline ga sunan kakarsu kasancewar hakan da uwar bata iya kira saboda sunan
sarakuwartace sai ta juya sunan a cikin harshen yarensu da yan mata.
Dama sunan da mahaifiya ke kiran da dashi shine mafi karbuwa a bakin mutanen dake kewaye dasu
don suma da wanan sunan zasu dinga kiran yaro saboda agane.
Yanda yariyace natsatsiya ga ilimi da Allah ya bata na addini dana boko wanda sanadin samun hakan
zaman da mahaifisu yayi a Abujan Nageria ne dasu.
Inda yake sana,anshi na sayar da kayan masarufi wanda daga baya ya dan samu kariyan arziki saiya
koma gadin gidan wani dan majalisan taraiya mutumin maiduguri.
Zamane na amna a tsakaninsu don matarshi mutumiyar arzikice dama ance silan gyaran gida yada a
wajen mata don ko hjy itace tasa Yaro ya dauko iyalinsa ya dawo dasu gidansu a inda suke wani unguwa
a cikin masaka.
Zuwan yairo birni da kuma kariyan arzikinshi kuwa ya samo asaline daga kiyayya irin na yan uwa daya
taso a cikinsa kusan bafulatani da riko haka kuma duk bafalatin asali suna da wani hanya irin ta kaucewa
da suka rike dimun dimun a zuciyarsu wanda ba kowane zaisan wanan ba sai su yasu yasun su yan
wajen.
Zaki gansu adaji suna rayuwa kiyi ta tunanen ko basujin tsorone wai idan kika zauna kikai nazarin fulani
da kyau koda a birni suke kuwa zaki fahinci asalin fulani yana da wani boyayyen siri nai kama da surkin
jinnu a cikin halaiyansu.
Wanan zancen ba karya bane haka zancen yake duk da fulanin yanzu ba damuwa da irin abubuwan
haka sukayi ba suma don wayenwa kai a yanzu.
Zakiga tsofin fulani ba kasafai zasu iya barin daji ba saboda anan Allah ya halicci rayuwansu tare da
dabbobinsu da tsuntsaye da sauran namun daji dake kewaye dasu da kuma sauran abin boye.
Kiyiwa kanki tambaya ke mai karatu su basu tsoron dajine wai ko basu tsoron dare da abinda ke cikin
darenne wai wanan amsan yana ga balafulatanin asali daya san kansa wanda bai iya ruwa ko a cikin
mutane sai gefen daji zai zauna shi kadai.
Irin hakane da Allah ya tsamo Yairo daga ruga don yawan tsagwaman yan uwa ya dawo birnin ya fara
sana,a sai suke ganin ai yaro ya lalace a yanzu ya zama dan duniya.
Abu ga Allah haka sukai ta jefo masa asiri tun bayan da sukaga da gaske yaro keyi da zaman birni tunda
har yazo ya dauki matanshi da tsohon ciki zuwa birno to tabbas zaman Yairo birni ya tabbata tunda har
ya iya daukan matarshi dele suka koma birni da zama.
To tanbada ya hau kan yairo ke nan a yanzu ka,ida wanda suke ciki daya zai tattara dan sauran abinda
ya bari ya hade da nasa na tsawon wasu shekaru idan bai dawo ba sun zamo nasa ke nan ladan kiyo.
Haka baffa sa,idu ya tattara sauran dabbobin mahaifisu ya hade da nasa ga bakar asirin dayai ta jefawa
Yairo din wanda gida ya fita ransa baki daya har yakai yayi haihu hudu duk bai tako gida ba.
Allah ya rufa mashi asiri rikon amanansa yaja mashi farin jini sosai ga Alh da iyalinsa da suka rikesu
amana a tare dasu da farko zuwa yake shi kadai sai bayan wata yace zai tafi dubo iyalansa.
Ranan Alh da hjy ya samu a tsaye yazo sallamansu akan yana son ya dan leka iyalinshi don bashi
dayane maigadi ba sukan shirya a tsakaninsu sai mutum daya ya tsaya ya fake gida har dayan ya dawo
irin hakane yazowa Yairo din .
Kudin mota Alh ya bashi yana godiya har ya dan daga hjy Falmata ke fadin wai kai Yairo har ina iyalinka
suke zaune kai din mutumin wani garine wai ?
Ya dawo ya gurfana ya soma fadin hjy ni mutumin nan Gembo ne nan wajajen tasanwa kasan Camero
saidai yan uwana da kowa nawa sun ketara yanzu suna kasam ccamero din da zama.
Iyalina kuma suna nan masakane zaune inda na kama haya a nan na barsu suke zaune nan masaka na
Abuja ko ince nan Nasarawa yace kwarai hjy nan na kama masu haya suke zaune don yafi min kusa da
zuwa can gida.
Matarka dayace yara nawa yace dayace hjy da yarinya daya da take goyo kallon mijinta tayi don a
gaskiya suna jin dadin zama sosai da yaro mutum ne mai mutunci da kamun kai sosai mutumin.
Ai ina ganin Alh basai na dako wata yar aiki ba indai matarsa zata iya min komai ai gara ya daukota nan
tunda ga wuri zaifi sauki.
Yafi muyi tafiya mu bar yaran nan a cikin zullumi ko yaushe ina ganin haka yafi ai ko meka gani kai
yaro ?
Hjy nikan in anyi min haka ai banda bakin godiya a hakan Allah ya kara daukaka da nisan kwana nagode
kwarai Allah kara rufa asiri amin hjy din ta fada.
Ta dora da fadin yanzu kaje duk shawaran da kuka yanke sai muji ko mu ganku tare ya kara mata godiya
donshi mijin yana ta faman amsa waya a lokacin.
Wanan ne sanadiyan zuwansu zama gidan Alh inda hjy taji dadin zama da Ashatu mata mai kirki bata
da kiuya ga tsabta da mutunta kowa har yara .
Jin dadin zaman nasu yasa hjy batayi kyashin sakasu boko ba tasa aka hada Yanda da yaranta suna
zuwa makaranta haka kuma ta islamiya da suke zuwa a tare da ita.
Wanan yasa yaran suka taso cikin jin dadi da natsuwa ba zaki taba sanin su din yayan tugga bane don
basu taba sanin wani abu rayuwan ruga ba.
Sun dauka Alh dan uwan mahaifisune don su kadai suka sani a danginsu lokacin kwatsan ranan
mahaifisu ya samu labarin rasuwan tsohonsu hakan yasa ya roka da zasuje gida har yaran.
Ba jin komai hjy tasa aka kaisu har garinsu cikin motan gida wanan zuwan shine yayi silan komai garesu.
Don kuwa mahaifisu bai dawo gida ba saida dafi da aka jefashi dashi inda ya dawo yayi ta jinya daya
zamo ajalinsa akarshe.
Anan babban asibitin Abuja Allah ya dauki rayuwansa ganin halin da iyalin yaro suka shiga yasa Alh da
hjy suka kaisu gida da kansa da niyar suje suyiwa yan uwansa ta,aziya su dawo dasu daga baya.
Saidai tun zuwansu budan bakin baffa fara tambaya yayi ina dukiyan dan uwansa daya tara abuja din ?
Mamakine ya kama Alh yace shidai a saninsa baisan Yairo yana da wani dukiya ba yasan dai duk wata
yana bashi hakkinsa kuma yaransa kaf sun dauke masu laluran karatunsu suke biya shida matarshi.
Karshe dai ba a rabu da dadi ba tsakaninsu da Alh saima sukace zasu bar iyalansa a nan don za a dinga
zuwa gaisuwa ana tambayansu daga baya in komai ya lafa zasu nemesu.
Sukan tunda suka roko ko yanda dake shirin zana jerabawa a bari suje da ita sukaki suka fahinci ba su
son yaran su koma hannunsu ne.
Haka suka tafi suka barsu a wajen yan uwan mahaifinsu karshe da suka gano ashe dukiyan da suke
zaton na yairone ba nasa bane ashe sai haushin hakan ya koma wajen yaransa.
Nan wanan baffan nasu ya rufe ido yana fada yana fadin indai hakane dole su biyasu hakkin kiyon da
Yairo ya gudu bai karasa ba ya koma birni da zama don iyalinshi suji dadi .
Wanan dalilin yasa suke zaune a hannunsu cikin ukuba da tsagwama ga yunwa da wahala daya juye
masu kamaninsu a lokaci guda.
Dan wayan dataje dashima garin baffan ya karbe ya sayaryan suturunsu duk sun koda a karshe dole
suka koma amfani da irin wanda mutanen wajen suke amfani dashi suka saje dasu baka gane sun taba
rayuwan Abuja a baya.
Irin wanan labarin da Yanda takan ba Abubakar a cikin waya shine suke tsuma zuciyarshi yana jin yana
son ya taimaka masu duk da yasan karfin sa baikai ba amma zai gwada sa,anshi ya gani ko Allah zaisa a
dace.
Da haka kuma ta kara shiga ransa sosai yake matukar jin ko ta halin kaka saiya taimaki rayuwan Yanda
din inma da son samu gaba dayansu zaiyi sanadin dasai sun dawo cikin gari da zama amma kuma ya kan
tambayi kansa da taya haka zai faru ?
( IKKO Ikon Allah )
Tafiyan jirgine yayi don haka bai huta ba washegari ya fita wajen business dinsa yabar zancen da sai
Meimbe ta nemasa da kansa don har yanzu bai kai ga yanke hukunci ba duk da malam na kusfa ya gaya
masu akwai alheri tattare da wanan abin saidai zai dan fuskanci baraza amma kuma ya bashi addu,a tare
da ruwan rubutu dayasha tun a wajensa.
Haka kuma baiyi sanyi a gwiwaba tun dawowan nasa yana duk abubuwan da kawunan nasa suka bashi
shawaran yayi don rigakafi a rayuwansa.
Har wani annashuwa yakeji don abubuwa yanzu sai budewa sukeyi tun dawowanshi daga gida kofofin
samunsa kamar an bude mai yake gani duk abinda ya taba cikin yardan Allah zaiga nasara akan abin.
Haka saida ya tabbatar da matansa sun horu sosai kafin ya fara daukan wayansu koshi saida iya ta
kirashi tana sheda mai zuwansu Asibiti da Saiba da aka tabbatar da tana da matashin ciki a jikinta na
wata biyu da kwanaki.
Kamar yadda iya ke fadamai tun bayan barinshi gida bata da lafiya wanan yasa ya kira Asmau ya fara jin
lafiyanta kafin ya kira saiba din a gurguje suka gaisa yayi mata ya jiki ?
Zata fara kawo mashi kissa yace aiki yakeyi zai kirata idan ya gama shine farkon da har yake saurarensu
idan sun kira wayanshi din koshi ya kira yaji lafiyan jikinsu.
Tunda ya tara guzame a gidansa don ko,wacesu tana dauke da cikinsa a yanzu ya zama dole ya kulasu
haka kuma duk sati yana turowa ko wacensu kudi a account dinta don bukatun yau da kullum irin haka
na mata.
Yau ya kasance saura kwana biyu ya cika sati biyu da dawowa gidane suka hade miss meimbe a wani
shago itace ta fara hangoshi ta nufi wajenshi cikin sakin fuska tana fadin kai kayi wuyan gani fa ?
Shima murmushi yayi cikin dan basarwa yana fadin mun daiyi wuyan gani koda yake naje gidane kinsan
mutum mai iyali sole inayi ina leka gida.
Dariya ta kwashe dashi tana fadin kajika sai kace wanda ya aje mata masu mata a gida sune bini bini
suke zuwa gida lokaci lokaci ba irin ka yaro karami ba.
Dariya zancenta ya bashi yake fadin nine yaro karami nida keda mata biyu a gida zaki kalleni kice min
yaro.
Dariya sosai ta kwashe dashi tana fadin abinda kakewa kanka fata kenan ka fada ka aje mata biyu
kamar yadda ku musulmai kukeyi ?
Sam kai baka dace da tara mata ba lover boy kada ka tauye kanka sa yawa mana mace daya is ok for
you ku more rayuwanku da lokacin ku.
Wani kallo yake mata kafin ta tsaigaita da maganan tana kallonshi itama tace iam tell you gaskiyata ke
nan har zuciyana na fadama saboda kai din mai tsadane zanso naga wanan mace mai sa,an da zata
aurenka ?
Me kika daukenine mrs na fada maki matana biyu wallahi kuma ko wace a yanzu tana da ciki da zata
haifa min baby.
Kallon serious tayi mai tana fadin kacire wasa abinda naga ya dace dakaine na fada sai yayi murmushi
don yasan ba zata yarda da yana da mata ko bama mata ba a lokacin.
Can ta dan tsagaita dariyan ta saita kanta ta soma fadin ina ta nemanka naji shawaran daka yake don
broda ya kirani yace ina guy din don kaya sun fara yawa yana son a fara plan din turawa arewa din.
Shima Jafar din gyara tsayinsa yayi ya soma fadin eh to gaskiya ban tsayar da maganan zanyi ko ba
zanyi ba a yanzu saina gana dashi yayan