Chapter 35 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   35 / 101

102K to 105K   out of 302.2K words

hikimarsu ta manya ya fara kebewa da kawu yaji ta bakinsa inda ya bashi iya abinda zai
iya bashi don shi kawu din cewa yayi a taimaka masa da wanda zai rika karban abu wajen wanda duk ya
bukaci abin hannunsa an kuma bashi din.

Saida kawu zai fita yace ya turo mashi Jafar yai wani magana dashi daya shafi zancen wajen aikinsa
hakan yasa kawu din ya fadawa Jafar da ya shiga zai gana da hardo.

Jafar din ya dan tsaya jim yana dauka akan zancen Rahamane kawu ya gana da hardo din sai bayan ya
shigane yace aida sun shigo tare da Habu inda ya kira wani yaronsa ya nemo habu yazo shima.

Bayan sun zaunane ya soma magana yana fadin ku saurareni kuji abinda zan fada maku don yanzu kun
zama yayana tunda kuna auren jinina.
Don abinda yasa na nemi ganawa daku shine kuna tafiya inwanku a waje don haka kowa ya taka ku
lokaci daya zai sameku don ku din kamar yayan rokone.

Suka dubi juna a tsakaninsu yace akwai wani abu da mata keyi yayin da Allah bai basu haihuwa ba sai
su kasa hakuri suga kamar Allah ya manta dasune.

Idan mace ta tsunci kanta cikin irin halin nan zata daga hankalinta har na tare da itama a lokacin kowa
yace ya iya zata kai kanta gareshi neman haihuwa don ta samu taga jininta a duniya.

Saidai kash irin hakan akwai hatsari a cikinsa indai ba malamaine suka bada wanan sa,an ta wani
is,simin sani da baiwan da Allah yai masu daga Al,kur ani mai,girma ba.

Mafi yawan mata suna halaka zurian su ta wanan hanyan zuwa wajen malaman tsubbu da yan bori
dake aiki da aljannu da sunan samun sa,a su wa yan nan diyan sune yayan roko da nake nufi.

Wani irin zufane ya tartsowa habu a gaban goshinsa take kuma mafalkinsa na baya ya fado masa a rai
har hankalinsa na neman gushewa a garesa lokaci guda.

Muryan hardo ya dawo dashi daidai hardo dake fadin irin hakan uwarku tayi shine kuma a yanzu yake
shafan dan uwanka kai habu harkai baka tsira ba saidai saukinka gudane haduwan auren ka da maria
shine hasken taurarinta ya hasko naka din.

Zama ya gyara yana fadin nasani baba nasan hakan tun ban hadu da maria ba don a ranan da zan taho
cameroon wata mace ta fada min kusan hakan a dunkule.

Nan ya kwashe komai har da zuwa neman matan da sukayi da mama dubu da kuma mafalkin da yayi
daga baya har yazo zancen bada maganin da nayiwa ya jafar din.

Sai lokacin Jafar da yayi suman zaune ya iya budan baki yana kallon dan uwan nasa yace yanzu habu
kasan da hakan kaki fada min komai na tashi tsaye inata wahala ?

Baisan komai ba iya abinda aka sanar mashi ke nan amma shi wanan kawun naku yasani yasan komai a
game daku saidai nasa manufan akanku ya hana ya fadawa uwarku gaskiya don amfanin kansa da yakeyi
daku yanzu.

Sanda dake gefensa ya dako ya aje a gefensa yace kunga haka hakan kuke tsakaninku dashi ba zaku iya
komai ba saida izinin wanan mutumin.

Saidai ku a wajen ku hakan biyayyane a gareshi wanda ba haka bane tsananin karfa ce dake tsakanin ku
dashi yanzu dai idan Allah ya maida ku gida lafiya ku san yadda kukayi da mahaifiyar ku takai wanan
sadakan da aka umurce ta dayi shine maslahan ku dasu haka shima abinda yayi a kanku din duk zai
karye.

Kofa habu ya duba kamar kawu din na tsaye yana sauraronsu yaji Hardo din yace wane shi nan ai tuni
na hadashi da abinda zai sakashi kwana ba zai taba jin abinda muke fada ba a yanzu.
Ku saki jikinku kuyi maganan da duk kuke son yi a wajen nan kun dai san baku tambayeni ba nice naga
dacewan in fada maku gaskiyan abinda ke a duhu gareku.

Shiru wajen yayi kafin habu din ya fara kawar dashirun da fadin baba na rasa me yake damuna haka
kudi zasu shigo amma ban iya abin kwarai dasu zasu lalace min h,,,,,,,,

Wanan sherin wanan kawun nakune da matarsa dake dorasa a hakan aiba halinsa bane sherin matane
matarsa ce matsalan taku tana hassadan da za ace uwarku ta fita sa,an haihuwa.

Jin zancen hardo sukeyi a wani bakon yanayi da basu taba zato ba a zukatansu wai kawune da wanan
halin hardon ne ke magana yake fadin.

Aishi baffa tsoron Anini yakeyi shine ya saka ya jata a jiki fiye da yar uwarta don da tana wajen shi har
yanzu na tabbatarda sai Anini ta karya duk wani shirinsa akansu.

Nan ya kwashe tarihin mu kaf yabasu da irin yadda baffa yaci kurwan dan uwansa mahaifinmu a
cewarsu ya gwada na yaran saidai tasu kurwan duk a boye take don duk aka haifesu sai na boye
inwarsu.

Shiko dan uwansa ya samu nasaran samun damansane a cikin abin sha da magariba sa,an mugun duk
wani mugunta da magariba mugu ke aiwatar dashi don a lokacin mumunai suna gagawan saduwa ne da
ubangijinsu sun sake komai a lokacin.

Taurarin Anini yafi duk taurarinsu karfi shi baffan nasa ya sani yau ko katsa ta diba taba mutum da
sunan magani sai karbu ga mutum balle wanan dafa,in mai karfi.

Sai daga bayane suka fahinci wace hardo din yake kira da Anini sunana na gado da suke kirana dashi a
ruggar tamu ke nan.

Zaka samu alheri sosai dan samari zaka ji dadin zabinka sosai koma ince haka dukkan ku auren ku da
yaran nan alherine gareku babba.

Saidai a hada da hakkuri yana fada ya dauko wani dan kullin magani a cikin jakkarshi ya banye kullin
yake fadin habu ya miko mashi hannunsa ya dinga murza mashi abin a tafin hannunsa yana fadin da
bafullace kake sai kowa yasan garakanka a nahiyar ku amma yanzu kai bansan abinda ka dosa ba.

Hakan yasa Habu sakin murmushi yana ajiyan zuciya hardo na daure maganin Jafar yace nifa hardo
saida hardon yayi murmushi yace wai ta Allah ta isheka bari dai kagani kofafinka zasu bude nan ba da
jimawa ba da zaran kun hade da matar taka ai.

Ai wanan baiwan taka yaja maka haduwa da hadadrun da kake fuskanta saidai Allah na karekane don
ibadan da kake dashi hakama mahaifiyar ku.

Duk da ana bata karfa kullum amma bata yarda tayi sakaci da ibadanta ba wanan ne ubangiji yake
kwato ku har zancen dan kabilan ibon daya jefeshi a kafa ya kumbure saida hardo ya fada masu da
zancen kawu dayasa suka kara shiga natsuwansu akanshi.
Kusan dai raba dare sukayi a wajen hardo din koda suka koma masauki sun samu kawu yana ta sharan
barci ba kwanciya sukayi ba alwala suka dora kowansu ya tayar da nafila.

Washegari dasu akai sallah asuba a ruggan an idar jama,a zasu watse hardo ke fadin akwai daurin aure
a kofan gidanshi da karfe bakwai na safiya.

Gabadaya kowa yayi mamaki dajin sanarwan hardo din inda suka fito da mamakin hakan sam basu
kawo cewa sune da auren ba don gidan hardo gidan jama,ane.

Hakan yasa suka dakata da tafiyan don kara gasu hardo din sai da akazo daurin aure ne abin ya basu
mamaki da hardo ke fadin kawu ya matso ya amsawa dansa auren Anini din.

Sukuma sune waliyan amarya su kawo sadaki dubu hamshin daga garesu kowansu yayi mamakin hardo
nan danan habu ya kirgo dubu dari ya mika a matsayin sadakin hardo yace baiki ba amma jafar ya bayar
da kansa yake so don shine mai aure.

Ya saka hannu ga aljihunsa ya ciro dauri biyu na yan dubu guda ya aje a gaban hardo din ka shiga
hidimar daurin aure kamar yadda sharia ya gada.

Kamar ance habu ya dago kai ya kalli kawu yayi mamakin yanayin daya hango kawu a cikinsa ya dan
radawa J din daya dubi yanayin kawu din a lokacin.

Anyi lafiya an watse sai lokacin sukaje godiya wajen hardo nan yake fada masu cewa idan sun koma
sun saka ranan tarewa sai ummah ta bugo waya mata suje ayi bukin acan wajenta kaduna tunda tana
kusa dasu shidai yayi nasa na uba a nan.

Haka suka bar rugga cikin jin dadin halarcin hardo garesu suka nufo gida cike da farin cikin sa,ar tafiyan
tasu zuwa ruggan mu.

Har suka iso gida ba wanda suka fadawa ga abindake faruwa tsaraban da suka dawo dashine irin na
wajen mu yasa Yanda tambayan ga kaya kamar na wajen mu dai ?

Yana daga kwance yake fadin daga can suke ai har can din muke hardo ya hadomu dasu akawo maku.

Yanzu yaya Habu zaku rugga shine baka fada min na bada sako zuwa wajen hardo ba saidai naji kunje
kawai kun dawo hannu sake ?

Waya fada maki hannu sake mukaje maria kinsan koni bankai abuba J zaikai don bai saba zuwa waje
haka hannu sake ba,shi.

Tashiga juya abin da mamaki saidai babu daman magana don haka ta kyaleshi ta shiga kawar da kayan
zuwa kitchen dinta.

A part din iya kuma washegari da aka shigo da tasu tsaraban take fadin kasan fulani kukaje ke nan daga
zuwa tafiyan wuni sai kuma kwana haka matar dauda ta ishemu da waya bataga mijinta ba.
Kamar wani yaro kuma yaran matanku basu damu kamar yadda ita ta damu ba ni Hansatu na rasa wani
irin so takewa dauda haka har tsufa.

Jafar ne ya shigo cikin wani dinkin shadda mai maiko ga laushi da santsi kallan ruwan konanen kuka sai
kamshi dake tashi a jikinsa ya kafa hular data dace da kayan da bakin takalma half cover ta maza

Ikon Allah wanan shigafa haka Jafaru sai kace wani ango dakai can kana zuba kamshi ya washe baki
kafin ya kai zaune yana fadin ai ango nake Iya tsohuwa.

Kema dai shigar tawa ta burgeki kenan iya ina amaryan tawa zataga shigan nan ta yaba haka kafin ke
iya ki gani ki yaba din.

Kunji ja,iri ni ba amarya bace ke nan kakarai ka fada wanan matar taka Nusaiba taji tayi muna dariya ko
ita dai na rigata ganin wanan shigar tunda ita bata yaba ba.

Ba zata jimu ba iya koda taji din ma ba zata samu hakoran dariya gareki ba a yau iya don nata ya
sameta tunda kin kirani da ango ya fada don ganin irin kallon da iyar tayi mai.

Itama iyan murmushi tayi tana fadin jafaru na dai gane kamar kana son kara aurene a yanzu don
abinda yaran nan sukai maka ?

Da dai kayi hakkuri dasu hakana don koka kara auren wa yan nan masu ido a tsakan kai ba fasa halinsu
zasuyi ba yaran da suka bushe fitilansu suka iya dawowa nan idonawansu a bushe haka ?

Kayi hakkuri ka shirya da matanka ku zauna lafiya tunda ita wanan mai idanu kwashi kwashin ido a kafe
mata na rashin kunya kowa ka auro a gidan nan ba zata taba barin ku zauna lafiya ba.

Iya komai kayi a duniyan nan saika samu wanda ya fika iyasa ai nata kuka gani bata san wace zan auro
mata ba a yanzu ki saurara zaki sha kallo ne a gidan nan ai kwanan nan.

Allah ya zaba maka mafi alheri a rayuwanka jafaru yace amin iya yama zaba har ya ban ki dai tayani da
addua kawai iya shi nafi bukata a wajen ku yanzu.

Jafaru uwarku ba zata yarda ka kara aure a yanzu ba yadda naga ta daukaka zancen yarinyar nan tun
dawowanta gidan nan ni har tsoro abin yake ban.

Wai mama ya tambaya yana mikewa yace mama kan ki tayani bata hakkuri don aikin gama ya gama a
yanzu saidai adfu,a a tsakanin mu kuma.

Ka daiyi niya baka jin kwabo nake gani Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri a rayuwan mu amma
daka shirya da matan naka har dai wanan mai tsohon cikin.

Aida cikin ta biyewa sherin yar uwarta a kaina iya ni sam ban ni tausaya mata don itama bata tausaya
min ba lokacin da nafi bukatansu a kusa dani ai.
Yasa kai ya fita iyan ta bishi da kallo ita kadai a falin take magana tana fadin tsiyan kakai namiji a bango
ke nan ai shimai hakkuri bai iya bultsewa ba dama yaron nan yayi hakkuri a rayuwansa kusan dai ace a
tauye yake.

Salima dake jinsu taki fitowa su gaisa don gudunsa da takeyi kan kada su hadu don zancen saurayinta
data turo mashi washegari daya dawo garin .

Kuma ya tabbatar mata da cewa yaga J din sunyi magana amma kuma baice mata komai ba har yanzu
game da zancen.

Au damake idon ki biyu kina jin shigowan yayanki kikaki fitowa take cewa salima din saida ta zauna
take fadin ina jin ku iya tsoronsa nake ji kada yayi min fada akan Yusuf.

Haukar banza shi zai zauna maki dashi da zai maki fada tunda kin dage saishi shi meye nasa naki kece
zaki zauna da abinki ai ba wani ba ?

Iya nifa zancen yaya kamar aure yake bida har zance yayi nisa don irin amsan da naji yana baki a yanzu
har cewa yayi ai Allah ya zaba mashi ko saidai addua.

Yo saidai adduan mana tunda nasan uwarku wanan karon ba zata yarda ba ko wanan sakaran daya
aure daga baya ai saida aka inmata.

To ita mama meye nata a ciki tunda shi zai zauna da abinsa kya fada kema yar nan nidai banga abin
sakawa yaro ido ba yana cikin lokacinshi.

Kuma ko banza tara mata ai gada yayi tunda ubanku ras mata hudu ya jera a gidansa ya zauna dasu
ashe ko aure gadonsa yayi.

Habu ya dauka suka fita don suje wajen mama suna daukan hanya daga gefe inda yake zaune yake
fadin muje samaru sai habun ya dan kalloshi.

Amma baiyi magana ba ya dauki hanyar Samaru din kamar yadda dan uwan nasa ya fada da kwanta ya
kawosu kofan wani gida mai dogon gina horn sukayi aka bude gidan daga ciki habu yasa kai da mota ya
shiga.

Bin gidan yake da kallo kafin ya dubi dan uwansa yana fadin wanan gidan fa J gidan waye haka baiyiwa
habun magana don maigadi daya iso yana gaidasu lokacin.

Hakan yasa ya bude motan tare da amsawa maigadin yace baba mun sameku lafiya habu din shima ya
fito yana kara bin gidan da kallo .

Ya juyo ya kurawa dan uwan nasa ido daga inda yake tsaye saida ya gama maganan da zaiyi da maigadi
yace to yaya kaga Surprise din ?

Kallon ban gane ba habu yayi masa yace ehh nina gina abina da kaina Habu da gurin in mama ta yarda
na baro can na dawo nan.
Yau shekara kusan biyar kenan ina wanan ginan ba tare da kowa yasan da hakan ba sai yau nake fada
maka don na fahinci mama ba zata bari na baro can ba a yanzu.

Wancan dayan ginan kuma na gaban wanan din kai da yazid na dorawa saidai rashin lafiyana yasa
komai ya tsaya min a lokacin .

A yanzu sam ba zan iya dauko saiba ko Asmau na kawosu gidan nan ba don na fahinci basu taba canza
halinsu na kazanta din nan.

Sai gashi faduwa yazo daidai da zama yanzu Rahama zan aje a nan ta zauna su kuma su zauna can din
har abinda hali zaiyi muje mana ka ga cikin gidan sosai habu.

Sai lokacin habu ya nisa yana fadin ninaso na riga wanan Surprise din ashe ka rigani saidai ni tawa
gaskiya ko rabin wanan baiyi ba J.

Tau ashe kaima kana da wanan dabaran ya ciro dan makuli daga aljihunshi yana bude falon suka shiga
ido waje Habu ke bin ko ina da kallon mamaki a gidan.

Don bai taba tunanen dan uwan nasa yana da irin arzikin da zai gina wanan mamaken gida haka ba a
ransa muryan Jafar din ne ke kara fadin.

Idan Allah ya nufa ina kuma rokonsa da yaban rayuwa na kammala gidajen nan Habu don na dankawa
kowa dukiyansa a hannunsa in huta.

Kaga wanan da kace ka fara ginawa sai na saye shi da sunan mama ta fito wancan gidan ta dawo nan
gaba daya ta zauna.

Wanan wacan kuma din sai mu barwa Saare da anty baraka da Salima a matsayin nasu rabon da suka
samu ka tayani addua habu in sauke wanan nauyin dake kaina ba tare da an samu matsala ba .

In sha Allahu habu ya fada a sanyaye kafin shima yakai zaune cikin sanyin jiki yake fadin kayi hikima da
dabara sosai J .

Could you believe not morethan one year saida kawu yayi min zancen kudin mu dake hanku inda na
nuna mashi banda matsala da hakan ai.

Yace ni yarone ya kamata yanzu nima na fara tawa plan din don haka zaiyi magana da mama a raba
kudin nan abawa kowa nasa ya rike.

Kawu kawu na dade a raina ina zargin mutumin nan ba tsakani da Allah yake muna wasu abubuwan ba
dama ?

Habu yace nina dade da fahintar hakan tun rasuwan baba ai na fahinci waye kawu don ba karamin abu
yayi a lokacin ba da sunan karfin mu bai kawo ba.

Quet sure yayi wanan maganan iyace nasan ta taushesu da zancen amma ina da tabbacin ya zauna da
mama akan hakan lokacin.
Ohh my god meyasa mutane suke kasancewa hakane a yanzu habu duk wanda ka yarda dashi sai ya
ha,ince ka ni kawu zai zarga akan na taushe kudin magada a karkashina.

Bayan yafi kowa sanin cewa ban wasa da wanan abin koshi wani lokaci daya bukaci da in bashi aron
wasu abu daga ciki na fada mai cewa koni ban taba taba kwandala da dukiyan nan ba Habu.

Nawa business dina na gashin kaina nakeyi habu shine kuma na dora ka kaima akai ka samu rabonka
ban amfani da wa yan kudin don in kara kaina Habu a harkan business na shigo da kayan masarufi din
dai na barsu a juya .

Sun dan jima suna magana kan kawu nasu kafin su bar gidan bayan sun leka ko ina na gidan habu sai
yaba kyawon gidan yakeyi yana ajiyan zuciya.

Suka dauki hanya zuwa babban gidan nasu a can ma basu samu shiga maza ba don rikicin da suka samu
anayi tsakanin dan umma da dan wanjen gwaggo kan gina sock away na masai daya dan shiga gefen
umma din.

Ita da diyanta suke fadin basu yarda ba tunda gidan dama rababene ai don me zasu shiga wajensu suyi
gina.

35 / 101