Chapter 101 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   101 / 101

300K to 302.2K   out of 302.2K words

sayayya sosai yayi masu suka shigo yanawa musa sheri da ke ashe kanin
naki aure yayiwa gudu yazo nan saida yaga za ayi mashi auren dolene ya tuna damu.

Harshe na juya ina tambayanshi yake fada min yadda akayi raina ya baci sosai da kawu abinci na mike
na kawo masu sukaci suka dasa wani hiran dashi.

Dakunan daba kowa a ciki na boys quarters yasa Aminu ya bude ya saukesu a ciki da yake ba nan gidan
mu yake ba saida zai tafine yakecewa dani ina ganin fa nan za a kawo yaran nan idan uwarsu zata
saudiya.

Su basma yace eeh don ban yarda da cewa da tayi wai akaisu gidansu ba Allah ya kaimu nace ban
yarda na nuna komai ba ga hakan.

Amma nasan akwai ta don yadda yaran suke basu jin magana kuma ba a tsawata masu amma ba komai
zanyi iya kokarina dasu insha Allahu.

Aikuwa hakan ya tabbata don kuwa tun ana saura kwana ukku su bar kasan sai gashi da yaran yazo
min ban ko san da zuwansu ba ya kwasosu zuwa gidana ba yadda zanyi dole na rugumesu .
Irin wasan da sukeyi ya fara daga min hankali wasane na alaman ba kwabo din nan ga yaro nan muka
fara kwasa dasu nayi masu serious warning akan hakan.

Ban yarda na sake masu ba sam da safe kuma zan tayar dasu suyi sallah akan lokaci idan angama kuma
nasa suyi brush biba tayi masu wankan safe.

Gaida mutane akan Aminu na fara koya masu hakan ya shigo suka bishi da kallo na daka masu tsawa
su gaidashi daga zaune inda suke sukace ina kwana nace ba zaku tashi ku gaidashi ba bakuga yadda biba
ta gaisheshi bane hakan yasa suka mike daya bayan daya suna gaida shi.

Nace duk wanda yazo baku tashi kun duka kun gaidashi ba saina tsunkewa mutum kunnensa da yuka .

Haka sunso su dinga irin barnan nan da sukeyi su halaka abu ana kallonsu ba kwabo su barnatashi ana
kallo haka zasu barna abu.

Shima cikin nasiha da fada na hana wanan da mamansu tazo gidana muyi ban kwana wai daga gidansu
take shi yaya ya kawota yadda suka gaida ita ya bata mamaki.

Har take fadin wai basmace nan kuwa a,a yan matan anty kece nan harda su makeup a fuska koba
kwali kika shafa a indonki ba.

Ina jin mijin tace mata waye anty ita ba zasu iya kiranta da mummy ba ko mama karna kara jin wani
anty can daga yau nace dashi ai haka suke kirana tunda sunji biba na fadan hakan.

Tana dan murmushin yake a fuskanta yace ki duba don Allah dan kwana biyun da yaran nan sukayi a
nan yadda suka koma keda suka gaidake da zuwa bakiji dadin hakan ba yanzu ?

Toni yaya me zance kai kome nayi ai banyi daidai bane a wajen ka kasan halinsu baji sukeyi ba nan ma
dai don suna shakatane ai to kada ki koya masu din ni ai nasan matakin da zan dauka don ba zan yarda
ba gaskiya.

Basu jima ba yace su tashi suje nasan don ganin da yayi yaran sun narke a jikintane saida ya mike yake
cewa dani ki shiryasu idan na dawo zamuje can gida ku sallami su mama.

Hakan ya faru don kafin ya dawo munyi wanka mun shirya tsaba duk da kayan yaran ga kaya na kwarai
sabbi amma duk sun nakashe daga wanda ya yage a tsakiya sai wanda zip dinsa ya lalace hakana dai
muka samu aka saka aka fita ina yaba sakaci irin na wanan matar a raina wai kuma harta iya hado wanan
kayan haka azo dashi.

Munje gidan ba laifi don mama har daukan Amir tayi tanawa mashi wasa da wakan yabo na mai
sunan, baban nasu yana murmushi ta dubi yaran tace indai ba idona ke gizau ba sai ince yaran nan sun
sauya a dan kwana biyun nan da sukayi.

Tunba Siyama ba ni dai har kiba naga tayi ai dole yanzu ta rage wanan alaulayin nata Saratu dake
neman shiri da dan uwan nata ke fadin hakan .
Yawan cuwon nan da kwanciya naga duk ta dainashi yanzu uban ya fada mama tace dashi aiko yunwa
ya isheta yaushe suke tsayawa su kula yara?

Jiyama nake ji ance anga uwar wai a nan garin na dauka ai duban tar tazo ko tazo ina zata ganta nayiwa
maigadi kashedi idan ya bari tazo min gida bakin aikinshi ranan.

Ni dai banyi magana ba ina zaune ina jinsu aka gama yace mu tashi muje da zan fito na mikawa mama
dubu biyar iyama dubu biyar muka fito.

Naso na rakasu har kaduna amma yaya Auwal yace kowa ya zauna gida sun gode sai mazan su suka
rakasu zuwa kaduna a ranan kuma akace sun tashi da dare don saida suka daga suka dawo gida.

Gaskiya munji kewa sosai gidansu mama Saratu aka bari da matar Yazid duk ita da ita da babu dukka
dayane tunda bata fitowa kullum suna ciki rufe.

Sai su Aminune isah yaya yace zasu dinga kwana gidanshi shi kuma musa a gidan su mama haka ya
rabasu ni dai najawa yaran kunne sosai a lokacin.

Nayi ta jira inji wani korafi daga mama game da yan uwana din sai baniji ba yasa na saki zancen a raina
suma basu da rugima sai hakan yayi min dadi.

Sana,anmu da Nafisa a yanzu ya bunkasa sosai don ba zannuwan gado kawai muke daukowa ba har da
kayan kitchen masu kyau sabbin yayi muke daukowa hakan yasa muka fara shawaran bude shago a
asirce ba tare da kowa yasani ba.

Ni da wata kawata da muke unguwa daya zata bude shagon kayan mata ni kuma nace na kayan kitchen
din da sauran abubuwan mata.

Na nemi shawaran yaya na fada mai ya yarda da yace zaiyi magana abokinsa ya nema muna shago a
bakin tiri inda za afi samun kasuwa.

Ni dai nasan baiyi niyar zuwa saudiya ba sai gashi kwatsam yazo min da zancen zaibi jirgin yawo ya cin
masu don hankalinshi bai kwanta ba tunda suka tafi.

Duka duka cikin kwana ukku ya daga yabi bayansu duk wanda aka fadawa ya tafi makka sai yayi namaki
tunda yace sai wani shekara zai tafi.

Ashe gara da Allah ya kaishi don kuwa mama tun zuwansu ta fadi ciwo yau ciwo gobe lafiya har suka
bar madina zuwa makka ana fama da ita hankalinsu yaya duk ya tashi sai ganinsa sukayi kwatsam yace
hankalinshine bai kwanta ba.

Zuwan shi ne dan dama dama don dole aka samu keke yana garata ta samu tayi aiki a lokacin ganin ta
dan samu sauki ya koma da ita madina sukai ziyara ya rigasu dawowa Nageria tunda shi jirgin yawone.

Saida ya dawo muke jin cewa ga abinda ya faru a can din da mama ai taji jiki sosai badon zuwanshi ba
zata samu aiki ba sosai amma bai dawo ba saida ta tabbatar da tayi ibadan daya dace tayi.
Yaji dadin yadda ya samemu da yaran don gaskiya ba yabo ba yaran sunyi kyau sosai duk da ba komai
nake masu ba amma tarbiya ba guda ba kowa na fadi.

Dan matsalan da aka samu shine fadan da akayi da Saratu yaya Habu kuma yaci mata mutuncu tun
ranan akan naman laiyane datace wai naman da aka bata bai mata ba tazo har gida taci min mutunci ina
fada mata ni banda labarin komai akai su yaya suka raba aka aiko min tace attabau laifinane tunda yaya
ya bar muna shanu da raguna shine don an raunata za a kawo mata nama kadan.

Karshe dai na biye mata mukayi cacan baki da ita Aminu ya kira yaya Habu yazo gidan ya sameta yaci
mata mutunci sosai tabi hanya tana kuka.

Da yaya ya dawo yaji abinda ya faru yaje nemanta ashe tana jin ya dawo ta gudu ta boye bata yarda
sun hadu ba dashi.

Labarin abinda ya faru da mama suna dawowa yabi gari nasan kuwa yan gidane ke fada akaji aka sauya
zancen kawu yazo taron ta don anyi belinshi shi yake tambaya ashe haka tasha matsala a can tace eeh
nasan ba komai bane Allah yati min haka in gane gaskiya.

Yaron nan Jafaru Allah ya kara mashi albarka dashi da zurianshi jafar yayi min komai duk da Jafaru
danane dole in nemi gafaranshi ko alhakinsa da ake sa inci yana hanani ganin rahama a rayuwana.

Baidai ji dadinta ba ranan har ya tafi zance zuwa makkan nan ya kawowa mama sauyi sosai a rayuwanta
dkn naga zuwata biyu gidan mu ko tsaraba ita da kanta ta kawo muna har gida ta kuma wuni a nan ita da
anty barakha sai dare suka koma gida.

Asmau ta dawo makka ta samu nasa yara makaranta inda na koya masu abubuwa da dama dole tasan
yaran sun samu natsuwa a yanzu abinda banji dadi ba shine da taso ta nuna min wai tafi a yanzu.

Ko don tana ganin taje makka ni bai kaini bane oho sai taso idan an hadu tayi min irin sakin maganan
nan na gugar zana na daiyi gaba na baya sai hange a raina nace taji dashi nasan abin da nakeyi ni.

Mama bata ragawa sararu ba kan abinda tayi min gashi taji ga Aminu mijinta tazo kwanashi ukku a
gidan lokacin da basu nan hakan ya batawa mama rai tace sai ta koma dakinta.

Ta kira kawo tace ta gaji yaba yara kudinsu ita ta gaji da abin kunyar dake faruwa hakana yayi mamaki
sosai da mama ta iya budan baki ta tambayeshi kudin .

Gaba daya yasan komai ya lalace mashi a yanzu gareshi wai ashe dama akwai kaddara da mutymin nan
ya boye yana jiran abu ya lafa ya fito dasu yaci bulus duk da dai ba duka aka samu kudin ba sun dai samu
abinda suka samu a wurunshi yazid yace ya hada da gidan iya ta mara mashi baya ya karbe gidan.

Ashe ya biya muna makka ni da salima nafisa lawisa kanwarsu yar wajen ummah sai matar yazid da
maria sai kannisa maza su ukku da zamu dasu dashi kanshi.

Kiri kiri yaki biyawa saratu makka kamar zatayi hauka yace bai biya tunda bai isa da ita ba ga auren
yayan yaya barakha da za ayi kafin tafiyan mu makka din
Ni ba abinda yai min dadi sai yan uwana maza da karatun su yanzu yaci gaba a nan da dawowansu a
kusa dani yayi muna dadi sosai yaso ya hada da ummah muje mijinta yace shi zai biya mata ta
bangareshi tunda yana dashi.

Anyu buki da sati ukku muka fara shirin tafiya mama taso Amir ya zauna hannuta amma yaya yaya yace
mama zata zo ta zauna dasu a gida da yar wajen yaya Ai babba.

Haka Asmau tace akawoshi gidansu yace a,a shine hakam ya dan hadasu hatsaniya tace yaki ya kawo
mata dana amma ita ya kwashi nata takai min na zauna dasu.

Yace yakai daya kai din bashi ba har ita taji dadin ganin yaran yadda suka dawo suka samesu ai don
haka ba zai kawo Amir ba ta kashemashi shida yunwa nata ma ya kwashesu yakai ma mama dubu yace
har ya dawo.

Dole ta kyale muka tafi muka sauke farali munyi aiki sosai muna can labari yazo muna dan wajen
Asmau ya fada tankin ruwa ya mutu.

Hankalinmu ya tashi sosai da jin hakan shiya fara tambaya ai gidan ba tankin ruwa wai ashe bayan
rafiyan mu uwar tazo ta kwashesu taje dasu gidanta wai zasuyi sallah a can shine wanan abun ya faru
dashi.

Haka muka dawo cikin bacin rai saidai nikuma muna dawowa ciki ya baiya a gareni ciki na biyu ke nan
haka nayi ta fama lauyi ga tajiigindin duniya wanda ba a rasawa a kullum dake faruwa na haihu lafiya na
kara samun namiji again nan kishin Asmau ya tashi saida yaya yayi mata iyaka dani ta shiga hankalinta.

Na kusa haihuwa kuma ciwon yar wajen Saiba ya tashi itama ta rasu nan hankalina ya tashi sosai Allah
dai ya taimakeni na haihu a lokacin.

Na dan huta da haihuwa don tazaran shekara ukku ban haihu ba nasake samun wani cikin na haifi
wani dan yanzu haihuwana biyar da nake maki labarin nan shagunana biyu manyan store daya a nan
zaria daya a kaduna.

Sau daya muka hadu da saiba ba don farin sani ba ba zan shedata ba muna dakin yaya kubura wajen
buki suka shigo wai suna tallan kayan mata tunda tayi arba ta gan mu nuda Yanda da matar yazid da
yanzu muke aminai ta saka kafa ta fita falin bamu kara ganinta ba.

Sai dai ince Alhamdullahi don muna zaune lafiya da Asamau Allah kuma yana ta budawa mazajen mu
Saratu daice a gida itama auren yaki ta koma tafito har sau ukku a karshe dai auren ya mutu iya kuma ta
amsa kiran mahalincin mu muna da shekara biyu da dawowa makka lokacin.

Alhamdullahi da fatan an dauki wani darasi a cikin dan takaitattacen labarina na fahinci rayuwa bai
tafiya ga mutum daidai sai tare da dan uwansa da duk maison ya ga haske a rayuwa ya rike zumunci in
mace ko namiji don naga hakan a rayuwan gidan mazajen Alhamdullahi muna cikin rufin Asirin Allah
sosai a yanzu fiye da lissafinki mai karatu da fatan zaki yafeni inda nayi kuskure Allah ya bamu ikon
cikawa da imani amin ya Allahu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA.

THE END

13/6/2025

101 / 101