Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
rayuwan kuma ?
Tun fitanshi na shiga kitchen na dafa ruwan dumi na saka a flask na juye saura naje bandaki dashi naji
dadin tsarki da ruwan dumin sosai don haka na kai har magariba ina gasa kaina da ruwan dumi hakan da
nayi yasa na samu walwala na iya yin girkin dare dan abinda zamuci da dare din.
Ko kafin ya dawo nayi tuwon semo da miyar busassan kubewa don shine gareni lokacin amma nayi
amfani da nama dake shake a cikin freezer kitchen din.
Inda na dan cika tattasai da albasa da dab attah kadan sai kayan yaji dana barbada don kamshin miyan
yabada dan dano nama kuma na dafeshi sosai tunda miyar yaukine nayi ga kamshin daddawa dake tashi
a ciki na hada komai na shiga wanka a gurguje na dade zaune a ruwan dumi kafin na fito nayi wanka
sabulu da soso na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina idarwa na mike kada jikina ya bushe sanyi
ya sauka min na nufi mirro na gyara jikina sallah isha nayi na saka wani dogon rigan cotton mai mayafi
rigan anyishi mai sharp na saka hula kalan kayan sky colour na dan yafa gyalen shi a wuyana.
Nasan don inda yake a lokacin ya kusa dawowa gida hakan yasa na kara feshe ko ina da air freshener
take gidan ya dauki kamshin dadi ban shafa turare a jikina saidai roll on a arm dina zuwa wuya don zufa.
Karan bude get din gidan dake bada wani sauti saboda nauyinsa yasa na gane ya dawo a lokacin.
Yana shigowa direct dakina ya nufo ina kwance nayi rigingine saman gado da littafi a hannuna da nake
dubawa ya shigo dakin da sallama.
Na dan dago kai ina mashi sannu da zuwa na sauke kafana daga saman gadon don in mike in karbi
ledan dake hannusa don malaman mu Lubbunah ta fada muna hakan waje biyu yake da amfani karban
kaya a hannun miji.
Na farko ladan da zaki samu daga Allah don girmama mijin da kikayi da aure sai na biyu kuma hakan na
saka wani irn kauna a tsakanin miji da mata na ban girma donshi ta horemu dayin hakan komai kankanta
abu muyi saurin karba daga hannuwan mazajen mu.
Mu,sanman mazan mu na hausa dake amfani da addini da al,ada lokaci guda hakan ya zama addini da
dabi,an malam bahaushe.
Ya gane me zanyi don idona na kan ledan hakan yasa da sauri yace No ki zauna abinki ba wani abu
bane ai a ciki kazace sai fresh milk na kawo maki kisha.
Ban dai zauna din ba na mike nazo na karba ina gasheshi da dawowa jikinsa ya hada da nawa ya matse
waje daya yana fadin yaya jikin naki yanzu ?
Naji sauki na fada a cikin kunya dajin nauyinsa don irin yadda ya hade jikin mu a waje daya din kamar
yana neman wani abu a jikin nawa.
Kin tabbatar ya kara fada nayi dan murmushi kawai ban bashi amsa ba yake fadin hankalina ya tashi
sosai dazun Rahama iam sorry banyi hakan don kaina ba so sorry kiyi hakkuri da hakan don Allah ?
Na boye kaina a cikin jikinshi yacigaba da fadin Allah yayi maki albarka naji dadi sosai jiyan kamar nayi
kuwa ban sani ba koma nayi din ai ?
Dariya yaso subbuce min na kara noke kaina saman jikinshi yace wallahi Rahama komai naki yai min a
rayuwata ina sonki sosai mu sanman kamshin nan naki don Allah ki bani hadin kai mu zauna lafiya.
Kaina gyada kana na furta a hankali da in sha Allahu yace ba zan manta da rayuwan daren jiya ba da
komai na cikinsa har wanan cizon da aka gyatsira min a wuya .
Ina son wanan daren har kullum ina son abinda ya faru a daren abinda ya faru a cikinsa wani irin nauyi
da kunyane suka rufeni nasa.
Yace Allah kuwa gaskiya nake fada Rahama na rasa inda zan saka kaina a jiyan kamar in bude cikina ki
shiga naji lokacin don tsaban sonki dan Allah kici gaba da inganta min sauran dararen da zamuyi tare
dake a rayuwan mu.
Ya dagoni yana kokarin mu hada ido dashi yake fadan hakan na kasa yadda yake so din na daiyi kokarin
daga mashi kai alaman in sha Allahu.
Naji yakai min kiss a goshi yana fadin bari naje na rage kayan nan a jikina in dan watsa ruwa in dawo in
baki abinci ya fada tare da sakeni ya juya ya fita daga dakin.
Zaune nakai a hankali bakin gado ina sakin ajiyan zuciya wai yau ni Rahama mutum kamar yaya Jafar
yake fadawa irin wanan maganan a kaina.
Dama ace ni kadaine fa in more miji har miji a nan saidai kash kadara ta riga fata nidin a haka ragowa
na samu ragowan wasu ma bako mutum daya ba.
Take naji wani irin kishin matan nasa ya tokare min zuciya a karo na farko tun faruwan alakan hada
aurena dashi sai wanan karon naji zafin matan nasa.
Zafi na daban ba irin wanda nake ji nasu ba a baya akan matsin da suke min kan yar uwata wanan wani
na dabanne ya ziyarci zuciyana.
Kwance nake rigingine a yadda ya sameni da farko na soma tunanen ko yaya zamana dasu yanzu a
matsayin kishiyarsu zai kaya oho ?
Na sandai wata rana dole a hadu an kuma ce mai hali baya fasa halinsa sai yayi koda kadan ne ashe
zan iya kyalewa in shanye duk wani cin fuskan da zasu iya min kuwa ?
Kai ina dole in rama a yanzu ga duk wace taso barazana a kaina basu ba koma wacece indai akan yaya
jafar ne ba zan taba kyale mashi ba kuwa.
Haka ya dawo ya sameni Tsarki da aminci su tabata ga Allah na furta a raina lokacin dana kyala ido
nagashi tsaye a kofana cikin kananun kaya wando da riga iri daya saidai wandon iya gwiwa ya tsaya
mashi haka kuma rigan ya dan sauka ya dan rufe zuwa cinyarsa masu ruwan kalan dorawa da akaiwa
rubutu a gaban rigan da gefen wando cikin manyan haruffa da FREE MAN.
Na nanata kalman a bakina har lokacin yana tsaye yana waya yana fadin gaba daya za a kwarai
massallacin na fada masu sai a kara mashi girman tako goma ako wani bangare tunda akwai sauran fili
wadattace da za ai hakan.
Duk wani kayan da za a kawata massalacin dashi na riga da naba garba kwangilansa shi zai sayo ya
kawo banson aikin nan ya wuce nan da wata biyu insha Allahu tunda akwai komai a kasa.
Aina fada mai Habu zai kawo mai kudin komai da mukai killisafi dana zirga zirgansa duka gaba daya ya
dan jima yana saurareb bayanin abokin maganan nasa kafin yace hakan ba matsala bane ai ayi komai
yadda ya dace kawai.
Ya kashe wayan yana kallona ban farga daya gama wayan nasa ba saida ya ware hannayesa alaman
inzo garesa niko na shagala da kallonsa ban farga ba lokacin na sauke wani irin ajiyan zuciya ina mikewa.
Na tako zuwa wajenshi hannuna ya rike a cikin nasa yana rada min tafiyan nan naki ba daidai bane har
yanzu Allah ya taimakeni ba kowa a gidan nan danaji kunyar hakan a idon mashi.
Ledan daya shigo dashi din ya dauka nidai har mamaki yake ban yadda shi bai kunyata ko nauyina
zakice mun dade da shakuwa dashine lokacin.
Falo mukayiwa tsinke saida yaga na zauna ya nufi gaban tv ya kunna ya dawo ya zauna lokacin nake
fadin a dauko abincine nan ?
Abinci kuma ya dago da sauri yana tambayana nace na girka abinci dazun danaji sauki Ohho no no a
hakan kika wahalal da kanki Rahama ?
Baki da lafiya fa kin sani da badon karna shafa maki bakin jini ba daga zuwan ki Allah ba inda zan fita
yau ina gidan nan ina jinyar abina nida nayi barnana da kaina.
To amma rashin fitana din zai iya shafa maki laifi ga mutane da yawa musan man mutanen gidan mu sai
a dauka kece kika hanani fita.
Da ina nan ba zakiyi wanan wahalan ba haka na dan kalleshi cikin marairaicewa nake fadin don nayiwa
yayana girki kuma shine wahala ?
Haba dai ai naji saukina kuma ban iya badin ka da yunwa tunda nasan kai kafi son cin abincin gida ko
yaushe meye a cikin dan girkin iya bakinka kadai ?
Na mike zuwa dinning na dauko abincin zuwa inda yake zaune na aje a gabanshi ya kalli kayan yana
fadin kinsha fama wallahi.
Allah yai maki albarka Rahama sunan ki yaci ke din mai tausayice da imani da har kika iya fahintana
wallahi kamar kin shiga raina kin gani ina tunanen abinda zanci mai dan nauyi da daren nan kafin in
kwanta.
Kinsan ni din rainon iyace ai ban wanka in bushe a gidan mu ina dakin iya duk da mahaifin mu bai yarda
na zauna a wajenta dindindinba saidai in tafi in dawo gidan mu in kwana.
Ya bude abincin daidai ina aje mashi ruwan sha dana wanke hannuwa ido ya lumshe ganin yadda
semon yabada ma,ana a cikin ledan dana daresu a ciki kulli biyune na saka mai ya bude miyan yana furta
masha Allah.
Zaman dirsha yayi a kasa da alaman haka zaici abincin a lokacin ina kokarin kaiwa zaune kujeran dake
kusa dashi naji yana fadin zo nan ki zauna yana nuna min wajen zama a gefensa kasa haka yasa na sauka
na zauna kusa dashi din kamar yadda ya bukata.
Naji yace waima in tambayeki don Allah Rahama kudin da gaskiyane kun taba zaman daji kuwa ni sam
banga alamun hakan ba gareku amma ance a rugga habu ya gano muna ku ?
Murmushi nayi ina fadin a can ya ganmu mana zama na shekara biyar mukayi a rugga tare da baffab
mu na fada ina zuba mashi abincin a plate yana bin zanen hannuna da kallo cikin mamakin abindana
fada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/18, 10:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Washegari shi ya shiga kitchen da safe ya hada muna breakfast ruwan zafin shayi sai dankali da kwai
suyan damke don duk ya wargaje kwan a wajen juyi saidai yayi dadin ci gaskiya a baki.
Ina daki ya shigo ya sameni duk dana falka daga barcin safen dana dan samu amma na kasa dagawa
daga kwancen ina kwance ina faman tunane ya shigo har dakin da abin kari.
Da sauri na tashi cikin mamaki ina gaidashi kin tashi ke nan ya fada yana aje kayan hannunsa din na
amsa da eh yaya ina kwana lafiya ya fada yana zama yake fadin dama nayi zaton baki tashi ba ai ?
Yau muna da baki gidan nan duk da ba wajen mu sukazo ba zasu dauki kayane su tafi wanan kayan dake
dakina kayan fadan kishiyace dana hadawa yan uwanki a a kai masu.
Saidai ita Asmau don haihuwan da zatayi nasa an hada mata har da kayan baby na kuma dan kara mata
ya dara na Saiba din.
Kallonshi na danyi yace ehh ai kinga in Allah ya raba lafiya ba sai na koma sayan komai ba kuma shike
nan na gama a yanzu.
Allah ya sauketa lafiya na fada ya amsa a cikin dadin rai da amin ai watan haihuwan nata ya kusa
kamawa Allah yasa lokacin kun samu hutu sai kawai in daukeki mubar garin nan na dan wani lokaci.
Ita kuma dayan antyn fa yaya yace wai Saiba kike nufi idan na dauketa yanzu wazai kula da ita Asmau
din, da hidima zaimata yawa ai ?
Maza ke nan na fada ni zainab makawa sai kiga namiji ya koma yaro karamin a gaban mace yana sakin
magana kamar bashi ba.
Balle J da yanzu yana da madafa dan magana zai tunar dasu cewa sun nuna suna kyamarshi a baya don
haka yanzu baida lokacin tsayawa dasu ai nasan dai abinda zai fada ke nan a karshen zancensa.
Tare muka karya dashi bayab mun gama nakwashe kayan zuwa kitchen na tsaya wankewa na gyara
kitchen din dana fito nima wanka nashiga na zauna bayan na fito na shirya tsab a cikin wani atamfa
dinkin zamani don dogon rigace amma tellan ya tsaya ya tsara dinkin kamar ba hannune ya dinkashi ba.
Dinkin akwai na ciki wanda zaki fara sakawa mai dan hannu saina sama mai adon da stely din dayasha
duwatsu har kasa saiki rantse daga egypt aka shigo dashi haka.
Hullane mahadinsa don dan kwali bai haduwa da kaya haka sai gyalena ainihin da akai amfani dashi a
matsayin gyalen yafawa da kayan .
A kyalen yadin kayan da akayi cin bakin gyalen dashi da duwatsu sai hakan yaba da mana,ana ga gayan
sosai zai fito da duk macen data sa a jikinta abuja ke nan.
Sallaman su yaya Ai yasa na fito don sunki zama sunata gwara sallama shima lokacin yana ciki dakinsa
kuma kofa a rufe.
Nice na fito ina amsa masu sallamansu suka juyo kofana muka fara gaisuwa nake ce dasu su zauna sai
bayan sun zauna din na gurfana ina gaidasu da zuwa.
Masha Allah anty Rukkaiya ta fada tana bina da kallo tace a,a lalai ba laifi gaskiya Allah ya baku zaman
lafiya amarya.
Na mike naje kitchen na dauko masu abinsha da snack gami da ruwa saida na ciko tire na kawo masu
na aje na juya ina fadin barina sanar dashi isowan su na nufi hanyar dakinshi din duk suka bini da kallo
anty Rukkaiya ke fadin.
Akace yayan fulanin ruggane gasu kamar ya Niger mana sun waye sosai ba zakice asalinsu rugga bane
tun wanan madin har tafi ta wajen habu wayewa ai.
Itace daidai da matanshi ai don yaran basu da mutunci baka zuwa gidansu kasha ruwa balle abinci ni
yaya Ai ko sun ban abincin su ai ban iya cima .
Yana zaune saman hasonsa ya dora kafa daya a sama dayan na kasa yana latsan laptop nayi sallama
nashigo dakin.
Kai ya dago ya dan dubeni kamar zai maida hankali ga abinda yakeyi bayan ya amsa sallaman tasa sai
kuma yayi saurin dagowa ya zuba min idonsa.
A dan maraice nake fadin su yayane sukazo suna falo zaune hannu ya miko min bakinsa na fadin har
sun iso ashe ?
Na tako zuwa gareshi ina fadin yanzun suka shigo hannuna ya kama ya jawoni na fada jikinshi ya
rugumini tsam yana fadin duk kayan da kika saka Rahama sai naga sunfi maki kyau ga wanda kika cire.
Wai meye sirin hakanne Rahama jin hannusa ya fara yawo a jikina yasa nace dashi cikin wani sallon
fitar da magana su yaya fa suna falo suna jiranka kada suga an barsu su kaidai zaune.
Yaja numfashi yana dagani yace kece ai kika kashe min jiki yasa na kasa tashi na manta da zancen su .
Cikin kissa na dan kalleshi ina fadin ni kuma yaya yanzu dana shigo don Allah me nace dakai da zakace
laifinane kuma ?
Au baki san abinda kikai min ba to ki duba nan da sauri na mike daga jikin nasa ina fadin nidai muje don
Allah kada suga mun jima haka ?
Kamahin nan naki Rahama ba karamin illanta min zuciya yakeyi ba har na fara tunanen yadda zan
koma maraya ranan da bani kusa dake wallahi.
Suma da kalan nasu a can da zaka shaka dama mata suna mukatara ai amma ba kalan mu daya ba a
wajen abubuwa kowa da irin nasa fasahan ai.
Wai ashe kina magana haka dama ya fada yana gyara saita jikinsa daya mike tsaye ni dai nayi gaba ina
dariya ya biyoni da yaya Rukkaiya data dauki cup tana shan lemo muka fara arba tayi saurin ajewa yake
fadi daga bayana ashe kun iso yaya.
Mun iso Jafaru kasan halin yaya Ai ai da nabita nata aitin bakwai muna gidan nan ita bataki hakan ba a
wajenta yayi dariya yana zama yace.
Haka ake son mutum ai da cika alkawari jin suna gaisawa yasa na koma dakin nasa ana basu waje
bandakin na gyaro kafin na fara gyaran gadon dakin nasa lokacin ya shigo dakin .
Baki dai gajiya da aiki ke nafi son ki huta yadda nima zanbi jikin ki in huta da dare in sauke gajiyana
yadda nake so amma sai ki wuni a tsaye kina aiki waike mai wayau don mutum ya tausaya maki ko ?
Dariya ya ban sosai saidai ba halin hakan shi yana mamakin sakewana nima haka mamakinsa nake ji
yadda yake abinsa da iyalinsa cikin sakewa haka ?
Dama haka yake amma matansa suke kullum cikin fada ko dashi ko kuma a tsakaninsu kullum ba zaman
lafiya a part dinsu can gida.
Ganin ya gara akwatunan biyu yasa na garo masa sauran muka fito dasu falo zuwa gaban su yaya din
ina ajewa na juya na bar wajen naje na karasa aikin da nakeyi na gyaran dakin.
Shine ya shigo yake fadin su yaya suna tambayan ki don ba lalai bane su dawo ta nan din kije kuyi
sallama dasu na fita na barshi a dakin.
Kudi ya dauka ya fito ya samemu yana fadin suje ko suka fice tare dasu bayan ya gama kwashe
akwatinan zuwa motanshi.
Nan kofan gidan na dan rakasu suka shiga mota suka tafi ajiyan zuciya na sauke bayan tafiyansu din
Allah yaso na hada masu leda su rike don basuci wani abin kirki ba ga abinda na aje masu a falon na
motsa baki.
Na tattara kayan na koma daki na kwanta tunda yace min sai yamma zai dawo gida don haka ba sai nayi
abinci ba ke nan.
Akwatuna shiddane suka fita dasu zuwa can gidan sai wasu jakkuna ban kuma tambaya ba tunda ya
fada min kanun zancen cewa zasuje dasu yaya can gidan kai masu kayansu na tausan gaba irin da wasu
mazan arewa keyi idan sun karawa matansu abokan zama.
GIDAN IYA
Gidan iya kamar yadda na samu suna kiran gidan da haka suna isa da mota Saiba da Saare suka hango
tsaye