Chapter 27 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   27 / 101

78K to 81K   out of 302.2K words

nan keyi min ko biyansu nakeyi zan iya
basu hakkinsune jinya wasane halan ?

Kedai baki san harara ba wallahi ashe kema kyamar dan uwan naki kikeyi yasa kina cikin garin nan
kikaki lekowa ki gaidashi ?

Haba mama kyamarshi kuma to na sani tunda zancen ku daya dasu baki wanka ki bushe kina wajensu
kina koyon iya shege don bandashi banga abinda suka karaki dashi ba.

Ke Rahama yayanku Habu ya baki maganin da za a dinga bashi din ?

Jin ta ambaci sunana yasa na dago ina fadin a,a mama bai bani ba bari dai in koma in karbo mashi na
sakai na fita na barsu zaune.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/1, 4:58 PM] Mmn Bibo: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
2️2️⃣
2️⃣
8️⃣8️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Daga kwancen da yake yake tunanen halin rayuwa yau shine a haka ake fama dashi mutumin da baisan
dadin zama a waje daya ba ko yace yasan dadin hutu shiko a yaushe cikin ujula yake haka ya taso ya
kuma saba da wanan rayuwa hakan yabi jikinshi sosai kuma don bai iya zama ba tare da yana wani abin
da zai taimakawa rayuwansu ba a gidan.

Yau sai gashi ubangiji yana ikonsa a kansa hutun dole na wahala ya sameshi irin hutun da bawa bai
kauna a rayuwanshi sai in dole ya kama irin haka din.

Yaushine matanshi suka hada mashi kai suke nuna mashi kyama da yake gani a idanuwansu karara tun
suna boyewa har ya fahinci hakan da gaske.

Gashi har Asmau don wauta irin nata har yarshi ta cikinshi take hana zuwa gareshi don kada cutan
jikinshi ya shafesu tunda ance dasu ana kamuwa da wanan cutan .

Don haka su kiyayeshi kada su kama dashi suma bai taba zato ko tsamanin ko kowa ya gajushi a duniya
su zasu iya gudun shi ba haka yadda sukeyi.

Hawaye masu zafine suka zubo a idanuwanshi duk yadda ake kai zuciya nesa yana kai akan matan nasa
da ba haka yaso dasu ba sai gashi shi bai watsa masu kasa a ido ba sune zasu watsa mai akan cutan da
Allah ya dora mai na jerabawa imani.

Ajiyan zuciya ya sauke yana kara kallon part din nasa da yai shiru alaman ba kowa a lokacin tare dashi
mamace da a zaune wajen ita kuma ta fita zuwa wajen iya.
Su kuma yaran nan tun safe baiga gilmawan su ba dama sukanyi hakan suje su dan huta mama ko kawu
su zauna dashi din tashi yake son yi ya gaza tun dazun so yayi ya dan mike ya kewaya bandaki amma
babu kowa a dakin wanda zai taimaka mashi ya tashi daga inda yake kwancen.

Fitowana daga part din iya naji gara naje can din in dubashi don yaya Habu nagida kada in takura masu
wanan yasa na zabi hakan na nufi can da yaro a hannuna.

Falon babu kowa banda niyar shiga dakin amma naga na dan lekashi ko idonsa biyu in gadashi lokacin
hakan yasa na yunkura saiga Saare a bayana batayi min magana ba nima banyi ba .

Na leka nishinshi naji yana yunkurin tashi zaune itama ta fado dakin da nata sallaman tana mashi
sannu taimaka min in tashi ya fada a cikin yar murya.

Ba tare daya amsa gaisuwan da take mashi ba sai naga ta dubi inda nake tana fadin meyake fadane
banji shi ba nace yace ki taimaka mashi ya tashi.

Bari dai in kira mama ta fada tana juyawa da sauri har tana bangazana a lokacin yaron na aje a gefe na
karasa na kama hannunsa da sai ranan na taba kamashi irin haka.

Ina mashi sannu ya mike zaune yana nishi Allahu akbar wai yaya J ne Allah ya mayar haka cikin dan
lokaci fitsari nake son zuwa don Allah ya kara fada.

Zaka tashine na fada a rude ya kada min kanshi dake duke yana maida numfashi hakan yasa na kokarta
na tayar dashi tsaye na kamashi zuwa bandaki yana kokarin zama a toilet na fito daga dakin saiga mama
ta shigo da saurinta tana fada.

Yaya zaice ki kamashi kice baki iyawa inba shashanci ba mutum kamar jafar yana da lafiya zai tsaya sai
an kamashine ?

To kedai kina kusa ashe ya samu ya mike ko nace ehh mama na kaishi bandakin kingani ba shiyasa
banson mu barshi shi kadai wallahi.

Ta karasa kofan tana kiran sunanshi ya amsa daga ciki banji meyace da ita ba dai a lokacin na dauko
yaron na fito falo tana zaune tana waya nayi niyar zama a lokacin amma sai na canza shawara zan fita.

Ke wallahi ni tsoro naji ina zan iya zanga kamar zai sai gani tayi shiru tana watso min harara a fakaice
fita nayi daga falon gaba daya.

Don yanzu ban kaunar wani abinda zai hadamu kuma da ita kowa ya tsaya matsayinshi a gidan shiyafi
sauki baya da gaisuwa ba abinda ke hadani da ita kuma.

Na fita muka hade kuma da abokanshi da suka zo dubanshi mun gaisa zan tafi suke fadin don Allah yi
muna sallama munzo duba J ne magaishe shi kice su umar ne da musa .

Na juya ina fadin ya kewaya amma bari in fadawa mama idan ya fito na shiga na samu mama a falo
take fadin ashe kin fitane Habu ya bada maganin ?
Ban shiga wajensu ba mama yanzu can na nufa dai akwai wasu a waje sunzo gaida yaya umar da musa
gashi ko ya kewaya nace na fada masu ai yana bandaki.

Bari mugani idan ya fito kice ya shigo ta shiga kuma naji tana kwala kiran sunana hakan yasa nabi
bayanta ina amsawa.

Kinga kayan nan nake son akwashe na manta dazun in shiga dasu ciki nace barin kwashe mama na
gyara gadon kafin naji fitowansu tana mashi sannu take fadin ya taka a hankali dai.

Magana yakeyi banji ba naga tayi dariya tana fadin yace ki fesa mashi kamshi a dakin kinsanshi sarkin
son kamshine.

Na dauko kamshin na fesa har zuwa bandakin sai kuma na shiga nayi flushing na wanke wajen
nagama na fito yana zaune bakin gado yake gaidani da kai na kawar da kaina gefe ba tare dana amsa ba.

Ni har ga Allah bala,in tausayin bawan Allah nake ji mutum mai kawaici da mutunci irinshi shine a haka
yau lalai bawa ba a bakin komai yake ba a wajen Allah.

Muryan mama ya katseni da take fadin kicewasu umar din su shigo na amsa da to na koma daukan
Abbati in fita dashi saidai hannusa yana cikin nasa hakan yasa na isa nayi masu iso suka shigo.

Ina gaba suna biye zuwa dakin hakan yasa naji jan tsukin da Saare keyi bandai kulata ba na dauko
yaron na fito suna gaisawa don da shiga umar din ya soma fadin ikon Allah Alhamdullahi J kaine a zaune
yau ?

Masha Allah gaskiya jiki ya soma kyau Allah yasa hakan kaffarane a gareka mamace ta amsa da amin
gaskiya mama naji dadin ganinshi a yau din nan ikon Allah mama ta karbe da ikon gaskiya.

Na samu ya habu a falo yana cin abinci na sake gaidashi zan shige yake ambatan sunana hakan yasa na
juyo gareshi alaman akwai maganan da zaimun ke nan na karasa gabab shi na tsaya.

Ki zauna yace dani hakan yasa na samu waje na zauna dan nisa dashi kadan ya dan dauki lokaci kafin ya
ture plate din yana aje cokalin ya kalloni yana daukan abin goge baki yace.

Rahama tambaya nake son maki kuma banson ki musa ki fada min gaskiya iya abinda kika sani zanj
dadin hakan idan baki toge ba.

Gabanane ya fadi yace wani magani kike ba J a ina kika samoshi kuma waya baki ki bashi shi ya jero
min tambayan a lokaci daya ?

Magani ?

Na fada a sanyayye ya amsa da eh magani wanda kike bashi nake son jin karin bayani daga bakin ki ?

Ke Rahama kece keba yaya J magani as how hakan ya faru Ramaah waya baki magani ki bashi Ramash
innalillahi wa inna alaihim rajiun kin kasheni Ramaah ?
Kaina dago na dan kalleta da mamaki a daidai lokacin ya habu ke fadin haba mana maria ki bari mu
saurareta.

Dole tana da dalilin yin hakan wa zai turota wajen mu balle kiyi tunanen zatai poisoning din shi kawai
ina son ji daga bakintane kawai yayi maganan a cikin hikima.

Jin abinda ya fada yasa hankalina ya dan kwanta ina fadin ni ba kissa zanyi ba taimakonshi nayi don
ganin irin wahalan da yakeyi.

Ki taimakeshi Ramaah ina kika san wani magani da zaki iya taimakawa dashi Ramaah ?

An fada maki haka ake shan magani ba tare da kasan aikinshi ba haba anty maria nifa Dage ya ban
makaru lokacin da muka je ruggan mu shine nake bashi yana amfani dashi yadda yace ayi.

Ina fadin Dage ne ya ban naga takai zaune rugwaf saman kujera tana dafe kirjinta da hannunta biyu ta
kara maimaita sunan da fadin Dage Ramaah ?

Baki na turo ina fadin to meye a dakin baffa fa ya debo maganin tunda yasan duk aikin da sukeyi ninace
ya debo min shi kuma ya debo.

Ramaah baki tsoron baffa ya sani koya sani tsakaninshi da dagene nidai na karba kuma na bashi
kudinshi.

Kasa magana tayi sai bina da kallo da takeyi baki sake ga kuma alaman tsoro a fuskanta saida mijin
nata yai magana ta juyo da kallonta gareshi.

Koma dai meye maganin yayi don haka shi za,acigaba da mashi har muga aikin maganin don tun ranan
data fara mai amfani dashi ya soma samun sauki a jikinshi.

Ban son wanan zancen ya fita ku kama bakinku kawai ku dai san halin gidan nan yanzu dai zaki dauko
min maganin in kaiwa mama da sunan nina karbo mashi a daina bashi a boyen da akeyi.

Jeki dauko maganin mu gani haka na juya jiki ba kwari zuwa cikin dakina na dauko maganin can kasan
jakata inda na boye mai yawan saidana rage na fito da sauran na kawo mashi.

Shane da kunu ko da madara ko wani abu dai hakka mai dan ruwa saidai idan ana amfani dashi mutum
zai kiyayyi duk wani abu mai yauki kada ya cishi.

Na bashi na magarya da dutsen tama da za a nemo ya amsa yana mamaki ya fice daga part din sai
lokacin ta samu daman magana.

Fada sosai tayi min tare da min kashedin irin wanan babban kuskuren dana tafka din da kada in kara
irin wanan wautan idan wani abu ya sameshi fa ta sanadiyana ?

Ni dai kasa magana nayi don sai a lokacin tsoro ya kamani don sam tunanen hakan baizo min ba da
farko sai yanzu din data fada.
Saare aka turo kirana nazo suna zaune har da kawu yaya Habu ke fadin ki duba wanab maganin da
kyau kece zaki dinga ba yaya J shi safiya da yamma don Allah a kula akwai wani na wanka da za a kawo
shima nayiwa mama bayanin komai.

Na amsa da to ina karban maganin da yafito a wajena gashi kuma a yanzu ya sake dawo min mikewa
nayi jiki na rawa sai lokacin naji yaya habu na fadin ita Nafisa don dan magana ya hadata da Saratu shine
zatayi fushin zuciya tace gida zata tafi ?

Ke Rahama kira min Nafisa na amsa da to na fita da sauri don a tsarge nake dama a falon ganin daga
kawu har ita mama basuyi magana akan maganin da yaya din ya miko min ba.

A zaune na samesu dasu iya ga jakkar kayanta a gefe daya tana duban wayanta nake fada mata sakon
yaya din.

Na fita don ban tsayawa saboda Saare dake falon kwance da waya a hannunta tana charting part din
mu nakoma yayata tana zaune tayi tagumi cikin damuwa.

Yaya kukayi dasu take tambayana maganin na fara nuna mata kafin na zauna ina fadin Allah ni da zuci
daya na bashi wanan maganin kuma Nafisa tana wajen itama.

In Nafisa na wajen fa Ramaah kiyi tunanen Nafisa aiba uwarsu daya ba dasu baki gudun ace an hada
baki dake a cuta mashi.

Shiru nayi ina wiki wiki da idanu don sai yanzu nake hango zalla yarintar danayi na daukan wanan risk
din don ba karamin magana bane idan ya fita anji .

To ya zanyi aikon gama ya gama sai fatan Allah ya kiyayye yanzu kan don mai faruwa ya riga da ya faru
magani kusan sati daya ana sha yanzu meya rage kuma.

Da yamma saiga su yaya sun dawo da wanan abinda na fada na karya asiri ba a bata lokaci ba mama ta
dafa aka kai mashi ya diba yasha yayi wanka.

Yana fitowa ina tsaye na kada wanan maganin kamar yadda yay habu ya fadi dokansa ya amsa ya
shanye gaba daya ya miko min cup din tare da godiya.

Ya tambaya ko magariba yayi mama tace kamar da sauran lokaci nafisa dake shigowa tace an fara kiran
sallah a wasu wuraren ai.

Saida yayi sallah magariba kafin ya kwanta kamar karamin yaro ya dunkule a waje daya lamo kallo daya
zakiyi mai ya baki tausayi.

Ina ganin haka na nisa ina fadin Allah ya sauwaka na fita da kayan wajen zuwa kitchen dinsu da yanzu
yake samun gyara don anty Nafisa ko yaushe tana tsabraceshi.

Tunda na dawo nashige dakina ban fito ba sai washegari nayi shirin school na fita na biya part din na
gaidasu mama ke fadin jiya ina ta jira ki dawo baki dawo ba kodana aika akace barci ya daukeki.
Nace ko kema kin damu da zancen shashan nan Saratune ai ita tazo muka kwana tare tunda Asuba ta
gudu wajen iya wai batayi barci da dadi ba a nan.

Nayi murmushi ina fadin mama maganin fa ina son shiga school kada in makara to sai ki hada din ki
bashi tunda maganin yana da ka,idan sha ?

Nayi mamaki jin furucinta na ka,idan sha watau yaya habu shima ya nunke su mama a baibai ke nan
don kada su gano wani abu kome ya fada masu oho ?

Da sallama nashiga duk sa safiyane sosai amma na samu har yayi wankan maganinsa yana kwance yayi
rigingine jikinsa saye da farar jallabiya mai dogon hannu.

Gaidashi nayi da yaya jiki ya amsa da Alhamdullahi nagode na sada kai kasa ina fadin zan shiga school
ko za a hada maganin yanzu ?

Har na gama kadawa idonshi yana kaina har na gama na miko mashi ina fadin gashi yaya don yanzu ba
sai an rike cup din ba yana iya rikewa yasha da kanshi.

Ya dan dago daga kwancen ya karba yasha ya miko min cup din yana godiya ya koma ya kwanta a yadda
yake bankai ga fita ba naji yayi wani irin gyatsa yana hamdallah.

Kodana fito ban tsaya ba nayi masu saina dawo na samu Nafisa zaune da mama suna magana a lokacin
bandai san akan meye ba.

Daga kwancen da take daki lamo jin ba motsin kowane ta daga waya yana ringing sai can aka daga ta
wayan ke fadin ai wallahi Saare nayi fushi.

Ta amsa da fushin me tace wai ace tunda nazo kaduna baki kirani ba haba saaratu amana baice hakan
ba ai, na zata kece ta farko da zata nemeni sai naji shiru Allah nayi fushi sosai da hakan.

Haba dai tawa nifa sai jiya na samu ya kara dawowa sai kuma na samu wai baku nan dukkan ku iya ke
fada min shirme wai kuna kyaman yaya yasa mama tace kuje gida har ya samu lafiya.

Humm ni bansan me zance ba banda wanan sakariyar Asmau data fitar muna da zance a fili yar iska ko
an fada mata inma kanjamaune haka ake kamuwa dashi ?

Ba kanjamau bane wallahi don yanzu yaya yaji sauki sosai ba kamar yadda nazo a ranan na sameshi ba
yanzu har tafiya yakeyi da kansa.

Don Allah ki bari !

Tace wallahi ko saidai abinda banji dadinsa ba shine wai fa Nafisa da yarinyar nan Ramaah suke taya
mama jinyarsa.

Su kuma wallahi iam telling you don nayi maganan hakan baiyi ba shine munafuka Nafisa waina nuna
ba mama ta haifeta ba kar kiso kiga fadan da mamake min fada wallahi akanta.
Nafisa fa ita har ta samu wajen hadaki da mama ke nan bari yar iska kanta zamu koma ksi ba ita ba har
wanan mai ido kamar glove saita bar gidan nan shiri nakeyi sosai wallahi.

Mutumiyar kin min daidai wallahi ina son ki wajen aiki da zafinsa ai dama kin gansune yadda suke
rawan kafa su kakansu ta yanke saka yan iska don a yabeau wai ?

Tsiyar banza wa zai yabesu din sunyi a banza wallahi zan matsa naga na dawo ko wata yar iska saina
koya mata wayau a gidan nan.

Ina yinki nawa Saare din ta kara fada har da fadin Allah yasa kin hada da wanan yar iskan duk su tafi su
bamu gida wallahi ni gaba daya haushi suke bani Allah na tsani wanan maria din wallahi haushinta yasa
bani kaunar kanwarta din itama.

Sun dauki lokaci suna sherin su har mama ta shigo ta sameta duk da bataji sosai ba ta fahinci da Saiba
take wayan a lokacin.

Saida ta fitone tayi mata kaca kaca ta zageta tas tace kuma zata dauki mataki akanta tunda abinda ta
daukowa rayuwanta ke nan munafunci.

In ba rashin sanin ciwon kai ba dakece za a hada kai ana mugunawa dan uwanki saratu matan nan fa
cewa sukayi suna kyamar shi.

Watau ya dauko mugun ciwo kada ya saka masu shine nufinsu ko ?

Mama ai cewa ake wai wanan ciwon mai karya garkuwan jiki ya kwaso a can wajen kwatakwali
shine,,,,,,,,,

Mama dubu bata bari wanan matar takai karshe ba ta karbe da fadin Allah ya kare al,umman Annabi
baki daya.

Duk wanda yaiwa yaron nan wanan sheri yaga abinsa insha Allahu watau su gasu sakatkaru shine suka
yarda da hakan ko ?

To mama

27 / 101