Chapter 72 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   72 / 101

213K to 216K   out of 302.2K words

Duk da gabana yayi wani irin faduwa amma saina dake nayi murmushi a fuskana kawai na samu waje
na zauna ina goge fuskana da dan kwali a cikin wahala.

Ki samu abinda kikaci kisha magani ya fada yana mai bina da kallo na dan sauke ajiyan zuciya na mike
tsaye na fita zuwa part din su mama.

Suna falon mu ita da mama da iya dasu inna na gaidasu na fita zuwa wajen anty Salima ko zan samu
abinda naci a part dinsu don ko shayi ba zan iya sha ba a lokacin saboda yadda zuciyana ke tashi.

Nan ma din ba wani abinda suka dafa a lokacin ma take girkin abincin ranansu take fadin bari ta hada
min tea da sauri nace a,a ta barshi nashiga dakinsu na kwanta.

Ina jin zazzabin na son ya dawo min haka na daure nayi sallah na koma na kwanta sai gata ta shigo min
da furan gora mai sanyi shi nasha sosai don yayi min dadi a bakina sosai lokacin.

Barci na koma sai zazzabin ya kara rufeni kuma mama tudu ce mai tambaya ina ina don bata ganni ba
ake fada mata ina can dakin su salima kwance.

Duk mun dauka dai zazzabin gajiyane haka kinsan halin malam ba haushe ba komaine ake saurin kaiwa
asibiti ba sai anga yan dabarun gida sun kiyane za a kai kafa asibiti.

Don kuwa ciwon kwana biyu ina kwance ragaraga dani abani wancan a bani wanan sai yayi dan sauki
zai dawo kuma gashi banson yawan hayaniya ga tara miyau a baki saina faki ido na zubar shiyasa ban ma
zama a cikin mutane a kwana biyun nan.

Na idar da sallah a dadafe na dawo part din mu inda na samu su mama dashi a zaune shi kuma yana
kwance a inda yake tunda na shigo mama ta bini da kallo tana min sannu ta dora da fadin.

Ni dai ko ince an samu dan jinyane wanan ciwon Rahama kamar na mai shigan ciki haka komai kaci
baya zama a ciki sai an amayeshi ?
Daga inda mama dubu take zaune ta dago kai da sauri tana fadin ciki kuma yaya don Allah ki daina
zancen nan .

Wanda ke kwance haka rai a hannun Allah ina zancen ciki kuma ya fito nan gareta kuma ciwon daine
yazo a haka balle dama wanda yai jinya haka ai sai yaji jiki daga karshe shima.

Dadina dake sai ki dinga magana kamar karamar yarinya dubu to ko cikin ne Allah ba yana iya kawosa
ba ko a hakan akwai abinda ya gagari Allah ne ?

Iya ke fadan hakan ga mama din mama tudu tayi murmushi tana fadin shi dai nagani nawa akayi irin
hakan muna gani dan wajen Rakiyana da mukaje jinya sokoto kwanaki da kariya ba sai anyi dori ya
gwauce ba sai daga baya likitoci suka gano inda matsalan nasa yake dole aka rabashi kwana da matarsa a
dakin .

Ai kariya kikace yaya wanan da yake kwance haka shatkaf dashi bako motsi ina wanan zance ya fito
haka kuma ki tashi ki danci wani abu kafin ki kwanta ta fada a karshe.

Gabana sai faduwa yakeyi duk da zancen ban dauka zai iya faru haka ba na mike zuwa falo ban iya
kallon abincin ba na samu wuri na zauna nayi tagumi.

Sai a wanan ciwon na tsani halin maria ta da mama ke zaginta dashi ina kareta ashe wani shirun idan
yai yawa wa mutum akwai illa don bata iya tabukawa kanta komai balleni ni kadai ta bari ina zugata a
cikin dangin miji tana gefe ta fake da laluran ciki ta fita batuna yau wa zan tunkara in fadawa wanan
magana.

Ban koma dakin ba saida su mama din suka fara fitowa don neman wurin kwanciya a nan falo suka
sameni kwance maman tudu take fadin ayyah dama aina fadi mu baki waje ki kwanta .

Na dai daure na kawar da kayan da komai dana saba na koma dakin kwanan mu na fara shirin
kwanciya a ranan har wani sanyi nake ji a jikina hakan yasa na nemi waje na kwanta na lafe a kujera.

Da farko na samu barci amma da tsakar dare barcin gagarata yayi na soma kaduwa hakan yasa ni kuka
ni kadai a inda nake din.

Cikin karariyar muryasa naji yana kiran sunana yana tambaya yayane nace ba komai na kara nadewa
don komai haushinsa nake ji a lokacin.

Dole ya gaji ya kyaleni don bai iya tasowa zuwa inda nake nasan yadda banyi barci ba shima baiyi barci
ba a ranan haka ya nade dai don ba yadda zai iya.

Washegari mamace ta shigo jin bataji motsina ba tashigo tana tambayan ko jikin ne da kyat na iya
daga kaina na bata amsa takai zaune tana dafani tace kina ko shan magani Rahama ?

Na dai amsa mata ta dade zaune tana kare min kallo kafin ta mike ranan ita da kanta ta gyara muna
part din su suna aikinsu na karfi yayansu daine sai a hankali gaskiya kuma abin kamar a jininsune yake
haka gaba dayansu yayansu mata basu da moriya sam.
A ranan itace ta bashi abinci na dai daure na gyara mai jiki da shimfida na koma na kwanta sauran
aiyukane har bashi abinci duk mamace tayi a ranan tana falo tasa min kira nazo mu karya dole na taso
nazo din.

Cibi daya nayi na taliyan da aka dafa muna wai abin karyawan safiya na dawo dashi da gudu naje na
amaye na jima na fito ina haki na kwanta mama ta dubeni tace anya Rahama kuwa.

Yanayin ki ya nunafa kamar cikine dake komai da kikeyi na masu cikine fa Rahama baki na turo ina
fadin haba mama na gyara kwanciyana .

Ina wajen nade na dunkule yazid ya shigo suka tsaya suna magana dasu mama da matan yaya Jafar
yake fadin

Ke yaya dai mijinki yace nazo na kaiki asibiti baki da lafiya gata dai kan kamar maman biyu zazzabi
kamar na mai ciki haka ta kwana tana wahala .

Ciki kuma mama kamar wace tasha a ruwa aida an saka mata ayan tambaya akan cikin nan kuwa
Saarece ta fada tana turo baki gaba har ta fara tafiya ta nufi dakin ta juyo tana fadin watan yaya J na
takwas ke nan fa mama hakan kwance ake zancen wani ciki kuma yanzu gareta ?

Dakuwa mama tayi mata tana fadin ja,ira mara kunya kinbi kina wani hakilo inma cikinne ina ruwan ki
yarinyar da mijinta zaki kama wani zance can ?

Har ta shige mama tudu naci gaba da fadin nina rasa menene tsakanin yar nan Rahama da saratu sam
bata kaunar yarinyar nan da alheri ko kadan wallahi.

Daga inda iya take zaune ta karbe da fadin ina zata kaunaceta tunda sheri yana ranta ita saratu watake
so Amina ai banda wanan mara kunyar da halinsu yazo daya banga wanda saratu ke kallo da gashi ba
gidan nan har yan uwan nata kuwa.

Abu kamar asiri zakice yarinyar nan ta asircesune ita da uwarta yadda suke kafa kafa da zancenta yanzu
ba taji hakan ba tana fita zakiga takai zancen nan wajen ta su dinga yiwa yarinyar nan kwakwaf inma
cikinne ai Allah ya kawo abinsa.

Ina lafe ina jin duk abinda suke fada a lokacin gabana ya soma faduwa ina tuna taraiyan mu da yaya a
asirce wanda mukeyi a yan kwanakin samuwan saukinsa wanda daga Allah sai mu muka san abinda
muka aikata din .

Kai ina hakama ba zai yuyu ba har wani abu mukayi da za ace ciki ya shiga ga hakan mutumin da baida
lakkan wani abin kwarai karfin haline irin na maza da yan adam kawai na kwakwa a wajensa.

Barci nayi abina bansan wainar da ake toyawa ba a gidan saida wani zazzabi ya tayar dani na falka ina
makyarkyata babu kowa a part din sai mama da shi dake kwance dakin na koma wajenshi na kwanta
agefensa na dunkule.
Ya zuba min ido da kyat ya mika hannunsa a kaina jikina ya gashe yayi zafi kamar garwashi ya soma
fadin on tashi a kaini asibiti sai naji sam banson zancen wani asibitin nan da suke min kamar yana son a
kara tsanatace a hakan gashi na fara jin zancen banza a bakunan su duk da banda yakinin cewa ga
matsalata nasan kuma zazzabine kawai na wahala ba komai ba yake damuna.

Shigowan mahaifiyarsu part din don ba kasafai take zama ba a nan saboda mama dake mata kara
takanas ta baro komai nata ta dawo nan ta tare saboda danta dole ta kawar da ido tayi kawaici akan
hakan dama kowa yasan jafar dan maman tudu ne inbada dan hatsaniyar rabon gado ya dan shiga
tsakaninsu ba a kwanaki bayan rasuwan mijinsu yanzu ko an daidaita hakan an koma kamar komai bai
faruba a baya.

Yar nan ku kaita asibiti fa muryan mama dubu naji tana fadan hakan a gefe taci gaba da fadin ciwon
nan kada yaci jikinta duba yadda ta fada a cikin kwana biyun nan ?

To shi dai da zai kaita gashi a kwance yana fama da kansa tun safe yaiwa Yazid magana tunda ya fita da
motan bai dawo ba tun dazun.

Dama yazid zai kaita aiko dai ya fita da nasa iyalan tun dazun nan J din ya fara danniyar fadanshi akan
dan uwan nasa a cikin karfin hali ya jawo wayarshi ya tura mashi text ba a jima ba sai ga yazid din ya
shigo yana fadin afuwan madam mijikin ya hauni da fada na bar mashi mata na ciwo a gida ?

Sannu tashi muje asibitin please ba zai barni in huta ba yadda ya hasalan nan dani yasa kai ya shiga
dakin wajen shi na mike ina son shiryawa mu fita.

Tare da mama muka tafi asibitin itace tayi min rakiya zuwa ganin likita da zanyi ancewa na kawo fitsari
aka kuma debi jinina tun lokacin nashiga damuwa .

Ni abu biyu najiwa tsoro na farko kar zancen ciwon ya J ya zamo gaskiya abinda kawai ya fado min a rai
ke nan yasa sukace zasu dibi jinina .

Munyi zaman jugun muna jiran sakamako saigashi anfito dashi ankaiwa likita Yazid ya shiga akai mai
bayani cewa ai akwai shigan ciki a tare dani dan wata daya.

Abinda yaba likitan mamaki shine da yazid dake fadin likita kun duba da kyau kuwa don mijinta fa
yana kwance baida lafiya almost eight month ke nan yanzu.

Shine me hakan bai iya ganetane ko bai sheda kowane har yanzu jin hakan yasa yazid din yin shiru na
dan lokaci ya mike yana murmushi sukai sallama da likitan bayan ya bashi takardan da za a sai min
magani.

Tunda ya fito yake min wani irin kallo daya sani tsarguwashi dan irin yadda yake kallona din mota muka
koma nida mama muka zauna shi yaje sayen magani.

Ya dawo muka bar sibitin saida muka dauki hanya da kyau naji yace mama akwai matsala fa don nasan
za ayi tsiya da sauran yayan ki idan suka samu labarin abinda ke damuwar yarki.
Subbahanallahi akan me za a samu matsala kuma wai wasu yayan nawa kake magana ban fahince ka
ba ?

Mama ki barshi kawai har mu isa amma sai anyi da gaske don kada hakan yajawo rikici barin dan faka
in sayo mata lemo ko zataso shi nan ya tsaya ya fita naji mama din tana ajiyan zuciya.

Kodaya dawo bai kara maganan ba har muka isa gida don waya da yakeyi a cikin harshen larabci mota
na tsayawa na sauka na barsu da mama din kodana shigo falon ba kowa hakan yasa na nufi daki kai
tsaye.

Nayi sallama na shiga yana zaune da matanshi ranan Nusaibace tayi girki tana zaune tana bashi abincin
don angamashi late evening sosai .

Ina shiga sukayi min ya jiki shike tambaya da hannu yaya nace da sauki na samu waje na zauna saida
yazid ya shigo min da magani da kayab marmarin da ya sawo muna mai yawa ya aje a gabana yana fadin.

Ki kula da shan magani likita yace asha na kwana ukku a gani idan bai bariba a koma Allah ya sauwaka
yace zai leka part dinshi ya dawo.

Sai bayan ya tafine anty Asmau take min sannu da jiki na amsa gami da murmushi ina gyara kwanci
shigowan mama tayi muna sannu da dawowa take tambayan yaya jikin nawa ?

Tunkan in bata amsa ta juya wajen mama tana tambayan me likita yace wahalan jinyane ko ke damuna
sai mama tace anya ban tsamanin hakan gaskiya ?

Don yazid dai akaiwa bayani an kuma auna fitsarina da jinina akai gwaji shinema ya tsayar damu bamu
dawo da wuri ba.

Awon fitsari kuma sai kace mai ciki daga zazzabi Nusaiba ta fada maman tudu ta amsa da fadin abinda
nake tuhuma ke nan saidai ban san me sukace dashi yazid din ba.

In ma cikin ne dai Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka haba dai sai kace wasan yara mama don
Allah ku bari dai ina zancen ciki yanzu mijinta na kwance haka ?

Anty Asmau ke fadawa mama haka cikin katse mata zancen da takeyi din ita kuma saiba cewa tayi haba
dai ciki a yanzu haka kuma drama ke nan ai ?

Ta fada tana wani mere baki ta juya zuwa cikin daki ta samu mijinta don itace da girki a ranan ni dai ina
kwance ina jinsu bancewa kowa komai ba.

Saidai a lokacin banda natsuwa don maganganunsu sun fara tsaya min a raina na fara tunane barkatai
a kan hakan ina yanke shawaran nisantan shimfidan yaya a wanan maran kada wani abu yazo ya auku
dani inga boni.

Yazid bai shigo ba sai bayan sallah isha,i ya shigo ya samemu dasu mama sai anty Asmau yayi min ya
jiki ya wuce zuwa wajen dan uwansa dake daki ya shiga ya samu dan uwan nasa yana sallah ya zauna
zaman jiransa.
Bayan ya idarne suka gaisa dashi nan ya zauna suka dan soma hira kafin ya fito mashi da zancen daya
kawoshi wurinshi din da farko cewa yayi dashi.

Ya dan uwa baka tambayeni abinda asibiti sukace game da matar kaba dazun da mukaje don dana
dawo akwai mutane a lokacin kuma maganan yana son in fara kebewa dakai tukun.

Ya dago ya kalli dan uwan nasa alaman meya faru a fuskanshi yace don gaskiya gwajin da akayiwa
amarya ya nuna tana da shigan ciki na wata daya a jikinta shine ke bata matsala a yanzu.

Cikin muryansa daya koma kamar a karye ya zaro ido yana fadin kana nufin cikine da Rahama yazid din
na kallon yanayinsa yace cikin gyada kai haka sukace dani gama takardan daya bada result din nan.

Ya fito dashi ya mikawa yayan nasa dan murmushi yayi ya karba yana bin takardan da kallo kafin ya
tura karkashin filon da yake kwance.

I hope dai kasan da hakan ko kada rayuka su baci daga baya kai kawai ya dagawa kanin nasa ya mayar
da idonsa ya lumshe har dan uwan nasa yaso ya fita.

Saiga mama ta shigo dakin tana fadin ashe ka dawo yanzu naga mota a waje dazun da kuka dawo ance
kuma ka fita yace ehh na shiga garine .

Yanzuma sakamakon asibitin na kawo mashi to maleria ne ko yake damun ta yace a,a kamar dai cikine
sukace ga dai takardan nan hannunshi nabashi.

Ciki ciki name cikinta ke ciwo kome donni ban fahince ka ba ai kayi min magana haka a dunkule yace
mama me kike son in fada maki yanzu tunda nace ance shigar cikine da ita yake sata zazzabi haka ?

Cabdi jam ciki ciki fa ita kuma yar nan a ina ta dauko ciki kuma a wanan lokacin badai cikin Jafaru bane
ko da sauri Yazid din yace wa,iyazu billahi mama ke kike wanan maganan kuma kanar wace bata da aure
mama ?

Hakan ya jawo hankalin mu a falo harsu mama suka taso da sauri zuwa dakin suna shiga yazid na
fitowa mama na biye dashi a baya.

Tana fadin kuji min wanan zance don Allah wai yarinyar nan cikine da ita ashe take wanan laulayin
haka ina Rahama din takene wai ?

Kiyi mata me zuwa zakiyi ki tambayeta dubu ta yaya ta kwanta da danki kome kike nemanta kiyi mata
yanzu ?

Asmau dake zaune a kusa dani dakin mama ta mike tsaye da danta a hannu tayo waje ta saurara
abinda ake fada lokacin mama dubu tana fadin.

Haba iya wanan ai abin a tsaya a dubane yaron nan kwance fa yake rai a hannun Allah ta yaya zamu
ganta da ciki ace hankali ba zai daga ba kuma ?
To kina da ja da ikon ubangiji ke nan dubu ko kin isa ki hana Allah ikonsa yadda yaso a kuma lokacin
daya ga dama wanan tambayan ba a bakinki ya kamata ya fito ba har in ana zargin hakan awajen
mijintane ya kamata ajishi bake ba ?

Akul naji wanan zancen ya koma fita a bakinki zan saba maki kafin ki shaganta masu da daga bakinki
bake ba kuwa duk wani baji ya fadi wani zancen aibancin daga bakinsa a gidan nan kan zancen cikin nan
zan fito masa a maryamuna ya sanni .

Shiru fslon yayi yayin da mama tace iya baki fahinceni bane gani nayi dai yaron nan yana kwance haka
mama ta ina zancen ciki yafito ?

Baki daddaraba ke nan dubu yarinyar nan da mijinta take kwana ko gadinsu kikeyi da dare bahaushe
yace tsakanin miji da mata sai Allah dama to ki kama bakinki da zancen nan kinji na fada maki.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/23, 10:32 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣3️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na idar da sallah asuba
na dauko wayata ina kiran maria.

Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai

72 / 101