Chapter 71 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   71 / 101

210K to 213K   out of 302.2K words

Ke dai bari abune da baka isa yau danice ai wace ta ta fito da zancen nan data san bata da wayau a
gidan nan ?

Ina batun yarona dake kwance ina naga wani batun dukiya can har in bari karamar yarinya ta dagula
min lissafina haka ?

Shiru nayi ina tunane wai wanan matsalan haka daga ina yake fitowane wai na kula fa ba damuwa
sukayi da bawan Allah nan ba sunfi damuwa da dukiya kawai akansa.

Muryan maman tudun ne dake fadin kinsan ita iya ba ruwanta fadin abinta takeyi kai tsaye tace duk
munafuncin daga Nusaibace da saratu ya fito.

Kamar a mafalki mukaji murya kamar nasa da karfi saidai yanayin kiran daya kwala min din ya sauya da
harshensa da muka sani sai gashi a ranan ya ambaci sunana .

Dagani har mama da sauri muka karasa zuwa dakin yake fadi cikin badaniya kamar me koyon magana
da Allah ya bashi ikon furtawa yace ko akwai kunama a gadon nan ne ?

Da farko bamu gane me take fada ba saboda yanayin dan saurin maganansa haka kuma yanzu da
harshen nasa yake kamar a karye.

Sai can nace ko kunama kake fada ya daga kai da karfi yace a wani irin yanayi eehh wani abu nake jin
kamar yana cizona na yunkura in dagashi na kasa hakan yasa mama fita daga dakin da sauri .

Ashe taje nemo koda yan uwansa suna gidan sai yazid ta sama ya habu ya fita tun yamma ya tafi
gidansa sai gasu tare da yazid din dasu mama da kowa don mama tudu tace dasu Jafar yayi magana yau.

Saidai ba a cikin dadin rai ba sabo harshensa da yake kamar a karye wanan yasa duk gaba dayansu
fitowa lokacin .

Koda suka zo Allah ya taimaka na samu na cirashi daga gadon zuwa kasa suka shigo sai wani irin nishi
da yakeyi mai karfi a cikin kugi na wahala.

Mun duba gadon ko ina har jikinsa da komai karkashin gadon duk an duba babu komai gashi kuma a
cikin wani wahala duk ana tsaye a kansa ana binsa da kallon tausayi.
Hankalin duk wani na tare dashi tsakani da Allah ya tashi a lokacin Asmauce ta fara kuka ta juya zuwa
falo don yazid dake mata tsawan yaya haka kuma kada ta tara masu jama,a ?

Hakan yasa ta koma falo ganin yadda wahalan yai yawa ga wani irin zufa da yakeyi yasa na shiga
neman magani a cikin wardrobe din da sauri na juya na fita zuwa kitchen na dora dan ruwan dumi na
sauke na fito.

Nan falo wajen Asmau na zauna muka fifitashi tare da ita na koma dakin lokacin yana wani irin wulle
wulle nace wa yazid din ka kamashi a bashi magani ?

Shiya kama min shi ya dago ina kokarin bashi naji muryan saiba na fadin wanan wani irin maganine
kuma a daina bashi abu barkatai don Allah haka ?.

Ki bashi kinji naji muryan yazid yana fada hakan yasa na bashi din naku fara shafa mai a duk jikinshi
yana nishi muna mashi sannu har na shafe mai ko ina ban damu da wai su mama na wajen ba.

Ga jikinshi har wani rawa yakeyi a lokacin hankalin kowa ya gama tashi da kuma tsoracewa lokacin ya
habu suka shigo da maria.

In fada maki mai karatu maria bata kyauta min ba nake gani a wanan gabar yadda takan share
lamarina a wanan lokacin sai shiru shirun ta ya zamo min illa a zuciyana.

Son nasan ko batazo don dan uwan mijinta ba ai zatazo don ni akai akai amma saita dauki sati biyu har
ukku ba tare data leko mu ba taga yanayin da muke ciki dashi.

Har na fara saka hakan a raina daga baya don sanin halinta yasa na share zancen nacigaba da
al,amurana.

Wanan yasa koda suka shigo ma a lokacin ban kulata ba ina gurfane a gaban yaya din mama da iya sai
faman fadi sukeyi Allah ya baka lafiya ya tayar da kafadanka cikin iyalinka jafar.

Ko asibiti zamune yaya habu ya fada a firgice ko anje asibitin me zasuyi da wanan lamarin saidai idan
za a din daga gefe kuma yazid ne ke faman karanto mashi addu kala kala daga bakinsa.

Sai zufan ya kara tsananta can yayi wani irin ajiyan zuciya ya lumshe idanunsa idabuwan mu yana
kansa har lokacin acikin tashin hankali dayawa duk sun koma falo anyi zugun an tsurawa sarautn Allah
idanu.

Don ba wani mai iyawa ko gwaninta sai Allah gabadaya kowa ya tsunke yayi kamar yana barci har
yazid din yana fadin ya samu barcine fa.

Can baya na koma na zauna nayi tagumi daga inda nake ina iya hangonshi daga inda nake zaune din
suna shawaran fita zuwa asibiti dashi .

Sai lokacin suka tabbatar da ya soma magana da gaskiya don yadda ya bude ido yana ambatar sunana
da karfi hakan yasa har wa yanda ke falon shigowa da sauri.
Jiki a sabule na karasa din wajenshi yana fada min amai yake son yayi in daga shi mun kasa fahintar me
yake fada a lokacin sai can nagane ina fadin amai kafin ma na rufe baki ya soma zubo amai ba
kaikautawa wani irin bakin amai yake zubowa a bakinsa din.

Ya Allah yasa dafin wahalan kake amayarwa jafar Allah yasa karshen wahalankace hakan maman tudu
ke fadin hakan a gareshi sai yayi kamar ya lafa kuma ya can ya fara kakarin amai din.

Oho har muna fadi kafara jin sauki sai kuma ga wanan lalura kuma yanzu nan fa muke zaune da yar nan
muna hiran akanshi.

Don yanzu akwai alaman sauki sosai a yanayinshi sai gashi munji daga ciki yana kakari ashe kuma
zancen ya baci .

Allah dai yasa saukin ke nan yazo da hakan mama tudu ta karasa zancen nata dashi tana kara mayar da
hankalinta kanshi.

Muryan yazid dake fadin amarya ki daga daga wajen wata daga cikinsu ta kwashe aman nan hakana ya
fada yana kallon inda Asmau da Saiba suke zaune.

Dan jim sukayi sai Asmau data yunkura tana daga danta daga jikinta yace No ke ki zauna ki rike danki
wanan ta kwashe ita.

Ai zancen ke nan wanan abin kowa ya shafa ba ita kadai ba amma sun mayar da zancen ya koma wani
abu na daban a wajensu yanzu iya ke fadin hakan.

Yace wace bata iyawa ta koma gidansu mana iya mu lafiyan shi mukajawa ba wani kishi ba can koda
sun bar mata din ai wanan zata iya ma tunda gashi tanayi ba tare data kula da abinda suke nufi ba ai.

Na lura da hakan sosai tunda na dawo garin nan iya dama ina son gaskanta hakanne da idona gashi ko
nagani a yau.

Tun safe daya fara aman nan yarinyan nan itace tsaye a kansa suna binta da kallo me hakan ke nufi ke
nan maganganun da kukeyi a kanshi damu yan uwansa ya zama gaskiya ke nan jira kuke ya mutu ku
wawashe dukiyan nasa yasa har kuke ragen dan uwansa daya kama komai ya rike a hannunsa yana ci da
iyalinsa.

Dagowa tayi tana fadin mu muka fadi hakan mu akace ma mun fadi hakan a ga habu din wazai fada in
baku ba inda kuka fada sako yazo kunnen mu ai ?

Kallon Saare tayi da sauri yace kwarai friend din munafuncin ki kenan ai ita ta fada inda za aji cewa
mun kama komai mun rike dani da habu koda mun rike din laifine hakan ?

Wanan magana ina kuma ya fito magana haka babu dadin ji mu da ke neman rayuwan dan mu ina
zancen wani dukiyansa kuma ya fito a yanzu haka ?
Ga sakaran nan mara mutuncin yarinya mana mama bada ita suke zama suyi gulman muba tunda ta
zama banza a cikin mu banga laifin maza dake gano halinta su gujeta ba don munafuncin saratu yayi
yawa mama.

Idan anyi magana mama tace an mata kazafi da sheri ba abinda take nufi ke nan ba yanzu tunda ana
zaman jiran gado ai sai kowa ya san zafin gadon da zaici din ke nan tunda ba wanan ce kadai zataci
gadon nasa ba.

Juyawa mama tayi gun saratu din tana fadin amma saratu abin yai maki yawa wai meyasa kike nuna
baki damu da dan uwanki bane ke ?

Kin taba ganin wanda yaki nasa yaso bare dan uwa marfin jallone fa yau jafar da sauran yannan ki sune
zaman mahaifin ku a gareki sabodawa kika san yarinyar nan ma a gidan nan ?

Wanan da kuka tasa a gaba da tsina tafiku sanin ciwon kanta don da biyu take kula dashi haka na farko
daukan da tayi masa na dan uwa wanda ya kamata ace kune kuke hakan sai na biyu alakar aurataiya
daya shiga tsakaninsu kinga riba biyu zuwa ulku ta samu a gareshi .

Kun dauka gulmace gulmacen ku da kyashin da kuke nuna mata zai sa ta gaza dashi hakan bai kara
komai ba illa karfi da kuzarin da kuka kara mata ga hakan yanzu.

Kada ku dauka bai san meke gudana bane a hakan wallahi yana fahintar komai dake faruwa wajen nan
ni ba yau ba yaran nan sun jima da zube min a idanuna .

Karku dauka gari ba a san me kukeyi bane ansan komai an kuma sakaku a baki tundau ke saratu kaf yan
uwa sun tsanaki a yanzu.

Ido rufe maman tudu take fada masu magana iya son ranta yazid na kamawa inda yakewa mama
bayanin cewa wai har saratu take fadawa salima cewa sunyi shawara cewa zasu kai karan habu kan ya
danne komai na jafar ya hana masu gaba ya hanasu baya basu san komai da ake ciki da zancen dukiyan
jafar ba ki duba fa mama da saratu za ayi wanan maganan haka idan ba sun saba hakan ba da ita dama ?

Shine salima ta samu habu da zancen take fada mashi abinda ke nan wallahi sunki shawaranane da tun
jiya ba wace zata zauna a gidan nan gaba dayab su.

A,a yazid ka cireni cikin zancen nan ai gasu nan idan suna abin su ban kulasu ina can ina aikina komai
aka kitsa nikan bada sanina bane wallahi tunda nice ke girki kullum saboda su mama dukiya yakai min
uban diyana da bai da lafiya Asmau take fadan hakan.

Dama na kula da hakan tun kwanaki cewa yarinyar nan ita kadai ke girkin nan don ko yaushe ka shiga
itace a kitchen tsaye .

Yau nasan ke munafukace Asmau dama kina hakane don munafunci ashe me nakeyi don munafunci da
kikace ba zaki kara girkawa kowa komai ba tunda mama tudu tace ba za a kwana dashi ba mena fada ki
fadi a gaban kowa mana yadda mukayi dake ?
Nan dai tonon asiri ya tashi a tsakaninsu inda har sunan saratu din yafi yawa komai da ake kitsawa ita
da saiba ce ke kitsawa har zuwa wajen malam da sukeyi duk Asmau ta fallasasu a bainan kowa yanaji
harda abinda basu zaci zata iya fada ba game da suratansu na hassada .

Ranan dai rayuka ba dadi a gidan ga mai ciwo ga kuma tone tonen maganan da yazid yajawo akayi na
fallasa inda mama dubu a karshe tafi kowa bakin cikin hakan jin saratu abinda take kullawa don kawai ta
bata tsakaninta da yayanta din kamar yadda Asmau ta fada.

Saida yaya jafar yayi kwana biyu a cikin wanan halin aman har yakai dole aka kara mashi ruwa leda
biyu manya ko zaiji karfin jikinsa.

Don gabadaya a wanan gabar duk yan uwa an debe rai ma a garesa gaskiya ga badama a koma asibiti
dashi haka tunda ansan ciwonsa dai sai Allah saukinsa bana asibiti bane don maganan likitoci gudane su
basuga abinda ke damunsa ba suke fada.

Barci yakeyi yanzu sosai tun bayan shigan wanan ruwan a jikinsa idan na bashi magani da safe zai
koma yayi barci mai nauyi na tsawon wani lokaci idan ya falka in bashi abinci yaci .

Allah sarki a hakan kuma fa tunda ya fara dan motsi sallah baya wuceshi zai min kwatance da zaiyi
sallah a dagashi yayi idan ya idar kuma ya koma kwancensa.

Kan zancen nan saida yan gidansu Saiba suka shigo zaria suka nuna bacin ransu ga abinda ya faru suka
bada hakkuri yazid yana zaune yace ai su batayi masu laifi ba wanan tsakaninta da wanda ya ajetane da
kuma Allah.

Tun daya fara jin sauki yake cin abinci sosai a yanzu don ya fara karban abinci da alaman ma kokon
dayake sha ya gunduresa a yanzu din.

Asmauce a lokacin take bashi abinci don ita ta girka duk wace ta firka zata zauna ta bashi yayin da
kuma wace bata girki zata zauna dashi a wunin .

Sai tsarin hakan yayi min dadi sosai don jikina ya fara nauyi da laluran gaskiya a yanzu ko ina samun
hutu sosai inyi ta barci.

Ina zaune a gefensa Asmau tana bashi abinci dan Asmaun na goye yana a hannuna ina mashi wasa a
gefe yaron yasa kuka uwar tana tsaye a gaban mijinta tana fadin saita gama ta kamashi.

Sam yaron baida yarda da kowa hakan yasa uwar take dauke dashi ko yaushe mikewa nayi dashi ina
jijigashi a cikin kafin naji yana badaniya da nufin na mika mata dan ta karba mana kukansa ya isheshi ke
nan yake nufi.

Ni kaina karfin hali nakeyi a lokacin don warin abincin nan ya isheni a hancina ina jin kaina wani iri a
lokacin.

A wurin karbansane na shaki turaren dake jikinta kuma wani irin amai ne naji yazo min lokaci guda
karo na biyu ke nan a yanzu dana ji abu mai kamshi zanji zuciyana yana tashi .
Da sauri na mika mata na nufi bandakin nayi mamakin irin aman da nayi a lokacin duk dan abinda naci
a lokacin saida na amayeshi a wajen haka na fito a galabaice ina share fuskana .

Idon su a kaina yake na samu waje na zauna a gefe tana min sannu kamahin ne ya kara dakan hancina
na mike da sauri na koma bandakin idonshi yana kaina har na shige ina kakarin aman da ba abinda ya
fito min a wanan karon.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[4/20, 9:23 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



7️⃣2️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A galabaice na fito daga bayin wanda yakai har mama tudu saida ta shigo tana min sannu yayin da gogan
ya wani tsareni da ido yana kallona daga kwancen da yake din.

Mamace cikin kidima take fadin me kikaci ko baki da lafiyane nace ina ganin zazzabi ke son kamani don
harda kaina yake min ciwo sosai.

Jam aima kikana da karfin jini ko yaushe kina tsaye tunda mukazo laluran nan ban taba jin kince ga inda
ke maki ciwo ba.

Bari a duba in akwai panadol saiki sha ki kwanta ko zai fada maki ta kara min da sannu na amsa da kyat
tare da fadin nagode.

Asmau take fadin balle kwanakin nan akwai sauro ko jiya saidana kunnawa yaran nan maganin sauro
muka samu barci dasu.

Ina gama shan maganin na nufi dayan dakin na kwanta barci mai nauyi ya daukeni har yamma ban
falka ba don na samu barci mai dadi a lokacin.

Kodana falka na danji dama wanka nayi na dauro alwala na fito na tayar da sallah ina jin marata tana
dan yanka min lokaci lokaci hakan yasa stil nake expecting din zuwan period dina na monthly da mata
keyi tunda yakan zo min da ciwon mara wani lokacin.

Abinci kasa ci nayi duk yadda mama ta matsa min kan naci amma na kasa ruwan zafi nasha na samu
waje na kara kwantawa banyi barcin dadi ba a ranan don yadda jikina ya gashi nake jin zazzabi.

Cikin ikon Allah zuwa asuba ya fada min sai gashi na tashi nayi aiyukan dana saba na dauraye mai jiki
yadda na saba yi masa don ban yarda in barshi da najasa a jikinsa ko datti hakan kan kasance ko da mun
yi aurataya nice zan masa wankan tsarki bayan na umurceshi da daura niya kafin kowa ya fito na gyara
ko ina kamar komai bai faru ba tsakanin mu.

Koda gari ya kara haskawa na gama da daki har falo lokacin ne mama ta fito tana fadin yar nan keda
kika kwana da zazzabi kece ke aiki haka tunda safe daki bari ai zan iya in kama maki ai ?

Murmushi nayi na dago daga sharan da nakeyi nace naji sauki mama na gaida ita da kwana take
tambayana karfin jiki nace Alhamdullahi .

Nagama komai na shiga nayi wanka na saka wani dogon riga na samu waje na kwanta a dakin duk
wanda ya shigo a gidan zamu gaisa dashi yayi min yaya jiki ?

A haka har aka kawo abin karyawa ina jin iya na fada tana fadin doya haka a bushe babu komai da zaca
hada dashi kaci ya gogema makoshi.

Hakan yasa banji sha,awan fitowa na karya din ba don nasan kayan takaici zan sama a wajen yasa
banko fita da sunan karyawa ba a lokacin.
Barcina nayi sosai a ranan don idona dama da barci ban samu barci da dadi ba da daren don zazzabin
dake damuna din.

Muryan mamace dake tsaye a kaina take fadin ki tashi haka tun safe baki karya ba kina kwance ko
jikin ne har yanzu ?

Na daga ina fadin a,a na mike da idona da sukai min ja zuwa bandaki nan kuma na kara jin aman yazo
min saidai ba komai a cikina haka na wahala na fito daga bayin .

Dashi muka fara arba ya kura min idanu yana bina da kallo kamar maye ni kallonsa har damuna yake a
yanzu idan ya kafeni da idanunsa.

Wai Rahama aman ne har yanzu badan mijinki na kwance haka ba ai sai ince ko Abba ya samu kani ne
Asmau ke fadin hakan.

71 / 101