Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
zamuji ba ina zai fada kuwa mama
tunda ba dole bane sai mun sani ai ba dai wa yanda yake son su sani sun sani ba.
Ashe kin gane nufina wanda zasuyi min addua da fatan alheri suna fadawa don nasan ko banza suna
farin ciki da samuna ko rashi.
Zata fara masa haushi ya dakatar da ita da fadin kina sake fadin tak wajen sai kin bar gida bari na har
abada kuwa in kuma kin dauka karya nakeyi ki tanka a yanzu din ?
Shiru tayi tana mazurai da ido ta kasa magana ya juya ya dubi mama kamar zsiyi magana sai kuma ya
fasa ya shige ciki zuwa dakinsa.
Barshi kada ki tanka mashi don baya cikin hankalinsa yanzu komai yana iya faru dama haka akeso to ki
kyaleshi.
Salima ta kawar da zancen da fadin mama ni zan je kasuwa in dubu wani yadi da nakeso bata bata
amsa ba ta juya ta tafi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/8, 9:51 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yar uwa saidai ince Alhamdullahi masha Allah don abubuwa sun kankama cikin dan kankanin lokaci
abinda ake fatan samu a rayuwa an sameshi don kuwa tafiyan nan da yaya ya samu yayi ba karamin
alheri ya jawowa rayuwan mu ba sosai mussanman mashi dani.
Don abinda yasa nace ni anyi sunan moh,d a cikin walwala da dadin rai anci ansha anyi alheri kuma
baby ya samu alheri wanda zance a sanadinsa na samu hakan .
Ubangiji Allah ya tsallakeni daga kaidin mama hassada ko bakin cikine ko kiyayya da ake min kasancewa
da yaya ya zamo min taki a rayuwa lokacin haihuwan dan nan.
Don ba karamin alheri na samu ba ga haihuwan dan da mama da kishiya suka sare min gwiwa tun a
cikinsa ba abinda na samune farin cikina ba sai irin yadda kowa ya dauki dan zai furta masha Allah wanan
photocopy ne kawai na Jafar da mutane ke furta a bakinsu don dan tun yana karami ubansane sak ya
kwaso a kamanninsa.
Ga kyauta ta inda ban zata ba da yake shigo mun in kuma an kawo din uban yace a ban nice na wahala
ai na rike ba kamar yadda muka soma zaman asibiti ba a takure yana karba din a lokacin.
Ni dai banda tacewa ina zaune mama ke fada min na dauki duk wani abinda zan dauka don ba a nan za
ayi taron suna ba can gida zamu tafi ayi taron don mama tace mu dawo nan ayi taro a gabanta.
Don haka tun daren suna muka dawo nan gidasu inda matanshi dasu iya da mama suke zama a gaban
mama a part din iya muka zauna.
Na samu salima ta gyara wajen tsab tsohon dakina a nan akai min masauki dani dasu mama da Biba
tun kan muzo saida mama ta gargadeni akam koma meye manufar mama in daure inyi hakkuri kada in
nuna hakan ya bata min rai don Allah.
Nidai kawai murmushi nayi bance komai ba tunda gidan ba bako na bane ai duk wani abu da nasan
cewa zan bukata a lokacin na dauki ba saj na tsaya nema ba a nan din.
Don haka koda ya iso a nan ya samemu don tun yana can ta kirashi ta gaya mashi umurninta haka yasa
daya iso ya nufo nan din ashe saida ya biya can ya aje duk wani abu da baison ya kawo masa fitina kafin
ya iso nan din ya samemu don tunda ya tafi bai dawi ba sai a daren sunan komai a waya aka shirya yadda
za ayisa a taron dashi.
Ina zaune ina bawa yaro nono mama tana zaune kasa tana cin abinci muna hira mukaji muryanshi suna
gaisawa da iya a falo ya gama ya shigo suka fara gaisawa da mama har yake tambayanta ba dai matsalan
komai ko a nan ?
Ai ba a rasaba yanzu dai ai gashi an kwaso mata maijegon an kawo mata bari muga iya gudunta kuma
dubu kam lamarinta sai addu,a gaskiya.
Kibar yarinyar nan ta zauna dakinta ayi suna kin kafe sai ta dawo gudan nan agabanki nan ayi komai ko
anyi nan gabata zata iya hana komaine ni ban sani ba ?
Ba komai iya gara da aka dawo din nan zaifi sakewama don can karshe a bata mata kayanta da sauran
abubuwa ba daida anyi suna gobe saita koma ba ?
Akace maka nifa nasan dubu nasanta sarai yanzu zata iya cewa kuma sai a bari har wani lokaci sam iya
hakan ya zama takurawa ai idan anyi suna su koma can kawai zaifi nan banda tsegumi me zata zaunayi
kuma ?
Daga kofa mama data mike ta fita ta saka masu baki tana fadin tunda anyi suna me kuma za a tsayayi
nan kuma ta koma dakinta kawai mana tunda ba wani wanka irin na da can yaran yanzu keyi ba ai.
Shina gani mama an daice sai tazo nan anyi suna tunda nan kowa yake anzo gobe da yamma idan an
watse zan mayar dasu gida insha Allahu.
Ya gama dasu ya shigo muka gaisa nan yake tambayan lafiyan mu dana yaro nace Alhamdullahi ba inda
ke maki ciwo kuma yanzu ko ya tambaya nace naji sauki sosai ai.
An kawo dinkunan naki nace ehh tun jiya anty salma ta ba driver Aminu ya karbo a gareji good ina
hanya na tuna wallahi na sake fadan ankawo ai.
Ya dan tsaya mukai hira kafin yai muna saida safe ya fita don gidan akwai baki da zasu kwana ga yaya
barakha da sukazo daga zamfara ita da kawarta.
Wai dan shigan da yayi ya jima hakan ashe ya zamo laifi kuma wai anshiga hakkin madam Saiba saida
sukai fadan hakan a cikin daren nam dashi yayi mata tas .
Don harda cewa tayi ana tauyesu ana nuna masu banbamci ga komai yazoyi saiya nuna bambamci a
kaina ya fifitani dasu don me zai yanka saniya a hada wajen bukin.
Nan yace koda sunan Buhari ban yanka shanu ba ko wanan ne zakiwa bakinciki kuma koka yanka ai
baikai wanan girma ba yake fadin.
Ooh ashe ke diyar sarkin fawane ban sani ba har kin fita kin duba shanun kinga wanan yafi girma ko to
komai da sa,anshi yake zuwa ina dashine yasa na sayi babba.
Ai Allah yana ganinka duk zaluncin da kakeyi da fifitata akan shi kuma zai saka muna wallahi tunda
haihuwa ai baifi haihuwa ba ?
Wanan yakawo masu fada sosai ya gama ya shige dakinshi don akwai gajiya a jikin yasa ya rufo dakin
da key ya kwanta bayan ya gama komai don ko abinci ita mai fadan bata aje mashi ba.
Koda ta fahinci ya kargame kofan dakinsa hakan ya kara bankata mata rai kuma dakyat taga safiya a
ranan ba abinda ke damun ta banda irin yadda labari yazo masu cewa katon shanun da jafaru ya yanka a
shagalin.
Akan shagalin sunan da sukaiwa ikirari da farko haihun rashi saiga ubangiji ya sauya abin a lokaci gashi
yaya Auwalne jagoran abin ba wanda ya isa ya kawo mai raini akan zancen aikin da akeyi din.
Kamar yadda jafar yace ayi da naman hakan akayi kowa don an rabawa yan unguwansu makwabta na
kusa dasu sadaka kana ya aika gida gida dukka tan uwa dake cikin gari asa albarka.
Kafin abinda ya rage ya aiko da wanda zayi aikin shagalin dashi nan gidan mama sai abin ya bakantawa
mama rai sosai don me Auwal yayi bugun gaba da abin danta haka bayan gasu ga tan uwasa zai shige
masu gaba.
Allah ya taimaka yaya barakha ta iso lokacin ita ke fadin mamanmu yaya Auwal nefa wallahi kina cewa
wani abu yanzun nan duniya zatajiku dashi.
Gara ki kama bakinki tunda shine a matsayin babanmu a yanzu shine babba kowa na bashi girman shi
yau don danki ya yanka shanu yaya Auwal ya raba zakice baki yarda ba da hukuncinshi.
Aishi jafar yasan me yakeyi da yake sakasu gaba a komai nasa mutanen nan duk da yan ubanci da
adawan da suke nunawa a garemu basu yarda sun nuna cewa muba yan uwansu bane.
Komai namu ya tashi suna gaba sunayj gwargwado yadda duk wani dan uwa zai tsaya yayima a cikin
gata tanzu akan wanan abin saiki nuna ke baki yarda ba.
Ke kuma Nusaiba zan fada maki wani magana da baki sani ba akan yan uwanmu uban mu daya dasu
dukkan mu kuma a tare kika zo kika samemu muna zumuncin mu.
Har idan ba zakiba mama shawaran alheri akansu ba to don Allah ina tokonki da kiyi shiru ki daina kawo
mata tsegumi tunda kinsan tana daukan zancenki kada ki hadamu fada da yan uwan mu don Allah ?
Ubanmu ya mutu ya barmu a tare dasu kada kiyi sanafin raba wanan zumuncin namu don kin zama mai
yukan yanke zumunta ke ?
Nina gane a yanzu tunda kika shigo gidan nan lamarin mama ga baki daya ya sauya wallahi a,a anty
barakha kada kiga laifina mana don Allah ?
Kafa biyu da kayan ciki fa aka kawo gidan nan ba dole inyi magana ba ace an yanke shanu wanan kadai
za a kawo muna ayi komai dashi ?
Kuyi amfani da iya abinda kuka gani mana wai tsaya ma in tambayeki kokin manta da bakece mai
haihuwan ba waib?
Don ita data sha wahala ta haifi danta inma korafi itace ya kamata ace ta fito tayi wanan tsegumin baku
dai da yunwan wani nama ko wani dangin abinci a cikin gidan nan to ki bari ayi taron nan lafiya don Allah
yadda ya tsara abinsa a tafi a hakan yafi ?
Gaskiyane dai baku so ni tsoron Auwal nake ji baby bani tsoron Auwal balle uwarsa karane kawai nake
masu tunda suna muna suma .
Ni dai na fada maku kada ayi wanan zance in kuma kince sai kinyi zakiga abinda zai biyo bayan hakan
muna dai zaune kalau dasu don Allah mama kada abin duniya ya rufe maki ido kuma yanzu.
Wallahi maman mu yanzu ya kamata ki natsu girma ya kama komu da kuka haifa muna kawar da idon
mu ga abinda mukasan ba hirminmu bane a yanzu don Allah ki barbin ta yaran nan suna bata maki suna.
Ita mai haihuwan haka kuka sakata gaba da abinda ta haifa dakinkine fa ya ajeta itama ba wani bare ba
wace tafita gidan nan yadda kowa yazo aure haka itama tazo aure danki don Allah mama ki bari ayi
wanan abin lafiya a watse lafiya kada aji bakinki ga komai don Allah ?
Kin daice sai nan za ayi suna yaran nan basuki ba sunzo nan din babu jayayyan komai don haka kada inji
bakinki ga komai don Allah ?
Wanan yasa dole ta kyale batayi fada ba da Saiba ta zugata wai an kwashe nama an kawo masu kadan
a gidansu tunda so tayi akawo shanun gaba daya a nan gidan.
Yaya barakha kuma a yanzu nagama da ita tana bayana akan diyanta don da sukazo bukin saratu suka
kwana gidana na kwaso duk tsofin kayana na basu ga Aminu dake karatunshi yanzu ta sanadina idan ba
butulu ba ai hakan dole ta soni ?
Washegari kuma tunda safe da nayi wanka na saka wasu atamfar super cikin wanda da akayo min a
Abuja mama ta hada min shayi mai zafi taban ina sha.
Lokacin anty barakha tashigo take labartawa iya abinda sukayi da uwar da fadan Jafar da nusaiba din a
dare har take fadin ta fahinci saiba bata bar uwar a banza ba.
Maman tudu ta tsoma baki da fadin Dubu ko banza bata bincke abinda aka fada mata dashi take
amfani haka take tun farko Alh yayi mata fadan hakan bata daina ba.
Saukina a yanzu ke Amina da yake dubu tana shakkunki har yanzu iya ta fada nagode wa Allah daya
barku tare da bansan iya inda abin nan na dubu zai tsaya ba.
Yarinya karama tana amfani da ita don ciwa manufarta akan yayanta amma dubu bata gane ba tana
ganin hakan sone bata san tana dafa kanta bane da kanta yarinyar nan tana cikin silar tabarbarewan
komai na gidan nan a yanzu.
Shi yayi sallama ya shigo yadda ya samesu ya bashi mamaki yaya barakha bata boye mashi ba ta
labarta mashi komai yace ta barshi kawai da ita yasan komai ai.
Ya shigo mun gaisa dashi ya tambayi jiki ya dan jima ya fita yana fita kai tsaye ya nufi wajen masu aiki
girki ana gaisawa yake tambayan ina naman da aka kawo aka fito mai da dan nama kadan da aka soya.
Ina naman kafa biyu da baya barakha tace matanka suka karba aiba mu suka bawa ba Asmau ya nema
yake tambaya akan me suka rike komai a hannunsu ga yaya barakha a gari ?
Ni nikan ban san komai ba na daiga ana yankan nama a gidan nan amma ba wanda tace dani komai ta
fada a cikin sanyi murya.
Ina Nusaiba ta fito tana fadin gata yace don me kika karbi komai da yaya ya aiko dashi ga yaya barakha
gari ?
Don me na karba fa kace don na karba shine abin magana kuma eeh ya fada a gadarance sai tace to ita
yaya barakhan ta kawo karana kome ?
Ke ina kayan suke nake tambaya ba dogon magana ba ta kawo karanki har kin kai wanan matsayin da
zakiwa yayata abinda zata kawo karanki a wajena ?
Ban aje wanan matar datafi karfina har ta wullakanta min yan uwaba tukun nazo ina tambayan nama
aka nuna min dan wani abu can a kasan kwano ?
Shina bayar ta fada a cikin gadara ki fito da sauran yanzun nan to idan na fito dashi mufa ta fada baki
sake cikin namaki yace kufa ?
Kufa name donki na yanka naman nan ko don sadaka ke koke kika haihu a gidan nan ba zaki min iko da
abina ba tunda ina da yan uwa fito dashi nace .
Tayi tsaye ya juya ya nufi part dinsu din tare da kiran Asmau tabi bayanshi ita Saiban ta bisu a can fada
ya turnike yayu mata dukan tsiya a gaban mutane aka fito da naman a cikin wani jan kula data shake da
nama har bai rufuwa.
Ga iyayyen suna magana sai zagi take aika mashi da cin mutunci ya kyale har ya juya take fadan ba dole
kayi min cin mutunci ba tunda matarka ta zugoka ?
Dama wani dane ba dan ,,,,,,,, ya juyo gareta kamar wani tsohon zaki yasa bata karasa ba yace karasa
mana tayi shiru yace ke Nusaiba kije gidan ku don Allah na dai sakeki wallahi.
Dama nasan shirinkine kika takura sai ayi suna a nan don kiyi muna tozarcin da kika saba saboda
mama dake kama maki kiyi min iya shegen da kike so tana sakeki wallahi.
Salati aka dauka muna tsaye bakin window daga dakin da muna kallon duk abinda ke faruwa a gidan
nida biba a hankali na juya zuwa bakin gado na zauna.
Ba zance ga yanayin da nake ciki ba a lokacin shigowan mama yasa na dago take fadin sun sami abinda
suke nema dama masu iya magana sunci idan zaka gina ramin mugunta ginashi ya zam gajere.
Sunyi hakan don su bakantawa mutane rai yanzu gashi abin ya juye a kansu ba komai bane na sani
wanan abin shirine dama don kawai su bakanta baki su bata shirin ga nasu ya baci a yanzu.
Ina dadi danka ya tsawata maka a gaban mutane dubu bata da hankali da har take kokarin batawa
danta ta goyi bayan wata gashi a gaban kowa ya bata kunya yau.
Fadan hakan yasa na fahinci bayan barin inda nake kallonsu wani abu ya faru kuma wai ashe mama
cewa tayi ba inda Saiba zata udan yace ta bar masa gida saidai shiya bar gidan baki daya yaje inda aka
tsafeshi ta sheda an tsafeshi din .
Mama matukar kika hana saiba fita wanan karon zanko nuna an tsafeni din ya fada ya shige cikin part
dinsu har ya shiga dakinshi ya fito ya kira Asmau tana zuwa yace ta fara tattara kayanta ta kalloshi yace
zamu bar gidan nan ya juya ya shigaciki.
Da wanan zance dai suka bata min plan fin sunan da sukeson raina ya baci sai gashi nasu ya bacisu yan
garin mu da sukazo suna suka sauka wajen mama kaduba sun iso zuwa rana.
Tare da tawagan mama har na debe rai da zuwan anty Salma sai gasu sun iso bayansu kadan naji dadin
hakan sosai a lokacin.
Muna tsaka da shagalin suna yan uwan saiba suka iso da tashin hankali yaya barakha ta tare zancen ita
da yan uwansu suka fara fada a tsakaninsu ko leke yan uwana basu leko ba har sukaci suka sude saiga
mama ta koma kuka don yadda yan uwanta ke zaginta da danta a gabanta sukace inma munafuncine
mamace ta hada ai.
Yanda da anty Nafisa suka shigo da girkin da akayi don yan uwana na kudi muka bayar don abincin yayi
dadi sabodasu don haka ba wanda yasan da hakan sai lokacin da suka shigo da manyan kulolin abincin.
A nan kuma sai hakan yaso zama laifi yaso zama don saiga sakon mama wai naki debo abincin inbawa
mutanen cikin gida.
Anyi ba dadi da hakan ya dagawa yan uwana hankali har suke fadin zasu daukeni zuwa gida shan
ruwan zafi tunda nan din ba kwanciyan hankali.
Tun basu fitar da zancen ba maman tudu da suka fara fadawa ta hanasu yin maganan acewanta irin
hakan a yanzu tsegumi yake kawowa su barni a dakina dana haihu ai haiwan tiyatane ba wani wankan
jego zanyi da ruwa masu mugun zafi ba.
Magananta yasa suka kyale zancen da wai kona koma kaduna ko can gidan camerro zan koma basu
kwana ba a ranan suka koma kaduna anty salma kuma ta nufi Abuja.
Munso brin gidan tun a ranan amma wai dare yayi mu bari sai washegari hakan yasa muka kara kwana
amma tun cikin daren mama ta tattara komai da muka samu aka kai