Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
10:42 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [3/5, 8:46 Yamma] Seenabu Makawa: Follow this link to
join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL
[3/5, 8:50 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kinji meta fada ai ashe baki cika yar iska ba tunda baki doketan ba a yanzu get out of side kafin ki kaiga
abinda kikeso ki samu a gurina yanzu.
Tana tsaye har yaci abincin yayi hamdala a gabanta yasha ruwa ya mike don ya fita a kofa ya tsaya baiji
kunyan idon da yan falon suka kafa masu ba a lokacin.
Nan ya tsaya tafito ya rufe kofan nasa dakinta ta nufa rai bace ta kira yar uwarta nan ta karfafa mata
akan tayi hakkuri duk abinda zai mata don ya kureta kada ta yarda ta kara barin gidan har suzo.
Zuciya dai bata da kashi duk maganan da yarta tayi mata haka baisa ta hakkura ba can dai ta sameshi
part din mama suna magana kan zancen anty baraka din ta fado falon cikin fitina.
Nan ya wanwanka mata mari duk da mama na magana ido rufe yake fadin shi zata kawowa rashin
mutunci yana magana da mahaifiyarshi ta zo mai haka.
Sai lokacin ta fahinci irin kuskuren da tayi don duk abinda sukeyi bai taba daga hannu ya duketa ba sai
wanan ranan kuma a gaban kannesa dani da muke dakinsu muna kallon wani dinki da salima ta jawo mu
gani.
Abin dai ba dadi a lokacin wanan yasa ba a jima ba yace mu fito mu tafi duk da iya tayi mashi magana
akan ya barmu yace yana son muje mu gaidasu mamane can family house din su.
Dole iyan tayi shiru ita mama abu yai mata yawa saukinta ma shi J din daya kira anty barakah din ya
bata hakkuri akan ta daina zancen ta bari zasuyi magana dashi daga baya .
Wanan ya kwantarwa mama din da hankali saidai muna fita daga gidanne kuma Habu ya kirashi yana
fadin kada yace zaiyi wani abu ya kyale yar tasu sai ta koyi hankali.
Shima bai samu dogon magana a wajenshi ba saboda ranshi dake bace na daiji yace dashi zai kirashi
idan ya sauke mu .
Nidai nasan badon hudubar dana samu gun anty salma ba dana kade a wajen Saiba don yadda ta
sakani gaba dani da mijin.
Amma sai Allah ya taimakeni nayi amfani da wanan huduban na anty salma nacire tsoro da fargaba ina
bata amsa ba tare da rashin kunya ba ko fitsara daidai da yadda tazo min nake daurewa ib dauki mataki
a lokacin.
Wanda ni kaina har mamakin irin daurewan da nayi din nake ji ina fuskantanta garan da garan gaba da
gaba ba shamaki ko tsoronta.
Mun shiga cikin gidan da kedojin da muka riko masu inda ko wani daki muka shiga muke aje masu
sabulun wankine da omo sai manshafi dana hado dashi din.
Ina dakin inna inda na yadda zangona dama tun kan na auri ya J idan nazo gidan nan muke dasu anty
Nafisa kiran Maria ya shigo min.
Da harshen fulatanci muke magana don su inna dake dakin zaune inda maria din ke tambayana ashe
abunda ya faru ke nan.
Yanzu take ji a wajen iya cewa Saiba tayiwa yaya rashin mutunci a kaina ya mareta har idonta daya ya
rufe wai sun tafi asibiti da Saratu.
Nan na fada mata abinda ya faru don ganin su salima ban samu mata bayanin komai ba har na fito a
lokacin.
Take fadin dama ta fada ashe duk ranan dana zo gidan saita wullakantani a gaban kowa gashi ni ban
wullakanta ba ita ta samu duka haka.
Inda take fadin yanzu ta shiga duba jariri ake fada mata abinda ya faru nace a cikin yarenmu na
fulatanci ban taba bin kowa da mugun nufi a rayuwana yanda amma idan kace zaka bini da wani nufi
akanka abin zai kare ai.
Shigowan Nafisa har lokacin ina waya nan ta zube tana fadin ke kunbar gida da jidali Saiba ido ya
kumbura saida mama tace a kaita asibiti ashe fada sukayi sosai har yaya na fadin zaman mama takeyi ai
a gidan ba zamanshi ba.
Kiji min mata wai kuma ashine take zaune bata tafi gidansu ba ko hakan aita wullakanta dai data sani ta
bar zancen nan tayi hakkuri har lokacin da aka gama hidiman nan sai tayi abinda zatayi din.
Amma yanzu har wanda bai wajen sai yaji zancen nan ta dauka irin bayane da take kada iskancinta
yadda taso kuma a zauna lafiya.
Wai ita Nusaiban ce ta tayar da fitina inna ke tambaya don ni tunda ta soma magana ban bata amsa ba
nan take fadawa mahaifiyarta abinda ya faru zancen bai tsaya a nan ba don duk gidan kowa saida ya tofa
albarkacin bakinsa.
Maman fambeguwa uwar gidansu mama Dubu ita ke fadin duk wani shashancin da matan Jafaru keyi
laifin dubune.
Don bata son a fada bata kuma yarda wani ya tsawata masu idan matsala ya faru haka kiri kiri suka
tauye yarinyar nan Asmau a gidan bata da wani power matsayinta uwargidanshi sai abinda yar nan
Nusaiba tace shine yanzu suke son ya faru da yarinyar nan.
Idan Jafaru ya yarda aka hadashi da yarinyar nan bai kara samun mace irinta a rayuwanshi diba a yan
watanin nan yadda shi kanshi ya koma ya samu natsuwa da kwanciyan hankali a tare dashi fiye da baya.
Aini ina dauka tana hakane kan son da takewa yayanta din amma sai daga baya na fahinci wani abune
na daban ga hakan kamar yarinyar nan ta asirceta za ace.
Daga daki nake jiyo zantukansu irin na yan babban gida da idan an samu magana kowa saiya tofa
albarkacin bakinsa inda na kula da rikon Biba da yaya ya dauko muna yaiwa kakan yarinyar dadi sosai.
Sai haba haba takeyi da jikan nata duk da nasan an sakata daki an mata bincike akan zaman namu da
ita duk da nasan ba zata fadi wani mugun abinda rai zaikai ga baci ba saidai wanda ba aka rasa kawai dan
dole a samun hakan ga rikon da.
Daga gidansu muka wuce gidan anty Rukkaiya taji dadin zuwan namu sosai bamu jima ba muka nufo
gidan yaya Ai nan mukai magariba muka koma gida a cikin dadin rai don ya zauna da yar uwarshi sunyi
magana ta fahinta kan yaya baraka da matsalanta inda muka bar gidan da shawaran da suka yanke a
kanta inda yaya Ai da yaya Rukkaiya zasu can garin wajenta din duk wanan hukuncin mama dubu bata
sani ba a lokacin.
Saidai na kula da yanzu kamar yaya ya tsame kawu a cikin lamarinsu a hankali yake abubuwa bada
sanin kawu din ba wanda a baya ba haka suke dashi ba.
Tunda muka dawo gida ban tayarda zancen matarsa ba shima haka baiyi wani zance kan abinda ya faru
din tsakanin mu ba.
Ranan dai da dare yake fada min su yaya Ai zasu tafi gasau wajen anty barakah dan tarewan
amaryanta da za ayi kada ayi babu kowa nata a kusa.
Allah ya kaisu lafiya hakan kuma gaskiyane don ba dadi ace ba kowa naka kusa irin haka ya faru don
koba komai zasu dan rage mata damuwa da zuwan nasu.
Zanje gida in sanarwa mama koda abinda zasuje mata dashi don tunda safe ibrahim zai kaisu gobe in
sha Allahu nayi mashi a dawo lafiya ya fita.
A zuwa lokacin na sakankance dai kamar aurensu da Saiba yana rawa kamar yadda naji wajensu nafisa
da salima shima kuma ya fada ranan a gabana da yace zaman mama takeyi gidansa aiba zamansa don
haka tabar saka baki a matsalanshi da matansa.
Na dauka a ranan zatayi yunkurin barin gidan don cin fuskan da yayi mata a gaban mutane sai gashi naji
Salima da muke waya tana fadin wai Saiba ta samu yaya kan abinda za ayi na suna yace a gidana za ayi
komai nasa da jama,anshi don haka zasu shigo su tayani aiki ke nan.
Nayi mamakin jin ta saura a gidan ashe batayi fushin zuciya irin na mata masu jan aji ta tafi ba har
lokacin wanan ya kara min wani haske game da zamantakewa.
Don hakan ya nuna itace mai cutarshi bashine yake cutarta ba don da shine ke cutanta nasan ba abinda
zaisa ta zauna tunda har hakan ya faru koma dai maiye tsakaninsune ba zan saka hakan a raina ba don
tare nagansu bani kuma fatan a sanadina tabar gidan in sha Allah.
Koda ya isa wajen mama yake sanar da ita cewa gobe da safe su yaya Ai da anty Rukkaiya da inna
amarya zasuyi sammako zuwa Gusau wajen anty Barakha don suga halinda take ciki.
Budan bakin mama cikin mamaki sai cewa tayi da dan nata akan me zasuje duk bai isa mu walwale
matsalan ba sai sunje ba Jafar ?
Kafin yai magana iya ta bata amsa da fadin keko dubu wani lokaci kikan yi abu kamar mara tunane .
Idan su yan uwanta basuje sun nuna mata gata ba kece zakije da kanki kowa wanan shawaran da yaron
nan ya yanke ko ita barakha din zataji dadin hakan ai idan ta gansu tare da ita.
Hakan kuma zai kwantar mata da hankali don za a san tana da gata idan anyi mata hakan don Allah
kadai yasan bakin cikin da take can ita daya take kumsa ?
To shike nan idan hakan yafi ni a zatona iya za ai mashi magana akan kudin tane ya bata abinta idan
anje ai sai ya dauka ayi na,am da zancen aurensane yasa sukazo din.
Kaiya ni kikan bani mamaki wallahi dubu sai in rasa ina hankalinki ya shiga ki barshi da dabaran nan da
yayi namijine fa yafi tunane abinda zaije ya dawo akan komai .
Tunda kikaga ya shirya hakan dole akwai wani hikima da hakan ke nufi ai ga Barakhan dole idan za ai
wata tsiyar ganin idon yan uwanta dole a raga mata ai .
Banda abinkima Dubu yau in ba Jafar din da kuka samu kamar ruwan sanyi ba wa zai tsaya har yai
hakan yadda kuka rufe ido ke da yayanki kuka so ku tozartashi gidan nan kan kudin nan .
Gashi ai shi baici ba wani kato yaci a banza har da tukwaici ya dora maku dashi kuma ba yadda kuka iya
dole ku barshi da kudin ko don haihuwan dake tsakanin su.
Irin abinda nakewa gudu ke nan tun farko da yaran nan suka zo da zancen a fito da kudin nan a raba
abawa kowa nasa to gashi an raba din sun kuma salwanta don da kudin na hannusa da yanzu tana
tsakuran abinta tanaci hankali kwance ai.
Kuma da duk haka bai taso ba ai irin wanan abu ina yai dadi in zaki sake hali gara ki canja akan
mu,amulanki da yaran nan.
Shi miskilin daki ai kinji amsan daya bada ko yace ai mijintane don yaci kudinta to meye aure kuma aiba
za a hanashi ba tunda yana da ra,ayin hakan aita sani ta bashi kudinta din.
Kai iya wake zancen habu don Allah koshi Jafar din ai nasan yaki saurarensane ya yanke wanan
hukuncin amma Habu ai sam baiyi ba wallahi.
To koke fa amma yaro yazo da abinda zai fishemu kina wani zance so kike ke kije idan su yan uwanta
basu je ba kome gashi har da abokiyar zaman ki za a tafi me yafi haka dadi don Allah kin kuma san ba zai
kyalesu su tafi hakana ba ai.
Yanzu dai zan hada da Saratu ko salima su tafi tare don kada ya kasance nan dakin ba wanda yaje a
cikin mu hakan zai kara kwantar mata da hankali ai idan taga dayan yaran nan cikin su.
Yanzu dai ke akeji kuma shi dai ga abinda yazo ya fada ai idan saratun zata tafi ba sai a fada mai ba idan
akwai waje ?
Akwai waje mana iya tunda su uku ya lissafa zasu tafi saida ya dawo take fada mai cewa da saratu ko
salima za a tafi yake fadin .
Mama banson abinda za aje ayi tashin hankali a can don Allah wanan yasa ban saka kowa acikinsu ba
har Nafisa.
Ka dai bari dayansu taje zanja masu kunne kada hakan ya faru bashike nan ba shi dai baice komai ba
saida zai tafine yace da karfe bakwai zasu wuce fon haka mai zuwa ta shirya a cikinsu din.
Washegarin din kuwa hakanne ya faru bakwai na safiya suka biyo daukan saratu din don ita tace zata
salima tace itama ba zata ba don zasu tsaya shirye shiryen suna a nan kafin a dawo.
Yaba dukkansu dubu ashirin inda inna yabawa kudin tabawa kowa don haka saratun nashiga motan ta
mika mata nata kason tayi wani kata ta bata rai alaman don me za aba inna din kudi ta bata.
Haka dai suka dauki hanya karfe dayan rana suna gidan barakha din inda suka sameta cikin tashin
hankali daga ita har yaran nata.
Taji dadi sosai da ganinsu tayi kuka tana masu bayani inda suka bata hakkuri kan ta daure namiji yafi
danan idan ya tashi kumsawa mace bakin ciki ai.
Ta shareshi ta nuna ba komai tunda Jafar ya nuna zai dauki mataki akan kudin nata miliyan biyar da
dan kai dayayi mata dadin baki ya karbe.
Ai kafin wani lokaci labari ya karade unguwa na zuwan yan uwan Barakha din kinsan halin mutane nan
makwabta suka fara shigowa suna fadin albarkacin bakinsu.
Yaya Ai tace ba komai ai tsakanin miji da matane ai aure karuwane idan akwai fahinta don haka fatan
zaman lafiya suke masu yanzu.
Wanan zancen sai a kunnen Iliyasu ya shigo yana fadin kwarai yaya abinda naso barakha ta fahita ke
nan taki fahintana aure mukkadarine banyi auren nan don in tozarta taba wallahi.
Ba wani kadai bata kudinta aiba auren akace kar kayi ba kudinta dai take bukata kawai a hannunta
saratu ta fada don tana kule dashi tun shigowanshi gidan.
Haba saratu ke da na dauka zaki goyi bayana kuma har dake cikin wanan tunanen yanzu dai ayi min
hakkuri nasan nayi laifi don Allah.
Ai haka zakace dama yanzu kai don Allah dama haka amaryan zatazo ta samu yaya daki kamar zauren
malam ?
Daki ba komai alhalin tana da kudin ta ka rike kana kumsa mata bakin ciki haba saratu yayanki fa taki
kwantar da hankalinta muyi magana.
Yanzu dai kawo wani abu a shiga kasuwa ko kayan amfanin daki a saya mata sai ya kwashe da dariya
yana fadin saratu hoo ?
Ya shura takalmanshi ya fita matar zata fara fada yaya Ai dai ta tausheta tayi shiru sukayi sallah sukaci
abinci sai suka dan fita.
Kudin da Jafar din ya turo masu da suka sanar dashi abinda suka sameta ciki suka dauki babban yarta
tare suka fita basu dawo gidan ba sai yamma lis.
Sun sayo gado har da sabon katifa dasu zanin gado kula haka dai suka hado mata kaya kamcankam
kamar amarya.
Allah sarki tana ganin hakan kuka ta saka don murna dama wanan ne burin mace da za aiwa kishiya
kada kishiya tazo ta sameta hondadakwai daki kamar zaure.
Basu zauna ba suka shiga gyaran dakin nata hakana ko fenti babu amma ba laifi kayan saiya haska
dakin ya fito neat dashi nan aka zaune hira saratu ta samu bakin fadawa yar uwar sakon mama din tana
fadin ai kingani yanzu dai sai ki san zamanki da mijin nan naki.
Yau badon ya J ba da kunyan duniya yaciki kan mijinki donshi ko a jikinsa bai damu da halin da kike ciki
ba balle yayi tunanen hakkinki yana hannunsa ba ya fidsake kunyan hakan.
Bari saratu har kunyan jafar nake ji idan na tuna da abinda ya faru yadda mukai ta sakin magana a
lokacin kan kudin nan amma hakan baisa yayi fushi dani ba sai ga hawaye na zubo mata.
Tana kuka saratun tace ai mama zaki godewa tunda ita ta tsaya yai hakan don badon mama ba wallahi
Ya Habu ba zai bari ya kalleki ba mamace ta datse shi yai hakan .
Muryan inna da basu san da zuwanta wajen bace tace ko yaya ta saka yayi in baiyi niya ba aiba zaiyi ba.
Ji inna don Allah saratun ta fada tace kwarai ku dai godewa Allah daya bamu Jafar a cikin mu wallahi ya
kamata a dubawa bawan Allah nan irin kokarin da yakeyi din kan yan uwa.
Bawai dakinku ba kawai duk wani abu na gidan nan yanzu Jafar ne jigo ko wani daki kuma ko haihuwan
matan isah shine ya aiko da komai da akayi ga hadin kan yan uwa da yake kokari yi a yanzu.
Barakha a cikin kuka take fadin ai gaskiya inna ta fadi saratu ko mama ta saka yayi inbaiyi niya ba aiba
zai min ba ko ?
Ni sai ince auren nan na jafar alheri ya zamo muna yanzu wallahi tunda kan gida ya haduwa ta
dalilinshi ba kamar baya ba da kowa yake a watse gidan.
Wanan zancen da inna tayi bai kwana ba saida saratu ta faki ido taje tayi waya da mama tana zuzuta
maganan ga abinda ya dace ta fada ta tsaya tana haddasana a tsakaninsu kuma.
Washegari dasu da yaran anty baraka din suka taru suka kara gyara gidan tsab da wasu makwabta aka
dora girki ta saka les din da mama ta aiko mata dashi ta hanyar saratu.
Wanan yasa duk wani iya shegen da aka dau damaran yi ba samu yiwa barakha din ba don dan uwanta
da yafitar da ita kunyan duniya lokaci guda.
Sai ga kayan kallo da frdge sabo ibrahim ya shigo dashi haba anty Barakha a gaban yan unguwa tasa
sabon kuka tana fadin Jafar jafar yau ka zamo min uwa da uba a cikin duniya na gane ba abinda yakai
dan uwa dadi a duniya.
Dan Uwa Murfin Jallo
Ya J ya dinke wanan wanjen sai kuma wani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/7, 10:38 PM] Zainab Idris Makawa Writer: Follow this link to join