Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
wai ban isa ba
a hada waje daya duka Asmau ta fada.
Don me zakice haka ba ita bace babba ita tasan yadda za a adana kayan ke meye naki a ciki tunda tace
haka za ayi jafar ya fada.
Au Allah ko ashe an fara babba a gidan nan yanzu to maji magani ashe ta fada tana mashi wani irin kallo
na yatsune.
Kedai baki zama a waje ba ai fitina ba saiba ni bansan abinda yasa kike wanan rayuwa haka ba juyawa
tayi ta bashi baya tana juye abincin data gama dafawa a plate ya bita da kallo kafin ya koma fadin.
Wait naga kin juye abincin duka sufa ba zasuci bane tace ka tambayeta mana ai dazun ta dafa itama taci
da yaran ?
Asmau yaushe kuka fara girki daban dabab a gidan nan gashi nan a cooler na zuba mata kuma ta gani
ta dafa wani ai.
Abincin da yayi sanyi kuke son inci ta juyo tana fada yace ke ba bawan gidan ku nake ba da zaki dinga
min barnan abinci haka in saka maki ido.
Gidan mu kan ai kaima kasan yafi karfin ka balle daga magana ka jefo gidan mu a ciki haka kawai daga
zance ka nemi ka zageni tunda dama kana hasale dani ?
Na dai fada maki kada na sake gani ko jin an raba min girki a gidan nan idan ba haka ba rai zai baci
wallahi ya fada a hasale ya juya zuwa dakinsa.
Asmau da saida ta gama gyara kayan ta fito tabar kitchen din ba gyara ta nufi dakin nasa daga kofa ta
tsaya tana gaidashi da wuni ya amsa yana kwance ya dago yana fadin.
Wai Asmau sai yaushe zaki daina zama hakane don Allah kayane baki dashi kome da kika zabi ki dinga
zama a haka don Allah ?
Kiwa kanki fada Asmau kece babba a gidan nan wanan halin da kikeyi yasa kike ganin kowa na rainaki
don baki mayar da kanki abin kwarai ba Asmau don Allah ki gyara banson haka me kika nema kika rasa a
rayuwanki ?
Naji ta fada ta juya ta fita daga dakin tana jinini a zuciyarta cewa ai dama ban taba fari a wajen ka
tunda baka kaunata yanzu kome nayi banyi daidai bane.
Shiko tsuki yaja yana gyara kwanciyarsa haushine ya kumeshi Allah ya gani yana son Asmau amma
halinta sam baiyi masa ba kazanta da yawan da abu da muhinmanci magana da har bata iya daukarwa
kanta mataki shi yake damunsa da ita.
Yaso tun farko ya sameta irin yadda rayuwansa keson matarsa ta kasance bai samu hakan gareta ba
yayi gyara ta kasa gyarawa yakai karanta har gaban iyayyenta an tsawata mata amma bata sauya dole ya
gaji ya sa mata ido.
Yadda Saiba tazo mashi da karya ya dauka ta kwaraice ashe halinsu daya sak da kawar nata kishiya
kuma a yanzu dole yai hakkuri ya zubawa sarautan Allah ido akansu.
Gashi shikan idan ka ganshi tsab tsab dashi zakice inda yake sai kin wanke kafa ki shiga saboda
tsabtanshi saidai kuma bai samu mata irinshi ba.
Ji don Allah wai wajen miji tazo a hakan ga wani riga duk jurwaye ta kawo wani zani sama ta dora tayi
daura gaba da shi wanan kayan takaicin ina zai kaishi don Allah.
Jin alarm din wayansa dake sanar masa da lokacin sallah ya mike zuwa masallacin nan unguwarsu inda
suke bi sallah.
Ana idar da sallah ya shiga motarshi yabar gidaa tudun wada ya nufa ya gaidasu mama kana ya nufi
gidan anty Ai da yake son zuwa ya ganta.
Yana gidan Habu ya kirashi a waya yana fadin J kana ina gasu malam sun iso aina dauka kana cikin
gidane saida na aika akace kafita.
Habu kuyi yadda ya dace gani nan tudun wanda daga nan kuma zamu fita da Nurane kai habu ya daga
ya dubi su mama da sauran jama,an dake wajen.
Baiso ace J din baya wajen ba za ai wanan rabon amma zai dage yaga an fitarwa kowa hakkinshi yadda
ya dace .
Aka bude taro da addua tare da bayanin abinda ka,idan kado ya bada ikon abawa ko wani mai hakki
kafin habu ya dora da kara masu haske kan yadda dukiyan nasu yake.
Masha Allah wanan bawan Allah yayi kokari matuka abin a jinjina masane sosai duba ga irin rikon
amanan da yayi da kurciyanshi.
Abune mai wuya a samu kudi har riba a wanan shekarun don haka su godewa Allah su kuma godewa
wanda yayi wanan jajircewan a garesu.
Habu yace ba wani bane illa yayan mu jafar shine aka dankawa kudin tun lokacin akan ya juya har ya
fara daga baya yayi shawaran gara ya bada wa yan nan kudin ga wani ya juya ya fara sana,an kanshi
amma yana bibiya ko wani lokaci malamin yace Na,am .
Shine dalilin da yanzu da yan uwan mu suka bukaci kudinsu aka fito dashi aka lissafa mun samu kudi ya
ninka ninkin ba ninkin muke so a warewa kowa nasa kaso a damkawa masu shi abinsu.
Daidai lokacin kawu ya shigo falon don bai samu karasowa da wuri ba saboda kauye daya tafi duk akan
rabon kudin don yana son a daure bakinsu wai.
Duka kudin su dawo hannunsa ba tare da an samu wanda ya mussa hakan ba a cikinsu don ya kula
yaron sun soma sanin ciwon kansu a yanzu.
Yazo ya zauna sai cicika yakeyi yana batsewa don me za a fara bashi daga baya daya fahinci ba a soma
kasafin kudin ba ashe shine ya dan washe fuskansa.
Malami na farko ya gyara zama yana fadi to ai abune mai sauki yanzu tunda da baya an raba ansan
yawan abinda kowa a nan ya mallaka daga mazan har matan sai a soma cirewa kowa nasa kason ko
kuma alabashin kasafa kudin a yadda wanan can kadon na farko yake har riban da kowa ya samu zuwa
yanzu.
Da yake aikinsune sun saba nan da nan aka fara lissafin yadda ya dace ana ajewa kows nasa gefe daya
da sunan da mama aka fara sai su maza kafin a debewa diya matan akasafa masu yadda ya dace.
Ba wanda aka cuta a cikinsu rabo na tsakanin da Allah malaman suka tsaya sukai masu inda Habu ya
mika hannu ya dauki na farko yana fadin wanan na J ne.
Jafaru kuma a yanzu ai baida abinda zaiyi da wanan kudin kan a,a hjy ba yana cikin magada ba ?
Suka amsa da yana ciki malam yace don haka a kwashe mashi tunda yana da hakki anya Jafaru bai yafe
kudin nan ba kuwa ?
Anty baraka ke fadin malamin ya sake fadin babu zancen yafiya a nan tunda ya gada shima dole a bashi
hakkinsa ai.
Sai kuma wanan nawa saina yazid daya mika hannu zai kwasa mama tace kada ka dauki na yazid habu
ka barshi za aci gaba da juya mashi kafin Allah ya dawo dashi lafiya ya karba mama ke fadin hakan.
Kallonta Habu yayi a cikin mamaki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya kasa furta komai daga
can Salima take fadin amma yaya Yazid yace abawa J nasa kason ya rike mashi a hannusa idan an raba ai.
Nina haifi yazid ba wani ya haifa min shi ba don haka nina san yadda zanyi dasu a wajena ta fada fuska
daure habu ya ciro kudi daga Aljihunshi yana fadin wanan na maine J yace a baku ai maku godiya.
Ya hada kudinshi zai fita yaji salima tace yaya Habu kada ka fita kudina nace a ba ya j ya aje a hannunsa
fa ?
Ba zan bashi ba akwai wanda zan ba a cigaba da juya maku kudin nan mama ta fada a tsawace ga
salima din.
Dakata hjy malamin da zai fita falon a karshe ya fada yace wanan hakine fa yarinyar nan yanzu ba
yarinya karama bace don ko wace ta mallaki hankalin kanta a yanzu.
Don haka yau ko cewa tayi ita zata rike abinta a hannunta za a iya danka mata dukiyanta don ita ta gaji
abinta daga mahaifinta.
Kawu ya hade wasu yawu yana gyara haban babban rigansa sai aikawa malamin harara yakeyi daga
inda yake zaune ganin malam ya tsaya jawo dogon aya yasashi magana.
Malam ina ganin kunyi abinda ya dace yanzu ai kowa yasan hakkinsa kamar yadda suka bukata don
haka abarsu suyi shawara da uwarsu kuma.
Ni wallahi ba wani shawaran da zanyi ya habu ka dauki kudina kaba yaya J na fada mai abinda nake
sonyi dasu nan gaba.
Salima zan safa maki fa ina fadin magana kina musayawa mama nace abu zan saya dasu idan sun kara
yawa kuma har na nuna mashi abin ya sani .
Habu ya dawo ya tsaya gaban kudin yace baraka kwashi naki ke saratu ki dauka a ban na salima din
tunda abu take son saya da kudin.
Idan abin bana amfani bane na tabbatar da J ba zai yarda ba baraka ta kwasa sai saratu ya duka ya
dauki kudin Salima din ya fita dasu zuwa part dinshi.
Ranan Salima tasha fada sosai wajen mama Allah ya gyara batayi maya baki ba duk abin nan anyishi
iya bata wajen don kamar an kadata fita unguwa tabi J ya sauketa gidan wani dan uwanta dubiya.
Yanzu yaya kaga yadda abu ya kaya kuma yaran nan kamar abin hadin baki kudin nan daga nawa saina
Yazid koshi don bai nan,ne .
Nasan da haka za ayi shima karban abinsa zaiyi sai na saratu itama naga take taken ta tun kan a raba
take fadin sana,a zata fara tunda karatun yakiya gareta ko Allah zaisa mata hannu.
Ni yanzu ai lissafin ya tsaya min saidai a kawo mu gwada ko zasu fara daukuwa a garemu hakana bai
bar gidan ba ranan saida ya karbe kudin mama da yazid din.
Dana saratu da mama ta raba biyu ta boye rabi ta mikawa kawu sauran ya daure leda ya tafi yana mata
sallama kada iya ta dawo ta sameshi .
Zance ya lalace yasan ko wanan rabonsane shiyasa yayi dabaran daya izata zuwa gidan dan uwan nata a
ranan ayi a kare bata nan.
Habu ne bayan fitansu ya dawo raka malaman yake waya da j yana fadin gaskiya j akwai abinda yake
damun mama gaskiya.
A nan dai ya kwashe komai daya faru wajen ya fada mai murmushi j din yayi yana fadin ba komai
matsalanta a yanzu kawune.
Iya ta fada min dazun a hanya cewa kawu shiya matsa a fito da kudin nan a raba don kawai wata
bukatanshi.
Dama ina hasashen hakan daga kawu mutumin nan ya kamata mu nuna mashi musan nufisa akan mu
yanzu.
No kada ka soma ba yanzu ba Habu idan kayi hakan ranka zai bacine da mama don haka ka kyaleshi har
gaba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/17, 11:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zaune yake falin yaya Ai itama a nan cikin tudun wada gidanta yake saidai akwai dan nisa da family
house dinsu din daga gidan daya sauke iya daketa bashi hakkuri akan rayuwa da kuma iyayye da yan uwa
ya nufo gidan yaya Ai din.
Da murnanta ta rasa ina zata sakashi a lokacin don jin dadin yau dan uwanta yazo wajenta abinda
basuyi mata ke nan kamar yan uwana na gudunta take gani saboda talaucin da Allah ya dora masune.
Don ita yaya Ai din mijinta dadtijone sosai kila kuma gami da talaucine yasashi tsofa a zamanin
kurciyarsa ya danyi tashen kudi saidai irin na rufin asiri din nan za ace.
A haka kuma iftila,i ya sauka,mashi a hanyansa na zuwa fatauci lokacin ya hadu da barayi suka karbe
duk abin hannunsa tun lokacin yake fama da rayuwa shi da iyalinsa.
Kasane bana hadin kai ba aure abu zai samu dan uwa maimakon a samu yan uwansa yan kasuwa su
tallafawa mutum a dagashi sai dai a sakawa mutum ido har sai yakai kasa waras kamar jira ake hakan ya
sameshi dama.
Na tabbatar da mata Allah ya umurta da kasuwanci kamar maza za a ga hadin kai da taimakon juna a
tsakanin su🙋.
Sai ya kasance yan uwa ma sam basu damu da ita ba da iyalinta don bata da komai a rayuwanta saidai
duk sallah nasan idan an fita ana zuwa gidanta boyan Allah ga son jama,a saita rasa ina taka saka mutum
idan yazo wajenta.
Yanzuma da J din yazo sai godiya take masa daga ita har mijinta da kishiyarta kamar wanda sukaga
yazo masu da wani abu a lokacin duk da hannu sake suka ganshi amma sunji dadin hakan sosai a lokacin.
Ta kakabe wajen da zai zauna tukun a dakin nata da babu komai a cikinsa sai dan gadon katako mai
dungu da wani tsohon zani gado shimfide duk ya kode.
Gefe guda wani tsohon kujerane da tsufanshi har yasa katakonshi ya fito fili ya zazzage an tula raga
don ya danyi taushi.
Nan aka gyara mashi ya zauna suka fara gaisawa da yar uwar nasa dake mashi sannu da zuwa a lokacin
take tambayan dazun nake jin kana gari a wajen malam yake fada mun yaji ance kaine kabada gyaran
massalaci kofan gidan mu .
Yace shekaran jiya na shigo da dare jiya kuma abubuwa sun min yawa yasa ban samu zuwa nagai dake
da gajiyan buki ba.
Haba dai aiyiwa kaine ya kara mata da godiya take fadin Jafaru aini ka karrama a zancen nan da har ka
tuna dani baka kyamace niba ka turo ayi komai a gidana akwai abinda yafi haka dadi a wajena.
Wanan ai yafi dan uwa yazo ya baka kudi indai ana zumunci haka da zumunci bai taba lalacewa ai a
duniya amma ina su isa gamu gari guda a waje daya sai inyi shekaru ban saka kowansu a idona ba garin
nan kuma ana raye inaga yaya in sun taso kuma kaga ba zumunci ke nan ai a tsakanin su idan sun taso.
Hakkuri ya bata yana fadan in sha Allahu za a gyara yaranta da suka dawo daga islamiya suka shigo su
uku mata maza biyarne ta haifa a gidan.
Wanan yasa tsufan wahala ya taso mata saika rantse batayi primary ba balle secondary idan ka ganta
lokacinsu sune yan mata masu tashe a gari duniya ke nan yanzu saboda talauci da yara ta koma haka
abin tausayi.
Ya Allah ka duba muna wanan zamani cikon tausayinka ya Allah ka sakawa duk wata uwa da alheri kasa
albarka ga zuria wa yanda suka kauce kuma ga tsufa ga zuria Allah ka shirya munasu badon halinsu ba ya
Allah mun tuba kaiwa kasan mu da musulman kasan mu agajin wahalan rayuwan da ake ciki Amin ya
Allahu.
Yaya Ai me malam keyi yanzune na ganshi a gida a wanan lokacin ko har ya taso daga kasuwan ne ko
yake tambayanta kan mijinta din ?
Haba ta kama tana fadin malam kace Jafaru ai malam yaushe rabonshi da kasuwa yau kusan kimanin
shekaru goma sha,ai tun wanan abin daya faru dashi.
Da yana dan zagaya abokan hurdanshi na kasuwa don samun abinda mukaci a gidan har yakai sun gaji
dashi sun fara kyamatarshi yazo ya daina fita yanzu dai sai abinda Allah ya kawo muna idan rabon mu ya
ratsa.
Innalillahi yake nanatawa a zuciyarshi har yakai fada a fili ya gyara zama yace yanzu kina nufin haka
kuke zaune bai sana,an komai ?
Haka muke Jafaru aiko nayi mamaki da baka san hakan ba duk zuwan nan da kukeyi ai kuna ganinsa
gidan nan ko ?
Na dauka dai don sallah ne kinsan nafi zuwa nan da sallah wani lokacin a,a wallahi halin da muke ciki
kenan ai shekara da shekaru kai dai Jafaru.
Allah ya sauwaka ya fada yarta datazo a karshe tana gaudashi zata kai shekara goma sha uku da
haihuwa yake fadin wana takice tace tawa ce ita autata take biwa takwaran iya ke nan ai Habiba.
A,a,a ashe kin samu mai sunan nan kema tace ina da ita ai gata nan yace ina ga ni zan dauketa kuwa ko
ita ko wanan autan naki ko inbawa Amaryata rikon ta su zauna tare idan zaku ban don banson zamanta
ita kadai don ni ba mai zama a garin bane sosai wanan yasa yanzun nan naji hakan ya fado min a rai.
Amma abinda ya kawoni nan shine ina son dake da anty Rakiya kuzo wanan gidana da amaryana take
ku dauki kayan tausan gaban wa yan nan kukai masu duk da nasan na daiyine kawai amma sai kuma yai
shiru bai karasa fadin abinda yayi niyar fadi ba din.
Sun dan jima ganin magariba daya gabato ya mike suka fito bayan ya aje mata kudi yan dari biyar biyar
ya samu kishiyar ta tana bakin murhu ya ciro dubu ashirin ya bata ta bata ai kuwa suka shiga godiya.
A waje ya samu malam sule na masa gadin motarshi saboda yaran unguwar sun dan jima dashi kafin ya
fada mai makasudin zuwansa din gidan.
Yaji dadin hakan don daga mijin har matan mutanene masu son zumunci saidai babu karfin yin hakan a
yanzu dole yasa suka lafa.
Shima dubu hamsin ya bashi ya barsu cike da tausayinsu a cikin ransa masalacin kofan gidansu da
mahaifinsu ya gina da yake raye nan yayi sallah magariba tare da jama,an unguwar.
Ana idar da sallah ya sulale ya fita bai zo gidana ba saida ya koma gidan daya sauke iya ya dauko ta
zuwa gida haka kuma yana son yai ma iyalinsa saida safe duk da ba dadin rai ya samu ga hakan ba .
Bai shiga part din iyan ba kodaya fito ya ja motarshi ya bar gidan don Nusaiba bata ko amsa sallamashi
ba daya shigo.
Sauri yakeyi yaje yaga halin da yar mutane take ciki donshi bai tsatsaya ba ya juya zuwa gidan amma
duk damuwa akan halin daya samu yaya Ai su ya daga mashi hankali.
Wa yan nan sune abin taimako a duniya shine amfanin samu a cikin dangi ina amfanin kana dashi dan
uwanka na cikin irin wanan