Chapter 52 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   52 / 101

153K to 156K   out of 302.2K words

ko bari na hada ruwan wankan kadin ka
dawo don nasan fita zakuyi kila ?

Na fada ina mikewa ya miko min hannu wai in dagashi dan murmushi nayi din nasan ina ni ina iya daga
mutum kamarsa amma banki ba na mika mashi hannun nawa ya jawoni da karfi na fada mashi a jiki ya
rungumeni.

Bai sakeni ba saida ya dan jahagulani ta hanyar kiss na samu dai ya sakeni yana fadin barin je naganshi
tunda korata akayi jiya aka nuna min ba a maraba dani nan .
Na samu na mike tsaye ina fadin ba hakana bane yaya tsoron shiga hakkin da ba nawa ba nakeyi ga
hakan baidai yi magana ba ya mike shima.

Nakai kofan bayin naji yace nasan abinda nakeyi sarai Rahama duk abinda kikaga nayi ina da dalilin yin
hakan so ki barni kawai na fiki tsoron hakan a zuciyana.

Ni dai banyi maganan ba na shige bayin na fara gyarawa don amfanin da mukayi dashi da safe na
wanko na fesa kamshi na hada mashi ruwan dumi na fice zuwa dakin shima na gyara shi fes kafin na fito
daga dakin.

Tsabta da yake so a zuciyarsa yakai karshe don haka nima nake ban son kazanta ko kadan abu kadan na
kazanta yanzune zai tayar min da hankali har tsikan jikina sai ya dinga tashi kan hakan.

Tare na samesu suna karyawa dasu don harda Nura ya shigo ashe nasan Nuran tun ban auresa ba don
yana da wuya idan yana gari bai tare da Nuran abokinsane sosai shakikinsa.

Hakan yasa na tsaya gaida Nura zan shige naji yaya din ba fadin Rahama karfe nawa zaki shiga school
ne ina son yin amfani da motarki idan ibrahim ya saukeki ya dawo zan fita da ita don nawa ba zasu shiga
ba yanzu sai an wanke min su.

Yanzun nan zan shirya in tafi don test zamu rubuta yau Ok ya fada idan ya saukeki sai ya dawo ya
daukeni ni dai na shige daki abina.

Na karasa shiri daidai yaya Ibrahim yazo don bai saba time gaskiya inba lokacin da yakai mama kaduna
dauko Saiba ba shine na biyo motan su Nuratu na dawo gida don basu dawo garin ba sai bayan isha,i a
ranan.

Nayi tuya na manta da albasa don da ta buga zata kaduna yaya Habu yace yayi tafiya shine mama tace
zatabi motar haya yaya habu din yace ta kira ibrahim yazo ya kaita.

A hanyarsu ta dawowane mamake tambaya dama makulin motar tana hannun ka ke nan ibrahim yace
ehh mama kinsan Amaryan yaya ke amfani dashi ita ake kawai school da motan .

Nan saiba taji wani sabon malolo ya tokareta a makoshi har suka kawo zaria bata kara magana ba sai
ajiyan zuciya da take saukewa lokacin.

Haka shima yaya daya shiga motar ya tayar yake tambayab ibrahim din da zai sauke ya akayi yaji
motar a haka don indai iyaka school da yake kaini ai baci ace tana wanan karan ba ?

Ya ibrahim din yace ranan da nakai mama kaduna da zata dawo da Saiba shine naji tana wanan kara na
so nakaita wajen gyara naji kuma tabar kara yasa ban kai ba gashi kuma yau tanayi again.

Da wanan motar kaisu kaduna ina motar dana aje donsu a can yace to ban sani ba nidai mama dince
ta kirani inzo da mota in kaisu kaduna ita da saratu shine na dauki wanan na kaisu.

Baiyi magana ba ya saukeshi shida Nafisa ya wuce da salima gida sai ganinsa sukayi kwatsam don ba
wanda yasan da dawowan shi a gidan.
Part din iya ya nufa tana zaune ta gashi tare da salima hannu ta fara tafawa tana fadin lale lale da
Jafaru yaushe garin inji maki bako saukan yaushe jafaru da safen nan haka ?

Iya jiya na dawo ta amsa da to sannu da zuwa yaya can ta dai shiga tambayansa irin na al,ada yana
amsawa da alhamdullahi.

Ga uwar taku ko yau zasu dawo sun tafi sokoto duba yar nan da take aure can tun shekaran jiya ko yau
zasu dawone oho ?

To sun tafi duba hauwa ke nan don yar wajen mamace ke aure a sokoto din akaiwa aiki wajen haihuwa
shine suka tafi dubanta sai suka samu tana jin jiki suka kara kwana.

Nan dai iyan tayi mai bayani ya mike yana fadin barin leka wa yancan ingansu ai ba gidan nan ka
kwana ke nan ba ?

Yace a,a iya wancan gidan na sauka yanzu shigowata kenan nan din a daidai lokacin Saratu ta fito daga
daki tana fadin sannu da dawowa yaya.

Au ke kina ciki ke nan jelar mama aina dauka tare kuka tafi dasu mama din ta amsa da ehh na dan
kwantane naji muryan ka nafito.

Kaji makira tana daki tun safe bata lekoni ba da badon yar nan matar habu ba wana shashashan data
kasheni da yunwa a gidan nan tunda ba iya girkawa zanyi ba ba kafa kasani ta fada tana nuna mashi
kafan nata.

Saratu din ya kalla yana fadin saratu why zaki barta da yunwa don Allah meyasa kike hakane saboda
Allah ?

Idan wa yancan basu da hankali ko basu san zafin iya ba saratu ke baki sani bane ashe da gaskiya da
ake fadin halaiyarsu kike amfani dashi ?.

Yaya kafa san hali iya da surfa komai akai mata ba ai mata daidai ba ni shiyasa na kyaleta baki kyauta
ba wallahi ya fada cikin daure fuska ya juya yana tsuki ya fita.

Part dinsa ya nufa suna falo dukkan su a lokacin falon dai kamar kullum kaca kaca dashi Asmau ta amsa
mashi sallama tana mashi sannu da zuwa.

Ya amsa yana tambayanta ya suke da yaran ya dan raba ido ko zaiga yaran bai gansu ba yake tambaya
yaran fa tace suna part din habu ina ji.

Ok bakima tabbatar dako suna can ba ke nan ina zasu yaya banda can tunda get a rufe yake yaja tsuki
ya nufi hanyar dakinshi kai tsaye.

Saiban taja tsuki tana magana kasa kasa har yasa key ya bude dakin ya dawo baya yana fadin me kike
nema a gidan nan ?
Ki koma inda kika fito kinji na fada maki in a serious voice yake magana don bai nuna wasa ko sanya ba
akanta fuskansa a daure.

Ai saika bari mama ta dawo kaji abinda nakeyi don ita taje ta daukoni har gidan mu Ok zaman mama
kikeyi ke nan to ki zauna zamanta din idan hakan yayi maki ya juya ya shige.

Asmau ta kalleta tace kema da son rigima kike wallahi Saiba meya kaiki yi mashi tsuki don Allah ta juyo
a hasale bayan ta mike tana fadin .

Wa,azi zaki min kome ina ruwanki da zancen mu banda munafunci sai Asmaun tace a,a meko ruwana
a ciki Saiba ni gaskiya na fada maki kibi abin nan a sannu fadan da yafi karfin ka sai ido ?

ZAMFARA

Tunda komai ya fito fili yanzu ba zancen boyo a wajen mijin anty baraka kuma ya fito fili yana soyewa da
bazawaranshi da ake shirin daura masu aure.

Ranan yarta tazo ta fada mata wallahi ga baba can na gani tsaye da Safiya kofan gidansu da leda suna
hira duk da hararan da yaiwa yar saida ta fada data shigo gidan.

Zuciya ya dibi barakan ta mike ta yafa hijab ta samesu a kofan gidan tundaga nisa ta hangoshi ya turo
hula gaban goshi kafanshi daya yana ta cikin zauren gidan daya kuma yana ta waje ya dafa bangon
kyauren na gidan.

Yayinda bazawaran nasa ke tsaye daga ciki kadan amma ana hangenta waje ta karaso tana huci sai jin
muryanta sukayi tana fadin.

Macuci azzalumi Allah ya tona maku asiri kaida yar iskan taka yau ya juyo yana fadin baraka hauka
kikayi ko me da zaki biyoni nan da rana tsaka haka ?

Ba hauka nayi ba daga turu na fito ke kuma macuciya mai laluben ramin labewa ahir dinki da mijina
wallahi don ba wajenki a gidan mu.

Dakata baraka ki gyara zancen ki kice mijin mu don ya biya sadakina tuntuni in baki sani ba ki sani
bakinki ya saba da fasin mijin mu a yanzu.

Sadaki ko yaudara kudi garesa balle ya biya sadakinki dashi kudin nawa daya yaudareni yayi min dadin
baki ya kawo maki wai sadaki ?

Masha Allahu in hakane kema kin samu lada ashe tunda kin taimaka za a raya sunnan ma,akin Allah da
kudin ki kai nayi maki murna gaskiya.

Ke sakarai wa zakiwa dadin baki a baya badon baida kudin kika kisa ba sai yanzu an samu kudin banza
za a dauko min wahala.

Ke baraka ki koma gida tun kan ranki ya baci dani wajen nan don zanci maki mutunci fiye da tsamanin
ki wallahi mijin nata ke fadan hakan cikin karfin hali ganin jama,a sun fara taruwa masu.
Nan dai aka taru aka fara bata hakkuri da ban baki data koma gida tayi hakkuri har ya dawo gida hakan
ba mutuncinta bane gaskiya.

Dole dai ta hakkura ta koma gida din cikin hasala da mijin da bazawaran tashi tana zage zage kamar
mahaukaciya da yawa sun san wanan aure za a daiyi ne amma safiyama bata da halin kwarai.

Zata dai bata masu zamane kawai shida matarsa da suke zaman rufin asiri a tsakaninsu shekara da
shekaru ba a jinsu ansan itace yan uwanta ke taimakonta take rike da gidan tunda shi ankoresa aiki
tunda yayi siyansa dake kalubalanta ta gwaunati aka sallameshi aikinsa yake zaune gida.

Yayinda wasu kuma suke jin haushin abinda safiya din tayi don me zata biyoshi har waje tana mashi
tonon asiri haka a gaban jama,a ?



ZARIA



Tunda ya shiga dakin yake bin ko ina da kallo saboda kuran da dakin yayi duk da a rufe dakin yake yabar
key din a gidana saida zai fitone ya dauko don idan ya barshi bude har yara suke bari suna shiga mashi
suyi mashi barna shine ya soma rufewa ya wuce da key dinshi.

Shi ta ina zai iya kwana daki haka kaca kaca donshine yasawa Asmau kira da tazo tana tsaye bayan ta
shigo yace ki duba saboda Allah dakin nan yadda ya koma Asmau saboda kazantar ku ?

Ki duba don Allah Asmau wanan wani irin rayuwane wai kika zabarwa rayuwanki Asmau ?

To yaya ai dakin a rufe yake balle a gyarama yaja tsuki yace kona barshi a bude aiba gyarab zakuyi min
ba ?

Wanda bai iya gyaran jikinsa bane zai gyarawa wani muhalinsa ki duba yadda kuka mayar da falon
gidan nan don Allah ku bakujin kunya azo a samu gida haka don Allah ?

Ni idan na saba wanda suke shigowa sun saba da hakanne don Allah baku jin kunya a rayuwan ku ku ki
duba jikinki Asmau son Allah ki dubi kanki ki gani don Allah ?

Yaya ni yanzu bata gyara nakeyi ba nima tawa ta isheni don Allah falo kuma ko an gyara a bata donshi
nima na bari kowa ya zauna hakana in gaskiyane.

Bayan haka meye dalililnku na rashin sawa iya abinci da bakuyi har yanzu ya kafeta da ido yana
kallonta don son jin amsan da zata bashi.

Tayi shiru ya dago yace badake nake bane idan ita Nusaiba bata san darajan iya ba ke Asmau nace baki
sani bane kome ?
Kinsan fa mama bata nan yarinyar nan Asmau kuma yaushe zata iya girka mata abinda take so wai
amma sai lokacin da matar habu tagama girki ta kawo mata zataci ?

Ke yanzu bakiji kunyar hakan ba Asmau duk wanda yazo gidan nan a yanzu keya sama amma baki iya
tunawa da hakan sai kanwar bayan ku ta tuna tayi hakan ?

Yaya kafa san halin iya da surfa in an dafa abinci tace bai mata ba kuma ai ita tace a bar saka mata kada
ya zama barna bata iyaci.

Shout Up my friend don tace hakan ke baki san tsufa bane ko baki san yakamata bane ?

Amma jeki ba matsala wallahi kowan ku will regret it don nasan abinyi a yanzu bai yuyuwa ina kawo
komai a gidan nan amma ace ba za a iya girkawa aba kakata for what reason za zaman kashe jikina a
banza.

Kayi hakkuri yaya za a dinga saka mata idan an girka ko bataci din kayi hakkuri yaja tsuki ya dan kalleta
ya juya yana daga filon saman gadon zai kakabd da sauri tana jan kafan don nautin da cikin yai mata ta
karba ya fito daga dakin gidan ya fice ga baki daya cikin takaicinsu a zuciyarshi.

A ranan mama ta dawo Zarian ita da abokan tafiyanta can family house dinsu suka sauka ganin Nafisa a
gida take tambaya take fada mata ai yaya ya dawo jiya shiyasa ta dawo gida.

Ko ya dawo aiba gidan zai sauka ba don me kuka dawo yau tayi shiru bata bata amsa ba don tasan halin
mama din haka kuma tana gudun hadin hasumi.

Saiga Nusaiba ta kirata tana kuka tana fada mata abinda yace ta bata hakkuri tace kar taje ko ina gata
nan zuwa gidan ai.

Haka yasa ta kwasa zuwa gidan don ta rutsa shi don saiba bata san fitanshi ba tace mata yana nan gida
lokacin




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/27, 10:29 PM] Zainab Idris Makawa Writer: {2\25\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa

MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,



5️⃣4️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Shiya daukoni daga school ranan muna hanyane aka kirashi a waya wai mama tana nemanshi saratu ce
ta bugo wayan lokacin ya amsa da Ok ta dawo ke nan ?

Tace ehh sai naji yace da ita gani nan zuwa zan sauke Rahama injuyo sai banji dadin hakan daya fada
ba a lokacin saboda nasan halinta yanzune zata iya juya zancen ya zama babba.

A samu na yamadidi dani a gari ana fadin magana ba dadi a kaina wanda bai dace kamar yadda akewa
mutum fatan sheri a yanzu don har jira mutane suke wani sheri ya sameka a fara yawo da sunan ka har
garin ku.

Muko fulani kowa yasan mu kunya garemu badai tsoro ba dan bamu jin nauyi ko girman abu idan mun
tashi yinsa kai Aaye muke abin mu ba boyo .

Saida ya kaini din ya sauke ya shiga yaci abinci sanan ya tafi kiran da mama din ke mashi inda ya samu
mama ta hau akansa don abinda saratu ta fadi har yaso zama fada a tsakaninsu da salima a lokacin.

Saboda lokacin da yace gashi hanya ya daukoni zai kaini gida bayan ta kashe wayan tace ke mama kinji.

Wai matarsa ya dauko sai ya kaita gida tukun zai zo wai Rahamace yaya yake kira da matarsa Rahama
dai Rahama dai wanan ai abu a fili yake kowa yasan hakan aikin asirine gaskiya.
Inba asiri ba me yaya zaiyi da Rahama don Allah wanan bagidajiyar yar kauyen yana da mata kamar
Saiba.

Aikin banza aiba wayewa akajawa ba hali na gari jarin mutum a hakan yar kauyen yake son abinsa don
tafi bashi kwanciyar hankali.

Balle ko makiyin Allah a yanzu baicewa Rahama yar kauye don koke tafiki wayewa sanin da dai kikai
mamata yasa kika kirata da yar kauye.

Tafini fa kikace Salima tace kwarai kuwa abu a zahiri ko kina gardaman hakanne koda yake ba mamaki
don kin dade baki ganta bane yasa kike fadan hakan akanta.

Ta dai fiki ko keda kika mayar da kanki banza wajenta saratun ta fada sai salima tace kona mayar da
kaina banza ba kaina bane farau ai don kafin nayi da Rahama wasu sunyi da Saiba ai duk ko da cin
mutuncinta da komai haka naga ana binta sau da kafa gidan nan.

Balle Rahama dake ban girmana da mutuntani tasan darajana dana dan uwana da kowa nawa kinga ko
kowa na son kyautatawa a rayuwa.

Kukan dabi,anku baida kyau wallahi ku zauna kuna cin junan ku kamar kishiyoyi kowa kamar yana jiran
dan uwansa ya fincika ?

Bama shiba dai su daiyi kokari su kama nasu dakin shi yafi garesu ba shiga tsakanin matan dan uwansu
suna saka ido ba iya ta fada.

Fada masu dai iya wanan abin takaicin dame yayi kama yara basu san ciwon kansu ba kullun jidali da
juna kamar kishiyoyi ?

Wanan yasa ran mama ya kara harzuka da zancen dan nata don koda yazo yana mata sannu da zuwa a
fusace ta amsa mashi zaice a yanzu hakane tsakaninsu da ita.

Mama ance kina nemana ya fada cikin maida hankalinsa a kanta tare da natsuwa yana saurarenta cikin
ladabi.

A,a ka bari idan ka gama abinda ke gaban ka jafar sai kazo kaji me nake nemanka dashi yanzu ai kana
uzuri tunda hankalin ka yana wajen yarinyar nan ayanzu.

Kallon bangane ba yaiwa uwar tace ehh ance kace saika sauke Rahama zaka zo kiran da nake magaka
shine nace kaje idan baka gama uzurinta ba kagama ka dawo.

Mama da Rahama zanzo gidan nan koda aka kirani na daukota daga school zan kaita gidane don da
motanta nayi amfani yau na bayar da datawa a wanke min.

Allah sarki ita Rahama ashe harda mota ka saya mata su sauran ina tasu take take ?

Baga mota a gidan nan na ajiye ba mama haka itama na aje mota ibrahim yana kaita makaranta dashi
da sauran laluran gidan.
Kadaiji tsoron Allah jafaru kasani dukkansu amana suke agareka baka nuna kana banbanci a tsakaninsu
ba haka a fili.

Kayi tafiya daga gidanta ka dawo ka kuma sauka gidan ta kayi adalci ke nan jafaru kana son kona
kankane da hakan Jafar ?

Mama kodana sauka gidanta jiya ai da hujjana na sauka a wajenta don kodana tafi kwanakinta bakwai
da Allah yace ayiwa budurwa bai kare ba na tafi wanan yasa na sauka na karasa mata kwana dayan daya
rage a can din.

Kadai ka sani tunda abin ya zamo bin bashi har kana rankon kwana a tsakaninsu dolene akace kayi
mata kwana bakwai dinta tunda uzuri ya kamaka na tafiya ?

Wanan shine adalcin

52 / 101