Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
saareb na magana kamar cikin fada.
Ita kuma Saiban tana gyada kai ya kallesu yana fadin kingan suko yaya yarinyar nan Saratu na rasa
meke damunta sam bata da tunane wallahi.
Saratu ai kowa yasani ita da wana matar taka kansu a hade yake ranan da aka kawo yarinyar nan
saida Iya ta shiga rigan arzikin ta a cikin mutane tayi mata kaca kaca ta shiga hankalinta.
Suma a bangarensu ido suka zubo masu saidai basu daina maganan da sukeyi a lokacin ba har su yaya
suka fito daga motan suka nufi hanyar part din iya suna wajen tsaye.
Shiya fito a karshe daga motan bai ko kallo inda suke ba shima part din na iyan ya nufa ya shiga suna
wajen suna shirya abinda suke gani shine daidai gulmata dana yar uwata sukeyi ba wani abuba.
Inda Saare ke kara ingiza Saiban akan kada ta yarda ta ban daman da zan samu wurin shiga ga miji don
nufin mu mugaje gida ko ?
Tunda mu mama ta haifawa yayanta inda saiban ke jin tankar taje gidan ta sameni tayi min tsinanen
dukan tsiya don a ganin ta tana iya murzata idan ta samu gamina.
Sai saratun ta hana tace wanan su bari idan yaya ya bar garin ko ita zata rakata ayi hakan illa dai ya
zageta dama an saba hakan ai kanta.
Tasan kuma mama ba zata kyaleshi ya sakata a gaba ba zata tsawata mashi sun dai dauki mataki a kaina
lokacin.
Saiban ke fadin ita ta rasa me J ya gani a jikina da har yaje ya aureni ba tare da ya tsaya tunane ba ?
Keko aiba kai sake bane wanan abin da gani ai aikin asirine asiri mukai mashi muka sameshi ai daba
haka ba ai ina ni inashi da za ace wai nice yake aure.
Gaisawa aka fara yi a tsakaninsu da iya mama dake daki taji muryansu ta fito suna gaisawan da ita
lokacin shima ya shigo.
A,a gaku kamar tare kuke tafe mana kun shigo lokaci guda haka mama dubu ke fadan hakan .
Sai Anty Rukkaiya tace daga can gidansa muke ai tafiyan nasane dama munzone gun sarakan mu da
kayan tausan gabansu.
Kaya kuma kayan tausan gaba kamar wani abin bin bashi tunda anyi angama haka ba wani shiri har
wani kaya kuma za a zo sayan bakinsu dashi ?
Yau aka fara hakan idan mijinki bai maki bake shi yana da ra,ayin yiwa iyalinsa hakan kuma nice nan
nasashi yin hakan gareshi ba wani ba.
Meye amfanin samu dama idan kana da zarfin yin abu kayisa a cikin lokacinsa tunka lokaci ya kure
maka don wata rana sai labari.
Kwarai kuwa anty Rukkaiya ta fada daga ta karbe iya dake magana ai har yanzu mama dubu ana hakan
ai silan zaman lafiya maigida yake nema ga iyalansa ga hakan.
Suna dai ta fadansu dagashi har mama shiru sukayi lokacin kowa da irin abinda yake tunane a
zuciyarshi idan yake auna zancen mama da rashin son hakan da yayi din karara.
Ita kuma mama sai auna irin yadda dan nata ke kashin kudi akan zancen matansa ko wani lokaci har
yaushe ya gama da zancen wanan auren daya dauko balle ya dauko wanan din ?
Ina kayan suke yanzu ta fada tana sauke ajiyan zuciya tana kallon yaya Ai don tasan halin Rukkaiya har
take ita ba kamar Ai din ba.
Suna mota ta bata amsa sai lokacin ya dago yana fadin mama aina jima da sayansu tun lokacin dana
hada lefen Rahama suma na hada masu nasu don ban garine ba a kawo masu ba.
Allah ya kyauta ta fada tana daukan jug din kunnun kamu da aka dama mata tun safe bata sha ba
salima yasawa kira daga falon.
Ta fito tana gaidasu ta juya wajenshi yake cewa Salima kira saratu kuje mota kaya na nan bayan mota
ku kwaso sai kije ki kira min su Asmau suzo nan.
A,a kaiko a can za a kai masu bakaji bahaushe yace tausan kirjiba a yaren mutanen sokoto wanan ai na
ban hakkurine ba zasuce dai bakayi masu ba ai iya ta tare da fadan hakan.
Kai tsohuwar nan tasan komai wanan gaskiyane mu da mukai masu laifi aimu zamuje mukai masu har
daki ko yaya Ai ke fadin hakan.
Salima dai tana tsaye yace jeki ku dauko salima ku kawowa su mama su gani kafin a mika masu ya fada
yana kallon Salima din.
Ta samu saratun zata shigo don su gaisa da yan uwan nasu take fada mata zancen yayan nasu ta wani
bata rai tana fadin kaya kuma kayansuwa kuma ?
Ni inana sani ta bata amsa a takaice ta wuce ta bata kara furta komai ba zuwa wajen motan nasa ta
bude bayan motar da dama saida ya bude ya fito.
Dankari kayan su waye haka wai ta kara fada tana karasowa wajen motan ita dai salima takaicine ya
kume ta sai gashi ya fito shiya taimaka masu ya fitar suna shiga dashi.
A tsakiyan falon iya suka tara kayan shiya shigo a karshe da wani daya dauko ya aje gaban mama yana
fadin mama ga naki nan.
Yaya Ai ban fada maku tun can cewa wanan na mama bane wanan kuma nasu iya dasu salima ikon
Allah kai Jafaru kace yan tausan gaban suna da yawa nikan naga abin da yawa.
Salima jeki wacan na wajen ki dauka ki mikawa matar habu duk suka kalleshi ya fuske yayi niyar hakan
shiyasa ya fada a gaban kowa yaya Ai wanan nasu Asmau ne idan kun tashi sai su kama ku mika masu.
Ikon Allah lokacin abu ayisa kanina kayi kokari Allah ya saka maka da alheri anty Rukkaiya ta fada cikin
nuna jin dadinta ga abinda dan uwan nasu yayi.
Kai haba ai hakan ya zama riya nime zanyi da wani kayan tausan gaban uwargida kuma da sauri
Rukkaiya tace a,a keko maman Habu.
Wanan ai sai dan da yasan darajan iyayye da yan uwa yake wanan wani ai kome za aji bai dameshi ba
albarka kawai a yanzu zaku saka mashi.
Sai lokacin ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yayi albarka an gode anty Rukkaiya tace Allah kuma
ya basu zaman lafiya ya kawo zuria masu albarka a ciki muzo suna haka kafin shekara.
Ya mike yana fadin zan lekasu tare suka fita da salima daga part din ta dauki na Yanda ta nufi part
dinta dashi cikin farin ciki.
Lokacin anty Rukkaiya ta mike tana fadin bari mu bude muga abin arziki muba ido abincinsa abu yayi
kyau wallahi jafar kayi ko yanzu da mama ta yarda tayi wani aurene bayan baba ai a kara haifo muna irin
jafaru bamu fushi.
Aka kwashe da dariya na mama aka fara budewa sai am barka sukeyiwa kayan turmi biyarne da lace
har da dadduman sallah a ciki yaya Ai tace kin gani maman Habu a samu na muna addua kenan tana
daga dadduman sama.
Turaren ciki suka dan fesa dakin ya dauki kamshi wanan aikin anty salma ke nan gaba daya an yaba
komai a wajen .
Rigiji rakwaf inji hausawa don Asmau dake zaune a falon tare da maigidan don ita Saiba daki tashige
tana jan kamshi.
Shiko tunda ya zauna bai daga daga wajen ba yana zaune tare da Asmau da yaran suna hira sai gasu
suka fara gaisawa yaya Ai ke fadin ina yar uwar takine ?
Tana ciki ta fada tana kallon hanyan dakin Saiban ta yunkura ta mike zuwa kiranta lokacin ya mike ya
shige dakinsa ya rufo.
Saiga su sun fito tare suka samu waje suka zauna ta gaidasu a tsatsaye da ina wuni suma suka amsa da
lafiya.
Yaya Ai ta soma magana take fadin to Asmau Nusaiba gunku muka zo wanan kayan nakune na fadan
kishiya aci da hakkuri don Allah.
Tsuweee Saiba taja wani tsuki da kowa wajen ya kallota yaya Ai cikin rashin damuwa da hakan take
fadin hakkuri dai za ayi tunda shi kowa keyi abinda muka gada ke nan.
Da fatan zaku zauna lafiya da yar uwar taku itama daga can muke munyi mata fada daidai gwargwado
da azauna lafiya don Allah tunda yanzu an zama daya.
Yaya Ai zaman lafiya kam ai babushi tunda tun farko ba a nemi a zauna lafiya ba yanzu daidaine J yazo
ya auro muna wanan yarinyar a matsayin kishiyar mu ?
Haba dai don Allah ayi muna adalci mana don Allah abinda akai muna anyi daidai ke nan ga hakan ?
Yaya Ai tace adaiyi hakkuri dama hakan muka gada ai a rayuwan mu tunda mun fito musulmai
Alhamdullahi ai kishiya inga hakkuri abokiyar zamace saidai wanda basu gane hakan ba .
Yanzu dai ga kayan fadan kishiya nan mun kawo maku don bai zaunu bane ba abayar a cikin lokaci ba a
yi hakkuri don Allah.
Babu komai yaya mungode Allah ya bamu hakkurin zama da juna mun gode ai muna godiya ta mike
zuwa dakinta itama nusaiban ta mike tabar wajen a fusace .
Anty Rukkaiya tace ikon Allah yar nan da karfin hali kike kuwa kema ai wata kika sama kika shigo kuma
tayi hakkuri ba a hakkuri haka aka zauna dake ?
Ashe taji sai ko ta dawo tana fadin in ita taga tana iyawa ta zauna ni banga ina iyawa ba dama anzo a
fada muna maganane a fakaice yadda aka saba ashe ?
A,a Nusaiba kar kice zakiyiwa su yaya rashin kunya a nan gaskiya Salima ta fada don tunda suka shigo
da kayan ba wanda ya fita a cikinsu.
Wanan hayaniyar yaji ya fito yana fadin wai meye meke faruwane wai haka ?
Yana kallon Salima din .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/21, 9:26 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Shiru tayi ta juya zuwa dakinta cikin hasala ashe baki ciki yar iska ba daki dawo ki maimaita abinda kika
fada a gaban yan uwana.
Yau in baki mamaki don da kinbar gidan nan na har abada su yaya zaki kawowa rashin kunyar ki sun
wuce hakan a wajena balleke.
Duk iya shegenki da iskanci ya tsaya akaina amma banda yan uwana don kamar iyayye suke wajena
bazan daukar maki wanan iya shegen daki dauko yi a gidan nan ba.
In zaki zauna kiyi hakkuri yadda kowa yayi ki zauna idan baki hakkuri kuma kofa a bude yake gareki tun
yanzun nan kaji min sakarai mara lissafi ba a hakkuri ke akai hakkuri dake aka zauna koba wata kika
shigo kika sama a gidan nan ba.
Akwai yar cin aman data fiki keda kika yaudari kawarki kika hana mu zaman lafiya don son kai irin
naki ?
Yi hakkuri Jafar mu ai mun tashi ke nan muma tunda munyi abinda ya kawo mu.
Mu yanzu idan bata so dai ruwanta Allah ya gani ka fita hakkinta ai ba kowani namiji ke wanan ba yanzu
don ya kara aure.
Yanzu a zamanin nan in bashi ba wani namiji zai kashe maki wanan galarin haka kuma baki shafa masa
lafiya ba gidansa ?
Shi ya daukesu don ya mayar dasu gida a hanya yayi fada sosai yake fada masu irim damuwan da
saiban har asmau suke sakashi ciki.
Sai hakkuri suke basu a nan family house suka sauka tare da nasu abin arzikin har yan uwan zaman
mama dubu alherin ya shafa.
Dama haka yakeshi muddin ya samu kudi sai kowa na tare dashi ya sani don zaibi yan uwa daga daga ya
dinga masu dan alheri daidai gwargwado.
Wanan yas arzikin yake bukansa kamar an bude masa kofofin arzikinsa ga baki daya shi mutum ne mai
yawan alheri.
To wanan alherin daya shigo maine yabi yan uwa ya raba masu abin arziki har mazan da yan unguwa
abokan arziki ya samu abinda ya basu a lokacin.
Kwana shidda ke nan yayi a gidana kuma zai koma washegari don aiki daya taso mai na bussiness dinsu
lokacin sun samu kaya irin wanda suke fita dashi waje din zai tafi ya gani.
Ance sabo turken wawa a yan kwanakin na saba da yaya Jafar sosai yadda yake jana a jiki hakan yasa
na fara sakewa dashi inda ko fita yayi kafin ya dawo na shiga damuwa.
Shiko sai shirye shiryen tafiyansa kawai yakeyi daga gidan iya har nan da nike ni kadai abubuwa kawai
yake shigowa dasu yadda ba zamu nemi komai ba ke nan a bayanshi.
Gwargwado yaya Jafar yana kamanta adalci a dan fahintar danayi mashi yadda yake a tsakanin iyalinshi
din haka kuma ina ganin yadda yake mu,amulansa a baya kafin na aureshi.
Missalin hudu ya shigo gidan nasu kai tsaye part din iya ya nufa wanan dabiansane yanzu sai ya fara
shiga yaga kwanansu ya wuce zuwa wajen matanshi.
Saidai ga mamakinshi a nan part din ya samu matan da kowa na gidan zaune inka debe yar uwara da
yanzu ke zaman kadaici ita kadai don kamar an hada mata kaine a gidan gabadaya sai salimane ke kula
lamarinta.
Suna ganinshi sukai tsuru tsuru bakin dayansu kallo daya yayi masu ya fahinci akwai matsala haka ya
daure ya gaida mama da iya ya samu waje inda saratu ta daga ya zauna yana fadin.
Lafiya dai ko ?
Ina fa lafiya Jafaru fitina su wa yan nan ai bata kwana a wajensu ko yaushe tsaye take suna figanta.
Wai kayan nan daka shigo dasu suke fada a kai yakai harda bugaiya suna nema su illanta kansu sujawa
mutane aiki.
Fada kuma akan me iya to gasu nan dai kaji a bakinsu ance waka abakin mai ita yafi dadi dama.
Duban inda suke zaune yayi yana fadin ke Asmau ya akayine tace ina daki Nusaiba ta sameni wai na
rage kayan nan dakai muna su yaya suka shigo dashi.
Wai da suka tafi na hurhura kayan cikin na kwashi masu kyau nabar mata marasa kyau don haka in fito
da nawa ta dauki abinta niko bansan wasu kaya dana dauka a cikin nata ba.
Innalillahi ya ambata a fili ya katse mata zancen da fadin iya kayan nan komai iri daya aka saka don
gudun haka yanzu haka kayan haihuwan ita asmau suna nan aje don kada tazo ta haihu ban kusa a
girsheni don hakane ban kawosu gidan nan ba na aje.
Amma kuma wai kinji abinda wanan mara hankalin take fada yanzu komai fa kala dayane a cikin
akwatin saidai a banbanta kala kawai .
Samu sukayi aida Allah bai kashe ya basu kai ba daka zama bawan matam da basu godewa irin hakan
ba zai faru ba to sun samu sai suyi iya shege ai mama ta fada cikin kunan rai.
Mama laifine yau na samu banwa iyalina ba au duniya saita zageni kan hakan to ya zama laifi kan a
wajen matanka yanzu .
Yanzu idan nayiwa Rahama kayan lefe ban masu komai ba ni kaina nasan sai Allah ya tambayeni akan
hakan tunda ina da halin yin hakan garesu duk da nasan karshe wullakantawa zasuyi tunda basu iya
tattali ba a rayuwansu.
Nusaiba baki da tsoron Allah a lamarin ki kayan nan bake kika rokeni ba ganin daman kainane na hado
makushi yan uwana da suka kawo kayan nan ranan saida kika nemi yi masu rashin kunya.
Don baki da kunya yanzu kece kika dawo kina fadan kayan kuma ke bafa dole bane zama dake Nusaiba
koda duniya muka haifa dake kin sani ?
Kawune ya shigo yasa yayi shiru bai cigaba da fadan da yakeyi ba lokacin gaidashi yayi ya mike yana
fadin mama ni gobe zan koma daga can ina ganin har kasan waje zan fita don mun samu kaya zan bi jirgi
in samesu can.
To wani kasa aiki kuma kuka samu na fita kasan waje yanzu Jafar kawu ke tambaya yace eh ba wai
kasan wajen turawa make nufi ba ai nan ghanane kawai na fadi hakan don ta gane.
Ghana ba kawai bane ai Jafar ya fada yana dan dariyan yake a fuskansa zuciyarsa kuma tana mashi
tafasa da wanan zancen da yaji don yasan a baya kome jafar din ya samu zai fada mai.
Yana fita part dinsa ya nufa Nusaiba ce ta fara mara masa baya ta bishi ganin ya nufi part dinsu yasa ta
biyoshi ba tare datayi magana ba .
Dakinsa ya nufa ta bishi a baya ta sameshi duke yana daukan wani takarda a drower ya dan juyo jin
anshigo dakin ya ganta tsaye a kansa.
Yanzu tafiya zakayi baka dawo gidan nan ba kome komu bamu da hakkin ka dawo wajen mune inka
gama kwanakin ka a can din.
Kwanakina ai bangama ba zan tafi tunda saura kwana daya in mata a gidan ta kinga kuwa ko ita ban
karasa mata kwanta ba ke nan ai ?
Cabdi wanan ai zaluncine wallahi mu meka maishemune wai yanzu ?
Abinda kika maida kanki shina mayar dake Nusaiba ke inkina da kunya har zakiyi wanan maganan a
gabana to inama kikaga kunyan balle babu sam baki da kunya don ban taba zaton haka kike ba ai sai a
cikin yan watanin nan nasanki tsab.
Kome zakace zakace ai tunda anke an baka kasha ka lashe baki yanzu mun zama banza da bamu da
amfani mu a wajenka.
Au ba wankewa tayi ta ban ba, kaina kafa nasha na lashe ,ai ban tsaya saita wanke bama nina kafa kai
na lashe komai da kaina.
Lalai akwai kazan uban nan kuwa don gabadaya an sauyaka yanzu har da abinda baka yi ka fara yinsa
gidan nan to mu zuba da ita wallahi.
Ki dai zuba yadda zaki iya kwasa aurene dai nayi baku da kudin wani na kara aure ba yadda na auroki
aka tara shedu haka itama na aurota gidana.
Yazo ya wuceta da takardan a hannunshi zuwa falo nan ya samu Asmau ya zauna yana duban
takardun nasa saiban ta fito ta sameshi tana fadin.
Wallahi duk abinda mutum keyi Allah na ganinsa ka dauko yarinyar nan don ka bakanta muna rai kan
abinda bamuyi