Chapter 66 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   66 / 101

195K to 198K   out of 302.2K words

daga dakin nan a yanzu sai mutum biyu kawai za a bari a ciki tare dashi da zasu
zauna su duba halin da yake ciki.

A daidai lokacin kuma su yaya Auwal suka shigo a rude don an kirasu a waya ana sheda masu halin daya
shiga din a lokacin suna wajen karbo maganin da ya habu yai magana a kai.

Ankara masu bayani ya isah bai tsaya likitan yakai karshe ba ya soma magana yana fadin amma na fada
ai kada wanda ya shiga bayan amarya saike mama din me za a barsu su shigo har haka ya faru ?
To ya zanyi inyi magana yarinya tana batun zagina don kawai na fada mata gaskiya ku yanzu ai ku
tsawata mata ta daina kila amma halin yarinyar nan ai baiyi ba wallahi.

Kishi har mutum yana kwance gadon asibiti ba zaki saduda ba yanzu da likita daku kuka fada ai zata
fahinta ko ?

To kuji don Allah duk wanda yazo ya gaidashi ya fita don ba zamu hanaku shigowa duban mijin ku ba
amma a shigo a tsanake a fice daga yau don ba zamu lamuci rashin hankali ba a nan lafiyan dan uwan
mu muke duba a yanzu ba kishin banza ba a nan.

Wanan abinda ya faru yasa jikin kowa sanyi har saiban da take jin take gani mamata lauya mata laifin
komai a kai duk da tasan ba gaskiya bane nice dai na fara gasa mata magana gashi kuma Asmau taki
magana har lokacin sai kukan da take faman yi akan laluran mijinta din.

Basu jima ba ganin ya samu barci ya koma normal sukayi sallama suka koma gida nikan ina asibitin
tunda naga maman tudun wada ta kama min na samu shiga a idanuwansu kishi ke nan dama.

Da kwatance kawu dauda suka tsaya a wani gidan zana dake can dan gefen garin wajen dake dauke da
wasu manyan itatuwa dake karawa mazauna wajen ni,ima.

A gaban gidan ya tsayar da motarshi yayin da mutanen dake zaune a innuwar suka zubo masu idanu
suga masu fitowa daga motan.

Kawu ya fara fita har hulansa na faduwa kasa kafin ya bude bayan motan iya ta sako kafa ta fito tare da
mama shi yaya habu shine ya fito karshe suka nufi wajen mutanen bayan ya rufe motar tashi da key.

Kawu ya fara gaidasu suka amsa tare da masu sannu da zuwa da yaya hanya bayan gama gaishe
gaishensune yake fadin don Allah Tuni fa da cewa matar kamar yadda ake kiranta dashi a wajen.

Wani daga cikin mutanen ne yace wai Tuni kan ai ta dade da barin mu saidai yarta kudidi ke aikin a
yanzu tana ciki in wurinta kuka zo?

Innalillahi iya ta ambata tare da fadin shike nan dauda son kanka ya halakamu ga baki daya yanzu
kuma ya habu yacewa mutumin kana nufin bata raye yanzu ita tuni din ?

Ai kaji me nace yau shekara kusan biyu ke nan da rasuwanta ai amma yarta na ciki itace ta gajeta ga
aikin yanzu aifa shike nan kuma kai habu namu ya samemu kuma a yanzu iya ta kara fada a rude mama
kan hawayene suka soma zubo mata lokaci guda takai tsugunne a waje daya cikin tashin hankali.

Dayan mutumin ke fadin ku karasa ciki koma meye yarta kudidi tana nan zata saurareku ai don ganin
yadda fuskokinsu ya nuna damuwa da tashin hankali lokaci guda jin mutuwan tsohuwan da sukayi.

Yaro aka tura yayi masu iso da matar da aka kira da kudidi din ta dan jima bata fito ba don tana
ganawa da wasu bakin a lokacin .

Yayin datayi masu ison su shigo kawune ya fara shiga dakin da take karban bakinta sai iya sai mama
dubu habune yayi karshen shiga dakin da sallama a bakinsa.
Neman inda zai zauna yayi ya kai tsugune don ita wace suka zo wurinta din tana neman wani abu a
lokacin don haka ta basu baya ba zasuce ga fuskanta ba .

Lokaci guda gabanshi ya fadi yayin da yai arba da wanan matar mai maciji a kwalla na shekarun baya
ba zai taba mantawa da fuskan wanan matar ba.

Ba annuri a fuskan nata gata saye cikin bakaken tufafi irin na mutanen dauri tun daga sama har kasa
sune a jikinta.

Yau Allah yayi kun samu zuwa ke nan abinda ya fito daga bakinta ke nan lokacin data juyo garesu shiru
dan dakin yayi na lokaci guda.

Ta mika hannu ta dauko wani dan kwarya ta girke a tsakiyarsu tana fadin tabaci ke nan tunda na ganku
nan kai habu aina fadama dole saika nememu dama tun abu baikai haka ba har kun bari komai yakai ga
lalacewa.

Sunan habu data kirane ya basu mamaki gaba dayansu har habu din da har lokacin kallon mamaki yake
binta dashi .

Kawune yayi kokarin soma magana cikin wani murya ta dakatar dashi da fadin kai mana shiru don Allah
kome ya faru laifinkane .

Da yar uwarka kazo nan neman sa,a kayi dace an karbama anyi a cikin sa,a amma ka bata komai da
hannunka saboda son kai irin na yan adam daka sawa kanka a rayuwanka.

Kaki yar uwarka kabi ra,ayin matarka duk da gargadin da mahaifiyana tayi maka a wancan lokacin akan
yar uwarka da kake son cin amananta.

Amma ka yarda ka,biyewa matarka kuka cutawa yar uwarka duk irin biyayyan da take maka kaida
matarka amma kukai amfani da biyayyanta kuka cuta mata ba tare da sanin taba.

Naso na taimaka tun abin nan bai kai haka ba amma shu,umar matarka ta hana hakan a lokacin don
bata bar yar uwarka a banza ba ita da zurianta.

Kai kanka kasani kasan irin yadda take duke kan wa yan nan mutane duk akan abin duniya kuke hakan
duk da kusan cewa karshen hakan ba zai maku dadi ba nan gaba.

Yanzu ba wanan ba kun zone akan dan uwaka dake fama da jikinsa ko habu ?

Saita kada kai tana bata fuska kafin tace shi an riga da an sameshi saidai ba yadda akaso samun nasa
ba.

Don ansone ayi mashi karaf daya wanan karon saidai hakan bai samu ba saboda wani dalili kai haba
kasani na fadama wanan yarinyar da ka aura tana da wani siri a tare da ita.

Hakama ita wace ke tare da dan uwar naka naga kamar yar uwar matarkace ita tana da natukar kokari
sosai don Allah ya kyauta zamata tare dashi matuka da komai ya jagule akansa wanan karon don
Abin nasa yayi masa yawa gida ajefeshi haka wajen neman halak dinsa a jefasa, ga makiya yan hassada
suyi masa yawa, haka kuma a gidan matansa basu barshi ba.

Ta sake girgiza kai tana duban wanan faifai din gabanta data rike tana fadin yanzu ba lokacin wani
bincie bane dole bakin rafi zamu a fara bada sadaka .

Saidai idan karyan nan yaki tafiya ya tsaya a waje daya haka na nufin sadakar bai karbu ba ke nan
saidai mu zurwa sarautan Allah ido gaskiya.

Amma da zaran an saka wanan kwaryan ya tafi yabi ruwa insha Allahu wanan sadakan ya karbu ke nan
don haka sadakan zai kasamce biyune a yanzu.

Da wanda zamuyi don dan uwanka dake fama da lalura a yanzu sai kuma naku kaida sauran yan
uwanka da a yanzu ba aikai gareku ba.

Don haka dole muyi gagawan yin riga kafin akanku kamar yadda al,adan abin yake murya iyace ya
katse matar da take fadin.

Aah, Ikon Allah inda ranka kasha kallo dauda nan kuma ka kawo yar uwarka da zurian ta don son kai irin
naku dauda ?

Tsohuwa kiyi halkuri ayi wanan hadayan kafin komai ya kai ga jagulewa a yanzu daga baya mayi duk
wanan bayanin daku a tsanake.

Ta juya gun mama dubu tana fadin kece zaki saka komai a cikin kwaryan nan zaki saka da niyar fansan
rayukan yayanki daga mutanen ruwa masu bada sa,a da yarda,,,,,,,

Kallon juna sukayi tsakani mama da iya har habu sai matar tace shi yasan komai don shi ya dauki
alkawarin hakan garemu tun farko.

Dole mama ta mike ama fada mata duk wani abinda zatayi suka dauki kwaryan dake da abubuwa a
cikinsa hardasu masa kosai alawa ayaba sukari da turmin zani zuwa bakin rafi .

Tun bayan isarsune wajen dole mama dubu din ta taka zuwa ciki ruwan tana bin matar da kwaryan
farko wanda zata fara sadakan dashi akan jafar din .

Gaba dayansu gabasu na faduwa wajen son ayi abin cikin sa,a ba tare da an samu matsala ba matar ta
karbi kwaryan ta fara jera kirari tana daga kwaryan sama tana saukewa .

Suna tsaye suna kallon ikon Allah a gefenta can ta mikowa mama dubu tace tayi niyar ga sadaka ta
kawo masu idan sune sanadin rike danta jafar tana rokon da su sakeshi ta biya sadakan da suke binta
akanshi .

Saidai yadda ta aje kwarya a saman ruwan ko alaman motsi baiyi ba hakan yasa gabansu ya fara
faduwa cikin tashi hankali.
Wanda hakan ke nufin cewa da alama jafar din yana da wuya wanan abin ya barshi hakan na nufin dai
sai abinda ya fito daga Allah gareshi kuma.

Anyi anyi kirari kwarya yaki matsawa daga inda aka ajeshi hakan yasa aka miko mata na sauran yaran
nata wanda shima yake da nasa kalan tarkacen abin mamaki a na dorawa a saman ruwan kwaryan ya
soma tafiya yana bin kabin ruwa da sauri.

Gani hakan yasa habu dake tsaye gefe daya bakinsa dauke da addu,oinsa ya tako daga inda yake zuwa
wajen kwarya farko da aka aje don jafar din ya cira shi ya daga yana fadin ka tafi kaima kamar dan
uwanka ya dora saman ruwa suka bishi da kallon mamaki.

Suna jin tausayin irin halin dayake ciki da har baisan abinda yakeyi ba a lokacin ciki yardan Allah sai
kwaryan ya fara dan juyawa sannu a hankali saman ruwa ya soma tafiya shima .




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/7, 10:35 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to
join my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ

[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa

MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



6️⃣7️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Dan uwa murfin jallo inji manya wasu sukace rabin jiki kuma don hakan ne ya kasance ga habu lokaci
guda don ganin kwaryan da ake nufi ta jafar taki motsi yasa ya dinga karanto addua da sunayen Allah
mai girma sai gashi a fusace ya daga kwaryan ya tura ya fara tafiya saman ruwa cikin yardan ubangiji.

Abin mamaki suke kallo daga iyayyen har mai maganin sun zubawa ikon Allah ido suna bi da kallo tun
wanan kwaryan yana kokarin turjewa ya tsaya a waje daya har yakai ya fara dan tafiya da sauri sauri
yana bin igiyar ruwan kamar yadda dayan kwaryan ya mike tsaye yabi ruwa suna kallo.

Lai habu kakai shu,umin yaro iya ta fada daga gefenshi hakan yasa ya dan kallo iyan yana fadin komai
zanyi akan dan uwana iya.

Amma baka ganin kayi kasada da shiga hurumin daba naka ba habu iyan ta kara fada a hankali yayinda
duk hankalinsu yake kan kwaren dake saman ruwan suna tafiya .

Kaga wanan abin kamar rayuwace malam habu haka ruyuwan bawa yake a wajen ubangijin mu shi ciwo
ba mutuwa bane wani lokaci.

Wahala kawai bawa yake gudu da fitinar ciwo don sai kaga mai lafiya ya tafi ya bar mai jinya a kwance
inda rabon mikewa sai majinyacin ya mike shi wanda yake tsaye yakai kwance.

Kallonta iya tayi kallo dake nuna akwai magana ke nan ga wanan zancen nata bata kula ba tana
surkullensu na yan bori har zuwa lokacin da ta dago garesu tana fadin da alama dai sadaka ya karbu ke
nan sai dai ayi fatan Allah ya tsare.

Akwai abubuwa da ya kamata ace kun sani tun wajen amsan maganin nan wanda nake ganin kai
malam dauda ya sani a lokacin.

Kawu dauda yana jin hakan ya gyara tsayuwanshi yana dan kame kame ta karbe da fadin baida matsala
tun lokacin da abin ya damu maman mu ta sanar dani komai akan haka har zuwan da matarka tayi daga
baya tana neman a bata aikin a mayar dashi wani nau,in sai daga bayane hakan ya damu maman mu
kuma bayan tayi aikin abin ya koma yana damunta wanan yasa na fita neman ku don kwantacen da
matarka tayi muna a lokacin . shi nayi amfani wajen nemanku nazo har zaria din a wajenta naji komai a
cikin hikima don yadda najata a jikina sosai a lokacin.
Naso ace kunzo lokacin da mahaifiyar mu take raye saidai hakan bai samu ba don kaddara ya riga fata a
cikin lamarin.

Kai yanzu ga yar uwarka bata san abinda kai da matarka kuke shiryawa akanta ba duk dadewan nan ya
kamata ace ka fito fili a yanzu ka sanar da ita manufarka a kanka dakai da matarka.

Me zai fada a yanzu ai gara kawai yayi shiru don hakan ma ai maganace don jin baida amfani a wajen
mu yanzu tunda ko yanzu Allah ya baiyana muna nufinsu a kanmu.

Ban taba zaton hakan ba yaya ko mutuwa nayi na taso akace kaine kayi min hakan akan zuri,ata zance
kazafi akai maka don a shiga tsakanina dakai.

Wai sai gashi da raina da lafiyata hakan ya faru yau a gabana yaya ka kasa mussa wanan zancen da aka
dade ana fada min ina fadin karyane zalla zumuncine kawai a tsakanin mu.

Ashe abin ba haka bane yadda na dauka kai a wajenka da wani manufa ka ke nuna min zumuncinka a
kaina don kawai,,,,

Kukane yaci karfin ta wanda yasa habu ya taso daga inda yake yazo ya rike mahaifiyar tasu da komai
yake iya faruwa da ita a lokacin don yadda yanayinta ya nuna a lokacin kamar bata cikin hankalinta.

Shima kawu dauda din sai fadi yake na dade da nadaman haka Dubu tun bayan dana fahinci cewa
kamar yaran nan sun gano irin abinda Hafsatu ke izani inayi akansu din.

Tundai ma shi Habu da har ya fara fitowa fili yana fada min magana a fakaice wanan yasa na fara
neman mafita daga kaidin ita hafsatu na yanke shawaran in kara aure,,,,

Daga baya ke nan dai dauda kaji kunya wallahi ka rasa wanda zaka zallunta sai yar uwarka akan abin
duniya me yaran nan suka rageka dashi a matsayin ka na kawunsu ?

Malam dauda kadai fadane amma hakan bashine nadamarka ba ko in fada a nan gaban kowa wanan
abinda ka fada bashi bane nadamarka mai magani ta fada.

Kinga idan abinda ya kawomu har an gama a barmu mu tafi don dan uwana dake can kwance ba lafiya
munzo nan da sunan wunine don bamuzo da niyar kwana ba nan da zaria akwai nisa sosai don haka
zamu koma yanzu .

Ya fada yana kokarin mikewa tsaye don duk wanan bashine a gabanshi ba zancen dan uwansa shine ke
zuciyarsa din yana ganin kamar wani abu zai iya samun jafar din kafin su dawo zaria a yadda suka barshi
din.

Ba yanzu ya shirya daukan mataki a gun kawu ba sai bayan komai ya lafa yake son su tunkari dan uwan
mahaifiyarsu din da matarshi.

Don tunda sukai waya da yaya Isah ya sanar mai halin da suke ciki asibiti da jafar din hankalinshi ya
tashi yake ganin ai kamar baida rayuwane sun boye mashine kawai.
Sai bayan sunyi nisa yake sanar dasu irin halin da akace Jafar din ya shiga bayansu wanan ya kara daga
masu hankali sosai.

ZARIA

Tun bayan faruwan hakan muna dakin zaune nida mama da inna don ita umma ta koma gida don basu
watsewa su bar gidan ba kowa sukace.

Inda yaya isa ya gargada yan uwa yace su koma gida ayi masa addua tunda likitoci sunce ba zasu bar
kowa ya shiga ba kuma dakin da yake kwance din.

Bayan na idar da sallah magaribane inda nake zaune makure a cikin damuwa wayata dake cikin yar
jakata ta dauki kara na dauko ina dubawa abin mamaki dan uwana Dagene ke kirana a lokacin.

Na dauka murya ba dadi ina amsawa yake fadin yaya yaji muryata haka kamar banda lafiya ?

Ban iya bashi amsa ba sai kukan dana fashe dashi lokaci guda a cikin harshen fulatanci nake masa
bayanin halinda mijin nawa yake ciki.

Wai tsaya Anini ko dai zancen mijinkine naji hardo da nayi da baffa dazun nan yake fada min yaji hardo
ya bugowa baffa waya suna zancen don ya bashi wani makari da zai masa amfani dashi.

Asalin maganin baffa ya dauke daga kakansu shi kadai kedashi a hannunsa yanzu nan dai yake fada
min a ranan idan baffa ya fita yawon darensa zai shiga ya dauko min tun da safe zai shigo mota yazo
zaria dashi .

Naji dadin hakan sosai don nasan tunda yayi alkawari har in ya samu daman daukowa zai kawo din naja
bakina nayi shiru don ba abinda zan fadawa wani bane zancen daya shafeni ni kadaine wanan saiko yar
uwata.

Karfe goma yaya Auwal yace na fito mu tafi su saukeni gida don zai mayar dasu mama da inna gida a
lokacin ba zan iya rokonsa ya barni ba .

Saidai furucin mamane yasa naji sanyi don ita ke fadin Auwal kubar yarinyar nan ta zauna kusa dashi
don ko dazun daya rikice badon itaba bamu san yadda zamuyi ba.

Taje dai ta shirya ta dawo nima zan tsaya a nan din tare da ita ya kasance ta samu mace a kusa da ita
sai yaya Isah yace amma mama kinga,,,,,,,

Abinda na fada ke nan isah kubar yarinyar nan a kusa da mijinta har in kuna skn ganin cigaban lamarin
nan ga dan uwanku.

Hakan da mama ta fada shine yayi sanadin zamana da ita a kusa da yaya din ko wani lokaci don mama
irin matan nan ne masu tsare gida ga bada umurni ga iyalinsu wanan yasa take jan girmanta akoda
yaushe.
A can gidan su Jafar din kuma tun bayan barin su asibiti da suka isa

66 / 101