Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
yarda yaran nan da goyon bayanki suke haka tana ganin tafi kowa a yanzu don an nuna mata
fifiko akan abokan zamanta har take ganin zata iya dukan saratu a gabana ko ?
Yau muna ga rasulu shine zancen mamakin iya idan abu ya daure mata kai shi kuma ta furta a lokacin
cikin mamakin mama dubu din dake gabanta.
Tace yanzu ai gata nan idan kinzo sakintane saiki bata takardanta kowa ya huta ina zance ya kare tunda
baki iya tsayawa can ki tsawata yarki datayi abin kunya ba haka ?
Iya ai abin bakai can ba don dai kawai abinda ya faru kar a koma hakan ne yasa mukazo mu tsawata
mata don gaba kada a ,,,,😑😑 kai dakata don Allah ta fadawa kawu daya soma magana.
Tace bakinku daya kowa ya sani kunji zafi ba itace akaiwa duka ba don baku da kunya kuka kwaso jiki
zuwa nan kuciwa yar mutane mutunci ko ?
To Dubu kin kai ga yadda kike so ai yau gari ya dauka ga abinda yarki dake kuka taru kukaiwa matan
danki har da kishiyarta abin kunya kamar yar nan zakuyiwa taron dangi haka dubu ?
Ganin yadda iya bata basu daman magana ba yasa mama ta soma fadin iya kinsan dole in tsawatawa
saratu ai duk abinda ya faru itace ta jawoshi.
Don anba yaran nan abu zataje ta fadawa uwarta ita kuma don bata da hankali takwashi jiki zuwa fada
duk nayi masu fadan hakan amma yadda yarinyar nan tayine bata kyauta ba tunda muna wajen muna
tsawata mata ai.
Daga gefe na bude baki nace mama kuyi hakkuri don Allah amma ni banje gidan nan da fada ba itace
tazo ta sameni ta soma zagina ganin tana da niyar kai min duka nima nakai mata.
Amma da nazo yakamata ki dubi tsufana ki ji me nake fada aiko ayi hakkuri nayi kuskure hakan ko
gobe ta kawo maki kada ki kyalesu tunda da niya sukai hakan iya ta fada.
Keko iya inji kawu ni tayi min daidai yau don Allah ya nuna masu mugun abinsu a fili gobe su kara in
halinsune gida kuma ba zata fasa shiga ba tunda gidan mijintane kuma yar uwarta na gidan zaune dole
ta shiga.
Ai don haka muka taso iya amma kin hana ayi magana kamar kina zugatane fa iya irin abinda kike fada
yanzu ?
Dauda so kake su daketa taki ramawa kome don ban fahince kaba har yanzu yarinyar nan kowa yasan
halinta magana ba magana ba duka ne zata kaiwa mutum .
Ba haka tayiwa Salima ba wani lokaci kan dan maganan fatan baki kuma yarinyar nan tasani suka dai
samu suka tafi don magariba daya kawo jiki lokacin.
Tunda na shiga daki ban fito ba don gaskiya jikina yayi tsami abinda na dade banyi ba biba tashigo ta
sameni take tambayana ta kawo min abincine nace tea zansha.
Zata fita nace ta miko min wayata a jaka ta dauko min miscal din dana gani a lokacin bana lafiya ba duk
kuma nasan akan abinda ya faru dinne ake kirana din.
Nasa kiran kusan goma sha hudu gana yaya habu har ukku sai na Nafisa da anty salma na anty Salman
na fara dauka .
Tana dagawa take fadin ke Ramaah meya kaiki hada jiki da kishiya ashe bana fada maki hakan tsiya
yake kawowa ba ga mutum ko ga miji ?
Idan ban dauki mataki ba dukana zatayi anty tace taci bulus aida kikayi kadan sai ki bari amma duka
haka kamar wace taci tauri Rahama ?
Maria tace min taji tsoronki dazun ta dauka ko kina da iskane tace fuskansu da jikinsu kin masu illa
sosai a wajen fadan ?
Na kwashe yadda abin ya faru na fada mata sai naji tace kin min daidai wallahi ya kirani hankali tashe
yake fada min shi a zatonshima wai ciki gareki kikaje kina fada haka ?
Tsuki naja jin abinda ta fada tace Allah yace with dis condition naki zakije kina fada a illantashi idan
wani abu ya samu cikin jikinki fa ?
Kyashi anty ni banda komai a jikina na fada muka kuma koma zancen su din inda tace wani lokacin irin
haka idan ba haka ya faru ba dama ba a samun natsuwa ai.
Yanzu tunda ta gwada hada jikin taga baci zata koma wani sallonne kuma in bi a hankali don zata fara
makirci tunda taga uwar mijin tana kama mata.
Ita kuma yar iskan nan sai taji a jikinta ai nace na dauka ai sakina zaiyi idan ya dawo tunda haka
uwarshi ke so na daki yarta a gabanta ke kin min daidai wallahi.
Maria tace ai mijinta ya dawo ya zo ya karanta masu hauka iya son ransa yace wallahi duk wani abu ya
samu matarshi sai yayi karasu kuma yace zai bar masu gidan ya koma gidansa ya gaji da jidali kullum.
Ashe ya dawo a gurinta nake ji tace ai ya dawo kuwa yayi masu cin mutunci sosai don saida ita Saiba ta
rufe daki akace saboda yayi niyar dukanta dakyat aka samu ya hakkura amma yace zai bar gidan don ba
zai yarda ba.
Mun kai wani lokaci da ita wayan shi dake shigowa ne yasa na katse kiranta din na dauka don inji me
zai fada a ranan kowa ina iyawa dashi don abin ya isheni gaskiya gara dai kowa yasan matsayinsa zai fi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/20, 10:23 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to
join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A sanyayye na amsa mashi murmushi naji yayi sabanin fadan dana zata zai min a lokacin yana fadin ashe
yar kokawa na aje agida ban sani ba ?
Abinda ya fada din yasa na sauke murmushi lokaci guda yace baki kyauta min ba Rahama with your
condition zakije kina fada haka idan wani abu ya sameki fa baki tausaya min ne don Allah ?
Kayi hakkuri don Allah ya daurone idan ban rama ba a lokacin sai su dauka ina tsorone shiyasa na rama
dukan da sukayi niyar yi min din.
Nasani amma kinsan illan hakan ai ina daukanki mai hankali sai gashi kuma kina son kifi Saiba hauka
agaban kowa kuka dinga fada kuna zubar da mutuncin ku why zaki biye masu kuyi hakan don Allah.
Na sake fadin kayi hakkuri yaya muryata tana nuna alaman karya a lokacin is ok amma don Allah kada a
maimaita hakan naji komai nasan ba laifinki bane zuwa gidan kuma har in zai kawo matsala idan ban nan
don Allah Rahama ki daina.
Katseshi nayi da fadin saboda su ba zanyi zumunci da yar uwata ba ke nan banje donsu ba kuma ban
takalesu ba sune suka kirkiro abinda zamuyi fitina har haka ai.
Nasani amma itama Maria din dole subar gidan ai tunda har haka ya fara faruwa yanzu haka mun gama
magana da habu zai gyara gidansa su koma ciki zuwa next week in sha Allahu .
Bance kicewa kowa komai ba duk da ance mama da kawu sun sameki a gida saidai banda fargaban
hakan tunda iya tana gidan a tare dake yasa wanan bai dameni ba amma ki kula don Allah hakan ba
mutuncin ku bane please ?
Nagode na fada sai nayi shiru shima dan shirun yayi ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a bangareshi
kafin yace ina dai baki ji ciwo ba kema ?
Banji ba na fada a takaice yace sure nace umm,umm Allah ya tsare ya jikin ita maria din duk da ance
kun dai fasa mata kaya amma ba a tabeta ba kinga illan fada ke nan bakyau don Allah.
Tausayi ya bani yadda yake maganan sai naji ba dadi a raina karon farko da nayi nadaman faruwan abin
kenan a kasan zuciyana wanda hakan ya ja na rage irin zafin da nakeji kasan zuciyana nasu.
Washegari saiga maria a gidana ita da yaya Habu sukazo nan muka zauna falo dasu da iya nan naji
yadda ransa ya baci ya fada ya kara zai bar gidan tunda mama bataga laifinsu ba sai na matarshi da yar
uwarta.
Habu kuyi hakkuri akwai abinda ku baku sani ba game da uwarku ina nan ina mata addua Allah ya
kwatota daga kaidin da take ciki a yanzu duk wani abinda za a fada a yanzu banzane don bai tasiri
azuciyarta don tana ganin ita daidai take.
Amma kaga Dauda da matarsa hansatu ka barsu nan inda ka gansu su dade sunawa uwarku bandan
kasa.
Yanzune abin yake yawo akanta haka kuma yar nan matar Jafaru itama da akwai wani shu,umancin
datayiwa Dubu a zatona wanan abin shine duk ya rikita kanta a yanzu din.
Kaga kuwa wanan abune dake son addu,a don ba yarda da hakan zatayi ba koda an fito mata fili an
lurar da ita zata iya mussan hakan mutum abin tsorone.
Ni kaina a lokacin ai hafsatu bata barni ba nasan komai ido na zubawa gudunsu tunda yadda suka so dai
bai samu ba.
Sunyi hakane don ku da yan uwanka ya kasance duk wani nema naku yana a hannusu sai yadda sukayi
daku da uwarku din sai gashi ku ba a kama kuba ita abin yafi shiga jikinta.
Nina sani iya don ko kowa bai yarda ba nina yarda kawu zai iya hakan fiyema da hakan sai yayi don irin
yadda yake muna wani lokaci sai mutum yakai zuciyarsa nisa don azauna lafiya.
Yanzu dai zan bargidan ba zan zauna ina gudun zuciyarsu ba ninawa yana baci a kullum don haka zan
kwashe kawai na bargidan ina ganin shine mafita a wajen mu baki daya.
Ita kuma saratu kai salima na fadawa yaya su fito da maza a daura masu aure kowa ta kama gabanta
zaman ya isa hakana musanman ma saratu da duk wani fitina itace ke kawoshi a gidan nan kuma mama
bata yarda da hakan .
Yanzu da safen nan saida muka kwasa da ita wai mun kadarwa saratu bamu kaunarta abu kadan ace
saratune har tana batun yi min kuka fa iya wai akan saratu.
Sai naji iyan tace kafadawa uwar taku zancen tashin naka yace ehh to cikin fada na fadi amma ina ganin
bata dauka da gaske nakeyi ba.
Don kyata da bala,i irin nata wai a falona Nusaiba zataje fada duk sun fasa min kayan falo amma duk
mama bataga laifin hakan ba sai fada rakeyi wai Rahama tazo har gida tayi masu rashin mutunci.
Me yaranan suka tarewa mama haka don Allah iya ta nisa tana fadin habu kayi hakkuri na fada maka
inda matsalan yake don haka addua zamu bita dashi a yanzu.
Ya juyo wurina yana fadin ke kuma baki da hankaline da kika biyewa haukansu Rahama idan suka
illataki fa badon Allah ya doraki akansu ba yadda ake fadi sun tarar maki ai saisu nakasaki a banza tunda
ba wajen hukuma za a kaisu ba a daukar maki fansa.
Don haka daga yau ki kama mutuncin ki dama ita abinda take nema ke nan abinda za ayi ta bata maki
record a idon mutane ba haka kikaga yar uwarki tana zama dasu ba.
Bayan haka ke kinsan yadda akai auren ku da J dole haka ya faru tsakanin ki dasu don ma ita Asmau a
yanzu ta daina saka kanta cikin iskancin Nusaiba don na kula ita a yanzu bata irin abubuwan nan don
haka kada nakara jin hakan daga gareki.
Duk abinda zatayi ai yanzu tunda ta gwada ba sa,a a wajenta aiba zata kara bari su hada jiki ba kuma
da dai ace ta samu sa,antace bata da sauran numfashi kuma a gidan nan yanzu.
Sai Allah ya kawo saukin abin kika rijayesu don haka yanzu iskancin zai rage akanki saidai ta fito wani
hanyar kuma nan gaba.
Ai tasha fadancewa saita wullakantani dake a gaban kowa amma ban taba tsayawa na kulata ba ina
jiran ranan da zata kawo iskancin ta akaina ta gane kurenta bata san naki dan maline ba don nafiki hauka
kyalesu kawai nakeyi.
Maria data karbi zancen iya take fadin hakan sai iyan tace gara dai kada akai ga hakan ai yanzu na fada
maku zasu shiga hankalinsu sosai tunda basu sha da dadi ba.
Na daiyi fama da tsamin jiki tunda jikin a yanzu ba wahala irin da can baya inda gadan gadan ya Habu
ya shiga gyaran gidanshi da zai koma da iyalinshi.
Unguwa dayane amma akwai dan nisa da inda nake saida yayi wani dawowan ya samu mama da
zancen tarewansu gidan akan ga gobe.
Me kake fada Habu zaka kwashe ka koma gidanka watau ban isa da kaiba yanzu saida yaran nan sukai
nasaran raba min kanku a gidan nan ?
Wasu yara kuma mama ta kalloshi a yatsune tana fadin wasu yara banda shu,uman yaran nan da kuka
dauko min a gida ?
Dama gurinsu kenan su raba min kan yayana gashi ko sunyi nasara na farko a gareni shigowan yaran
nan cikin ahalina bai haifar min da komai ba sai tarin bakin ciki da takaici .
Kowa yasan asalin nono dama daga ruga yake ashe gaskiya ake fada akan fulani ba a fadi karya ba duk
wanda ya auri yar filo sai yabar kowa nasa gashi kuwa nagani a kaina.
Saita fashe mashi da kuka ya mike ya fice daga dakin bata kara ganinsa ba saida yammane saratu ke
fada mata da gaskiya yakeyi fa tafiya zasuyi don ashe har sun kwashe duk wani abin amfani nasu sunkai
wancan gidan.
Ranta ya baci ta mike tsaye da sauri saratun ta tareta tana fadin mama kada ki fita don yaya ya ganeni
zaice nice na fada maki.
Yace mana idan yace fa shi har ya isa ince ban yarda da hakan ba yace min don me koshi jafar daya
dauki wanan yarinyar ya kaita can tunda abin ya zamo iskanci ai nan zai dawo da ita dole yanzu.
Tunda tana ganin hakan da yai mata kamar tafi kowane a yanzu har take iya ganin zata tako har cikin
gidan nan taciwa mutane fuska jiransa nakeyi ya dawo garin nan ai,,,
Sallaman ya Habu dake shigowa dauke da dansa a hannunsa sai maria dake bayanshi sabe da jakarta
na hannu shiya saka suka juya suna kallonsu.
Zama yayi yana gaida ita ta amsa a dakile kafin yace yaune zamu tafi wancan gidan mama na fada
maki zamu koma gidana to yaune komawar tamu insha Allahu.
Kai habu saboda ka auro yar gwal mai takobin raba zumunci zaka ture dokana kace zaka bar gida don
ra,ayinta tunda su da manufa suka shigo cikin mu dama ?
Meye laifin Maria anan mama tunda ba itace ta gina min gida ba ninayi ra,ayin hakan don haka a barni
da shawarana don haka nake son tsarina.
To ba zaku ko ina ba kaji na fada maka wace zata iya zama a nan ta zauna wace bata iyawa kuma hanya
a bude yake ta fice ta kama gabanta.
Ashe gaskiya da ake fadin dangin filo dangin bala,i yanzu don matarka har zaka iya kyatare dokana don
kada ranka ya baci.
Mama ba ra,ayinki nazo nema ba a yanzu don na riga dana gama shirina ba zan bar iyalina gidan nan
kina kallo ana ci mata mutunci ba tare da daukan mataki ba.
Yanzu zanyi abinda ya dace a zauna lafiya kuma zakice ban isa ba a zatona hakan abin farin cikine a
wajenki ai mama tunda har Allah ubangiji ya hore muna muhalin kanmu haka da taimakon dan uwanmu
dake son cigaban mu a rayuwa.
Ashe hakan ke a wajenki ba abin godiya bane yau don danki ya samu farin ciki mama kinfi bukatan
ganin rayuwan mu ko yaushe a tauye ?
Habu ni kake musayan harshe dani yau haka kan wani tsari da aka doraka sama yace ba wanda ya
dorani na fada maki ra,ayin kainane hakan.
Banda ra,ayin zama a cikin yawa haka shima jafar din da aka tauye ya zauna ai banga wani abin
karuwan daya samu ba ga haka.
Abinda yakamata ace kin dage akansa mama kin kasa dage muna akan masifan dake bibiyan rayuwan
mu ki sa kawu gaba zuwa garin matan nan dayaje ya karbo maki haihuwa kin kasa haka mama kin tsaya
ana zugaki a kan mu don mu lalace .
Ba laifi idan yau kin min baki kan na bar gidan nan na koma muhalin kaina na zauna don in samu zaman
lafiya a rayuwata.
Kullum kana wajen aiki hankalinka ba a kwance ba kana tsoron abinda zaije ya dawo na samu Allah ya
hore muna kuma zakice baki yarda ba sai dai kiyi hakkuri donnni na tashi ke nan bafasawa zanyi ba.
Haka kuma dolene muje wajen nan a wanan karon abada duk wani abinda akai alkawari bayarwa don
dan uwanmu dake cikin matsalan rayuwa.
Zuwa lokacin kuka sosai mama takeyi akan ya daina amma ya tsaya sai daya gama fadin abinda ke
bakinsa ya kallo maria yana fadin tashi muje.
Maria kinyi nasaran rabani da dana yau har yakai habu bai saurarena sai ke hakan bai maki ba kin
shiga kin fita kin cusawa Jafar ra,ayi akan yar uwarki to ki saurari shirina yadda kika rabani da dana haka
kema zaki rabu dashi indai harni na haifeshi.
Tsoro ya kama maria din dajin furcin mama ga kowa dake gidan tsaye an fito haka ya cusata mota ya
shiga yaja motar suka bar gidan .
Nan suka shiga bawa mama hakkuri mai sunan zugi suna fadin aidama haka aka tsara tunda anan idon
kowa na kansu ba a samu yadda akeson a mulkesu ba yanzu ko ai shike nan sai dai mama din tayi
hakkuri.
Jin irin abinda saiba ke fadi har tana cewa su dai da aka mayar shakatafi ai an tauyesu an hanasu
walawa din ga yan kauye don samun waje sunzo sun karya dokan da aka kafa kuma ba ai komai ba.
Haba keko Saiba wanan maganan bai dace ba mana samunefa koshi ya J ai ra,ayinsane zama a nan din
don kowa yasan yana da halin hakan