Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Jafar kake ganin su nan zasu fahinci hakan da kayi jahilcine ko tauye hakkinsu
akan wata tunda daga gidanta kayi tafiyan?
To ita kuma saiba dakace meta dawo yi a gidanka nice nan naje na dawo da ita don banga abinda tayi
maka na wanan hukunci ba har da saki ?
To shike nan ai mama ta zauna ga gidan nan amma ni abinda ya dace nayi akanta naga yayi don ba zan
zauna da mace haka ba tana gurbata min gida.
Au ita saiba ce kadai take gurbata maka gida su sauran basu wani mugun hali da baka dauki mataki a
kansu ba jafar ?
Ikon Allah ke nan kada ya dauki mataki akan iyalinshi dubu wanan wani irin rayuwane wai don Allah
gaba daya kina neman hanawa yaron nan walwala a rayuwansa.
Shin yar nan daya aurace baki so dashi ko shine yayi maki laifin da har kika tsaneshi hakan dubu don
abin yayi yawa gaskiya shima fa yana da hakkin a kanki idan kin tauyeshi da yawa dubu ?
Yanzu iya ni zakiwa sheri kina zargin ina zuga mama nice zan zuga mama kuma ?
Iyan tace ke ungo nan yar banzan yarinya mara mutunci duk abinda kukeyi ina kallon ku keda uwarki .
Ki dubeni da kyau banyi tsufan da ban fahintar komai a yanzu ba nan gabana yanzu kika gama zuga
uwarki akan yaron nan har abin yaso zama fada tsakaninki da yar uwarki don haka ki shiga taitayinki dani
na fada maki niba dubu bace dake daukan maganan ki.
Shiru tayi don tunda taga iya dinbta juye tasan yanzu idan ta matsa ranta zai iya baci don haka tayi
shiru, ya mike yana fadin yi hakkuri iya ki barta ai tayi Allah na ganinta.
To wanan kalamin da yayine yasa saratu din kuka wai iya taja dan uwanta yana yi mata Allah ya isa kan
abinda bata aikata ba.
Bayan fitanshima iyan bata kyalesu taci gaba da fada tana fadin ta yaya zaki zauna kina bin maganan
yara dubu ?
Ko yaushe yarinyar nan ta zugaki kika aikata abinda ba daidai ba aka yaron nan idan aka taliyo sai a
iske kune baku da gaskiya.
Yaron nan yasan abinda yake yi dubu idan bai isa ba baya tara mata ukku a karkashinsa don haka daga
yau ina son ku cire masa ido akan iyalinsa don Allah ?
Ku barshi ya zauna lafiya da matansa ku barshi ya tsara irin rayuwan da yake so dasu a gidansa don
Allah .
Ke kuma duk abinda zakice kice saukin abin dai gidan wani zakije kema don ba a nan zaki tabbata gidin
uwarki ba saratu dole dai wata rana kiyi aure ki barta.
Kina wanan halin na hade haden fada saratu wa zai yarda da hakan a gidansa in wanan dan uwankine
yayi hakkuri ya zauna dake da halinsa can inda zaki fada ba lalai bane suyi hakkuri da hakan.
Yarinya tana abu mara kyau kina mara mata baya wanan hali idan tacigaba ba zai haifar mata da mai
ido ba nan gaba.
Ranan dai bai samu dawowa gidana ba sai kirana yayi yana fadin mu rufe gida ba zai samu dawowa
gidan mu ba a ranan.
Kishi kumallon mata a take naji wani abu a raina lokaci daya kishi ya rufe min zuciya naji wani irin ba
dadi a kasan zuciyata.
Zancen anty Salmane ya fado min da take cewa Rahama ki cire ido akan duk abinda mijinki zaiyi akan
matarsa matukar kina son ki zauna lafiya ki tsira da aurenki.
To sai kin dinga kawar da kanki ga rayuwansa dana matansa kada ki zamo mai bin kwakwafin abinda
yake tsakaninsu har ki dinga tada jijiyan wuya akai don Allah.
Mace mai wanan halin itake sayawa kanta bakin ciki da kudin ta itake sawa hankalin mijin da kishiya
dana zagaye dasu su farga da halinki mara kyau a kan kishi.
Duk abinda zakiyi Ramah kada kiyi wanda zaki yarda ki kona kanki ki kona mijin ku don Allah tare da
matansa kika sameshi bawai bai sonsu bane ya auroki ?
Suma so da kaunace ya hadashi dasu don haka kada ki yarda kuje lahira ana shari,a dake kan namiji don
Allah ?
Kiyi kokari ki yaki zuciyar ki akan zaman kishi donshi dashi aka halicce mata kishi tun muna kanana
muke da abin mu a cikin jinin ko wace mace yake don kishi kamar hassada yake a zuciyar mace sai ka
tsira daga sherinsa kake samun haske a rayuwan zaman auren ka.
Tayi min irin huduban nan sosai taka min kwantace da kanta tace kingani nan idan D baya gidana
kwata kwata nakan cire zancensa a rainane amma da zaran ya dawo gareni kuma ya zama miji sai ranan
daya bar gidan nan .
Take naji abinda nake ji a lokacin yana ragewa a zuciya inda na fara karanta wallahu Ghalibun har
karshe ina jin wani sanyi a zuciyana.
Karshe falo na fito nasawa Biba kira ta fito muka zauna nan muna dan hira da ita don mu rage dare
karfe tara nace zan kwanta tace to bari ta je daki nace a,a ba zan barki ba ki dawo dakina mu kwana tare
tunda ba kowa a gidan.
A Gaskiya ina jin dadin zama da yarinyar sosai a rayuwata don gwargado tana da gudun zuciya sosai tun
da safe da zaran ta sallame sallah asuba zata fito tayi shara da ta gyaro ko ina har kitchen idan na
kammala abinci takaiwa su salima dake daki kwance ta dauko namu zuwa falo muyi wanka muyi shirin
fita don tare muke barin gida da ita.
Shiyasa nake son shakuwa na tsakani da Allah ya shiga tsakanina da ita tun yanzu kada ta koma tana
shakkata har a zata ina mata wani mugun riko.
Dakin Asmau ya kwana a ranan don saiba tunda ya shigo ta shige daki a zatonta zai biyota irin da suka
saba tun tana jin motsinsu a falon har yakai ta daina ji ta leko ta samu daga shi har Asmaun basu falon a
lokacin.
Duk yadda taso ta taushi zuciyarta yadda kowa ke bata shawara ta kasa hakan a lokacin cikin daren
nan ta kira yarta tana labarta mata abindake faru.
Nan dai ta bata hakkuri akan ta bari da safe zata je gun wani malami suji yadda za ayi inya kama tazone
da kanta saita san karyan da tayi tazo kaduna din suje tare.
Zancen yar uwar nata ta yarda dashi har taji dan sanyi a zuciyarta inda ta kwana tana tunanen daga
mijin har mu biyun don ko Asmau ba kyaleta zatayi ba tunda tagane tana munafuntar ta ko ita fitar da ita
gidan zatayi ta huta da wata kishiya.
Kaiya koda ta samu sa,an hakan ai wata zai dauko mata abinda mata basu gane ba ke nan don Asmau
dai bata tare mata komai ba a rayuwanta.
Don itace take kwarar Asmau ma idan za a fada tsakani da Allah amma tace dani din da take ganin
shigowana gidan da bakar tsafi mu na fulani na juye kan miji ya koma gareni gaba daya yanzu da Asmaun
da bata dauka bakin komai ba duk zatai muna kan mai uwa da wabine lokaci guda ta huta.
Ita dai butinta shine ta bude ido taga ita kadaice a wajen miji sai yarta ban mantawa da case din da
sukayi lokacin akan cikin da Asmaun ta samu ita bata samu ba kafin mijin ya kwanta ciwo.
Case sosai akayi don saida kawu dauda shiya yazo gidan da sunan sulhuntasu aka zauna da mijin dasu
akai case din.
Wai ashe ita Saiba data haihu tace zatayi planning don karta samu ciki yarta karama mijin ya kaita
sukaje sukai planning din.
Sai gashi kwatsam taga Asmau na laulayin ciki tace sun munafunceta ita dashi ta tayar da bala,i ta hana
zaman lafiya a tsakaninsu.
Inda planning din ya sako mata reaction dinsa tana jini akai akai nan kuma hankali ya dawo ya tashi
sukayi ta zuwa asibiti sai da kyat ta samu lafiya.
Bai shigo gidan mu ba don yasan mun fita school sai karfe biyar na yamma yaje ya daukoni school
muka dawo tunda na tunkaro motan naga yadda ya kura min ido nasan ya tsargu shima.
Ina zuwa kan na bude motan nake cewa dashi ina wuni yaya ya mutanen gida kuma ?
Ya dan washe yana fadin shigo mota mana kafin mu gaisa kya tsaya waje kina gaidani muje saimu gaisa
a hanya ya bude min nashiga na zauna yaja motan muka tafi.
Saida muka hau titi da kyau yake fadin ya kuka kwana nace lafiya kalau yasu mama dasu iya kuma
suna lafiya iya ai tace dani wanan zuwan bazan koma ba saina kawota gidanki.
Allah sarki nima haka nace ai kafin kabar gari zanje ina son zuwa na gaidasu ai don baka nan ne banje
ba amma abin na cikin raina sosai.
To dake da ita bansan wa zai fara zuwa ba sai kiyi hakkuri tazo gidan naki inyaso daga baya sai in kaiki
ki gaidasu ko ?
Abinda kace yaya shi za,ayi naga yayi murmushi ya kai hannunshi saman nawa yana murzawa yace iya
sarkin rigima na kula ita kadai ke mara min baya sai salima da Habu game dake Rahama ?
Nace to ayi hakkuri kowama zai mara ma idan sun fahince ka daga baya rashin fahintane a yanzu din
don anyi masu ba daidai ba ?.
Haba dai ni abinda ke ban mamaki dayane shine wai yadda mama ta kasa fahintar manufata har take
zargin wai bani cikin hankalinane.
Na zata manace zata fara farin ciki da wanan abin sai gashi makiran yaran nan sun shiga sun fita suna
neman hadani da ita a yanzu kuma ?
Bandai tambayeshi suwaye ba shi kuma bai fadi sunansu ba nace anty Yanda fa da Abba suna lafiya
ko ?
Wai maria kike nufi sai naga ya bugi bakinshi yana fadin wai sorry sister nake nufi nama rasa yaya zan
kirata a yanzu sai abin ya ban dariya nace to ai surukarkace mana ba dole bane saika saya mata suna
koka kirata da maman Abba kawai idan kana jin nauyintane a yanzu ?
Fine sunan yayi min sosai maman Abba din zaifi sauki an wuce wajen yanzu ai maman Abba din yafi
min saukin komai sosai wallahi.
Bamu je gida ba naga ya dauki hanyar cikin gari wani waje mukaje ya tsayar da mota dan nisa da
mutane ya fita ya shiga wajen .
Ya dan jima a ciki sai can na hangoshi ya fito da ledoji ga wani a bayansa sun nufo wajen motar mu kai
tsaye ya bude bayan motan aka loda mai kayan a ciki ya sallami wanda ya rakoshi din yana mai godiya.
Yana zama yake fadin sorry na barki zaune ko na danyi murmushi na dago kai ina fadin ai baka jima
sosai ba ya tayar da motar muka bar wajen.
Mun hau titi yake fadin naso na dan tsaya in saiwa Asmau magani jiya taban tausayi sosai da dare shine
naso in biya in karba mata magani wajen abokina.
Bari dai in saukeki sai in dawo haba dai idan hakan yafi sauki muje mana Allah dai ya sauketa lafiya naji
yace amin tana wahala sosai don tace min duk kwanakin nan haka take fama da dare.
Allah ya bata lafiya na kara fada cikin rashin wani abu a kasan raina da nake tunane watau a dakin
Asmaun ke nan ya kwana ba saiba ba yadda nake tunane da farko na zata gun saiba ai zai sauka ashe ba
haka abin yake ba.
Munje ya karbo maganin mun kamo hanya yake fadin yanzu da bakowa a gida ita habiba fa dawa take
zama ke nan ?
Na dan nisa ina fadin nima tunanen da nakeyi kenan a raina don nasan ta dawo tun karfe biyu gashisu
anty salima basu gidan yau don da kota dawo suna gida zata samesu.
Kai gaskiya hankalina bai kwanta da hakan ba don kinga diya mace ce kuma gashi ba wani gida kuke
hurda dasu da zata zauna kafin ki dawo ba.
Bayan haka nima ba zanso tana shige shigen gidaje ba gaskiya gara dai din a samo wata mace da idan
ta dawo tana gidan tare da ita.
Saidai banson kuma ai yawa a hana min hutawa na a gidan koda yake bari zan daiyi tunane akan hakan
asan abinyi da zai dace.
Mun isa gidan ban tsaya ba son fitsarin daya cika min marata a lokacin na shiga gidan saida na rage
maratane na fito na samu ya shigo da ledojin an aje a falo.
Biba kuma ta gyara gida har ta dora girki ruwa yana batu tafasa lokacin hakan yasa natsaya na tuka
muna dan semo da zamuci.
Haka kuma na dibar mata kayan miyan da zata daka muna inyi amfani dashi kana nafito na nufi
dakinshi na sameshi yana zaune bakin gado yana waya ganin hakan na juya zan fice dakin da hannu ya
kirani na dawo ya nuna min waje in zauna.
Zaman nayi a gefenshi dan nisa kadan dashi kafanshi yasa ya tokaro kafata hakan yasa na kalloshi yayi
murmushi yake tambayata da hannu wai na kara matsowa na make kafadata alaman a,a.
Ganin zai kamuni yasa na mike tsaye da sauri na fice ina dariya kitchen na koma na samu biba ta hada
miyan tana soya markade na tsaya na karasa na hada.
Ina gab da karasawane naji yasa min kira a falo na amsa na fito bayan na fada mata yadda zatayi ta
sauke idan yayi.
A zaune na sameshi falon naji yace dani why kike guduna tun shekaran jiya Rahama na fahinci hakan.
A,a ba hakana bane yaya ina dai guje muna shiga hakkine shiyasa amma ai ban gujeka ba akan me zan
gujeka kuma ?
Zonan ya fada yana nuna min kusa dashi duk da akujeran dake gefenshi na zauna a lokacin haka yasa
na dan matsa kusa dashi din naji yace Allah sarki.
Kisa a ranki mijin ki Rahama ba jahili bane duk nasan wanan kada ki tunanen hakan a kan mu don Allah
baice don bake keda girki kada in tabaki ba.
Iyaka dai kada mu wuce gona da irine a halaka da har zan shagala in manta da wata a gabana ko a da
Rahama ni jafar banyi hakan a tsakanin abokan zamanki ba balle yanzu da shekaruna suka karu.
Na san me nakeyi na kuma ji dadin hakan da kika san wanan a zuciyar ki don haka ki saki jikinki idan zaki
saka amma tabaki saina taba gaskiya don ni mutum ne mai son hutu a jikin matana dake kusa dani
lokacin.
Ban daiyi wani magana ba yake fadin ga wanan kayab mana kira habiba ta dauke makushi zuwa ciki ki
duba ki gani ban zaunu ba balle na san abinda za a karo maku na amfani.
Mun gode na fada yayi murmushi tare da mamakin komai yayi min irin hakan na amfanin gida zanyi
mashi godiya kamar ba kanshi yaiwa ba abinda bai saba dashiba ke nan ga matansa.
Alam din wayanshi yayi kara ya dauka yana fadin bari yaje massalaci yayi sallah ya mike ashe yana da
alwalanshi ya fita.
Bayan ya fita na kwashe kayan naga lemukan sha masu sanyi a ciki har naman kaji da dai yan abin
makulashe su yughut nakai kitchen na adana na tafi sallah.
Bayan isha,i ya dawo gidan abinci nayi mai tayi baiki ba don ya samu biba tana cin nata a falon ya zauna
ya soma ci yakai rabi wayanshi yai kara ina aje mashi ruwan sha a lokacin ya dauka naji yace gani tafe ya
karasa cin abincin nasa ya mike.
Yake fadin zan je gida wai Asmau ce ke jin jiki nace Allah sarki agaida ita dasu mama zasuji yace ya kara
min saida safe ya fita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/1, 11:07 PM] Zainab Idris Makawa Writer: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A cikin dare muna barci ya bugo min waya saidai wayan tana a silent ban samu dagawa ba lokacin sai
washegari ya sake kira har na shirya lokacin naga kiranshi na dauka a zatona zai tambaya ko mun tashi
ko kuma yai min ina kwana ?
Sai gashi bayan mun gaisa yake min albishir din haihuwar matarshi Asmau data haifi da namiji a cikin
dare .
Da murnata nake fadin cikin farin ciki lah anty Asmau ta haihu Allah ya raya Allah yasa albarka ga yaron
yasa mai akidar addini a zuciyar shi ita kuma uwa Allah ya bata lafiyan shayar dashi sai faman fadin amin
amin nagode Rahama yakeyi.
Nace a shafa min kan baby kafin nazo ganinsa yace zan shafo maki baki ganshi ba bouncing baby dashi
kamana wallahi .
Na kwashe da dariyan yake zakice yana gabana a lokacin sai bayan mun gama wayan nake fadawa
Habiba zancen haihuwa tayi wani dunkunkun tana fadin Allah ya raya.
Abinda su a kullum sukaga mutane sai su nuna basu sanka ba sai ka tsaya kana ta masu dogon
kwantance karshe suce owooo ba zasu ba mutum ko ruwan sha ba.
Kai habiba kowa da irin halinsa haka suke su halinsune hakana ai tace Allah anty shiyasa muka bar
zuwa gidan gaidasu amma da ko wani sallah muna zuwa ai mu gaishesu muka daina.
Shiyasa da akace zan zauna a wajenki na zata halinku daya dasu ai nayi ta kuka ina fadin ban zuwa
maman mu tace in taimaka inzo kada ran uncle ya baci saida nazo naga ba haka kike ba ashe anty ?
Da farko nazone in kwana biyu in koma sai naga ke kina son mutane kina kallon kowa da mutunci kai
biba watau daba ba zama kikazo yi ba ashe tayi dariya tana fadin zan zauna ai anty ba inda zanje yanzu.
Shigowan ya Ibrahim yasa muka mike gaba dayan mu muka fita ya sauke kowan mu ya juyo kamar
yadda ya saba muna a kullum.
Yar uwa na taushi zuciyana sosai akan yaya J da matansa ina kuma rokon Allah daya sassauta min zafin
kishi