Chapter 31 Reading MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

MAR FIN JALLO BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   31 / 101

90K to 93K   out of 302.2K words

ya damu da lamarin mu.

Kada kika ban dauki mataki akan abinda matana suke maku ba ki dauka sunfi karfinane a hakan ?

A,a akwai matakin da nake son dauka wanda duk sai sun raina kansu a karshe kan wanan rayuwan
banza na kazafin da suke kokarin maki.

Dago kai nayi na kalleshi don jin abinda ya fada din ke nan shiya tsame kansa a ciki nice ma suke
batawa ke nan hakan yasa hawaye ya soma zubo min don zuciya daya kawo iya wuya .

Koma me suka fada maki nasan Allah zai wankeki ga sherin su Rahama don Allah yayi hikimarsa daya
bar shari,a a hannunsa akan bayinsa.

Ni nasan kin taimakeni taimakon da ko mama data duka ta haifeni ba taimin irinsa ba tunda ta kasa
tsamoni cikin halaka saike Allah yaba wanan dama da ikon data sanadin a yau gani a saman kafata tsaye.

Banda Allah waya isa hakan ga bawan shi Rahama toni na sani kuma ba butulu nake ba dan hakin da ka
raina shike tsone ma ido inji manya.

Suna maki kallon dan haki a wajensu ni kuma ina maki kallo na mutum sak a idanuna don wanan sirin
banda habu da Allah ya nunawa dagani saike sai nafisane muka sanshi.

Shiyasa nake matukar girmamaku a cikin lamarina girman da a gaban kowa kuke ba zan iya boye hakan
a raina ba sai na fitar fili kowa ya sani.

Yau kin kwaso kin dawo Abuja wajen anty ki Rahama kin zauna yaya kike son na kasance a can quite
sure basu fadi karya ba a kaina nina sani Rahama.

Akwai wani fleeling da ban iya boyewa a kanki matukar zan sanya idona a kanki ko a gaban wa kike
kuwa zan kasa controlling din kaina a lokacin.

Ina kike son kai alhakin hakan a kanki Rahama a yau nazo maki da wata tsiga ta dabance banzo nan da
sunan dan uwa ko yaya a gareki ba na zo makine a matsayin jafar din da kowa ya sani.

Don haka kiyi hakkuri kada kice zakiyi fushi da gidan mu Rahama ki dawo nan Abuja da zama akan
laifin da bamu muka aikata maki ba .

Su basu isa su fitar dake gidan muba sunzone kamar yadda kema a sanadiyan aure Allah yayi zaki zauna
damu din haka suma suke zaune damu.

Kaina yana kasa na dukar lokacin mukaji takon anty Salma ta nufo falon tana waya kafin ta karaso tana
sallama.
Shi ya amsa mata don ni kona amsa ma ba zataji ba a sannu da hanya ta fada tana zama kallo daya yayi
mata ya kawar da kansa gefe daya.

Dan zaria ina fatan ba kazo dauke min kanwata bace ya danyi murmushi yana fadin banzo daukanta i
hope muma ba dauke muna ita kikayi daga can ba ?

Eh to kusan haka gaskiya don ka canka da kyau saboda matanka sun saka min kanwa gaba da haushi ba
zan lamuci hakan ba gaskiya har yaushe nawa Ramaah take balle wanan zancen banza ya taso kanta.

Bakai naso kazo ba don banda case dakai da mijin Maria da aka bashi amana don aure amanane ya
tsaya ana yi masu hakan yana kallo kai kan ai matankane ba zasu taba laifi a wajenka ba don da an dauki
mataki.

Hjy ko yanzu daukan matakin da nake son yi shine yasa kika ganni a nan zaune .

Ok to muna jin ka nima abinda ya fito dani ke nan yanzu ka fada min manufar biyotan da kayi don ina
da bukatan ji idan hakan zai gamsar dani.

Amma taya don Allah bawan Allah mata zasu zauna suna ciwa yarinya fuska haka amma a rasa wanda
zai daukan mata mataki a gidan har kai da abin ya sha ?

Allah da nayi niyar yin karansu kan zancen nan amma sai nayi duba ga maria dake zaune daku naga
rashin dacewan hakan da zanyi din.

Shine yasa na daukota baki a laikum zuwa nan komai iskancin da suke ji ba zasu taba biyota ba nan suyi
mata ai ?

Ya langabar da kansa gefe daya yana saurenta sai da yaji tayi shiru ya soma fadin da kinyi hakan kin
dauke ta hjy baki kyauta min ba donni abin zai shafa a karshe.

A daiyi hakkuri ina mai bada hakkuri a both side amma a gabanta aina fada masu matakin da zan dauka
ga hakan da sukai min ba zaiwa ko wacen su dadi ba a rai .

Wanan yasa naki daukan komai da zafi hjy don in gasa masu kwakwansu a hannu kafin na kai ga
daukan matakin ni zuwata nan ai yayi min dadi tunda acan boyewa takeyi bani ganin ta.

Ba anty salma ba ni kaina saida na dago ina kallonshi da mamakin abinda yake fada ko banda hausa zan
fahinci wanan magana amma kuma bai fadi dalili ba.

Shike nan ai tunda har kayi tunane kamar nawa sai a je a hakan Ramaah dai zata zauna a waje na sai
hutu ya kare insan abinyi a kai idan haya zan kama mata anan zaria din har ta karasa karatun ta tadawo
nan ko kuma idan a hostel zata zaune dai zanyi shawara a san abin yi ko ita maria bata san kudirina ba a
yanzu.

Shike nan hjy ba sai ta zauna a hostel bama tunda ga gida nan dole dai matakin da zan dauka yasa
kowansu natsuwa a yanzu.
A yanzu a son samuna don Allah ba wani boye boye ko kwanaye kwanaye don so nake ta ban baki daga
nan in wuce can wajen hardo mu gana dashi.

Zubur na mike tsaye don jin maganan da nayi kamar saukan aradu a kaina na fara tafiya a baya baya
ina kada kai na juya zuwa ciki da sauri na barsu a nan din.



ZARIA

Ringing din wayantane ya tayar da ita daga barcin data samu tun bayan fitan Saare a dakin da suka
gama dariyan plan dinsu na jiya yadda yayi daidai da abinda suka hada din.

Dauka tayi a cikin magagin barci tana amsawa wayan mamansu shiyasa tace hlo mama ke ba mama
bace nice Rashida naga kiran kine ai dazun ban kusa da wayan.

Jin hakan yasa ta watsake daga barcin tana fadin wallahi anty Rashida na kira in fada maki komai ya tafi
daidai yanzu haka tabar gidan nan tun jiya ta tafi abuja wai hutu.

Nasan ko ba hutu bane tagudune don kunya na dasawa shegu bakin ciki daga ita har yarta din yan iska .

Ke kice min kinyi maganin shishigi ke nan gobe ta kara rawan kai ga mijin wata mugani ita gata sarki
iyawa ko bari a koreku a yabeta ?

Ta dauka zataci bulus ne ta tafi a banza rabuda yar iskan yarinya tana wani daukan kai kamar diyan
wani da wata ?

Yanzu ina mijin naku yake shi kuma wani dan iska guda haka kawai uwarka ta kore matanka kayi zaune
a kwaso maka wasu yan iska suna maka karairaya kana binsu da kallo ?

Haba dai dayan fa kanwarsace ya Raahida mahaifisu daya sai ita dayan mara kunyar su a dole ga jikan
munafukai don ta gyarawa yarta hanya a yabeta mu kuma a kushe muna.

Ni yanzu ko Asmau takai min ko ina wallahi yaya ina bakin ciki in bude ido inganta a cikin gidan nan a
matsayin matar sweety.

Ke na fada maki bar wanan shasha,shan makarine a wajen ki bar banza a haka ki fita zancen ta don
yanzu kina kawar da ita gidan nan wallahi wata zai jajibo maki tunda ya saba zama da mata biyu a yanzu.

Shima anyi rigimame dan wahala kamarshi zaije rigimar aje mata har biyu don Allah nifa idan ya jero
daku nakan ga kamar ma kun girme mashi ga shekaru ?

Haba dai yaya Rashida wallahi ya girmemu kawai dai rigimace irin ta maza dashi kawai ni dama nafi son
hakan mu tsufa tare da abin mu.

Wai yana inane yana nan yana fushin har yanzu ko ?
Yanayi wai yayi tafiya dazun shine bai sanar da kowan mu ba sai a bakin sakaran nan saratu nake ji wai
ya zo nan kadu daga can kila zai wuce katsina.

What baki tunanen hakan plan ne dama ko tare suke da yarinyar nan tunda jiya ta wuce itama wallahi
ba abinda namiji ba zai iya yiba Saiba.

Kai haba yaya Rashida Allah ba zaiyi hakan ba kawai dai tafiyan yaje dama tun ranan ya fada zaiyi tafiya
a yau din kafin zancen nan.

To shike nan nidai kibi sannu kinsan dai kece mai dan maski maski a cikin mu kada kije ki jawo wani
sabon wahala kuma abubuwa suzo su tsayawa mutane.

Haba dai aiba zan yarda akai hakan ba kawai nima ido na zuba mashi ya kare fushinsa nasan ina nan
zaizo aiya sameni dama mun saba .

Ni wallahi tausayi ya ban sosai da ake maganan amma haka na badawa idona toka naci masa mutunci
ga kowa nasa a zaune ya kasa daukan wani mataki tana fada ta kwashe da dariya.

Ni dai shirun nasa ne nakewa tsoro wallahi kinsan halin Jafar fa Saiba dan duniyane na karshe wallahi
saita tare yar uwar da fadin barshi ba abinda zaiyi wallahi haka yafi shegu su daina dagawa mutane kai ai
yanzu gidan.

In kinga yadda Habu din nan yake ririta wanan yarinyar da yar uwata zakice wani romiyone da juliya
suke soyayya duk da sun haihu ba abinda suka rage ga komai wallahi.

Ai shiyasa naji tsoro kada shima jafar yaje ya jajibo maku yar bafulatana boni ya cimu ina mu ina kishi
da mugun iri ina ganin yadda yaya larai take fama da nata bafulatanan.

Barshi ai kafin ya gama fushinsa ya dawo hanya nagama duk wani shirina da zanyi a kansa wanan karon
zaisan ko wa nake kudina ba zasu tafi a banza ba.

Sun gama hiransu yunwa ya fito da ita falon ta duba ko Asmau dake da girki ta karasa saidai ba motsin
Asmau din kitchen ta leka nan ma wayau babu wani alaman girki a kitchen din.

Ta fito ta nufi dakin Asmau din dake da tsohon ciki kwance ta sameta tana barci cikin daga murya take
magana da nifa ban gane ba Asmau ba za ayi muna abinci bane yau ?

Hakan yasa ta bude idanu tana kallon abokiyar zaman nata tace banji dadine akwai miyar jiya na nan a
fridge idan na tashi zan dafa muna shimkafa ko taliya.

Kinsan kuwa karfe nawa yanzun Asmau yanzu fa karfe biyu ake nema nifa wanan halin idan shi za ayi
wallahi saidai kowa ta dinga girka abinda zataci yafi min sauki gaskiya da wanan halin .

Kina iya zuwa aiki dafa ko yanzu ina jin jikina sai ibtashi in shiga kitchen dafa maki abinci to naki ki
dinga dafa naki abinci mana sai me ?

Haka kikace ce tace eeh na fada haka kawai ina barcina zakizo ki tayar dani daga barci ?
Zakiga abunda zanyi din ta juya ta fita tsuki Asmau taja tana fadin haka kawai zakiyi kokarin yi min
turaja.

Cikin bacin ran da take ta kira wayan mijin nasu duk da tasan yana da wuya ya daga yadda yake fushin
nan.

Tayi sa,a kiran nata ya shiga yana tsaye bakin mota Isah na kwashe kayan dayazo muna dashi kiranta ya
shigo wayanshi.

Duba wayan yayi yaja tsuki har wayan ya katse bai dauka ba bai kuma dagawa din ko kira nawa zatayi
ya fada a zuyarshi da tasan abinda yake ji game da ita da bata kirashi wanan lokacin ba.

Yaja motansa ya fita a cikin sanyi sam bai tsanmaci hakan ba daga yarinyar nan ya dauka ba zai samu
wani matsala sosai wajen shawo kanta ta amince dashi ba sai gashi gaba daya ta nuna bata yarda da
tsarin nasa.

Wanda yasan badon komai ta nuna hakan ba sai saboda wa yan nan baka more din matanshi daya tsani
duk wani halinsu na banza yanzu.

Amma zaiyi kokarin duk yadda zaiyi wajen ganin bata subuce masa ba a yadda ya hango hakan ayanzu
gareta.

Meye laifin da wanan hjyr zatace haka bai yuyuwa tunda ga yar uwarta a gidan itama tana fama da
kanta balle ita kuma tashiga ciki.

Ke nan saboda matanshi ke nan suke ganin hakan ba mai yuyu bane kome yarasa mesa mutane ke
daukan al,ada fiye da addininsu.

Hotel din daya saba sauka idan ya shigo Abuja ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa saidai duk yadda
yaso ya huta hakan ya gagareshi a ranan.

Don ransa da yake bace da wani zaiji a zuciyarsa bacin ran saiba da yake ciki ko wanan abinda yake
ganin yana nema ya zamo mashi matsala ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/2, 9:41 PM] Zainab Idris Makawa Writer: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,



3️⃣3️⃣



GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Gado na fada ina sakin kuka ba zance ban fahinci inda ya J ya dosa da zanceshi ba maganan gaskiya shine
ya J yana nufin yana sona idan bani bace ban fahinci zancensa ba ?

Ina ni ina ya J me tarin mata har biyu inje ata uku yar uwata tana ta farko a wajen mijinta ai gara na
yarda da Faruq dana buge ga auren ya jafar da wa yan nan mata nasa kome yake kuwa ina .

Ai in an gani lahira maza suka kaini badani ba da wa yan nan dambun dankaron matan nasa ai kazanta
zai kasheshini don ko ruwan goran part dinsu ba zan iya kaiwa a bakina ba yadda nake da tsandan tsiya
din nan bakin kyan kyami ke gareni ta ya zan jefa kaina ga halaka ina gani.

Me zan gane da auren ya J a rayuwata banda fiti ki duba yadda kullum ta Allah ta waye sai sunyi fitina a
tsakaninsu anshiga rabon su can dai gasu gada inji bahaushe.

Wai anty har da tsayawa tana saurareb shirmesa shirme mana ta yaya don tabin hankali zai tunkareni
da zancen soyayya tunda aure ai soyayyan ke kawoshi toni ina soyayyan da ke tsakanina dashi ?

Banki ba dai mutunci da tausayi saboda halinshi da kowa ke yabo na kirki ga kyautatawa na tare dashi
yasan darajan dan adam fiye da tsammanin mutum.
Baya da wanan ba wani feeling da nake dashi akansa banda zumunci sun rikeni kanwa na rikesu
yayyuna aje a hakan.

Na idar da sallah la,asar ina zaune a wajen nayi tagumi anty salma ta shigo dakin nawa tunkan ta
karaso take fadin ke kuma meye haka ?

Kin wani zauna kin buga uban wanan tagumin duk a kan zuwan wanan yayan naki kike haka kome ?

Babu komai anty na fada cikin cool voice takai zaune tana girgiza kai gami da fadin ban yarda ba
Ramaah ?

Ta yaya zakice min babu komai bayan nasan abinda kikewa tagumi meye na tagumi a cikin zancen nan.

Bayan duk wani mahuluki mamallakin hankali ya dubi zancen bawan Allah nan hanyan daya dauko
itace hanya mafita a kan ku baki daya.

Bafa ko wani namijine zai iya daukan wanan matakin da yake shirin dauka a yanzu ba zargi da tozarci
babu kyau Rahama sam bashi da dadi wallahi.

Let him prove himself to them yakai namiji namijin gwadawa gobe su kara irin wanan katobaran basu
bama duk wata macen arziki zata kama kanta da zargin mijinta ai idan yayi hakan.

Bayan haka duk wanda ya zauna dake kike fada masa irn halaiyan bawan Allah nan zaiso kasancewa
dashi Rahama .

Tun kafin na ganshi irin labarinsa da kike min yasa na fahinci kin kamu da kaunansa ba tare da kinsan
hakan ba saidai kina gani kamar halinsa kawai burgeki yakeyi hakan ba kauna bace kike masa.

Tun farko Rahama ke kika cusa kanki gareshi ba tare da kinsan maza basu san hakan ba sai su dauka
kaunace ta soyayya kake nuna masu idan kana masu hakan .

Wanda ke kuma a wajenki kin dauki hakan da ramuwar alherince zuwa gareshi don kyautatawan da
yake maki fiye da mijin yar uwarki.

Meye a ciki don kin aurensa banda alheri ke a kaddarama ba aure zakuyi ba aje a hakan wallahi kin
rama abinda sukai maki don dole zukatansu ya kusa bugawa idan labarin kun sarku dashi ya riskesu.

Kinga ko a nan kin dauki fansan bakin cikin da kika cusa masu idan yaso daga baya in za a shirya din a
shirya idan ba shirin ma a zauna a hakan kin dai rama sun kuma razana.

Balle d guy is handsome and wealth kinga akwai hutu a tare dashi so banga abin tsayawa kina wani
saka kanki a cikin kunci irin haka ba ?

Ta koma matsowa tana dafani tace ko da baki sonshi a yanzu let play a game to his wife ki nuna kin
amince din da bukatanshi yan iska muga iya gudunsu.
Ba sunce sun iya yiwa mijinsu zargi ba don suna kishin yar uwarki zasu hada dake to zamuyi wasa da
hankalinsu fiye da yadda suke zaton sunyi muna a yanzu.

Kici kudinshi kawai suna kallo saidai yaji daga baya kin tsayar da mijin aure amma don ramawa sai mun
rama wallahi .

Daga goben nan zaki fara fita wani vocational school dake nan cikin gari zaki koyi gogewa da wayewa ki
iya tako da kowa a garin nan.

Wanan hjy Yabi yar kawar mama itace ta bude wajen don tallafawa mata halin rayuwan nan da ake ciki
saboda mace macen aure dayai yawa a yanzu so na kirata tace ba matsala in turoki kawai goben.

Kinga kafin hutunki ya kare kin dibi na diba a wajen ai so ki maida hankali don Allah ki koyi abinda ya
kaiki duk da nasan ke baki da shiririta irin haka.

Naji naji dadi sosai a raina don ko banza zan rage zaman kawai da nakeyi zan dan shiga mutane in rage
nauyim zuciyata .

Har anty Salma ta fice dakin juya zancenta nake a kasan zuciyana ta yaya zan iya tsayawa da yaya jafar
a matsayin soyayya mutanen da nakewa kallon yayyuna najini.

Nafita na

31 / 101