Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
muke dasu duka har shi.
Asmau cema suka kwasa dashi sosai da zancen ya fito cewa Saiba zata dawo gidan har sukai fada yace
idan yayi niya ita bata isa ta hanashi ba .
Wanan zancen kuma yazo min shima na nuna kamar banji ba saidai a wanan karon na kasa daure
hakan tunda nima mutym ce mai jini a jika ai.
Na danyi fushin hakan kuma ya fahinceni saidai tunda banyi mai magana ba shima ya shareni akan
zancen ya nuna ba komai.
Ranan daya dawo gidan muma ban bashi wani kulawa sosai ba kamar yadda na saba bashi abinci kafin
ya dawo daga sallah na aje mai komai na koma dakina na kwanta.
Ina jin motsinshi daya dawo ya zauna falo yana waya amma ban fito falon ba yanayi yana kallon kofana
har ya gama yake tambayan Biba ke ina antyn ki take ?
Tana daki uncle naji muryanta tana bashi amsa lafiya take kuwa ya tambaya yana mikewa naji tace in
dai ba yanzu ba lafiya kalau take.
Mikewa yayi ya shigo dakin ina kwance kasa da tasbaha a hannuna da nake ja ya tsaya daga kofa yana
fadin yaya dai lafiya kike kuwa ?
Na dago na bashi amsa a takaice kamar yadda Biba ta fada mai don ba halin karya gareni yanzu nace
lafiya sai yabini da wani irin kallo na shareshi tunda na bashi amsan.
To yaya abinci fa ya fada a inda yake din nace yana falo na aje ma yayi shiru kafin yace ba za a bani ba
yau ke nan ko ?
Nayi shiru can naji yace bakiji me nace bane kin kyaleni yana falo na ajema ai na fada kamar a hasale
hakan yasa ya karaso yana fadin wai lafiya kike kuwa Rahama ?
Lafiyata kalau nace maka ban dai jin tashine yau Allah ko yau ban samun gata ke nan nan ma ban bashi
amsa ba na kyaleshi.
Ya dan jima tsaye a kaina yana kare min kallo kafin ya gama nazarina ya tabbatar da lafiya din nake sai
naji ya juya yana murmushi ya fita.
Har yakai kofa yake fadin idan kin gama saiki taso ki ban abincin ban amsa mashi ba ya fice ina jinshi ya
jima a wajen zaune naki tasowa in sameshi din.
Saida na tabbatar daya gama ya shige na fito don kawar da kayan na kwashe zuwa kitchen a lokacin na
farga da kamar bai taba kayan abincin ba kenan haka na nufin baici ba ko ?
Na bude warmer din abincin naga bai taba ba nima na shareshi shiya sani tunda duk kyautatawan da
nake mai bai gani yafi bukatan ya dawo da yar cin mutuncin matarshi azo a dora inda aka tsaya tunda ba
barin halinta zatayi ba.
Na juye abincin nasa a fridge don kada ya lalace na koma dakina na kwanta ban ko tayar da Biba tazo
dakina mu kwanta ba yadda muka saba da ita idan baya gidan.
Barci ko a ranan rabi da rabi nayisa don haka bai taba faruwa a tsakanin mu ba inba lokacin da baida
lafiya din nan ba sai wanan karon.
Washegarima ban lekashi ba bai fito ba har na kare abin karyawa na aje mai na koma daki nayi wanka
na gyara jikina na kwanta ina jin biba ta gama gyaran gida har ta saka kamshi yana tashi na lumshe idona
tagama shirinta zuwa school lokacin ta shigo dakina tana fadin anty nagama zan tafi.
Hakan yasa na bude idona da sukai ja a lokacin don bacin rai dana sakawa kaina ina fadin ga kudin
motarki nan dana kashi saman mirrow ta nufi wajen ta dauka.
Da yake tayi wayau a yanzu harta dan juya zata fita sai kuma ta tsaya tana fadin anty lafiya kike kuwa
ko jiya uncle yana tambayana da bai ganki ba nace ban jin dadin jikinane Biba tayi min sannu ta fita.
Ina jinshi ya shirya ya fito ya leko dakina ina kwace saman lafiyayyen gadona daya sha gyara na harde
kafa nayi makari da hannuna na rufe fuskana.
Ya dan juma a tsaye kafin ya juya ya fita can naji karan motarshi ya tayar ya bar gidan na sauke ajiyan
zuciya ina jan tsuki.
A lokacin yadda nake jin haushinsa a zuciyana komai zai faru ya faru din tsakanun mu tunda ba
kwanciyan hankali yake kauna bashi.
In mama bata damu da kwanciyan hankalinshi ba aishi yasan abinda ke nan da zai biye mata don kawai
taga farin cikin mu ya ragu a gidan.
Tunda yanzu tana zaton rashin Saibane duk ya jawo mata wani matsalan da take ciki na rashin samun
hankalin danta yadda take son ta mulkeshi.
Sunce da Saiba tana nan wani abin dole yayi don dole ko yaushe yana gidan ai amma ita Asmau da ita
da babu duk dayane a wajenshi tunda bata maida kanta abun kwarai ba a wajen kowa.
Shigowan Aminu da yayine yazo ya tsaya daga kofa yana fadin mummy ina kwana yasa na fito falon na
zauna a tare dashi yana karyawa yana ban labarin zirga zirgan da yakeyi don cika takardunshi a school
din .
Bayan Aminu ya gamane nan ma ban shiga daki ba nayi zaune a falon lokacin ya shigo Aminu ya
gaidashi ya mike ya fita ni kuma nayi zaune ban dago kaina bama balle in gaida shi.
Abinda yasa nake baki wanan labarin shine wani lokacin mu mata idan haka ya faru bamu tsayawa mu
duba mu,amulan mu da namiji akan ai zancen bai shafemu ba shiya shafa makin mu kara kyautata hakan
sai mu barar da daman mu daga wajen jan ajin da muke nema wajen miji din.
Dakinsa ya shiga ya fito ina kallo bai taba abin karyawan dana aje mashi ba alama ya nuna shima ya
hau dani lokacin ban kumayi dabaran yi mashi magana daya karya ba .
Har ya fito saida yakai kofa ya juyo yana fadin shi zai shiga kaduna wani abu wani zafinsa na kara ji a
zuciyana a yan kwanakin nan ya matsawa kaduna din nan sosai yana shiga lokaci lokaci ashe bikon
matarshi yake zuwa yi na raya hakan a zuciyana bance dashi komai ba dai har ya fita.
Ashe hakan yaci masa rai bai bar zaria ba saida yakai karana wajen maman tudu akan tayi min fada kan
halin dana dauko mashi tunda abin bai shafeni ba a cewarshi.
Matsalansuce shi da matanshi baiga abin da ya shafoni ciki ba tun nan mama tace dashi ya shafota
takan malami tunda in haukan Nusaiba ya tashi kowa hadewa takeyi tayi dashi.
Ita dai ta bari tunda bata da matsala da haka sin tana gidanta daban meye nata a ciki sun jima da mama
kafin ya fito ya bar gidan zuwa inda zashin .
Da rana tsaka saiga mama a gidan nayi mamakin zuwanta don in zasuzo aida safe suke zuwa yaya
Auwal daya kawota tace dashi ya tafi idan ta gama zata hawo motan kasuwa ta dawo gida.
Tun nan na gane akwai magana kuma gashi ita kadai tazo ba Nafisa dake rakota idan zatazo din na dai
tareta yadda na saba na aje mata komai na koma kasa gefe muna gaisawa.
A lokacin ta fara yi min maganan daya kawo ta din wajena wai yace baiso ya fadawa iyayyena tunda
haka bai taba shiga tsakanin mu ba dashi.
Mama ya fada mana sai me ko cikin nan da nake jira in haife yace ba zan haifa a gidan nan ba ina da
wajen haihuwanshi ai.
Ni dai ba zan shaganta abina ba tunda Allah ya sheda shi yayi min cikin wallahi ban taba zina ba balle
kishiya ta kira min zina da aurena.
Shiyasan abunda yake tsunta a wajenta har yake ganin a yanzu ya dace ya dawo da ita dakinta tazo taci
gaba da aibanta min abinda zan haifa a gidan.
Kukane yazo min da nake fadan hakan a lokacin da sauri mama tace tana farashi yadda ta kodu din nan
bata farawa ai inane bataje kamun kafa ba don ya maidota dakinta.
Anyi na malamai da bokaye baici ba yanzu ta koma na lalama ga yan uwa da abokan arziki har sukaciwo
karfinsa ta yarinya yanzu ya yarda.
Mama shi ya shafa cikin nan kawai ya tsayar dani gidan nan wallahi da ba zata sameni a gidan nan
bama to a nan na sameshi nan zan haifeshi in wuce.
Ke yar nan kada ki soma wanan gangancin da kike kokarinyi a yanzu don Allah ki wuce ki bar dan ko yar
dawa hannunta ta kama maki ko me ita bagata ta dawo don yarta ba ?
Sai kece da baki da mafadi zaki bar naki ki tafi a yadda na amsa kuma nakeyi tasan zan aika don sanin
halin mu fulani da karfin hali da tayi.
A,a Rahamatu kada ki hakan don Allah kina aon mijin ki yana sonki kada ki yarda fushin zuciya ya
rudeki ga banza kan wata can da bata shiryawa aure ba.
Sau nawa zan fada maki hakan ne ita fa abinda take nema taga ya samune a tsakanin yau ko wani
shirin tayo a kanku nuna mata kinfi karfinta ke.
Sai Allah ba boka ba malam kike lamarinki barsu badai dubu ta kafe sai ya dawo da ita a yanzu sukace
ba to zai fita a tsakaninsu.
Kusa ido kuyi kallo kawai indai dubu ce ita kuma itace kwana nawane za a fara jin tsakaninsu ?
Nayi kuka sosai haka na nunawa mama din na hakkura amma itama ta fahinci da sauran zance a
zuciyana saida tayi sallah la,asar na rakota zuwa titi nidasu Aminu muka daukar mata drop har gida na
biya .
Koda ya dawo gidanta ya fara zuwa take mayar mashi da yadda mukayi tace kasan halin fulani malam
to kada kace zakaja zancen nan a bangareka don Allah ?
Don yarinyar nan ta nuna min cewa haihuwan cikin nan na jikinta ya tsayar da ita tafiyanta zatayi ta
barku .
Har ya soma fadin ta tafi mana mama halan tare aka haifemu da ba zan iya rabuwa da ita ba ko an fada
mata idan ta tafi rayuwana zai bar,,,,,,,
Karka soma wallahi don ka yarda yarinyar nan ta subuce maka malam saika dawo ka raina kanka
wallahi ana zama da mace don wasu abubuwa nata daga ciki da zan iya fada na farko ga yarinyar nan
shine hakarci ko iya wanan kadai ya isheka shiga wani hali idan ta barka a yau din nan.
To mama me nayiwa Rahama da zata dauki fushi dani haka in ma fadana da Asmaune takewa ai,bada
ita nayi ba don me zata saka kanta a zancen mu ita.
Yanzu dai na fadama yarinyar nan kasansu fulani da riko don haka kabi sannu idan ka yarda ta
subucema kuma sai kayi nadama wallahi.
Duk mutumin da zai zauna dakai tsakani da Allah shine abokin zama ba mutumin dake son ka a fatar
baki ba kaidai kasan wanan yarinyar kaduna din komewa halinku zakuyi da ita ko yanzu.
Ya dago ya dube mama din tace kwarai kaika yarda da tuban mazurun da tayine a yanzu ai hali zanen
dutsene amma mama tayi alkawarin daina duk wani hali nata na baya za a zauna lafiya sosai da ita yanzu
.
Aifa ni yanzu bance kada ka dawo da matarka ba malam amma kada kayi saki reshe kama ganye a
gidan ka tunda uwarka tace ka mayar da ita meye nawa yanzu a cikin hana hakan da zanyi.
Da tun farkone wallahi malam zan hanaka ka dawo da yarinyar nan gidanka duk da nasan harkan
aurene idan bai mutu ba ba mahalukin daya isa ya raba tsakanin ku yanzu ko mahaufiyarku ta riga da ta
ciwo kanka ka yarda da hakan kaga idan na hana a yanzu Allah ba zai barni ba nima tunda uwa nake
nima ga wasu yayan.
Wa yan nan maganganu na mama tudu sun tsaya mai a zuciya don har sun sakashi wasi wasin a
lokacin.
Nayi abincin kamar yadda na saba amma a ranan ban aje a falo ba kamar kullum kitchen na barshi na
koma daki na kwanta bai shigo gida ba sai bayan isha,i ya biya can gidan yayi masu saida safe.
Ina jin shigowanshi amma ban fito ba har ya shiga daki ya dan jima a ciki ya watsa ruwa kafin ya fito ba
zance maki yaya ya warke garau ba a yanzu.
Har yanzu akwai sauran jin jiki a tare dashi idan ka sanshi a baya ka kalleshi yanzu kasan da sauran ciwo
a jikinshi karfin hali yakeyi irin na dan adam mai tafiya da buri a tare dashi.
Dakina ya nufo direct ya shigo sai kamshi yakeyi cikin dakewa da sanyin jiki yake fadin kwance ake ne
kingani sai yanzu na dawo na biya can gidan nayi masu saida safene.
A raina nace ai dole ka kai dare a can tunda an mannaka da bokaya ance mai kishiya bata mutuwar
Allah haka zancen gizo bai wuce na koki ba ai.
Jin bance komai ba yasa shi fadin banga abincina a falo ba mana ko yau baki iya girkawa bane kuma sai
lokacin nayi magana nace.
Naga ka daina cine yasa ban aje falo ba amma nayi girki tun dazun ai dan murmushi yayi cikin tsigan
neman shiri a tsakanin mu yace kai Rahama kina dai son zance ni banga abin fushi a cikin zancen nan
ba ?
Nusaiba ce fa ba wata mace zan dauko wace baki sani ba kin riga da kinsan halinta saidai ban san
abinda dan gulman naki yazo ya fada maki ba kika hau fushi haka.
Wani dan gulma aini ba wawiya bace da wani zaizo ya zugani ni mutuncina da darajan abinda zan haifa
na jawa tunda ita dabbama ya fita hankali.
Taso kiban abinci don Allah tun safe dana fita ban karya ba har yanzu har ji nake kamar banda lafiya yau
a jikina tunda an saba cika min ciki kwana biyu kuma anki kulani ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/30, 9:50 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zance ya tabbata kuwa don Nusaiba dai Aminu ya fara fada min yana ganin kamar wanan dayan matar
uncle fa ta dawo.
Don yaga motoci da mata sun shigo sunata guda zuwa part dinsu a hakan kuma salima ta kiran ita da
Asmau da yanzu tun bayan kiran da Asmau din tayi min muke dan gaisawa da ita sama sama don data
kira cewa tayi dani.
A Amarya Rahama dai kin sharemu gaba daya ko kizo gidan nan ki duba yaranki inmu ba dubamu ?
Nace ban shareku ba anty gani nayi dai ya kamata naje gida na dawo kece yakamata ace kinzo kin
duba jikina ai sai naga ba haka ba.
Lalai kuwa anyi haka to amma ai kinsan halin gidan mu Rahama yanzu da anji nazo gidanki sai a fassara
min abin da wani manufa ta daban shiya ban zo ba.
Anty in baki zo ba saiki turo min yaran ba tayi dariya kafin tace to kinji dai mutumiyar mu zata dawo ko
mama ta matsa wai ta dawo tunda dukkan mu bamu da amfani kanmu kawai muka sani mu sai yan
uwan mu.
Ikon Allah mudin to da wa zamu sani banyan kanmu da yan uwan mu dake kulamu wanda bai
kaunanka ai kaima kayi nisa dashi ni ban damu wani yasoni ba bayan Allah.
Son Allah kadai da Annabinsa nake nema sai mijina ban damu da son wani ko wata ba can don basu a
gabana don Allah anty ki sa masu ido ki daina kula kowa da shirmensu neman bakinki sukeyi dama aji
dadin bata labarin idan ta dawo.
Ta dawo mana ba daina halinta zatayi ba ai saima abinda zai karu a yanzu don hakani dawowanta bai
taba damuna ba anty ni kawai abinda nake so dake anty shine kiyi hakkuri don Allah.
Ban dai daukeki makiyana ba don zama tare ya hadamu a yayata nake kallon ki har yanzu naji tana
fadin wallahi nasani Rahama.
To kiyi hakkuri abinda kika san baiso ki daina don Allah kema ki zage yadda kowa keyi a zama daidai ki
fita batunsu kada ki biye mata yaran nan sunyi wayau a yanzu sun fara fahintar komai fa.
Mun jima da ita muna magana har ina mamakin ko nawa ta saka a wayanta lokacin data dade haka
tana magana dani din.
Tun bayan haka muke gaisawa shine a ranan ta kirani take fada min zancen dawowan Saiba din ita ma
na fahinci nufinta so take ta hada kai dani a yanzu ni kuma ba zan yarda da hakan ba hadin kai da kishiya
cutane adaiyi zaman lafiya kawai kowa ya mutunta juna shike nan a zauna lafiya.
Munyi hakan na kashe wayan tare da dimbin tunane a zuciyana a ranan yaya bai gari yayi tafiya amma
ya kirani tunda safe yana sheda min cewa zai dawo a ranan .
Don yanzu tafiyanshi ba irin na dadewan nan bane da yakeyi a baya iyankashi yayi kwana biyu ko ukku
ya dawo gida.
Duk da nasan tunda Nusaiba ta dawo bai garin don haka idan ya dawo a can zai sauka donshine ban
matsawa kaina da mashi girki ba duk da nice da girki idan ya dawo din.
Ashe wai hakan plan din Saratu ce na saiban ta tare a lokacin don su bata muna plan su hadani fada da
yaya don dole sun san in anyi hakan zamu samu matsala a tsakanin mu dani dashi.
Tun yana can ya samu labarin dawowanta din don suna waya yake jin hayaniya yake tambayan tana
ina tace zaria dakinta don ta dawo tun jiya daga haka baice komai ba.
Koda ya dawo din kuma gidana yayo direct ana ruwan sama a lokacin muna daki nida Biba dake zaune
tana assignment ya shigo ita naji tana fadin uncle ya dawo.
Jin hakan yasa nace ina take fadin taji muryanshi a falo kafin nayi wani magana sai gashi a dakin nawa
yana fadin nakan fada maku idan kun shiga ku dinga