Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
a can wajensu sai zuwa lokacin data haihu sin yanke shawara kan
mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita wanda already sunyi maganan hakan da hardo shine ya yanke
shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita din a asibitin.
Azuciyarshi shi kadai yasan yadda yake ji a ransa a yadda yaga part din yar uwata din data gyara shi fes
wanda shi a rayuwansa bai samu hakan ba duk da uban daulan da yake labta masu agidan.
Haka yasa ya kara jin bacin rai a zuciyarshi yana tuno irin zancen da suke fada akan auren bafulatana
da Habu din yayi saida wata rana ya fito ya tsawata masu akan irin maganan da suke yawan fada a
lokacin kafin a auro yanda din a gidan.
Yau sai gashi bafulatanan da sukewa dariya tazo da tsarin da su suka kasayiwa kansu suna tauye kansu
da nasa hakan yasa a yanzu yakan sharesu na tsawon lokaci ya zauna a can abinshi yana harkokin
gabanshi.
Hakan kuma bai hana idan ya tashi zuwa gida zai tsaya ya sayo masu kaya na alfarma na kyace raini da
za,a gani a fada a wajensu.
Sai kamar bayan kwana biyune da faruwan haka ranan jumma,a kowa yaci kwaliya da dogayen rigunan
daya sayo masu inda na dauki wani kampalana dinkin dogon riga na saka a jikina .
Zaune muke muna kallon film tare dasu mama dubu suka shigo part din gaidasu muka farayi ban faye
zama a falon ba idan suna falon nakan daga in koma ciki ko in fice zuwa wajen anty na muyi hira.
Sai bayan sun gama gaisawa na mike na nufi cikin dakin kwanan mu lokacin mama dubu ke fadin niko
Jafar ina ta son in maka magana akan wani abinda kayi da ban samuyi ba sai yanzu.
Ya kamata ace kayan nan daka sayo ka hada da wanan yarinyar da zamanta yanzu ya dawo a nan bai
kamata ace idan zaka sayowa matanka da yan uwanka abu kana debeta a ciki ba.
Naji nauyi sosai da kunya tunda yau da kowa ya saka tsarabansa yai adon jumma,a dashi a gidan nan
sam banji dadin hakan ba wallahi.
Mama wace yarinya kike nufi tace kanwar matar habu din nan mana da take tare da yar uwarta gidan
nan .
Yarinyar da kwazonta wallahi ko wanan abin da kake ta yabon matanka sun hada itace yarinyar nan ta
hada masushi .
Hakan ma ba girma bane duk zancen da suke kanyi baice uffan ba don a saninsa ya fada masu cewa da
matar Habu da yar uwar nan nata a cikin tsarabansu sai Habu din yake fadin .
No ki barshi mana mama aiba sai ya basu abinda duk ya kawowa matanshi ba hakan wani sabon fitina
zai iya kawowa kuma a tsakaninsu ai.
Ke nan itama matarka ba a bata ba ke nan kake nufi ba,a bata ba gaskiya yaya Saare ta fada daga
gefensu tana kallon yayyun nata.
Nasan udan kince sai anyi hakan zai iya kawo matsala a gidan nan don Allah a barshi kada a kafa wanan
hujjar don ni kaina ba zan iya hakan ba ko wani lokaci.
Amma Habu kai kace kai ai karami sama dashi ba dole bane sai yabawa matarka amma yar nan dake
tare da yaran nan hakan da nauyi gaskiya ace komai ba a bata ba cikin abindaya sayo a gidan nan .
Mama ta dauki takakmana idan zai mata ban faye son takalma irin wanan ba dama Salima ta fadawa
uwar nasu dake magana cikin damuwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
1️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ranan monday da safe na samu labarin abinda ke faruwa a gidan koshi abakin anty Salima da yanzu
muke dan shiri sosai da ita.
A wajenta nake tsuntar labaran abindake gudana gidan nasu don ni ban damu da nasan komai ba abu
daya zuwa biyu nafi rikewa a raina shine nidai yar tafiyace ma,ana yar rakiyar aure.
Nazo gidansu a sanadin rako yar uwata aurene saboda debe kewa a gareta nasan kuma rashin gata
yasa aka hadomu tare ba wani abu ba don a ragewa mahaifiyar mu nauyi a gabanta.
Idan bashi ba a shekatuna goma sha nayi girman da zan zama yar tafiya na koma Murfin Jallo ga yar
uwata da yanzu auren nan kamar ta danballene ma nake gani don da da dan kuzarin ta amma a yanzu ta
koma wata sau da ita bata da lakka ko wayau.
Don haka tuna sanadin zuwana gidan bai bari na wuce iyakata ba iyaka dasu halin zama tare sun bani
mafaka ni kuma in basu karfina wajen abinda ya dace.
Zance bai tasowa tun zuwan mu gidan kaji sunan yar uwata a ciki balleni musan yadda muke takon mu
dasu bakaji zance a bakin mu saidai a kiramu don shedan muna wajen abin ya faru.
Koshj wanan zancen a zaton salima nasan da zancen take fadin gobene za a kai Maria asibiti ko ?
Azotana irin zuwan da sukeyi suje awone take tambayana sai nake cewa eh gobene sai naji tace dani
Allah sarki ni tausayi mariya ke ban wallahi a daidai lokacin da mutum yake son zama da mijinshi ace za a
rikeshi asibiti ya zauna har sai ya haihu wanan abin akwai takura ai a cikinsa wallahi ?
Anty Maria din zata zauna cikin asibiti har sai ta haihu anty Salima tace ba haka akace ba Ramaah koke
baki fahinci zancen bane wai Ramaah ?
Kodana dago kai hawayene ya bata min fuska ban iya magana ba ta juya ta shiga bandaki don dama
wanka zata shiga muke hiran .
Mikewa nayi na fito daga dakin zuwa wajen yar uwata da akwanakin nake ganinta cikin damuwa zaune
na sameta a falonta ta kifa kai a saman hannun kujera.
Nayi sallama na shigo fuskanta kawai na kalla nasan itama tayi kukan a lokacin nafara fadin meyasa baki
fada min abindake faruwa dake bane Yanda ?
Duk da sunan yanda din da suka san ma,ananshi a yanzu sun mayar da sunan akaina a gidan ni kaina a
yanzu ina kokarin karbe mata sunan nata da mahaifanmu ke kiranta dashi na yan mata.
Mezan fada maki Ramaah tashin hankalin da nake ciki kema ki shiga amma ai ba yau muka fara
fadawa junan mu tashin hankali ba yanda nakirata da sunan da muka saba kiranta dashi din.
Nacigaba da fadin ko a yanzu ban cancanci naji damuwanki bane kamar baya yadda muka taso daga mu
sai Allah sai mahaifanmu a tare damu.
Ramaah me kikeso na fada maki nace dake likita yace ba zan iya renon ciki ba sai da kulawansu duk na
tayar maki da hankali kamar yadda nawa yake a tashe ?
Kallon kofan dakin su da takeyi yasa na juya mijintane a tsaye yanayinshi kadai zaka kalla kasan yana
cikin matukar damuwa shima din a lokacin.
Hakan baisa nayi shiru ba don da yare muke maganan nace kinsan matsalan ki yanda bata asibiti bace
dole sai mun koma wajen baffa an suhunta dashi zaki zauna ki tauye kanki a nan kuma ?
Ba wai hakana bane Ramaah abinda likita ya fada suke bi duk da nasan abin nada alaka da baffa amma
su nan birnine ai ba zasu yarda da hakan ba su.
Gyaran murya yayi na sake juyawa gareshi karasa fitowa yake zuwa falon ya samu waje ya zauna yana
fadin lafiya dai ko ?
Kalloshi nayi cikin yanayin damuwa ina fadin ina kwana ya amsa sai naji tace zance take akan tafiyana
asibiti wai lalurana bana asibiti bane sai naga ya tsuke fuskanshi lokaci guda.
Yana fadin idan bana asibiti bane na meye ke likitace Ramaah da zaki fadi taki hasashen abinda likita ya
hasaso gareta ke nan ba zatayi wani dogon motsi ko daukan abu mai nauyi ko wani abu da zai iya taba
lafiyan mahaifan dake dauke da jinjirinta ba a yanzu ?
Don haka dole sai sun riketa a wajensu suna bata kulawansu su saka ido ga duk wani motsi nata a
yanzu shine kawai dalilin da zata zauna a wajensu din ai.
Ummah zatazo daga Jimeta a gobe insha Allahu itace zata zauna da ita asibiti don haka wanan ba wani
abin damuwa bane insha Allah.
Duk da naji ummah mu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadin zuwan nata ba don nasan wahala
kadai zatayi a can din tuno da lamarin baffa da zuciyana ke min.
Akan bakin halin baffa a lokacin a gaban idona naga yadda yake tauye Hanne data shiga huruminsa
abinda bai kai ya kawo ba amma haka baffa ranan don fada kawai akan yara da suka kora shanunsu
zuwa kiwo suka samu hanne ta riga su zuwa da nasu shanun a inda zasu sake shanun mu.
Sukai magana ta kwashe taki kwashe shanayen nasu tace aita rigasu zuwa dole suka juya da nasu
shanun zuwa wani waje suka sakesu kiwo.
Bayan an dawo gidane baffa ya taresu yana fadin yau shanu basu koshi ba yasan kuma komai shi
Hanne zatayiwa tsageranci zai nuna mata ko ubanta bai isa ja dashi ba balle ita.
A gaban mu ya fito da wani babyn roba mai gaba gaba zakice mutum ne kamar wata jaririyace a
hannunsa ya shiga dakinsa dashi a hasale.
In gajarce maki labarin nan duk lokacin da baffa ya murda wanan babyn roban idan kafa ya murda haka
hanne zatayi ta tsala ihu da sai mujita a namu ruggan saboda azaba.
Idan hannun roban ya murda ranan hannunce zata lamkwashe ta dinga ihu tana neman taimako masu
magani sunzo kala kala ankai hanne asibiti birni an kashe kudi yafi a kirga amma hanne bata samu lafiya
ba.
Ranan da na girsheshi yana murda kan wanan babyn roban cikin mugunta daya bayyana afuskansa
yana wasu suraita naja baya a hankali don baisan ina wajen ba.
A ranan muka samu labarin wuyan hanne ya kare tana batun mutuwa haka da baffa din ya fito daga
daki idonsa a kaina ya sauka yana min alaman gargadi ban nuna nasan abinda yake nufi akaina ba
lokacin.
Don zuwa lokacin na daina tsoron baffa tunda yake kirana da shu,umma idan dare yayi yaji ina rewa
kira,an da muka koya a abuja don mu din mun sauke alkur,ani a lokacin gidan Alh tun barinka nono zaka
fara bin yan uwa karatu don haka ya gargadeni da na daina naki sai dai in rage sauti yake kirana da
shu,umma abakinsa ni kuma tsoron shu,umancinsa ya fita raina.
A wanan case na hanne na yarda baffa shu,umine na gaske don dashi mahaifin Hanne ke fadi tashi
dashi aketa zuwa asibitin birni ana kashin kudi wani lokacin shine mai zuwa amso maganin kan matsalan
hanne din.
Shiyasa bahaushe yace makashinka yana tare dakai ko wani lokaci muna tare da makiyan mu bamu sani
ba a duniya.
Haka Hanne ta wahala sosai dukiyan mahaifanta yana tafiya baffa yana mata dariyan mugunta yana bin
babyn roban daya sihirce da sunan hanne yana lugudewa karshe shanayen mahaifin hannene sukai
rauni.
Saida Allah ya nufi hanne tana da sauran rabon shan ruwa a duniya ranan baffa din ya tafi Adamawan
cameroon wajen wani amininsa aka ga wuta ya kama a bukkansa.
Ko yaji tsoron kashewa andai zuba ruwa har angaji wutan saida ya lashe bukan Baffa kaf yadda wuta ya
kona roban haka jikin hanne yaji amma ta samu kubuta.
Da Baffa ya dawo daureshine kawai ba ayi ba don duk wani kayan tsafinsa ya kone a wanan gobaran
wasu tun yana yaro wasu kuma da girmansa ya karbo sihirin yake aiwatar da sherinsa akai.
Har yau kuma ba a san nice na hada baki da dan uwan hanne yazo ya saka wuta a bukkan baffa ba a
cikin wa yanda suka samu saukin hakan har da mahaifiyar mu da yanzu take iya mayar da magana a cikin
iyalan baffa din daya rufe mata baki haka yasa na gane muma baffa ya kullemune a lokacin da sihirinsa
don a lokacin muka fara samun sauki a cikin hakan kuma zancen auren Yanda ya taso har ya rasa me
zaiyi yace ya barwa hardo mu da sharadin baiba da ko Nagge guda don shanun babanmu sun zama nasa
a yanzu.
Baffa mugune ko cikin muggai nasan zai iya illanta anty Maria tunda ya kufulemu a cikin ransa zai iya
aiwatar da wani mugun nufinsa akanta yanzu.
Allah yafika baffa na fada a hankali wa Allah yafi Ramaah naji muryan ya Habu yana tambaya nace
baffa na juya na fita daga dakin rai bace.
Part din iya na koma suna zaune dukkansu a falo mamace ke tambayana da Ramaah kin karya kuwa
tana kallona.
Kai na girgiza mata don shiririta Ramaah zaki zauna da yunwa a cikinki har wanan lokacin maza dauko
kofi kizo ki hada shayi kisha ga kuma dankali a wanan roban ki diba kici tafada.
Nima takan ban mamaki wani lokacin idan tace bata karya ba mutum ya tashi yayi wanan uban shara
da wanke wanke amma kuma yakai wani lokaci yace baici komai ba.
Zama nayi kamar yadda mama dubu ta umurce ni dan zuba ruwan zafi kadan na hada shayin na dan
dibi dankali ina tsakura a hankali.
Suna hiran su sai iyace ke fada dani kan na dibi abu kadan kamar za abawa jariri murmushi kawai nayi
don zuwana dake tuna min da baffa a lokacin.
Banda natsuwa a yau ina tunanen shu,umancin baffa a raina zai iya fiye da hakan a kan yar uwata
tunda ya fada da bakinsa taje koba aure ba taji tayi auren kado din data saka kanta ya gani.
Waiba muryan anty Asmau nake ji ba anty Saare ta fada tun dazun nake jin muryansu ai inji salima sai
mama dubu tace yau kuma me suka tashi dashi da wanan fitina ?
Turo kofan da akayine yasa mu kallon kofan don kofan yana bada kara idan an tabashi wanda naciki zai
gane anshigo dakin a lokacin.
Asmauce matar ya Jafar ganin mu a zaune gaba dayan mu yasa ta soma gaida tsofin da kwana kafin ta
dora da fadin mama kiwa Nusaiba iya dani dan Allah.
Mekuma ya faru da safen nan kasa magana tayi sai hawayen dake zubo mata hakkuri suka shiga bata
suna fadin kiyi hakkuri Asmau kinsan halin abokiyar zaman ki sai kici magananin zama da ita ta hanyar
kawar da idonki a kanta.
Mama don Allah wani irin kawar da ido ake son inyi ga Nusaiba yanzu kuma bayan wanda nakeyi yanzu
akan mimi fa da yarta Nusaiba ta dokan min yarinya har wani wayau sanin haka mimi tayi mama saboda
Allah ?
Duka kuma me yarinya kamar wanan zatayi mata har da duka duka sosai tayi mata mama ki duba
yadda bakin yarinyar nan ya fashe wai don kawai suna wasa a falo fada ya hadasu ta kayar da yar uwar
shine Nusaiba ta fito ta duketa fa haka ?
Tir da halin wanan yarinyar wallahi banda abin namiji banga abinda yaron nan ya gani a jikin wanan
yarinyar mara mutunci ba wallahi.
Iyace ke fadan wanan maganan inda tacigaba da fadin wanan yar yadda take baka haka zuciyarta yake
baki ba digon rahama a tare da ita,,,,,,
Iya baki san kan zance ba kin zauna kina zagina ai tana tsaye yaran suke fada bata rabasu ba har ta
kayar min da ya tana duka don rama kuma shine wai nayi laifi ni wallahi ba zan yarda da irin wanan
ab,,,,,
Ke don Allah ku fita ku fita masu daga shiya kuje can ku kashe kanku da yayan naku kada kuzo ku tayar
masu da hankali a nan kuma ?
Ya Habune ke fadan hakan da yashigo part din ransa a bace yana binsu da idanu duk suka juyo suna
kallo shi.
Wanan wani irin rashin hankaline da zaku dinga fada akan yaya tun suna kanana ku koya masu mugun
dabia wani irin halin banza kuke son yayan ku su taso a cikinsa ?
Indai hakane zan karbe yaran a waje da zaran kun yaye kada wace ta raba min kan jikoki mama dubu
ta fada garesu .
Ace mata baku da abinyi sai fitina a kullum ku kwana jidali ku kwanta da jidali mama sin tacigaba da
fada tana fadin maganganu akansu.
Dama ace fitinan nan naku shine halin arzikiku da mijin ku zai dawo ya sameku a cikin farinciki da jin
dadi da walwala ba yazo kulum ga jidali kuma ya sameku a cikin kazanta da doyi ba.
Iyace take wanan katobaran a gabansu daya saka aka kwashe da dariya bandani dasu da suka hade rai
tace Allah ko banda kazanta da tijara ba abinda suka koya ga uwayesu da zasu barwa diyansu gado
suma.
Iya da banda tarbiya ai Jafar ba zai auro niba gidan nan fada kuma kowama yanayi idan antabashi ai ta
juya ta fice daga part din ranta a bace.
Anan tabar kishiyar nata su mama suka haita da fada ya Habu yaja tsuki ya juya ya fice daga part din a
hasale yana maijin haushin abinda yake faruwa din.
Iya kin damemu da fada don Allah ki bari idan mijinsu ya dawo ki fada mashi mana Saare ta fada tana
kallon iya din dake faman jinini ba fada bane fadan gaskiyane da bakwaso ayi mama ta fada.
Nasan maganin su ai idan na hade kan yaran na tafi dasu can babban gida sai muga ta tsiya kuma da
sauri Saare din ta kara fadin a,a mama barsu da yaransu don Allah matan nan basu da mutunci .
Har sukayi suka gama ban ko daga kai na kallesu ba ina faman tunane kasan raina dan na dauka
matsalan yayata din wani babban lamarine na tashin hankali lokacin.
Duk da ance mahaifiyanmu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadi ba a raina idsn na tuno da sheri
baffa a ranan haka na wuni a cikin damuwa da fargaba ina zullumin abubuwa da dama a raina.
A haka barci ya daukeni sai wajajen yamma na samu na tashi sallah nayi na fito